← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 211

Sashe 198

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ya sauke alamar ya ji daÉ—in murmushi nata, sannan ya yi continue take his coffee. Kasa ta É—an yi da kai tana jin zuciyarta ya É—an sanyaya. Ga dikkan alamu ba iya Jaish bane yake da kunya a Æ´aÆ´an King, har da Aunty MieMie ma tana da shi, dik yadda aka yi tsakanin Akka da King Abdul Malik akwai wanda kunya take yawo a jinin jikinsa, sai dai idan da ga baya ya yaye kunyar ya jefar saboda yanayin rayuwa, to kun san idan abu tun ainahi a jininka yake ko ka yayesa ka jefar dole a jininka asamu masu gado, ga dai Jaish da Aunty MieMie sun yi gadon kunya.

Ramish ne ya shigo cikin room ɗin bakinsa ɗauke da ɗan siririn sallama ƙasa ƙasa. Har suna haɗa baki ita da King wajen amsa mashi sallamar. Yanzu tashinsa daga barci ya yi wanka kenan ya nufo wajen daddyn nasa, dan fa bashi da burin da ya wuce ya gansa a tare da mahaifinsa, dan suna jimawa basu haɗuwa sai dai a video call.

Gefen bed É—in ya zauna yana faÉ—in. "Good morning our dad".

Kallon tsab Aunty MieMie ta yi mashi tun daga kan arab hairnsa har izuwa kan kyawawa kafafunsa, sanye yake da white arabs jallabiya mai bala'in kyau, sai ya yi wa kayan kyau over kamar dan shi aka yi jallabiyas, ga arabs hairnsa da ta sha gyara matuƙa, sai tashin daddaɗar kamshi yake yi.

"Big bro good morning". Aunty MieMie ta faÉ—a cikin zolaya tana É—an murmushi.

King ne ya amsa da. "Morning my son how was your night?".

Alhamdulillah ya amsa da shi sannan ya dubi Aunty MieMie ya ce. "Morning big Aunty".

Harara ta É—an watsa mashi kafin ta ce. "Kai baka ji kunyar haÉ—a ido da ni ba ko?".

"For what kuma kunyar?". Ya faÉ—a idanunsa a kanta babu ko gezau, da alama dai babu wanann kunyar a tattare da shi.

"Tun yaushe kake cikin gidan nan da ba ka nemi in da nake ba? Sannan kace baka ji kunyar haÉ—a ido da ni ba? And last two months na je Dubai baka nan i know they told u, kuma baka kirani ba, ka fa yi mun laifuka dayawa". Ta kai karshen maganar tana É—aure fuska irin ba da wasa take yi ba.

Ɗan shafa Arabs hairnsa ya yi ya ɗan yi shiru yana tuna ta yadda zai tsarata su rabu lafiya, yasan dik cikin ƴan uwansu babu wanda ya kai Aunty MieMie and uncle Abbas tsananin madarar kaunarsu kauna ta haƙiƙa, haka kawai zata tashi ta ɗaga jirgi ta nufi Dubai dan kawai ta je ta gansu face to face ba a video call ba, haka shi ma uncle Abbas yake ɗaga jirgi ya je wajensu, so ba zai so ace ya ɓatawa su biyun nan rai ba.

"Don't think anything da zaka wanke kanka, dan ba wani excuse da zan yi accepting, see ur big eyes a wajen". Ta faÉ—a tana harararsa.

Hannu ya kai ya karɓi cup na coffee da dad yake sha ya ɗan kai saitin bakinsa ya yi sipping, dara daran idanun nan nasa a kanta ya rasa abin cewa, ta riga ta ganosa.

King ne ya ce. "Idan ya zo part É—inki sai ki titsiyesa dan kun fi kusa, now dai gaya mun damuwarki, dan shi ne a cikin rai'na, ko dai son ya fita ya bamu waje ne".

Kawar da kallonta daga kan Ramish ta yi izuwa kan dad É—in, a sanyayye ta ce. "Ya fita kuma dad?".

Kai King ya gyaɗa alamar e. Girgiza kai ta yi kafin ta ce. "A'a ai babu wani abin da zan iya ɓoyewa our big bro, so na ma ji daɗin zuwansa saboda zai tayani fighting a kan abin da na zo nema".

"Aunty MieMie karfi da ya ji fa kin mayar da ni babba ko?". Ramish ya faÉ—a idanunsa a kanta.

Siririn murmushi ta saki tana faÉ—in. "To ai dik in da namiji yake shi ne babba, na baka girman ne, ni yanzu ma harta Jaish ni kanwarsa ce".

Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya sake furta uppan ba, dan yanzu ma idan ba ita da King ba ko uncle Abbas baya hira da shi haka, gara ma Bilal idan tsiyar Bilal É—in ta motso yana sanya shi biye mashi su É—an yi hira, amma ko da Dr Raj baya maganar wuce 1 mins, sai dai ya yi shiru yana sauraronsu idan suna hira da su Rizwan, ba zai dai yi magana ba, amma zai saurari dik abin da suke faÉ—e.

"Okey to faÉ—a mun menene yake damunki da har kike fatan É—an uwanki ya tayaki faÉ—a a kai'na?". Cewar King.

ÆŠan gyaran murya ta É—an yi haÉ—e da gyara zamanta kafin ta fara magana a nutse kamar haka. "Dad dama magana ce a kan Jannat da Jawad, wlh dad ba Rizwan ne yake son Jannat ba, Jawad ne yake sonta, ni shaida ce a kan hakan, dad please ka fahimceni kuma ka fahimcesu, kasan da cewa saboda auren Jannat da ka bawa Rizwan shi ya kwantar da Jawad ciwo?"

"What!!". King ya faÉ—a yana zaro idanu, dan shi kanshi ya yi zargin hakan, ganin bashi da wata hujja yasa ya watsar da batun, bugu da kari shi fa dama Jawad yake son bawa Æ´ar tasa ba Rizwan ba, amma amsawa da Chuchu ta yi da bakinta cewa Rizwan take so ba Jawad bane yasa ya ja baya da kudurin nasa, idan baku manta ba akwai ranar da ya cewa Jawad tun da ba zaka gaya mun gaskiya ba nasan maganinka, da safe zan É—auki mataki, to dama niyarsa a wannan lokaci da safe ya samu Akka da batun haÉ—a Jawad da Chuchu aure ne, sai wani abin ya É—auke mashi hankali har Rizwan ya rigasa.

___________________________🌹

"Kwarai dad, saboda Jannat Jawad yake kwance rai a hannun Allah a yanzu, ita kanta Jannat É—in ba lafiya ce da ita ba, tun around karfe 7 take part É—ina, ta tasani a gaba sai kuka take yi mun, na yi maganar duniyar nan amma taki amsani, idan na matsa mata sai ta ce mun Jawad É—inta har yanzu bai tashi ba, shi ne kawai abin da take iya faÉ—a, dan Allah dad ka duba wannan lamari da kyau, ka kallesu da idanun basira dikkansu, kada mu yi abin da daga baya zamu yi danasani". A marairace ta kai karshen maganar, alamar damuwa sosai ne ya kara bayyana a saman face É—inta.

Zuba masu idanu Ramish ya yi yana ta kallonta ita da King É—in dikka bai furta uppan ba, yana dai shan coffee É—insa a hankali hankali.

"Amma Daughter how comes hakan zai kasance?". King ya tambaya.

"Dad i don't know nima, what i know here's Jannat Jawad take so, and shi ma Jawad Jannat yake so".

"No daughter, in kin ce Jawad yana son Jannat ba zan musa maki na, saboda nima ina zargin hakan, amma ki ce mun Jannat tana son Jawad ba zan yarda da wannan ba, saboda baki da baki ni da ita na tambayeta tsananin Rizwan and Jawad waye take so ta ce mun Rizwan, maybe saboda shakuwar dake tsakaninsu ita da Jawad ne yasa take kukan ciwon nasa".

Shiru Aunty MieMie ta ɗan yi kamar mai nazarin wani abin, can kuma sai ta ce. "Okey dad, amma ina ganin ka duba lamarin Jawad ɗin, ka bashi aurenta tun da kaga saboda sonta ya faɗa cikin wannan hali". Jiki a mace ta yi wannan magana, dan bata taɓa tsammanin Chuchu Rizwan take so ba Jawad ba, abin ya ɗaure mata kai ita ma, bata yi tunanin Rizwan Chuchu ta zaɓa ta bar Jawad ba, da tasan haka ne ba zata tinkari King da zancen nasu ba. Ita ma dai Aunty MieMie an ruɗar da ita, kanta ya shiga duhu, a gaskiya Mammie hegiya ce, ji ta ruɗa mutane cikin ƙanƙanin lokaci!.

"Kin zaɓi na yi wa Jannat aure da wanda bashi ne a ranta ba? Wanda ba shi ta zaɓa take so ba? Na ɗauketa na bawa wani dan shi yana sonta? Shi Rizwan ɗin ce maki aka yi baya sonta? Ko shi ba mutum bane?". King ne ya jera mata waɗan nan tambayoyi masu wuyar amsawar.

Shi dai Ramish ko uppan bai ce ba amma idanunsa a kansu.

King ya ɗaureta da tambaya, a nan ta rasa amsa gaskiya, saboda ba ta yadda za'ayi ta amsa magana ɗaya daga ciki, haƙiƙa ba zata so kanwarta ta auri wanda ba shi ta zaɓa ba, baka san cikin zuciyar bawa ba, watakila da gaske shakuwa ce tasa Jannat take yi wa Jawad kuka, watakila da gaske ba son Jawad ɗin take yi ba Rizwan take so, so idan ta matsa a bawa Jawad aurenta ya zamana Rizwan take so kunga da waye zata yi kuka? Ai kunga da Aunty MieMie zata yi kuka ko? Sannan kuma uncle Abbas ya tabbatar mata shi ma Rizwan yana son Chuchu sosai, kuma King ya karyar mata da zuciya a lokacin da ya ce shi Rizwan ɗin ba mutun bane. Babbar magana! Ruɗu iya ruɗu sun shiga!.

"Daughter ina son ki sani shaƙuwa tasa Jannat yi wa Jawad kuka ba komai ba, ita Rizwan take so, kuma idan kin bibiya ma ita bata taɓa sanin cewa Jawad yana sonta ba, dik laifin Jawad ɗin ne da ya yi nauyin bakin kin gaya mana tun wuri yana sonta, dan haka dole ya karɓi kaddararsa ya hakuri da Jannat, ina son yanzu idan kin fita ki faɗawa mommarku nace ta shirya Aneesa gobe a tare za'a ɗaura auren Jawad da Aneesa danasu Rizwan, na bashi Aneesa a madadin Jannat tun da ya yi nauyin bakin faɗa mana gaskiya".

ÆŠan zaro idanu waje Aunty MieMie ta yi, cike da damuwa da tashin hankali ta ce. "Dad, ka bawa Jawad Aneesa kuma?".

Kai ya jinjina mata kafin ya ce. "Ko Jannat da Aneesa suna da banbanci ne?".
Chapter 198 · 0% Book details