← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 211

Sashe 97

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa da bata san a wani hali yake ciki ba, sannan a yaya mafi soyuwa a gareta ta É—auke shi, sai ta buÉ—e baki ta sanya hakwara ta kama yatsan nasa tana É—an cizawa a hankali.

Ai bai san lokacin da ya furta wash da karfi ba, da sauri ya rabata da jikinsa, lumshe idanu ya yi kamar wani mara lafiya, kasa iya riƙe kansa a tsaye ya yi, dan jikinsa tamkar wadda aka zarewa laka, dan haka sai ya koma saman bedside drawer ɗinta ya zauna yana cigaba da lumshe idanu tare da shaƙar daddaɗar kamshin perfume ɗinta da ya gauraye ko'ina a ɗakin.

Yana zama kuma Momma tana shigowa cikin room É—in nata, Allah ya taimakesa, da kuwa yau zai sha faÉ—a a wajen Mommar, dan kuwa dama ta gaya mashi yanzu ya sani son Jannat da aure yake yi, dan haka ta tashi daga kanwarsa, duk wani rungume rungume da suke yi na oyoyo tsakanin yaya da kanwa to ya dakatar da shi, in kuma ba haka ba ba zai ga da kyau ba, sosai dai ta yi mashi faÉ—a, amma bai ji ba, to dai Allah ya rufa mashi asiri yana raba jikinsu Mommar ta shigo.

Ganinsu a tare yasa Mommar ta fasa yin abin da ya kawota, dama wajen Chuchun tazo zasu yi magana a tsakanin uwa da Æ´a, amma da ta ganshi a É—akin sai kawai ta juya, dama room nata zata wuce ta biyo nan, daga parlon King take.

"Momma lafiya?". Da kyar ya iya jefa mata tambayar, muryarsa sai sarkewa yake yi. Jin yadda ya yi maganar yasa Mommar yi mashi kallon tsab kafin ta ce. "Babu komai, Jannat idan kin gama ki zo kin ji?". Tana magana tana kare mashi kallo.
Ya fahimci ta gane wani abin, dan haka sai ya kawar da kallonsa daga kanta kawai, tunani ya fara yi a kan yau zai sha faÉ—a a wajenta in suka haÉ—u, dan bashi da kalaman kare kansa, sai dai fatansa Allah yasa kada ta yi wa Jannat É—insa faÉ—a.

"To Momma". Chuchun ta amsa. Wucewa ta yi ta fita, ita kuma Chuchun ta zauna a saman mirror chair É—in tana sakarwa yayan nata murmushi.

"Ina zaki je ne ma da kika yi irin wannan kyalliya mai tsayawa Jawad a zuciya?". Ya faÉ—a yana É—aure fuska alamar kishi ta motsa.

"Yah Rizwan zan je in yi wa oyoyo".

Ba tare da tunanin komai ba ya ce. "Shi ne sai an É—auki irin wannan kwalliya haka tamkar zaki je neman saurayi ko mijin aure? To ban yarda ba, canza kayan nan ki sanya normal kayanki na gida, kuma ki saka hijabi, shi ne cikar mace ta gari". Fuska a É—aure ya yi maganar.............. (My people's kun ji Yah Jawad da karfin hali, shi ya ganta da irin shigar da ta yi É—in amma wai bai kamata kowa ya gani ba, yau ga ikon Allah.)

Turo baki ta yi kamar zata yi kuka ta ce. "Yah Jawad na sha wahala fa wajen tsara wannan kwalliyar, please ka bari mana".

Ƙara ɗaure fuska sosai ya yi tamkar bai taɓa yin dariya ba, alamar babu wasa fa. "A'a ban yarda ba, ki cire kayan ni sai na tayaki yin wani dressing ɗin".

Sam bata san yin ja in ja da shi, dan tana jinsa a ranta sosai, kuma tana respecting ɗinsa sosai, hakan yasa tana tura baki ta nufi dressing room ɗinta. Mikewa ya yi ya bi bayanta yana faɗin. "Ni zan zaɓa maki kayan da ya dace ki fita da su". Sarkin kishi ba, yaga ta yi kyau sosai ne a cikin kayan shi ne bari yasa ta canza dan ma kada ta burge wani.............. Yah Rizwan ka yi sauri ka zo ga nan Yah Jawad zai ci amanarka ya yi maka kwacen mata.

Wata simple gown wanda babu kwalliya a jikinta ya zaɓa mata, rigar mai tsada ce sosai, amma babu wani kwalliya da zai ja hankali a jikinta, ita ya bata dan ta sanya, sannan ya zari mayafin rigar ya miƙa mata. Ba dan ranta ya so ba ta karɓa ta wuce toilet, shi kuma ya koma saman bedside drawer ya zauna.

Jim kaÉ—an ta fito, da yake ita É—in kyakkyawace sosai kuma munafikin jiki ke gareta mai É—aukar kowani irin kaya ya yi mata kyau, sai kayan ya yi mata kyau sosai. ÆŠan dafe kansa ya yi tare da cewa. "Sister har yanzu dai kin yi kyau sosai, kamar kada na barki ki je nake ji".

Turo bakin nan ta yi, a shagwaɓe ta ce. "Kai Yah Jawad wai ni kam me matsalarka da idan na yi kyau kada na fita ne?". A takaice ya ce mata. "Saboda ina kaunarki mana, dole na kula da ke".

Da yake ya saba cewa yana kaunarta sai ta É—auka yau ma irin dai kauna ta tsakanin yaya da kanwa ne, bata kawo komai a ranta ba sai ma cewa da ta yi. "Nima ai ina kaunarka".

Wani irin sanyi ya ji ta ratsa mashi ƙashi da ɓargon jikinsa, miƙewa tsaye ya yi. "Zo mu je to in ɗan rakaki dan zan je wajen Aunty MieMie ce, ta ce nazo yanzu na sameta a part ɗinta mu tattauna, nace mata a'a sai naganki naga da kika cire kayan Fanan ɗin wani irin kwalliya kika yi".

Guntun murmushi ta saki tare da ƙarisawa gabansa, hannunta ya riƙo suka nufi waje, har cikin ransa yake jin daɗin lallausan hannun nan nata yana ratsa shi. A dai'dai tsakanin part ɗin Momma da Mama ya saki hannun nata tare da manna mata sumbata a goshi, sannan ya ce. "To a gaishe da Yah Rizwan".

Da okey ta amsa mashi, daga haka suka raba hanya, shi ya yi wajen Aunty MieMie ita kuma ta nufi wajen Yah Rizwan É—in.

Sai zumuÉ—in son ganinsa take yi, baki a É—auke da É—an siririn sallama ta shiga part É—in uncle Abbas. Babu kowa a parlour, dan haka sai ta nufi part É—insu, already ta san a in da part É—in yake.

A bakin kofar shiga parlonsa ta tsaya ta yi sallama. Shiru ba'a amsa mata ba, sake yin sallama ta yi a karo na biyu, nan ma shiru ba'a amsa mata ba. Hakan yasa ta kutsa kai ciki kawai. Babu kowa a parlourn nasa face sanyi Ac haÉ—i da kamshin perfume dake tashi.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da nufar kofar master room É—insa.

Dab zata shiga shi kuma yana fitowa manne da waya a kunne yana waya, ya ji alamar kamar anyi sallama a kofar parlour ne yasa ya fito dubawa.
Karo suka ɗan yi ya ja baya kaɗan da sauri. Ita ma bayan ta ja a hanzarce tana sunkuyar da kanta ƙasa haɗi da ce mashi sorry.

Subhanallah tsayuwa ya yi tare da zuba mata idanu yana kallonta, ya manta yana waya ne, ashe a hoto bai ga komai ba, yanzu ne ya ga madarar kyau, wai a hakan ma Jawad ya sa ta canza kwalliyar farko, da se yaya kenan?.

"Yah Rizwan sannu da zuwa, ina wuni?". Ta faɗa kai a ƙasa.

Subhanallah, ai ƙasa iya amsa mata ya yi, sai ma fitowa parlon da ya yi yana kare mata kallo da kyau da kyau, da yake yasan halinta da shegen son ace mata ta yi kyau, nan fa ya hau yabon kyanta da ya sanyata farinciki da annashuwa.

Da hannu ya nuna saman sofa tare da cewa. "Zo ki zauna". Kamar wata bakuwa haka ta zamto, ba karya zuciyarsa ya kamu da matuƙar sonta.

Zama ta yi sai faman ɓoye fuska take yi, haka kawai take jin kunyarsa saɓanin Yah Jawad da suke ƙurawa juna idanu suna karewa juna kallo. Saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna while ita tana saman mai zaman mutun ɗaya, sai satar kallonsa take yi, ya yi kyau cikin arab jallabiyar tasa, da alama bai jima da fitowa daga wanka ba, dan kuwa ga shin kansa da sauran danshin ruwa, alamu sun ya nuna wanka ya yi ya biya basussukan sallolin dake kansa.

"A fili kuma kunyata kike ji my Jannaty?". Ya yi maganar idanunsa a kanta babu ko kyaftawa.

Ƙara ɓoye fuska ta yi tana ɗan murmushi ta ce. "A'a kawai dai na ji ba zan iya haɗa idanu da kai bane".

Ajiyar zuciya ya sauke. "Yanzu nake cewa zan shirya ya je part É—in dad in sameki, idar da sallah na kenan".

"Ai ba zan iya jiranka ba, ina marmarin ganinka, dama nasan zakazo ai shiyasa na yi saurin rigaka". Ta bashi amsa ba tare da kallon in da yake ba.

"Wow ashe my wife ta girma sosai fa! Kai shi ne na tsaya yin sanya salon wani É—an sarkin ya mun kwace, gaskiya da na yi shirme babba". Seriously ya yi maganar.

"Kai yaya Rizwan ni fa yarinya ce". Ta faɗa a shagwaɓe.Ɗan leƙo face ɗinta ya yi yana faɗin. "E wato yau dai ba za'a ce mun my husband ba kenan ko?".

Girgiza kai ta yi alamar a'a tare da cewa. "Zan kira mana"

"To shikenan a kirani in ji".

Hannayenta dukka biyu tasa ta rufe fuska tana murmushi ba tare da ta kira É—in ba.

"Kin gani ko? Ai nasan a waya ne kawai aka iya yi mun wannan soyayya, yanzu gani nan an ɓoye mun fuska, a barni naga kayana ma an hanani ni da fuskarta, kuma naga alama a iya waya kawai ake mun shagwaɓa yanzu ba za'ayi ba ko?".

"Kai Yah Rizwan ni fa ban hanaka ganin face É—ina ba". "To meyasa aka rufe mun shi?".

Zame hannayenta daga saman face ɗin nata ta yi tare da faɗin. "To ga shi nan na buɗe shi ka gani". Ta yi maganar tana ɗan turo baki alamar shagwaɓa.

Habawa nan take ta ƙara tsunduma shi cikin gogin kaunarta. Zuba mata idanu ya yi yana rakon Allah da ya kara mallaka mashi ita, a gaskiya yana yi mata wani irin son da bai taɓa yi wa wani abin ba, yana jinta har cikin ƙarƙashin zuciyarsa.
Chapter 97 · 0% Book details