← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 211

Sashe 57

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kai ta gyaɗa mata tare da amsa mata da e. Hakan yasa Sweetien ta cire abin ta bawa Prettyn a kan ta ajiye shi, dan haka yanzu Spender dai yana hannun Pretty ba hannun Sweetien ba, in dai har Sweetie tana son rayuwarta kuma tana son barin wannan Daula to dole sai Pretty ta zo, dan ita ke rike da Spender, ita tasan in da ta ajiye shi..... Tashin hankali gaskiya Sweetie tana tsaka mai wuya, yanzu ma shin ina Prettyn take? Sannan a ina ta ajiye Spender ɗin? Lallai ya tabbata ita ma Pretty tana da shegen wayau, duk yadda suke da Kamran bata taɓa gaya mashi ba ko da sunan wasa, amma ni tambayata a nan shi ne, ta ya aka yi Black Tiger yasan mum ɗinsu Sweetie ta bawa Spender ba Pretty ba? Dan kunga dai kai tsaye Sweetien suka nufa, and shin sun san su twin's masu kama ɗaya ne ma ko dai basu sani ba kawai sun kama Sweetien ne? Wa ma ya gaya masu Spender na hannunsu? Anya basu kama mum ɗinsu ba kuwa? To idan ba ita ba ai babu wanda yasan ta bawa Sweetie abin, ko ita mum ɗin kuma bata san da cewa Sweetien ta baiwa Pretty abin ba, ita dai tasan Sweetie ta bawa ba Pretty ba, akwai cakwakiya babba kuwa, ta ina za'a nemo Pretty ta zo ta kuɓutar da ƴar uwarta daga RAWANIN ZALINCI? Dan kuwa sai ta zo kam, saboda ko ita Sweetien bata san a ina Prettyn ta ɓoye shi ba..... Wannan shi ne babbar magana!!!.

Tunanika kala kala take ta faman yi a ranta, kamar ance ta ɗaga kanta sama ta ɗaga. Tana ɗagawa ta kalli flourescent bulb da take a zaune saitinsa yana ƙoƙarin faɗo mata a kanta, sai wani jijjiga yake yi da karfi kamar zai ɓallo.

Ihu ta kurma tare da fara ƙoƙarin tashi ta bar wajen dan kada ya faɗo mata a kanta, sai dai ta kasa iya motsawa daga wajen, ihu ta rinƙa yi tare da datse idanunta gam ta kuma takure jikinta waje guda, sai ƙoƙarin miƙewa take yi amma ta kasa.

Ganganrowa ƙasa flourescent ɗin ya yi har gabanta, ihu ta rinƙa kurmawa, kuma ihun nata baya fita, ga dai ɗan bakinta ta wagesa tana kurmawa, sai dai ba wani sautin da yake fita daga cikin bakin nata, abin da ɗaure kai sosai........ Ni ma dai ya ɗaure mun kai sosai gaskiya.

Nan take ta ji kamar ana juyata, a ɗari ta buɗe idanunta, me zata gani? Sai ganin parlourn ta yi yana wani irin jujjuyawa kamar fanka, komai na cikin parlourn juyawa yake yi, gabaɗaya light na cikin wajen bulbs sun fi gida 30 suka fara kawo light suna mutuwa lokaci guda, bulbs dake cikin gold parlourn sun kai guda 20 sai kawowa suke yi suna ɗaukewa suma, lokaci guda suke ɗaukewa su sake kawowa kamar ba lafiya ba, idan suka ɗauke kuma wani irin duhu mai ban tsoro ne yake sake bayyana a gabaɗaya gold parlourn, sai ta rinƙa ganin wasu irin halittu da bata taɓa ganin irinsu ba a cikin duhun kafin hasken ya sake dawowa, idan haske ya dawo kuma sai ta ga komai normal babu waɗan nan halittu.

Kanta ne ya fara juya mata ta fara fita daga cikin hayyacinta saboda bala'in tashin hankali, jikinta sai kerma yake yi. Da alama sun lura Sweetien fa bata da niyar basu Spender ne yasa suka fara azabtar da ita da tashin hankali kala kala haÉ—e da yi mata gizo, a tunaninsu idan ta sha azaba dole ma zata gaya masu in da yake,.........Babbar magana!!.

Tun tana iya gane in da take, tun tana iya ganin hasken light dake ɗaukewa yana sake dawowa har ta dai'na gani, idanunta suka rufe ruf ta sulale ƙasa ta kwanta a wajen.

Kafin wani lokaci komai na gold parlourn ya koma normal in da yake. Ita kuwa sai farkawa ta yi ta ganta a saman wani haɗaɗɗen bed cikin wani irin haɗaɗɗen ɗaki wanda ya fi ɗaki na farko da aka kaita kyau, ko kamshin dake tashi a cikin ɗakin na musamman ne, bata taɓa jin irinsa ba a duniya, kamshi ne mai kwantar da hankalin mai shaƙa!!.

A hankali ta waro idanunta da suka yi mata matuƙar nauyi waje, gabaɗaya jikinta ciwo yake yi mata, yadda kuka san wadda aka yi wa duka da itace, gashin kan nan nata a watse kamar na mahaukaciya, olive eyes ɗin nan nata har sun kumbura saboda kuka.

Yunkurawa ta yi zata miƙe saboda ta tuna da sallah. Kasa mikewar ta yi, saboda tsami da jikinta ya yi mata, kuka ta fara yi tana ji kamar ta gaya masu cewa Spender yana hannu Pretty su ɗaukota ta zo ta basu sai su sakesu su koma wajen zamansu, dan ba zata iya jurar wannan azabar ba, amma da ta tuna mum ɗinta ta ce in dai ta bada Spender ɗin nan to tabbas ta sadaukar da rayuwar babanta da kanta ne, to me haɗin ran babanta da spender? Akwai rina a gaba sosai ma kuwa. Tuna hakan yasa ta ji ba zata iya gaya masu ba, zata haƙura ta jure azaban!!.

Ajiyar zuciya ta sauke ta rasa mafita, sake yunkurawa ta yi cikin dabara, da kyar ta iya miƙewa zaune, ƴan kafafunta ta zuro ƙasan gadon, tsabar yadda gadon yake sama kafafunta basu iya taɓa kasa ba, mattress na bed ɗin ƙaton ƙosasshe da dollof ne sosai, ga shi gadon bango ne guda, tsab zai kwashi mutane 10 manya ba yara ba, har filli ta rage, king bed ne na musamman.

Dirowa ta yi ƙasa, wani irin zafi ta ji gaɓɓan jikinta suna yi mata. A hankali ta miƙe ta nufi kofar da take zaton toilet ne, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, fargaba kamar zai kasheta.

A guje ta fito daga cikin toilet ɗin, saboda irin abin da ya faro a toilet ɗinta na farko ne ya sake faruwa a nan ma. A tsakiyar ɗakin ta tsaya, wasu irin siraran hawaye masu zafin gaske ne suka fara bin ƙuncinta, ta rasa me abin yi.

Turo kofar ɗakin aka yi aka shigo. A ɗari ta kai kallonta wajen. Harɗe hannunsa ya yi a saman faffaɗar kirjinsa tare da zuba mata idanu, ya yi matuƙar kyau a cikin dressing ɗin nasa, hoodie ce a jikinsa, ya sanya hular kayan a kansa, ya yi matukar kyau, daga school ya dawo, yau yana da class, da yake ɗakunan cikin daular rana bata ratsa har ciki sai ba zaka iya sanin shin dare ne ko rana ba, yanzu haka almost karfe ɗaya na rana, tun jiya bata samu ta yi sallah ba, dan bata san time ba.

Ganinsa yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, shi da Floris kawai take son rinƙa gani a cikin empeirn nan, bayan su bata kaunar ganin kowa, dan duk wanda zata gani bayansu bala'i ce a gareta.

Wani irin haɗaɗɗen murmushi ya sakar mata kafin ya tako ya ƙariso cikin ɗakin, tana tsaye bata motsa ba har ya ƙariso in da take tsaye.

Yana zuwa ya kyasta mata yatsunsa a saitin face É—inta, dan ya kalli ta tsaresa da ido tun da ya shigo bata iya kawar da kallonta ba har ya iso wajenta, shiyasa ya kyasta mata yatsunsa.

Ajiyar zuciya ta sauke, taga kyau iya kyau shi ne ta tsare shi da kallo, ta shagala da kallon nasa har bata san ya iso gababta ba sai da ta ji kyas É—in yatsunsa.

"Mekike yi a nan?". Ya tambayeta cikin sanyin murya.

Da kyar ta iya kawar da kallonta daga kansa, sannan ta amsa mashi da. "Ina son ne na yi alwala na yi sallah amma ina tsoron wajen da ruwan alwalan yake".

Ba abin da ya gane tsakanin alwala da sallan, dan haka sai ya yi tunanin ko dai wani al'ada ne nasu na daban? Tuna hakan yasa ya ce mata. "Ruwa kenan kike so yanzu?".

A hanzarce ta gyaÉ—a mashi kai. "To ki shiga cikin toilet akwai ruwa, ko dai ruwan sha kike so?".

Girgiza kai ta yi tare da cewa. "A'a ba ruwan sha ba ruwan alwala dai". "Menene alwalar?". Ya gefa mata tambayar idanunsa na'a kan face ɗinta, tana matuƙar yi mashi kyau haɗe da burgesa.

"Alwala da ake yi kafin ayi sallah mana". Sanin cewa bai gane ina ta dosa bane yasa ya ce. "Ruwa mai kyau dai kike so ko idan na fahimta?".
Ya ce mata hakan ne kuma dan baya son wahalar da kansa wajen tsayawa sai ya gane nufinta, dan yasan ba wani ganewa zai yi ba tun da ita ba ƴar cikin birnin nace bare ya ce al'adunsu iri ɗaya, shi bai taɓa ɗauka ma akwai wasu al'adu a duniya da suka sha banban da al'adun su na birnin ba, shi ya ɗauka kowa ma christian ne kawai kamar su.

Toilet ya nuna mata. "Akwai ruwa mai tsabta a ciki". Girgiza kai ta fara yi mashi, tsoro ne bayyane karara a saman face É—inta. Ya lura da hakan, ya lura a tsorace sosai take, dan haka sai ya ce su je ya rakata.
Chapter 57 · 0% Book details