Sashe 48
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai san lokacin da ya ce mata. "Waye kuma ya koya maki É—aga gera É—aya?". "Yah JAISH". Ta bashi amsa bata kawar da kallonta daga kansa ba.
"Kuma ya yi maki kyau sosai". A sanyaye ya faÉ—i hakan.
Mamakin jin abin da ya faɗa ta yi, bai taɓa yi mata magana haka ba, shi daga karɓar umarni sai aiwatarwa ya iya.
"Kin barni? Kin hakura da cire mun hula?". Ya faɗa ƙasa ƙasa. Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata hakura ba idanuta a tsaye kyam a cikin nasa.
"But why?". Yadda ya yi maganar zaka fahimci ya yi nisa, baya tare da ita, da alama ya mance da wanda yake tare magana kawai yake yi.
Mamaki ne ya kara kamata, tunani ta fara yi a kan anya Hoorain ɗinta ne wannan? Guy shiru shiru baya magana, yau tana son ɓata shi da magana, har tunani take yi dama yana magana bayan e da a'a kenan? Yau maganar tasa ma ta musamman yake yinta kamar ba shi ba.
"Hoorain to please meyasa kake ɓuye mun face naka?". Kamar zata saka mashi kuka ta yi maganar. "Babu komai, kawai dai baya a tsarin aiki na ne".
"Tom shikenan sai wace rana zaka nuna mun?". A takaice ya ce mata. "Sai ranar da Abbona ya yarda na yi hakan".
Sai yanzu ta fahimci cewa shi yana aiki ne bisa umarnin babansa, Allah sarki, sai ta ji ya ƙara burgeta, baya son ɓata ran babansa
"Amma kai kyakkyawa ne ko?". Da alama ta mance cewa a jikinsa take kwance. Shi ma da alama ya mance.
"A'a bani da kyau, ai babu wani kyau da kyansa zata yi tasiri a waje idan kina nan". Ya bata amsa yana cigaba da kallon face É—inta, daga karshe ma sai ya sanya hannu yana goge mata hawayen face É—inta na kukan da ta sha.
"Yanzu kana nufin kamar yadda Yah Jaish yake cewa nafi kowa kyau a gidan nan da gaske ne?". Jinjina mata kai ya yi alamar e da gaske ne tare da lumshe idanunsa.
Cool murmushi ta saki wanda ya ƙara mata kyau dimple ɗinta suka lotsa sosai kafin ta ce. "To bari naje naga madubi".
Cikin sauri ya ce "Ai bamu ba fita daga nan sai dare, dan ba hanya". Zaro idanu sosai ta yi har sai da tasa ya kawar da nasa kallon daga kanta. "To ni yanzu me zan ci? And idan uncle na islamiyanmu ya zo karantar da mu ya zan yi? Wanka da sallama dukka a ina zan yi?".
ÆŠan shafa kumatun nata ya yi bayan ya gama goge mata hawayen nata. "Nima ban san me zaki cewa uncle naku ba, amma dai zan nemo maki abin da zaki ci, sannan zaki yi sallah a nan, kamar yadda na gaya maki sai dare zamu fita daga nan to hakan ne, dan dole fita zamu yi a sace ba tare da kowa ya ganmu ba".
Ta fahimci me yake nufi, sai dai tsoro ya kamata, me zata ce wa Mommarta da uncle É—in islamiyarsu and Gimbiya Chuchu, sannan idan Yah Jaish ko Yah Omar suka kira Momma zasu yi waya da ita ya zata yi?.
Katse mata tunanin nata ya yi ta hanyar taɓa mata lips ɗinta a garin shafa kumatunta da yake yi, shi kansa bai san ya yi hakan ba sai da ta zaro ido tana kallonsa ya farga, dan yana shafa kumatun nata ne ya afka duniyar tunani wani abin da bai bayyanar mana ba ya barwa zuciyarsa.
Sorry ya furta mata tare da sauketa daga jikinsa ya miƙe tsaye, sai zogi wajen wannan cizon kunama yake yi mashi. Wucewa ya yi ya nufi wajen bishiyoyin dake wajen dan ya nemi maganin da zai saukaka mashi wannan zogin ya kuma cire dafin kunamar tare da ce mata yana zuwa.
Da kallo ta bishi da shi har ya kurewa ganinta, yana tafiya cike da jarumta sosai. Yana kurewa ganinta ta koma saman sofar ta kwanta tare da lumshe idanu, kafin wani dan lokaci barci ya É—auketa.
Ko da ya dawo sai ya samu ta yi barci. Tsayuwa ya yi ya zuba mata idanu yana ta kallonta, tsabar shagala da kallonta har ya mance da zogin da hannunsa ke yi mashi, hankalinsa ya bar jikinsa.
________________________🔥💘
A can cikin gida kuwa. Wanka Chuchu ta yi ta canza kayan jikinta, kwalliya sosai ta cancaÉ—a, kun san ta da shegen iya kwalliya dama, ta yi kyau sosai cikin riga da wando Pakistan dress, ta yafo gyalen kayan a kanta kamar wata amayar, ga shi kalar kayan pink and black sun yi mata kyau sosai.
Waje ta nufa bayan ta zuba perfume masu kamshi sosai. Room ɗinta ta nufa. Wayarta ta je ta ɗauko, a bakin bed ɗinta ta zauna ta fara lalauɓar number Yah Rizwan, tana kewarsa sosai da sosai.
Bugu ɗaya ya katse kiran ya kirata, shima yana kewarta sosai, sai kiranta yake tun ɗazun bata ɗagawa, yanzu da ya ga call ɗinta ba ƙaramin daɗi ya ji ba, duk da suna tare da Ramish da har yanzu bai motsa ba hakan bai hana shi fitowa waje ya kirata ba, dan yana kewar voice ɗinta sosai.
Hira suka fara yi cikin nishaɗi, rigima ta sanya mashi wai ta yi kewarsa kuma tana son ya zo gaskiya ta ganshi ai dama ya ce mata zai zo, hakuri ya shiga bata tare da gaya mata zuwansu ba zai yiwu ba, sai dai wani lokaci. Sam yaki gaya mata saboda an harbi Ramish da bindiga yasa ba zasu zo ba, sai ya ɓoye mata ya ce mata dai sun fasa zuwa wannan karon sai wani lokacin.
Kuka ta sanya mashi a kan ita lallai tana son ganinsa, shi ma da yake ya iya sai ya sanya mata rigima a kan to su yi video call su ga juna, kukan shagwaɓa ta sanya mashi a kan ita a zahiri take son ganinsa. Sai da ya rarrasheta sannan ya ce mata dole zai zo ko dan aurensu, yana zuwa kuma ba ɓata lokaci za'a ɗaura aurensu ya wuce da ita Dubai, jin hakan ne yasa ta hakura ta dai'na kukan.
Part É—in Akka ta nufa tana tafiya tana waya, a hanya ta ci karo da Gimbiya Fanan. "Chuchu Mammie na kiranki, wai ki zo yanzu". Cewar Fanan É—in.
"To Aunty Fanan ina nan zuwa yanzu bari na gaishe da Akka tun safe bamu gaisa ba". Da okey Fanan ta amsa mata tare da wucewa room ɗin Momma......... Hmmm Fanan tana son zuwa part ɗin Momma, kuma Mammien ɗin tasu ce ta ce ta rinƙa zuwa dan ta rinƙa yi wa Momma abun kirki tana nuna mata halin kirki ta yadda ko sun samu sun shawo kan Jaish ya yarda zai aureta kada Momma taki yarda, kunga Mammie ta yi dabara, Momma zata ce Fanan yarinyar kirkice mai kyan zuciya, a wayo zasu saye zuciyar Momma, amma kam Mammie ta iya basaja.
Amma my people's me kuke tunani game da kiran da Mammien ta yi wa Chuchun? Menzata ce mata?.................
____________________🔥💘
NIGERIA...............JIMETA 🔥💘
Har dare can wuraren 9 bappa yaga su Mahreen basu dawo ba, ya san dai basa kwana a gidan ArÉ—o, kome za'ayi masu basa yarda su kwana, dan bai koya masu hakan ba.
Shi kuwa Jaish tun da ya buÉ—e idanu ya sake rufewa bai sake buÉ—ewa ba, wannan abokin bappan shi ma ya bada nashi gudumawar magungunar kafin ya wuce nasa gidan.
Bappa bayan son fita ya bar Jaish ɗin shi kaɗai, dan haka sai ya leƙa waje ya kira wani matashi dake zaune cikin matasan da suke kofar gidan suna hira. Ko da matashin ya zo sai ya ce mashi jeka gidan Arɗo ka kira mun su Mahreen, and ku taho tare fa.
Da to matashin ya amsa sannan ya wuce. Shi kuma Bappan ya koma cikin gida, ya É—auki abincinsa da Mahnoor ta zuba mashi a kwanonsa ya zauna kusa da Jaish É—in ya fara ci.
Wannan matashi kuwa ko da ya je Mahnoor dai ta ce yau a gidan ArÉ—o zata kwana saboda tsoron aljani Jaish, Mahreeh kuwa da yake bata da wani tsoro, dama yadda Jaish É—in ya waro idanunsa ne yasa ta tsorata sosai, hakan yasa ta bi bayan matashin suka komo gida, in takaice maku ma Mahreen kam ta mance ma da idanun Jaish sun bata tsoro, tuni ta shiga shargallen duniya.
Tana shiga É—akin Bappan ta hau gaya mashi É—azun aljanin nan da ya kawo ya buÉ—e idanu, ba ko sallama fa ta fara bashi labari, shi kam matashin nan ya juya ya koma abinsa.
Mamaki ne ya kama bappa a in da ya ce. "Mahreen kema yanzu kin yarda wannan bawan Allahn aljani ne? Kece kaÉ—ai dama a kauyen nan baki yarda da cewa aljani bane, ko bappa geÉ—e da ya zo yanzu ya duba shi shi ma ya tsorata da ganinsa, ya dai daure ne kawai ya yi mashi magani, amma ya tsorata da ganinsa"
Zama ta yi tare da sanya hannu suka fara cin girkin Mahnoor a tare. "Bappa aljani ne nima na yarda, saboda idanunsa wlh sun kai ukun na Adda Mahnoor da ya buɗesu, suna da girma sosai gasu jajir kamar jini, amma fa ni bana tsoronsa koma aljanin ne, ai ina da karfi, kuma wlh ko aljani ne sai na taɓa kumatunsa, yanzu ma bari mu gama cin abinci nazo na taɓa, ni inaruwa ya je ya yi ta aljanancinsa a can ni dai kumatunsa yana mun daɗin taɓawa, amma bappa wai daman menene aikin aljani ne da kowa yake tsoronsa?". Ta kai karshen maganar tare da ɗage kai sama kamar mai tunanin wani abin, irin bari ta tuna wai shin menene ma aljanin?...... Mahreen manyan ƙasa, wato ita fa dama bata ma san meyasa ake gudun aljani ba, in fact bama tasan me aljani yake nufi ba, wato dai ko Jaish aljani ne sai ta taɓa kumatunsa, gaskiya justice for kumatun Jaish, ya shiga uku da Mahreen, kai wannan yarinya sai shirin Allah.
"Mahreen É—in Bappanta, babu abin da aljani yake yi, kawai dai mutane ne suke tsaronsu, ina Mahnoor take? Taki shigowa saboda tsoron bakon nawa ko?". Cewar Bappa kwairaga.