Sashe 138
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tsiwar nan dai nasu ma gadon masifa da faÉ—a ta ce. "Sai kuma ka yi, kanka ake ji, ni dai ba zaman a gidan nan zan yi ba koma me zaka ce, bari ma kaga tafiyara".
A takaice ya ce. "To Allah ya bada sa'a". Yana kai karshen maganar ya juya ya bar wajen.
Mamaki ne ya kamata, bata yi zaton zai ce mata ta je ba, ta yi zaton hakuri zai bata ita kuma ta yi mashi walaƙanci dan ba son shi take yi ba, sai ta ji ya ce Allah bada sa'a.
Jikinta ne duk ya mutu, bata taɓa zaton hakan ba, dan haka sai ta wuce sumumui sumumui kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Tsaye take a gaban garken dabbobin nasu tana tunanin rayuwa, tana tunanin yadda aka rabata da Hammanta Faisal wanda take masifar so.
Daga ta bayanta ta ji an yi mata sallama. Da sauri ta juyo da kallonta. Ƴar matashiyar yarinyar Inna Rabi ce, yarinyar da zata iya kai shekaru 14 zuwa 15 haka, da kaɗan ta fi Mahnoor ɗin girma.
"Ina kwana Mahnoor". Yarinyar ta faÉ—a tana kallonta. "Lafiya lou jumma, yasu Inna?".
Da lafiya ta amsa mata kafin ta É—aura da cewa. "Mahnoor na ji daÉ—i da Allah yasa aurenmu zai kasance a cikin sati guda, wannan chewing gum ne na kawo maki, kada ki gayawa kowa na sayesa, jiya ne da muka shiga birni da bappa na saya dan na bawa kawayena, na aurena ni da bobbo Bello ne". Ta kai karshen maganar murmushi a kan face É—inta.
Ƙaƙalo murmushin dole baiwar Allah ta yi tare da cewa. "Amma gaskiya Jumma na maki murna da Allah yasa kika yi nasarar samun dama zaki auri wanda kike so, Allah ya kai mu jibin Allah kuma ya baku zaman lafiya, na ji maki daɗi sosai, sai dai ni kuma an rabani da Hamma Faisal ɗina, ina jin kamar in yi ta kuka kada na dai'na". Ta kai karshen maganar idanunta a cike da kwallah alamar tana son yin kukar.
Matsowa kusa da ita Jumma ta yi, shoulder ɗinta ta dafa da hannu guda, cikin sanyin murya ta fara faɗin. "Mahnoor ki yi hakuri, nasan da ciwo a rabaka da wanda kake so, amma kuma ki sani bappa ba zai taɓa haɗaki da abin da zai cutar dake ba, sanin kanki ne yana kaunarki fiye da kansa, kuma ke ki godewa Allah ma ɗan birni aka aure maki, kin dai san wannan Hamman naku bai yi kalar ƴan rugar nan ba, ga shi kyakkyawa wanda gabaɗaya kauyen nan suke son kallonsa idan ya fito......."
Katse mata maganar ta yi da cewa. "Suna son kallan kyansa amma kuma suna jin tsoron haÉ—a idanu da shi ba". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar.
"Haka ne muna jin tsoron haɗa idanu da shi, amma ina son ki sani har laɓewa muke yi mu leƙesa dan muga kyansa, wlh ki godewa Allah da wannan ni'ima da ya baki, ni ba dan tsoronsa da nake ji ba wlh da babu abin da zai hanani tinkararsa in ce ina sonsa, yana da kyau sosai, ki duba gashin kansa sam ba irin namu ba, har kyalli nasa yake yi, kai koya zan gaya maki ba zaki gane ba, amma dai yana da kyau ki san cewa kin yi sa'a, wannan ko da haɗi a kwatance ba za'a haɗa shi da Hamma Faisal ba".
Shiru ta É—an yi tana tattauna maganganun a cikin kwakwalwarta, dan ita a gaskiya Faisal take so, da wuya zuciyarta ta yarda da wani bakon.
"Kada ki tsaya yin wani dogon tunani Mahnoor, tunani ba naki bane, kawai ki rungumi mijinki ku zauna lafiya, idan ma baya sonki ki koya mashi sonki, idan ma kece baki sonsa to ki koya, yana da kyau ki dai'na tunanin Hamma Faisal a yanzu, yin hakan kin dai san Inna ta ce babban kuskure, da auren wani a kanka kana tunanin wani hakan sam bai dace ba, ba tana karantar da mu hakan a islamiya ba?". Ta jefe mata tambayar tana leƙo face ɗinta, while hannayenta suna a saman shoulder ɗinta har lokacin.
"Amma kuma Jumma kin ji fa jama'a suna cewa maye ne shi É—in?". A tsorace ta yi maganar, muryarta har kerma yake yi.
"Ke kin yarda shi mayen ne?".
A hankali ta É—ago kai suka kalli juna ido cikin ido, wani irin tausayinta ne ya kama Jumma, tasan yadda zafin so yake, yarinya baiwar Allah, marainiyar Allah, sam kukanta baya da kyan gani ga koma waye ne idan ba bakin azzalumi irin Nenne ba.
"Jumma a da can baya na yarda Hamma aljani ne, amma ban taɓa yarda cewa shi maye bane". Tana kai karshen maganar hawayen da suka cika mata idanu ne suka gangaro mata sama face ɗinta gwanin ban tausayi.
"A yanzu fa? Kin yarda shi aljanin ne?". Ta sake jefa mata tambayar tana mai da kallonta a kan shanu biyu da suke ƙoƙarin fara faɗa a bayansu.
"A'a yanzu na dai'na tunanin shi aljani ne, shiyasa ma na dai'na jin tsoronsa, amma kuma ba zan iya zama da shi ba Jumma, wlh idan ni da shi ne kawai zan ji tsoro, har yau har gobe ina jin tsoron haÉ—a ido da shi". Tsananta kukanta ya yi a lokacin da ta ce idan shi da ita ne kawai zata ji tsoro.
"Shin ya taɓa yi maki wani abin na mugunta ko na ban tsoro ne?". Ta yi maganar tana kai hannu saman face ɗinta dan ta goge mata hawaye.
"Bai taɓa yi mun komai na mugunta ko ban tsoro ba, sai dai ma taimakona da ya sha yi, ko ranar da su Hamma Salisunku suka biyoni zasu dakeni shi ya tare mun ya hanasu dukana........".
A hanzarce ta tari numfashinta ba tare da ta barta ta kai aya ba ta ce. "Yauwa Alhamdulillah, to kin gani, kinga shi bangone ma a gareki, ki riƙesa hannu biyu zaki sha mamakin kulawar da zai baki, ina mai tabbatar maki watarana zai hana Nenne ma zalincin da take yi maki, ki jarraba ki gani".
Tunanin abin da ya faru a yanzu na hana Nenne dukanta da ya yi ne ya faɗo mata a rai, da alamar kamshin gaskiya a maganar Jumma fa, amma to taya zata fara iya zama da shi waje guda? Wannan abu ne mai matuƙar wahalar gaske a gareta.
Ganin ta afka duniyar tunanin ne yasa Jumma ta katseta da cewa. "Yanzu abin da nake so dake ki je ki faki idanunsa ki kure mashi kallo anjuma idan kin zo islamiyya sai ki gaya mun me kika ji a ranki lokacin da kika kare mashi kallon". Ta kai karshen maganar tare da kara goge mata hawayen da har yanzu suka ki dakatawa daga zuba.
Kai ta ɗago da nufin ta yi mata magana karaf idanunta suka sauka a kansa, yana tunkaro in da suke tsaye hannunsa riƙe da sandar bappa na kiwo, da kuma igiyoyi da zai ɗaure kananan shanu, basa fita kiwo da kananan ciki irin waɗan da suka kusa kai yayen nan, tsaka tsakiya kenan, a haka ake koya masu yaye, za'a rinƙa fita da uwar ana barin ƴaƴan, tun suna kuka har su zo su fara sabawa da rashin shan nonon, a hankali hankali har su manta da shi su dai'na sha, koda uwar ta dawo sai kuga basu wani damu da su zo su sha ba, saboda sun ci abincin da ya dace da su a gidan sun ƙoshi sosai, so basu wani damuwa da nonon, a haka dai har su yaye kansu da kansu daga shan nonon.
So ya nufosu da nufin ya É—aure yaran kafin bappa ya fito su tafi, yau bata dama mashi fura da nono ba ta zo ta tsaya suna hira da Jumma, ko É—umamen safe bata É—aura ba, ko wutar ma bata hura ba.
"Jumma idan na zo islamiyya zamu ƙarisa maganar ga Hamma nan yana zuwa, sannan In Sha Allah na san bappa zai barni na je dandali shagalin bikinki". Tana kai karshen maganar bata tsaya jin maganar da Jumma zata sake cewa ba ta yi saurin wucewa.
Jumma kuwa tun daga nesa ta kafe shi da idanu tana kallonsa babu ko kyaftawa, tamkar taga bako daga wani duniya. A cikin zuciyarta sai santin kyansa take yi, Allah ya gani tana bala'in son ta yi ta kallon face ɗinsa, kun san larabawa da turawa kyan gani ne da su ga daɗin kallo.........😂
Sai dai kuma tana tsoron ya kalleta su haÉ—a ido, dan haka da ya kusa isowa sai ta yi maza ita ma ta bar wajen ta nufi hanyar gidansu, tana tafiya tana waigosa, shi kuwa in da yasa gaba kawai yake kallo, ko ya É—ago ya kalli amaryar tasa ma yaki har ta zo ta wucesa tamkar bai santa ba.
Tana shiga cikin gida ta isko bappa da ya fito daga banɗaki a yanzu, hannunsa na riƙe da buta. Cikin girmamawa haɗe da nutsuwa ta ce. "Bappa ina kwana".
Ganin alamar kamar ta yi kuka ne yasa ya amsa da. "Lafiya lou me ya sameki kika yi kuka?".
Ƙasa ta yi da kai ta rasa abin faɗa, sai ta fara ƴan kame kame kamar wata maras gaskiya.
"Mahnoor ba dake nake yi bane? Meyafaru kika yi kuka?". Fuska a É—an É—aure ya sake tambatar tata, dan a duniya babu abin da ya tsaya da ya wuce ya ganta a cikin damuwa.
"Babu komai bappa, wani abin ne ya shiga idanu na". Ta bada amsa a tsanake.
Ya fahimci karya ta yi mashi, amma bai nuna ya gane karya take yi ba, sai ya ce mata. "Ina hammanku?".
Da hannu ta nuna hanyar fita tare da faÉ—in. "Yana walde".
Shiru ya ɗan yi yana tunani a kan abin da ya sanyata kuka, to kenan kukan nata yana da alaƙa da hammansu? Dan yaga waje guda kenan suke, daga wajensa ta fito kenan, to me ya haɗasu ya sakata kuka kuma?. Ya jefawa kansa tambaya yana mai cigaba da zancen zucin nasa.
"Bappa in tafi ne? Ina son na je na kunna wuta na yi maku É—umame kafin ku tafi kiwo".