← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 211

Sashe 36

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin ƙanƙanme shi ta yi tare da fasa kuka. Zare injection ɗin ya yi a hankali tare da fara ce mata sorry. Ita kuma Floria ta ɗaura katon glass tray ɗin abincin a saman carpet ta haye saman gadon ita ma. Haɗuwa suka yi ita da Ronnie suka rarrashi Sweetien har sai da suka tabbatar ta yi shiru. Sannan ne Ronnie ya rabata da jikinsa ya sauko ƙasan gadon.

"Beb ki kula da ita ta ci abinci sai ta yi wanka ku zo mu je muga wasan su Ovil". Yana gama magana bai jira amsarta ba ya nufi waje.

A kowace Daula akwai jarumi da yake gaba da kowa. To a Daular Dark World dai Ronnie ne jarumin da yake cinye duk wata gasar da black Tiger zai sanya, yana da karfi sosai da kuma dabara, ga ilimi, idan suna Wrestling in dai ya shiga shi zai yi nasara, kasancewar suna cikin ɓata ba musulmai bane yasa a duk lokacin da ya yi nasara zai kashe wanda ya faɗin kamar yadda yake a dokance ba tare da ya ji wani ɗar ɗar ba. Kakkaifar wuƙa yake ɗauka ya datsewa wanda ya faɗi ɗin wuya ba tare da tausayi ko makamancinsa ba, sai dai bai cika shiga gasar ba, dama dan ra'ayin kansa yake shiga, sai ranar da yake cikin nishaɗi yake shiga kuma ya yi nasara. Duk ƴan'matan cikin birnin Dark world suna mahaukacin son suga zai yi wasa, suna son ganin wasan sa, domin idan ba'a wasa ba ba sa samun damar ganinsa, baya fita, ko school kaisa ake yi a mota mai tinted, kowa tana santin kyansa kuma tana kaunarsa, sannan suna son ganin wasan sa ne dan suka ga jarumta, jarumin gaske ne wanda yake da karfi.

Yana fitowa daga cikin É—akin suka ci karo da Delisha a kusa da É—akin ta nufo wajen. Harara ta wurga mashi ba tare da ta ce mashi uppanba.

Wani irin ƙayatatcen murmushi ya sakar mata har sai da dimples ɗinsa suka lotsa sannan ya kashe mata ido ɗaya kamar wani tsohon kwarto. Hannunta ya riƙo tare da jawota jikinsa, a kunne ya raɗa mata cewa. "Sarkin faɗa sai ina kuma?".

Sake banka mashi harara ta yi, shi ko ya sake sakar mata wani lallausan murmushi, shi fa har daÉ—i yake ji idan tana wannan hararar tasa, kyau take karawa.

"Sake ni in tafi ka ji?'. Ta faÉ—a a sanyaye kamar ba ita ce mai shegen tsiwa da faÉ—a ba.

"Haba mana beb kafin na sake ki gaya mun in da zaki je tukun nan". Yana magana yana wani lumshe idanu kamar wanda yake cikin yanayi.

"Wai kai meyasa a rayuwarka ka cika neman faÉ—a ne? Yanzu ina ruwanka da in da zanje?".

Matso da face É—insa dab da tata ya yi kafin ya ce mata. "Saboda haka nake, kuma ai ke da kanki kinsan ni jarumi ne dole na takali faÉ—a dan nasan zan kare kai'na na kuma kwaci kaina".

Cigaba da banka mashi harara ta yi tare da faÉ—in. "Wajen wannan yarinyar zanje".

"Dama ai na sani, kin ɗebo zafinki zaki je ki sauke a kanta ko? To zo mu je ki bani abinci a baki yunwa nake ji ka fin ki dawo ki je ki zalinci ƴar mutane". Yana kai karshen maganar bai bari ta yi magana ba ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa ya nufi downstairs da ita.

Shi fa Ronnie idan ba su Delisha dake cikin Daular black Tiger ba baya kula kowa, a waje cikin birnin ɗaukin ganinsa da ido ma kawai suke yi, bege jin zazzaƙar voice nasa suke yi, saboda kowa yasan shi ne mafi kusanci da black Tiger, black tiger yana kaunarsa kamar me, kowa yana son ganinsa da ido, shi kuwa yana nan yana biyewa su Delisha ko a jikinsa, bai ma san ana haukar son ganinsa a cikin birnin ba. Idan ya fita wajen gasa ya zama cikakken jarumi da babu biyunsa a kaf faɗin birnin, idan kuma ya dawo cikin Daular ka gansa tare da su Delisha sai ya zama kamar na mata wanda bai da karfi ko kaɗan haka yake.

Ɓangaren su Sweetie kuwa

Sosai Floria ta hau lallaɓa Sweetien a kan taci abinci, amma ta kafe a kan ba zata ci ba har sai taga Pretty and Kamran. Da kyar ta iya shawo kanta ta yarda zata ci, sai da ta yi mata karyar gobe da safe za'a kawo mata Pretty and Kamran ɗin nata, sannan ne ta yarda ta ci.

Mandi rice Floria ta zuba mata É—an dai'dai a plate, sannan ta zuba mata watermelon juice a wani haÉ—aÉ—É—en kuma tsadadden cup. ÆŠan kaÉ—an ta ci abincin saboda yunwar ta rigada ta yi mata yawa, kaÉ—an É—in nan da ta ci ma har wani murÉ—awa cikinta yake yi saboda yunwar.

Bayan ta ci ta sha ne Floria ta ce taje ta yi wanka. Ƙasa iya miƙewa ta yi har sai da ta taimaka mata ta riƙeta. Bayan ta miƙema sai da ta taimaka mata izuwa bakin toilet ɗin.

A bakin ta saketa ta juya ta dawo, ta barta da nufin ta ƙarisa shiga cikin toiletɗin, sai kallon ɗakin take yi, komai ya ruɗar da ita, dan Allah yasa tana da nutsuwa sosai ne yasa ta danne tsoronta da kauyancinta haɗe da al'ajabinta tana dai bin ɗakin dakallo, da Pretty ce ai da ta yi masu hauka, dan bata taɓa ganin irin wanna ɗaki ba.

A hankali ta ja kafafunta da suka yi mata nauyi ta ƙarisa shiga cikin toilet ɗin. Tsantsar tsoro ne cike fal a cikin ranta, gani take kamar ɗakinma gabaɗaya zai ruguzo mata a kanta, gani take kamar zata faɗi ƙasa ta ƙasa ganewa. Amma dai ta yi jarumtar danne tsoronta.

Tana shiga cikin toilet ɗin Tv dake manne a bango yana magana ya haukatata. Ga wata kyakkyawar ƴar tsana dake ta kusa da kofar shigowa wadda take amfani da battery ta yi mata welcome ta hanyar furta hakan da turanci. Ƴar tsanan ƴar babbace da zata kusa kaita tsawo, kawai ta ce mata welcome, unexpected ta ji maganar.

Ai a wanna karon tsoron nata yaki dannuwa, da gudun gaske ta juya ta nufo waje tare da kurma ihu wandan sai da ta tsorata Floria tasa ta ta kusa rugawa a guje. Kai tsaye Florian ta nufa tana ihu.

Da yake mutanen birnin Dark World ba dai jarumta ba sai Floria ta tsaya tare da tambayarta me ya faru take wannan ihu.

Ƙasa yin magana ta yi sai nuna mata toilet da hannu take yi tana kuka. Riƙota ta yi, dan ta fahimci Sweetie fa ƴar kauyece bata san komai ba shiyasa ta tsorata. Hakan yasa ta kama hannunta tana gaya mata ta yi shiru ba komai, haka ta rakata har cikin toilet ɗin. Gane cewa bata san komai bane yasa ta tsaya ta hau nunnuna mata abubuwan da yadda zata yi amfani da su.

Ai ina Sweetie ta ce bata san wannan ba, Floria ba zata bar wannan toilet É—in ta barta ita kaÉ—ai a ciki ba, sai dai ta hakura da yin wankan su fita a tare. Da yake suna son ta yi wankan sai Floria É—in ta ce to ta yi wankan bari ta jirata.

Nan ma kuma sai ta maƙe mata kafaɗa a kan a'a ita ba ta yarda ba, ba zata iya cire kaya a gaban kowa ta yi wanka ba, ko da take makauniya idan Pretty ta rakata wajen da zata yi wanka tafiya take yi ta bata waje, dan haka ita ba zata cire kayanta a gaban Floria ba. Nan ta ta fara sakawa Floria ciwon kai, zata fita ta ce ba haka ba, zata zauna nan ma ta ce ba zata cire kaya a gabanta ba, to wani irin masifa ce wannan?.

Dafe kai ta yi tana tunanin ya zata yi da wannan yarinya? Ga shi dai shekarunsu kusan ɗaya, da ƴan watanni ƙalilan Floria zata fita, amma ta kafe ita fa ba zata cire kaya a gabanta ba, abin ya bawa Floria mamaki sosai, dan ita dai tasan a tsakar gida ma mamanta tana yi mata wanka kafin Ronnie ya ɗaukota ya dawo da ita cikin Daular black Tiger, kuma da dawowarta cikin Daular bai wuce 1 year ba, so da girmanta ma a tsakar gida ake yi mata wanka, kowa ya shigo zai ganta kuma ba abin da ya dameta, yau taga sabon salo wajen Sweetie mai kunyar nuna jikinta a gani. Floria fa ba marainiya bace, da mamanta da babanta a raye, kuma suna cikin birnin Dark World, Ronnie ne kawai ya ga ta burgesa ya roƙi alfarman da black Tiger ya sanya a ɗaukota ta dawo cikin Daular da zama, shi ne sanadiyar dawowarta cikin Empire ɗin.

Da kyar da suÉ—in goshi Sweetie ta yarda Floria ta fita ta barta a ciki. A gaggauce ta yi wankar, ruwa ta kwarara kawai, ba wani fitan da ta yi, sam bata yarda ta kunna shower ko wani abin ba, fanfo ta kunna ta tari ruwa a borket É—in da ta gani a cikin toilet É—in, ruwan da sanyi haka ta zuba a jikinta daga kai bata surka da na zafi ba, jikinta duk dauÉ—a, da yake tana tsoro sosai ne yasa ta kwara ruwa bata wanke dauÉ—ar ba ko soso ma bata nema ba.

A gurguje ta sanya kayanta ta fito. Sai muzurai take yi, a tsorace take da komai na É—akin sosai.

A zaune saman gadon ta isko Floria, ganinta yasa ta miƙe ta sauƙo ƙasa tana binta da kallo.
Chapter 36 · 0% Book details