← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 211

Sashe 206

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kun san idan ana biki a waje ana samun damarmaki daban daban, ina ga shi ne yasa ya yi amfani da wannan dama domin ya yi abin da zai yi kunga ba za'a zargesa ba, za'ace akwai baki sabbin fuska da suka zo sai dai in a cikinsu ne wani mugun ya aikata hakan, kunga shi ba za'a zargesa ba saboda ya jima a cikin kingdom ɗin bai taɓa nuna wani mugun hali ba, shiyasa yake son yi wa ƴaƴan King ɗauki ɗaiɗai kenan? Tab akwai matsala kuwa.

Ajiye wayar ta yi tana tunanin meyasa Auta zata ce su haÉ—u a wannan waje? Ita dai tasan wannan fili sam mutane basa zuwa wajen, to me ya kai Auta can?. Ta jefawa kanta tambaya.

Da farko kamar ba zata je ba, sai kuma ta tuna Autar tana jiranta a can, dan haka sai ta miƙe zaune tare da zuro kafafunta kasan gadon ta miƙe tsaye, jiki ba kwari ta ɗauki wayarta ta nufi waje.

Tab zata fita part É—in Akka kira ya shigo cikin wayar tata, har lokacin bata daina kwallah ba, daga ita sai kayan barci daren jiya a jikinta, ko wanka taki yi, da Auntynsu Jawad ta matsa mata da tazo ta yi mata wanka ne ma ta gudo part É—in Akka ta kwanta ta cigaba da rera kukanta, silk scarves ne É—aure a kanta, ta rufe arabs hairnta da ya sha gyara sosai.

Wani irin dum dum ta ji zuciyarta ya buga a lokacin da taga sunan my melody a saman screen É—in wayar yana yawo, Yah Jawad É—inta kenan. Zaro idanu ta yi, jikinta na kerma ta yi picking call É—in tare da kara wayar a kunnenta.

Kasa yin magana ya yi yana daga zaune a bakin bed É—insa, dik ya rame bawan Allah, sai ido gulu gulu farare tas zaka gani.

Kuka mai sauti ne ya kwace mata jin yaki ya yi magana, cikin kuka ta ce. "Yah Jawad ka yi magana dan Allah".

Shiru bai iya furta uppan ba, sai ma kara shiga tashin hankali da ya yi na jin tana kuka, yana son ya ce mata tazo ya ganta amma ya kasa iya buÉ—e baki, tongue É—insa ta yi mashi wani irin tsananin nauyin gaske.

A karo na biyu ta sake cewa. "Yah Jawad dan girman Allah ka yi magana ka ji?".

Nan ma dai shiru bai motsa ba, jin ba zai iya jurar sauraron kukanta ba ga shi ya kasa yin magana ne yasa ya katse kiran tare da yin jifa da wayar gefe guda, idanunsa sun cika da zafafan hawaye sosai.

Ai tana jin ya katse kiran ta watsa a guje ta nufi part É—insa, ta fasa zuwa su haÉ—u da Autar da mu munsa ba ita bace dan bata raye.

Akka ta je ya kira uncle Abbas dan ya zo ya rarrashinta, sai suka zo suka tarar da bata nan, zama Akka ta yi tana mitan yaran zamani da iyashege suke, shi kuma uncle Abbas ya juya ya koma wajen jama'arsu.

Ko sallama babu tana kuka ta afka cikin part É—in nasa, still dai waÉ—an nan kuyangu masu yi mashi hidima ne kaÉ—ai a cikin parlourn nasa, bata bi ta kan kowa ba ta afka cikin bedroom É—in.

Tana turo kofa ta afaka ciki, sai ta tsaya a bakin kofar ta ciki tana haki sama sama idanunta a kansa.

Miƙewa tsaye ya yi na ganin da ya yi, idanunsa shi ma a kanta amma ya kasa yin magana har lokacin, ya kuma kasa takawa izuwa in da take. Sai ya tsaya kawai bawan Allah.

Da gudu ta watsa ta je ta faɗa jikinsa tana sakin kuka mai sautin gaske. Rungumeta sosai ya yi tamkar zai mayar da ita cikin jikinsa gabaɗaya, sai a lokacin shi ma kwallar da suka cika mashi idanu suka samu damar zubowa, wani irin raɗaɗi suke ji a cikin zuƙatansu.

Cikin kuka ta fara faÉ—in. "Yah Jawad meyasa zaka bari a rabani da kai? Meyasa baka gayawa dad ba zamu iya rabuwa ba? Meyasa ka yi shiru? Ni ba zan iya zama da kowa ba sai kai? Ba zan iya rayuwa da kowa ba sai kai? Dan Allah kacewa dad ya warware aurenmu da Yah Rizwan dan bana sonsa, Aunty Fanan ta ce mun an É—aura!".

Can ƙasan maƙoshinsa da kyar, voice ɗinsa sam bata fita ya furta. "Amma Jannat kece kika cewa dad Yah Rizwan kike so ba ni ba! Meyasa zaki yi mun haka? Meyasa kin san Yah Rizwan kike so tun farko baki sanar da ni shi kike so ba ni ba? Meyasa kika bari nayi zurfi a sonki? Ko so kike yi ki kashe ni ne? Kin san me nike ji kuwa? Kin san ya zuciyata take a yanzu kuwa, tamkar ana gasa mun zuciyata da wuta haka nike ji Jannat..........."

Kasa iya cigaba da maganar ya yi a in da ya dakata yana wani irin jan numfashi mai ban tausayi.

"Yah Jawad nasan kai ne kaɗai zaka yarda da ni, na gayawa su Aunty MieMie dukkansu cewa bani nacewa daddy ina son Yah Rizwan ba amma sunki yarda dani, har cewa suka yi daddyn zai yi musu karya ne? Wlh ni ban ce ina son Yah Rizwan ba, kai nike so, ni dai nasan daddy ya kirani, kuma na amsa kiransa na je, tabbas kuma naga Yah Rizwan a wajen, ban san me suka tattauna ba, ni dai sai ji na yi daddy ya ce to in tashi in tafi ya ji zaɓina, kamar zan ce mashi wani zaɓi sai kuma na yi shiru, dan Allah kar ka gaza yarda da ni ka ji?".

Tana magana tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Kasa iya magana ya yi, sai kawai ya kara rungumeta sosai ya yi shiru, tabbas har cikin zuciyarsa ya yarda da ita, dan bata yi mashi karya, sai dai kuma tambayar da yake yi wa kansa a nan shi ne ya aka yi su dad zasu ce ita ta amsa masu da bakinta cewar Rizwan take so? Abin akwai ɗaure kai matuƙa wlh.

A hankali aka turo kofar É—akin, a tsorace gabaÉ—ayansu biyu suka kai kallonsu wajen. Ai Chuchu bata san lokacin da ta saki Jawad tana zaro idanu ba, ganin wanda ya shigo cikin É—akin ya É—aga hankalinta, shi kansa Jawad É—in zaro idanu waje ya yi ga hawaye ya wanke dikka fuskokin masoyan biyu.

Mekuke tunanin zai faru my people's, waye kuke tunanin ya shigo ya samesu a haka? Ya kuke tunanin family zasu yi a lokacin da zasu farga ankashe Auta bata a tare da su? Waye kuke tunanin zai kasance Hoorain? Shin fansa yazo É—auka ne ko dai menene? Meyasa ya kashe Auta?. Mu je dai zuwa, yanzu wasan zai fara fa, ku gyara zama.

_________________🌹💘_____________

Busoshin yaki da ake bugawa ne ya karaɗe ko'ina a cikin kingdom ɗin, nan take hankulan al'umma ya tashi, ga jama'a sosai da suka zo biki, babu wanda ya shiryawa yaki dan basu yi tunanin za'a kawo masu hari ba, ba su shriya yaki ba hakan ba ƙaramin ɗaga hankulansu ya yi ba.

Mayakan cikin Kingdom É—in ne gabaÉ—aya suka fara gudu suna haÉ—a kan al'umma waje guda dan kada a samu asaran rayuka sosai.

Dama a sama wajen bakin gate na farko akwai wasu warriors guda huɗu da suke zama a round wall dake wajen, can sama suke, aikinsu kawai dubawa da camera suga menene yake kusanto masarautar, so sune suke bada masaniya idan sunga zugan mayakan wata masarauta ta dinfarosu, suna bada masaniya kuma warriors masu kula da wajen busoshin yaki zasu bawa na ƙasa dasu umarnin da su buga bososhin domin kowa yasan halin da ake ci, dik wanda ya ji wannan kara fa to yasan babu zaman lafiya, wannan shi ne.

Waye kuke tunanin ya kawowa kingdom of power hari ana tsaka da biki basu shriya ba? Shin evil kingdom ne? Or kingdom of justice su Queen Zarina kenan? Ko dai mai gayya mai aiki ne wato babban hege Black Tiger? Waye daga cikin waɗan nan? Gaskiya in dai black world ne to suka kawo wannan hari fa sai dai muce Allah ya jiƙan kingdom of power ya kwacesu, dan bana jin ko sun shriya zasu iya kwatar kansu a hannun Black Tiger bare kuma basu shirya ba basu san da yakin ba.

To koma dai me ina yiwa kingdom of power fatan alkhairi tare da fatan nasara. Mu damalmale daku a asibiti Kasar Nigeria garin Abuja wajen Khadija mu leƙo meyake wakana kafin mu dawo muga wannan zazzafar cakwakiyar.

_________________🌹💘______________

NIGERIA..............ABUJA🌹💘

Naƙuda gadan gadan ne ya tasanwa Khadija, tamkar zata haihu a cikin wannan keken napep ɗin, da kyar suka iya karisawa asibitin.

Cikin gaggawa nurse suka karɓeta, tamkar sun san wannan mata, dan cikin mutunci suka tarbesu. Kai tsaye labour room aka wuce da Khadija da bata san in da kanta yake ba.

Zee da Auntynsu ne suka tsaya a bakin labour room É—in suna ta kai koma haÉ—e da yi wa Khadijah addu'ar sauka lafiya.

"Zainab tashin hankali yasa mun manta bamu taho da kaya ba, ko zani bamu É—auko ba, dama kinga bamu bawa mai wannan keken napep É—in kuÉ—insa ba, dan haka ki je ya mayar dake gida ya É—auko akwatin kayanku dan bamu san tsawon lokacin da zamu É—auka a nan na".

Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce. "Kenan in tafi in bar Æ´ar uwata ita kaÉ—ai a nan?". Cike da damuwa sosai a tattare da ita ta yi maganar.

"Ban gane ki tafi ki bar ƴar uwarki ita kaɗai ba? Ni ba mutun bace ko so kike ki nunawa jama'a bani da wata alaƙa daku?". Cikin ɓacin rai ta yi maganar, da alama maganganun Zee sun sosa ranta.

Kai Zee ta girgiza alamar a'a kafin ta ce. "Allah ya baki hakuri Aunty ni ba haka nike nufi ba, bari na je to".

Jinjina mata kai kawai Auntyn ta yi. A ruɗe take baiwar Allah har ta manta hanyar fita ta je tana ƙoƙarin buɗe kofar labour room ta afaka ciki, sai da Aunty ta riƙeta tana faɗin. "Lafiyarki kuwa Zainab? Baga hanyar can ba".
Chapter 206 · 0% Book details