← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 211

Sashe 163

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2024-11-20....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

41

KINGDOM OF POWER

A ɓangaren uncle Abbas kuwa, wajen King ya nufa, bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ne uncle Abbas ya buƙaci da yana son su yi magana da yayan nasa.

Uncle Jahiz yana cikin parlourn shi ma a lokacin, yana kwance saman doguwar sofa, sanye yake da arabs jallabiyar shi ma, ya tasa waya a gaba suna hira da wani shararren abokinsa, shi ma shararren É—an kwallone wanda suke bugawa a team guda, sai hira suke yi cikin kaunar juna.

Saman sofa mai zaman mutun biyu King ya zauna, shi kuma uncle Abbas mai zaman mutun uku, Akka tana part ɗinta, bata jin daɗi, zazzaɓi take yi, sai da aka kira nurses daga hospital na cikin Kingdom ɗin suka zo suka hau dubata.

Uncle Jahiz ne ya kira number momma. Tana É—auka ya ce. "Hello kanwata a kawo mana cappuccino mana".

Harararsa King ya yi kafin ya ce. "Ka raina mun mata ko Jahiz?".

Ba tare da ya katse kiran ba ya amsa da. "A'a yaya ni fa da kanwata nake yi ba matarka ba".

"Ba cinya ba kafar baya". In ji uncle Abbas da shi ma yake wurga mashi harara.

Dik abin da suka faÉ—a momma tana jinsu, dan bai katse kiran ba.

"Yaya na zo mu yi magana ne fa". Uncle Abbas ya sake faÉ—a. Katse kiran uncle Jahiz ya yi domin ya samu damar saurarawa ya ji me É—an uwan nasa ya zo da shi.

"Okey ina jinka". King ya faÉ—a a nutse.

Gyara zamansa uncle Abbas ya yi tare da É—an jingina bayansa da jikin head na sofar, sannan ya fara magana a nutse cikin girmamawa, da alama suna girmama King sosai, ko da yake babban yaya ai ba wasa ba.

"Yaya dama batu ne a kan Jannat da Jawad".

Tattara hankalinsa King ya yi gabaÉ—aya a kan kanin nasa, dan ya ji kamar ya zo mashi da sabon magana.

Cigaba uncle Abbas ya yi da cewa. "Jawad ya gaya mun yana son Jannat, ko in ce maka suna son junansu, sannan ya nemi da a nema mashi aurenta". ÆŠan dakatawa ya yi da maganar ganin yadda face É—in yayan nasa ta É—an sauya, sai ya dakata ya ji me zai ce kafin ya É—aura.

Uncle Jahiz da ya ji zancen sai ya ɗan taɓe baki yana mamakin wai su me ya haɗasu da yi wa yara auren wuri ne? Nawa Jawad yake da zai ce zai yi aure? Baga yayyunsa su Ramish da suke manya ma ko batun aure basa yi ba, sai shi yaro? Su ma ai basu gama wani girman da za'a ce su yi aure...... Hmmm uncle Jahiz dai baya son batun auren wuri, su Ramish kuma ai ba yara bane, sun kai almost 30 years a yanzu fa, amma yake ce masu yara, ko da yake shi da yake da 35 to 40 years ma ga shi bai yi aure ba, gani yake yi har yanzu bai kai ace ya yi auren ba, rayuwa cikin turawa ya lalata shi, kun san su basa auren wuri sai aukin zinace zinace suka iya, to da irin wannan zinace zinacen ba gara auren wurin sau dubu miliyan ba? Amma shi ina, gara mashi a yi rayuwa kawai, tun yana kyamar al'adunsu da ɗabi'unsu har ya zo ya saba abin ya zame mashi jiki, ya koyi wasu al'adun nasu ma abinsa.

Jin King bai ce uppan bane yasa uncle Abbas cewa. "Yaya yanaga kamar face É—inka ta sauya?".

Nisawa ya yi kafin ya ce. "No ka gama maganar naka sai na yi tawa".

Jinjina kai ya yi tare da cigaba da cewa. "Cikin satin nan da zamu shiga nake son a ɗaura aure, idan Sarina da Fanan sun aminta da waɗan can prince's ɗin sai a haɗa auren gabaɗaya, babu abin da za'a jira ko a tsaya ɓata lokaci a kansa, gara kawai mu aurar da su a wuce wajen".
Dakatawa ya yi yana sauke numfashi a hankali hankali.

"Yaya wai meyasa kuke son dole dole sai kun aurar da yaran nan da wuri ne? Nawa Jannat take da kuke batun aurenta? Wai me suka tare maku ne? Ku bar yara su girma su san Æ´ancinsu da kuma menene rayuwa, sannan sai ku aurar da su, yanzu sun yi yara, idan kuka aurar da su Allah cutar su za'ayi, dan kwata kwata basu san me rayuwa ba, basu gama yin wayo ba". Cewar uncle Jahiz, yana magana yana É—aure face É—insa irin bada wasa yake yin nan ba.

"Jahiz kai baka san me duniya take ciki bane, a rayuwar nan na yanzu aurar da yara da wuri shi ne mafi a'ala a garemu mu iyaye, dan yaran yanzu da wayonsu ake haifarsu, so ba wani wayon da zasu kara, already da shi aka haifesu, zaka ga yarinya tun tana Æ´ar 11 years tasan komai, kaga yara tun basu kai ko'ina ba suna soyayya, gara auren a kan zinace zinace".

Shi dai uncle Jahiz he didn't not green with this season da uncle Abbas ya faÉ—a, sam bai yarda ba, dan haka sai ya sake cewa.
"Yaya to why su Jannat? Gara ma Sarina ta É—an fara girma amma ba sosai ba, Fanan da su Jannat fisabilillah me suka sani? Cutarsu kawai za'ayi, shi ma Jawad he's to yong, ga su Ramish da suka fara girma ba'a ce su yi aure ba sai shi? Ko da yake su Ramish É—in ma da sauransu su ma".

ÆŠan girgiza kai uncle Abbas ya yi tare da buÉ—e baki zai yi magana King ya rigasa da cewa. "Ba su Ramish zaka ce ba, ka fara da kanka katan gwauro, gaka a zaune 35 years ne ko up to 35 ne ba mata bare yara, kake kwantance da su Ramish waÉ—an da bama su gama cika 30 ba! Ai dik kai ka lalatasu, halinka suka É—auko"

"Yauwa gaya mashi dai yaya". Cewar uncle Abbas.

"A'a yaya, ni ai ban girma bane, sai na kai 40 or 45 haka zan duba batun auren, yanzu dai a'a, ai shiyasa nace maku su Ramish ma basu girma ba, yara ne, basu kai aure ba, dan Allah a barsu sai sun cika 40 years haka, ku bar yara su shana mana!".

"To idan ka kai 40 years kuma sai ka auri yarinya mai shekaru nawa?". Cewar uncle Abbas.

"Mai shekaru 25 haka is okay, 25 years tasan me take yi, ta yi wayo, ba zata sanya maka ciwon kai ba, amma Æ´an under 20 nan dik wahala ne, ciwon kai zasu saka maka, ai ni nama wuce auren irinsu, Allah ma ya kikaye". Ya kai karshen maganar yana É—aure fuska irin ba da wasa yake yi ba, shi yafi karfin Æ´an under 20.

Girgiza kai kawai King ya yi, dan ya lura uncle Jahiz fa ya yi nisa ba zai ji kira ba, dan bashi da Æ´aÆ´a ne yasa yake wannan magana, amma dik uba na gari wanda yake da Æ´aÆ´a mata to yana cikin tashin hankali da fargaba har sai ranar da ya aurar da su zai samu sukuni.

"Yaya kaga rabu da Jahiz, bai san me duniya take ciki ba, mu cigaba da maganarmu". Cewar uncle Abbas.

Wani irin ajiyar zuciya King ya sauke kafin ya ce. "Abbas Rizwan ne yake son Jannat ba Jawad ba, ina ga kayi kuskuren fahimta ne!".

Tashin hankali.

Zaro idanu uncle Abbas ya yi, a ruÉ—e ya furta. "A'a yaya Jawad ne yake sonta ba Rizwan ba, kai ne dai watakila baka fahimci maganar da kyau ba".

Gyara zama uncle Jahiz ya yi tare da fara bin brothers É—in nasa da kallo, dik wanda zai yi magana sai ya bisa da ido, yaga abin yana neman kawo ruÉ—ani a tsakaninsu.

"No Abbas, kai ne ka yi kuskuren fahimta, ko daren jiya mun yi maganar da Akka da kuma Jannat É—in, Akka ce ma ta fara samuna da maganar, nima nace mata kamar Jawad yana son Jannat fa, kuma ita ma Jannat É—in kamar Jawad take so ba Rizwan ba, shi ne Akka ta ce a'a da Rizwan suke soyayya, kawar da ruÉ—ani yasa muka kirasu dikkansu biyu, na tambayi Rizwan shi yake son Jannat ya ce mun e, na sake tambayar Jannat da Jawad take soyayya ko da Rizwan? Sannan wanenen take so a cikinsu". ÆŠan yin shiru ya yi yana sauke ajiyar zuciya kafin ya É—aura da cewa.

"BuÉ—ar bakin Jannat ta ce mun ita Rizwan take so, da shi kuma suke soyayya ba da Jawad ba, to kaga a nan kai ne kake cikin ruÉ—ani ba mu ba"....... Tashin hankali.

Abin da baku sani ba, idan baku manta ba ita Chuchu dik wanda take tare da shi a lokacin to da shi take yi, idan tana tare da Rizwan tana mantawa da Jawad, idan kuma tana tare da Jawad mantawa da Rizwan take yi, a lokacin da Akka da king suka tambayeta waye take so Rizwan ne a wajen, so dole shi zata ce, dan a lokacin ta manta da Jawad.... Akwai tashin hankali sosai da ruɗani a wannan al'amari, ta ya aka yi dik son da take yi wa Jawad zata rinƙa mantawa da shi idan ta haɗu da Rizwan? Wannan ruɗani dayawa yake wlh, ita dai Chuchu gatanan gata nan ne kawai, mutun mutumi.

Shiru uncle Abbas ya yi, kansa ta É—aure, ya shiga ruÉ—ani dayawa, ya za'ayi ace Rizwan Jannat take so bayan ya sha ganinta a tare da Jawad ciki nishaÉ—i! Sannan ga shi Jawad ya tabbatar mashi da soyayya suke yi! Kai gaskiya abin ya É—aure mashi kai sosai.

Shi dai uncle Jahiz har yanzu bai yanke hukunci ba, yana ta binsu da kallo kawai, yana jiran su gama tattaunawa ya faÉ—i nasa albarkacin bakin.
Chapter 163 · 0% Book details