Sashe 168
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mahreen ce ta ce. "To ki zuba mana ni da Hamma mu ci a tare, yunwa nake ji".
Wani irin faɗuwar gaba ta ji lokacin da ta ji Mahreen ta faɗi hakan, domin kuwa cin abinci a tare da shi yana ɗaya daga cikin shawarin da Jumma bata, ta ce mata ta rinƙa ci a tare da shi, cin abincinsu kwano guda zai sa su kara jin kaunar juna sosai da sosai, yana kara dankon soyayya......... Ni kuwa nace ashe Jumma ma hegiya ce tasan kauna, a lallai zuwanta birni ya yi amfani........😂
"A'a Mahreen zan saka maki naki ke kaɗai dai ni kuma zanci a tare da Hamma". Ta yi maganar tana kara yin ƙasa da kai sosai, sam bata fatan yau su sake haɗa ido, saboda kunyarsa kamar zata nutse cikin ƙasa.
Turo baki hajiya Mahreen tamu ta zamani ta yi kafin ta ce. "Wato dan mijinki ne shi ne zaki ce ke zaki ci tare da shi ko? Tom shikenan ni ma nawa mijin zai zo, kuma kema ba zaki ci a tare da mijina ba".
Aka ce kuruci dangin hauka, to idan ba hauka ba ina ruwan Mahnoor da wani cin abinci da mijinki, ita fa bama ta san me ma'anar mijin ba, ita dai kawai ace mata ana biki a saki kiɗa ta ci uwar sabada da rawa ta sani, shikenan abin da ta ɗauki aure kenan, hmmmm kila da ta san menene auren bazata ce mijinta yana nan zuwa ba, ko daga ina zai zo? Ni dai da bappa zai bi shawarata da ya haɗa ƴar ƙaniya aure da Hamma Faisal, su je can su kashe kansu in sun gadama, idan ya bata baby ai zata nutsu ne, haba yarinyar ce sai iya tsaro maganar da ita kanta bata san ma ina ya dosa ba, kawai a kwasosa a sharɓa.
Tabbas Jaish ya yi mamakin jin abin da ta faɗa, saboda yasan halinta da shegen kunya kamar dai shi ɗin, dik da baya a cikin hayyacinsa kaifin ƙwaƙwalwarsa tana nan, hakan yasa ya fahimci wannan magana da ta yi tabbas watace ta koya mata, dan ita bata da kwarin gwiwar cewa zata ci abinci a tare da shi.
Taki ɗago kai tasa hannu ta buɗe kular, ta zubawa Mahreen nata daban ta zuba masu nasu su biyu, ta matso mashi da shi gabansa, ta miƙawa Mahreen kuma nata, ta rufe sauran na bappa ne, kuma baya nan, dan haka sai ta rufe mashi ta matsar gefe guda.
Sai kuma me? Ai kasa motsawa daga in da take ta yi bare ma ta matso su ci abincin a tare, shi kuwa ya zuba ido yana son ganin zata iya hakan ne ko dai da gaske wata ce ta tsara mata maganar ba daga bakinta ya fito ba.
Mahreen kam tuni ta ja abincinta ta fara kaiwa baki, dama yunwa take ji, dan haka hannu baka hannu kwarya ta fara yi.
Shiru shiru har almost 10 mins tana tsugunne a wajen bata motsa ba, shi ma kuma bai motsa ba, bai fara cin abincin ba, yana ta kallonta kawai, ga Mahreen har ta kusa cinyewa, sun yi sa'a Mahreen idan tana cin abinci bata kula kowane, da sun sha mamakin abin da zata yi masu, ina ga da sai ta ciyar da su a baki ma, sa'ansu dai ba ruwanta da kowa idan ga abinci a waje, hankalinta gushewa yake yi nake gaya maku, bare ma idan abincin ya ji man shanu, habawa, girkin Adda Mahnoor ba wasa ba jama'a, shiyasa Jaish yake iya cin abincin nasu, dan fa Mahnoor ta kware a girki, so Mahreen tana tafiya dubiyar santi ne idan tana ci, kai har wani lumshe idanu fa take yi abinta.......😂
Ganin kai ba zata iya cin abincin a tare da shi bane yasa ta yunkura zata miƙe ta gudu ta bar wajen.
Cap ya kai hannu ya capko nata hannun, hakan kuma ya yi dai'dai da Æ´ar karar da ta saki sakamakon yunkurawa da gudu da ta yi yasa ta fama ciwon da ta ji shekaran jiya da kwalba.
Jini wajen ya fara yi. Ganin jinin yasa ya miƙe tsaye daga zaunen da yake, ya saki hannun nata tare da riƙo shoulder ɗinta.
A saman tabarman ya zaunar da ita, sai ya É—an tsugunna a gabanta wajen kafafun nata. Slippers É—in kafarta ya cire, ta taka kan yatsun nata ne yasa ciwon ya buÉ—e, dama ya É—an haÉ—e, ya buÉ—e kuma ai kunga dole jini ya zuba.
"Da kika tashi zaki gudu ina zaki je?". Ya jefa mata tambayar yana É—auko ruwa a galon wanda bappa yake ajiyewa a wajen dan shan su.
Tana ciza laɓɓanta saboda zafi ta ce. "Babu". Idanunta sun cika da kwallah.
Bai sake tanka mata ba ya wanke mata kafar tas, sanan ya koma wajen zamansa ya zauna, ya janyo abincin ya fara ci.
Shiru ta É—an yi tana tunanin meyakamata ta yi? Anya zata iya bin shawarin Jumma kuwa?.
"Juyo ki sa hannu muci". Muryarsa ta katse mata tunanin da take yi. A miliyan ta zaro idanunta waje, ko me ta tuna kuma sai ta É—an saisaita nutsuwarta.
A hankali ta juyo kanta a kasa, tamkar kasa ta shage ta shige ciki haka take ji a lokacin da ta kai hannunta cikin kwanon.
Da kyar ta iya fara cin abincin, a lokacin ita kuma Mahreen ta gama cin nata ta miƙe tsaye, tana wani gyatsa ta nufi rafi dan ta wanke kwanon nata ta sha ruwa mai sanyi, bata son shan wanda bappa yake ajiye masu.
Shi kansa Jaish ɗin kunyar cin abinci a tare da ita yake yi, amma haka kawai ya ji yana sha'awar su ci taren, ba komai ne yasa hakan ba kuma face nunawa da ta yi tana son ci a tare da shi, yana tausayinta matuƙa shiyasa yake son abin da take so, dan ta yi farinciki yasa ya danne kunyar tasa suka fara cin abincin a tare.
Sun yi nisa cikin ci babu wanda ya ce da wani uppan, babu kuma wanda ya iya É—ago idanu ya kalli É—an uwansa, haka kaman wasu kurame kuma makafi suke cin abincin, ba zato ba tsammani kwatsam sukaga bappa yana tunkaro in da suke.
Ai a fujaje har suna rige rigen cire hannun daga cikin kwanon, abin nasu ma gwanin ban dariya, dik suna tsananin kunyar bappan ne.
Da sauri Jaish ya miƙe ya bar wajen, ya bi ta bayan itacen da suke karkashin nasa. Sarai bappan ya gansu, tun daga nesa ya hangosu, su kuma basu gansa ba sai da ya iso kusa, amma sai ya yi kamar bai gani ba, da ya ƙariso wajen ma har da tambayarta ina hammansu ya yi? Irin shi bai gansun nan ba.
Kanta a ƙasa ta ce ya tafi yanzun nan, kamar bappan zai ce mata to ta ƙarisar da cin abincin mana, sai kuma ya fasa ya ce ta zuba mashi nasa. Bayason tasan ya gansu ne.
A hanzarce ta zuba mashi ta miƙa mashi.
"To ku koma gida kinga ke Mahnoor bai kamata ma ki fito ba, ban ma san me ya kawoki ba! Ki tashi ku koma ke da Mahreen, ita ta shirya ta tafi islamiyya idan lokacin ya yi, ke kuma ki yi zamanki a gida ko nan da kofar gida kada ki sake takawa". Cewar bappa da ya wanke hannu zai fara cin abincinsa kenan.
Kai a ƙasa ta amsa da to, sannan ta miƙe tana ɗan ɗingisa kafa ta nufi wajen rafi.
Nan ta isko Mahreen tana aikin shirirta, wato wasa da ruwa, kiranta ta yi a kan ta zo su tafi.
Da sauri ta fito suka nufi hanyar gida Mahnoor É—in tana gaya mata bappa ya ce kada ta je islamiya yau. Suna tafiya suna hira gwanin birgewa.
Abin mamaki baya karewa, suna isa gida suka isko Nenne ta dawo, Arɗo ne ya ce ta wuce ta koma gidanta, kuma ita ma izuwa yanzu ta yarda Jaish mutun ne ba aljani ba tun da aka aura mashi Mahnoor bai yi mata komai ba, sai dai ni princess Teema ban yarda da dawowan nan nata ba, ban yarda ta tuba ba, munahika da walaƙin goro a miya, sun kullah wani abin ne idan aka bibiya.
Ga mamakinsu kuma shi ne yadda Nenne bata kulasu ba, bata ce masu ko sannu ba, suka zauna a tsakar gida suka sha hiransu har la'asar, sannan suka É—aura ruwan wanka a wuta, Mahreen ta fara yin wanka ta je ta yi shirin tafiya islamiyya, ita kuma Mahnoor sai ta sake É—aura wani ruwan bayan ta juyewa Mahreen É—in.
Nenne kuma ta fito ta shiga maƙota, dama shegen kafar gantali gareta, bata son zama waje guda.
Sallah Mahreen ta yi lokacin da ta gama shirin nata, sannan ta fito riƙe da Alqur'aninta hizbu 10, a lokacin Mahnoor ta fito daga wanka ta zauna saman dutse zata yi alwala.
"Adda Mahnoor na tafi islamiyya". Cewar Mahreen.
"Tom sai kin dawo". Ta bata amsa tana fara alwalar.
Da to ta amsa mata sannan ta wuce. Ita kuma ta É—auro alwalar sai ta shiga kitchen, ta É—aura tukunya a kan wuta tasa ruwa fin rabi, a cewarta ta É—aurawa Jaish da bappa ruwan wanka idan suka dawo, sannan ta wuce ta nufi É—akinta dan ta shirya ta yi sallah.
Tana shiga kai tsaye wajen kwallar kayanta ta nufa, hijabin jikinta ta fara cirewa ta ajiye a gefe, daga ita sai ɗaurin kirji, ta ciro ɗayan dogon rigarta wannan yellown kenan, ta ɗauko ɗan kwandon kayan kwalliyarta da zata ɗan yi, ta ɗauki pant haɗe da wani hijabin, ta dai haɗa dik abin da zata buƙata, tana juyowa da nufin ta je bakin mattress ɗinsu ta zauna ta yi kwalliya ta shirya kenan suka yi ido huɗu da shi, yana kwance a saman mattress ɗin yana kallonta dik abin da take yi, tun lokacin da bappa ya zo gona ya samesu suna cin abinci da ya bar wajen gida ya dawo, shi ne ma yasa kuka ga Nenne bata kulasu ba, dan tasan yana cikin ɗakin yana kwance, in ta yi mata wani abin zai ji, kuma tsoronsa take ji sosai, ita kuma Mahnoor da ta shigo sam bata lura da shi a ɗakin ba.