← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 211

Sashe 74

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ɗan ɗauki lokaci kaɗan yana latsa laptop ɗin nasa kafin daga bisani ya kashe laptop ɗin ya miƙe tsaye. Kai tsaye haɗaɗɗiyar bedroom ɗinsa ya nufa. Wanka ya sake yi ya fito........... (Wai ni kam my people's ba Smart ɗin nan aka kira a waya a kan roket ta kwace masu ba? Ga shi ba'a gama haɗata ba bare a shigar mata da control 🤔 amma yana zaune ko a jikinsa🤔 da alama guy ɗin nan zai azabtar da ni 🤔 ka ji mun ɗan abin da babana ya hanani faɗa.)

Shiri ya tsake yi cikin ƙananan kaya, ko da ya gama shiri ya dawo cikin room ɗin sai ya isko Tigersa kwance a kan gadonsa, a takaice ya ce mashi ya tafi. Da farko damisan ya so binsa, hana shi ya yi ya ɗauki wayarsa kawai ya fito waje, sai gurnanni damisan yake yi amma bai kula shi ba ya wuce kawai.

Wani irin haɗaɗɗen mota ya ɗauko ba wanda suka zo da shi ba, wannan mota da ya ɗauko motace mai tuƙa kanta da kanta, ba sai ka wahala wajen tuƙata ba, da zarar ka shigar mata da location ɗin in da zaka je a map ɗinta zata bi komai a sannu ta kaika in da ka buƙata, idan gudunta bai yi maka ba kana da damar cewa ta ƙara gudu kuma zata ƙara sosai, haka zalika idan kana son ta kara gudun Ac ma zata kara maka, abin dai ba'a magana, shegiyar tsada ce da motar nan fiye da tunanin ku, billions of dollars ne. (Kun san ni bana son kiran sunan kuɗin abubuwan dan kada mu sume da jin kuɗinsu🤣 wlh ban san meyasa ba ban son faɗan kuɗin duk abin da na rubuta😅 ya fi mun in ce yana da tsada kawai, kuma wlh kuɗinsu na gaskiya ne, kiran ne kawai ban son yi.)

To billions of dollars motar nan take, ta haɗu ta gaji da haɗuwa, ita ya ɗauko ya shiga, gidan baya ya shiga, kai tsaye ya shigarwa motar in da yake son zuwa. Securitys ɗinsa sun so su raka shi ya hanasu, dama dan kada ya rinƙa yawo da kowa a bayan idanun daddynsa ne yasa ya sayi wannan motar, sannan baya son driving da kansa, kunga a saukake motar zata kaisa in da yake da buƙata.

Haka shi kaÉ—ai ya bar gida, duk wannan uban tsaro da dad ya haÉ—a mashi kullum a nan yake zuwa ya jibgesu ya yi fitarsa shi kaÉ—ai, dad yana can ya saki baki a kan ya bawa É—ansa tsaro na musamman, bai san jibge tsaron É—an nasa yake yi a gida ya yi fitarsa shi kaÉ—ai ba...........

Kai tsaye bayan gari ya nufa, wato daji kenan, gabaɗaya wajen ƙanƙanra ne, ice palace kenan, motar tasa ma ba dan ta amsa sunanta mota ba bata isa ta keta wannan hanya ba, wajen akwai sanyi sosai da sosai, dusar ƙanƙara sai zuba take yi kamar ruwan sama.

Ya yi tafiya mai nisa a cikin ƙanƙaran nan kafin ya dakatar da motar, sannan ya ɗauko wani jibgegen jacket mai bala'in kyau ya sanya a jikinsa, dan ba karya akwai sanyi kam, komai sabonka da sanyin ƙasar idan kazo wannan wajen sai ka haɗawa kanka kayan sanyi ko kuma sanyi ya busar da kai.
Already dama kun san ƙasar France ba dai sanyi ba, suna da ita sosai, to amma dole wajen da za'a haɗa boma bomai irin waɗan nan ya kasance da sanyi, shiyasa suka nemi in da yake da matuƙar sanyi, dan idan baku manta ba nuclear bom's fa wuta ne, wuta kam mai rai da lafiya ma kuwa, kunga dole a nemi waje mai sanyi domin haɗa su, idan ba haka ba in waje mai zafi ne sai ma'aikatan su yi ta mutuwa, zafin sai ya yi masu illah over, kai bama zai yiwu a waje mai zafi bane.

Fitowa daga cikin motar ya yi bayan ya sanya jacket É—in, nufa kofar shiga underground É—in ya yi.............. Kana sako kafarka a cikin wannan katafaren wajen nasu gabaÉ—aya warin chimical na haÉ—a nuclear bom's irin su, Uranium-235 U-235, Plutonium-239, Pu-239, Deuterium D2, Tritium T2, Lithium-6 Li-6 zaka ci karo. Dukkansu is for atomic Bombs Fission, gabaÉ—aya wajen idan baku saba ba kuka shiga sai mutun ya mutu har lahira, cikin tamkar engine bread, saboda zafi, ga wasu chimical É—in yadda suke tafarfasa kamar wuta, kai abin dai sai wanda ya gani.

Yana sanya kafarsa a wajen wani katon ƙosasshen bature fari tas mai rai da lafiya dake tsaye a wajen bakin kofar shiga ya yi hanzarin ɗauko mashi wani irin riga mai ɗan tsawo zuwa gwiwowinsa da kuma face mask and katon glass mai haske. Sanya rigar a saman kayan jikinsa ya yi tare da ƙarɓar glass ɗin haɗe da mask ɗin ya sanya a face dinsa.

Yana yin tsarin wajen fili ne mai matuƙar tsaro wadda wane mutun ya iya gane me ake yi a wajen, duk munarfurci wata ƙasa bata isa ta iya gane abin da ake yi a wajen shagon ba, ga wajen underground, sannan ga uban tsaro da aka yi amfani da na'urori wajen sanya mata mahaukatan mataƙan tsaro na ban mamaki.

Wasu irin jiga jigan fararen turawa ne birjik a cikin wajen, kowanne da aikin da yake yi, yadda kuka san wani irin katafaren Company ne a wajen, ko da yake wannan ya ci uban company ma, dollars suna kuka a wajen nan, dan ana cin uban kuÉ—i kam, kuÉ—in da ake zubawa a wajen nan wane budget É—in Nigeria.

Gabaɗaya cikin wajen tiles ne a kasan floor, ga wasu irin engines masu matuƙar girma, side da suke haɗa chemicals kala kala har su sarrafa shi su mai da shi wuta filin ɗan adam bai isa ya tunkara ba idan ba aikinsa bane, daga jefe guda ga wasu irin na'urori wanda da wuya ka iya samun irinsu a ko wace iriyar ƙasa, dan kuwa Smart shi ya kyara kayansa, a cikin wajen ta can gefe akwai wani part da aka ware na daban, system ne birjik a wajen, duk wasu irin nau'in abin da ya shafi system irin su laptop, desktop computer, kai duk dai abin da ya shafi system akwai shi a wannan wajen

Duk in da ya sanya kafarsa zai wuce sai waÉ—an nan jaruman ma'aikatan nasa sun bar abin da suke yi sun É—aga hannu sun sara mashi.

Kai tsaye wajen system É—in ya nufa, har ya kai tsakiyar wajen sai kuma ya juyo ya nufi wajen chemicals É—in da suka haÉ—asu cikin wani irin jibgegen engine da yake buÉ—e kamar baf, a nan suke zuba chemicals É—in sai engine ya yi masu mixing É—insa, sai ya haÉ—u sosai kafin su tura shi izuwa wajen da zai narkasu kuma.

Ma'aikata sama da guda biyar ne tsaye a gaban chemicals ɗin suna aikinsu, yana dososu suka buɗa mashi hanya tare da ɗaga hannu suka sara mashi. Ɗaya daga cikinsu ne ya yi hanzarin ɗauko hand gloves ya sanya mashi a hannunsa, ƙurawa chemical ɗin idanu ya yi na ƴan sakanni. Chemicals ne irinsu Deuterium-Tritium D-T, Fusion fuel, Lithium Deuteride LiD.
Slowly ya dawo da kallonsa a kan ma'aikatan nasa, shiru ya yi yana kallonsu kamar ba zai yi magana ba, can sai kuma ya ce. "This chemicals is it not for Hydrogen Bombs?".

A hanzarce suka amsa mashi da e sune cikin girmamawa. Juyawa ya yi ya nufi wajen systems ɗin nan. Binshi da kallon mamaki suka yi, kai guy ɗin nan ba dai ƙwaƙwalwa ba, an cakuɗe chemicals ɗin waje guda ma amma ya iya tantance na wani irin nuclear bom ne, kuma chemicals ɗin kusan kala ɗaya suke a kamanni, amma a haka yana iya tace kowanne koda kuwa zasu haɗa da na nau'in boma bomai daban daban su cakuɗa ba'a gabansa ba yana zuwa kallo ɗaya zai yi masu ya ce masu ya suka haɗa na kaza da kaza? Tun suna mamakinsa har sun hakurar da zuciyarsu sun dai'na, dan sun gane baiwa ce daga Allah ke garesa.

Yana isa wajen systems É—in wani katon bature mai rai da lafiya a hanzarce ya cire mashi hand gloves da waÉ—an can suka sanya nashi, bayan ya cire sai ya cire mashi glass dake face É—insa ma, wani wajen ya nufa dan ya je ya ajiyesu, shi kuma Smart É—in wata black glass ya É—auko daga cikin drawers da wasu daga cikin nau'i na laptop suke É—aure a kai.
Sanya glass ɗin ya yi tare da shiga cikin na'urar da kyau ya fara ƙoƙarin control na nuclears da suka tattasa sama ɗasun dan gwaji, harta nuclear da ya kwacewa ma'aikatan nasa ma ya iya sarrafata, saboda already ya shigar mata da control su ne basu sani ba, dama ɗazun lokacin da yake gidansa ma'aikatar nasa sun gwada wasu nuclears abin da ya duba kenan a laptop ɗinsa da ya ɗauka a lokacin da ya haura sama a gidansa, to information da ya samu kenan shiyasa ya taso ya zo wajen dan ya ga ya nasarar aikin ya yake da idanunsa.

Abin da kuma masu karatu baku sani ba, idan baku manta ba na ce maku yana da aikinsa na daban, to shi ɗin jami'in Secret Intelligence Service, the most powerful Jami'an sirrine in the whole kasar France, haka zalika ma'aikatansa dake wajen nan dukka aikinsu ɗaya, yaransa ne, dukka waɗan da kuka gani a cikin wajen zaƙaƙuran masu kishin ƙasarsu ne, basu da wasa ko kaɗan, da ka shiga hannun waɗan nan gara maka mutuwa, ko da yake ba sai na ɓata bakina ba wajen dogon bayani, mutanen da suke cikin irin wannan waje mafi haɗari a duniya ai bama sai an ce maku komai ba, wajen da in suka yi mistake kaɗan gabaɗaya birnin Paris zata bambame da wuta ne, babu abin da zai rage, dan kuwa ba ƙananan boma bomai ake haɗawa a wannan wajen ba, yadda suke haɗa chemicals suke tafasa suna ci da wuta haka zuƙatansu yake.
Chapter 74 · 0% Book details