← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 211

Sashe 144

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Burinta a nan shi ne ta kwaÉ—aita masu surar jikinta ta yadda ko sun tafi tunaninta zai hanasu sakat, sannan ta tabka masu rashin mutuncin da sai sun yi danasanin zuwansu wajenta, tana burin su tafi suna masu danasanin zuwansu, sannan kuma su tafi suna masu kwadayin surar jikinta, sha'awarta ta hanasu sukuni, su sha bakar wahala wajen yaki da zuciyoyinsu dan su cire tunaninta, wannan shi ne dalilin da yasa dik namijin da aka ce zai zo wajenta sai ta tsaya ta tsantsara kwalliya na wuce tsara, sannan ta tunkari in da yake.

Shegiyar mata ce yarinyar, ta san kan duniya sosai, sai dai ni kuma na ce in ta san wani ai bata san wani ba ko my people's? Mu je dai zuwa.

Wani irin É—an iskan athletic wear ta sanya, kayan sun matseta sosai, dik wasu albarkatu na jikinta sai da suka bayyana, ta sake arab hairn nan nata har baya, sannan ta sanya wani sheÉ—anin high heel, daga karshe sai ta É—aura wani irin after dress mai kama da transparent net a saman dressing É—in nata, ta É—aura silk scarves a kanta, wasu irin siraran doggin diamond earrings ta sanya a kunnenta, ta yi kyau kam na karya.

Yanayin dressing É—in nata dai tafi kama da tantiriyar shaiÉ—aniyar karuwa, sam bata yi kama da mutanen kirki ba, dik kuma abin da take yi kada ku manta mammie É—insu ke goya masu baya.

Sai dai kuma hali ya sha banban a wannan waje, dan kuwa lokacin da Mammie ta saƙawa Fanan ga yadda zata yi ta kori wannan yariman nata sai ta ce wlh ba zata iya ba, ita ba zata yi mashi rashin mutunci ba, su kyaleta tasan ta yadda zata yi ta rabu da shi lafiya, sosai mammie ta ji haushin hakan, amma ba yadda ta iya face ta kyaleta ɗin, dan idan ta ce zata ɗaga murya uncle Abbas zai iya sanin me yake faruwa, idan kuma ya sani kun san ba zasu wanye lafiya ba, asirinta ne zai tonu.

Wani irin luxury glass cup ta É—auka, abin sha ta zuba a ciki dai'dai tsakiyar cup É—in, sannan ta shiga room É—in Mammienta ta yi mata sallama.

Sai sa mata albarka Mammien take yi tana yi mata fatan nasar. Me kuke tunani Sarina zata yi wa wannan guy É—in? Muje dai zuwa.

Ita kuwa Fanan dressing ta yi tamkar Æ´aÆ´an manyan sarakuna da ake ji dasu, dressing irin ta addinin musulunci, har da alkyabbar ta É—aura a saman kayan jikin nata, ta fito a jinin sarautarta da kyau.

Ita kam Sarina ai ta yi nisa bata jin kira, cikin wani irin shaiÉ—anin takun da dik in da ta taka sai halittun jikinta sun motsa ta nufi wajen nasu.

Duk wasu bodyguards kai har da mayakan dake cikin part ɗin sai da suka ji wani abin ya motsa masu a lokacin da suka sauƙe kallonsu a kanta, dik sai da suka kwaɗaitu da surar jikinta, ta ja hankulan su sosai, ta tafi da imanin dayawa daga cikinsu.

Harta tsofaffin dake cikin dokaran yariman sai da suka haÉ—iyi yawu na ganin santala santalan cinyoyinta game da coca colar shape É—inta, ga bayanta yadda yake wani juyi.

Tana dinfarar bakin kofar shiga ta kara canza salon tafiyarta izuwa mai jan hankali sosai, sam bata É—aga idanu ta kalli ko mutun É—aya daga cikin waÉ—an da suke harabar gidan da suka shagala da kallon surarta ba, kai tsaye ta afka ciki abinta.

Sam bata yi fargabar ko zata ci karo da uncle Abbas ko wani nata a ciki suna gaisawa da bakin ba! Ba shakkar kowa bare tsoro yarinyar nan ta afka ciki ba tare da ta yi sallama ba sai wani É—an iskan excuse da ta ce masu.

Ta kuwa yi sa'a babu kowa a ciki sai yariman da wani abokinsa É—aya, sai dogarawa guda biyu da suke tsaitsaye a kansu ta bayansu dan basu tsaro.

Hannunta na rike da wannan cup mai É—auke da abin shan a ciki, wani irin É—an iskan taku ta iya izuwa tsakiyar parlon, idanunta na'a kan abin shan nata, sam bata É—ago ta kalli in da suke ba!.

Ai yarima da abokin nasa basu san lokacin da suka miƙe tsaye ba, gabaɗaya kallonsu a kanta yake, da alama fa haƙanta ya cinma ruwa ta ɓangaren sace zuciyar yarima, ko da yake dama can soyayyarta ta kawo shi, ba dole aka yi mashi ya zo ba!.

Wani irin ɗan iskar kallo ta bi dogarawan dake bayansa da shi, cikin tsantsar nuna isa da jiji da kai irin na jinin sarauta ta furta. "Me waɗan nan ƙazaman kuma suke yi a nan? Ko da su zan yi hiran?".

Da alama yarima dai sai sorry za'ace, dan kuwa kamar fa ya tafi, dama tun da ya ganta a wajen taron da mummy ta haÉ—a yake ta faman santin kyanta da surar jikinta, sai kuma yanzu gata a gabansa cikin shiga mai tada hankalin lafiyayyun maza, ai dole ya rikice.

Ga shi namiji har namiji, arabs guy ne lafiyayye kuma É—an gayu da ba zai wuci 28 to 30 years ba, ya yi shiga irin ta prince masu ji da kansu, yana wani shan kamshi ga mutane, sai dai a gabanta tuni ya mance da cewa shi yarima ne mai ji da isa da izza, muryarsa har tana É—an kerma wajen buÉ—e baki zai bata amsa, sai dai bai kai ga furta uppan ba abokin nasa ya rigasa da cewa.

"Ranki ya daÉ—e dogarawa ne masu bada tsaro............"

Hannu ɗaya ta ɗaga mashi alamar ya dakata da yin maganar, cikin wani irin isa ta juyo da kallonta a kansa, ga idanun nata sun kara haske saboda bakin kwallin da ta sanya masu, idan ta juyasu sai kaga wani irin fari na musamman, ga shi ta iya juyasu kuwa, matsiyacin kallon up and down ta yi mashi kafin cikin nuna isa a walaƙance ta ce.

"Who the hell are you da zan yi magana da wani ka tsoma mun baki a cikin maganata? I think bakaga kalar hakan a tattare da ni ba ko?!".

Wani irin shan jinin jikinsa yarima ya yi, domin kuwa bai taɓa zaton haka take mafaɗaciya ba, shi kallon so silent ma ya yi mata a karon farko, bai san cewa ja'irar yarinya bace.

Shi kuwa abokin nasa da ya kasance É—a ne ga kanin mahaifinsa, dikkansu dai jinin sarautar ne suma, suna ji da izza da isa sai ya wani uban É—aure fuska, ya dubeta da kyau up and down, sannan ya ja wani É—an siririn tsaki, a tsiyace ya furta. "Rubbish! Yana da kyau ki san da wanda kike magana fa, am not your mate, and am n...........".

Katse shi ta yi ta hanyar É—aga mashi hannu a karo na biyu, sannan ta kawar da kallonta izuwa kan wanda take zaton shi ne yariman, dan ita a cikinsu bata ma san wanenen yarima na ainahi ba.

"I don't have time for listening all this your nonsense! What i want to know here is between the two of you who's the prince? Is it you or him?" Ta yi maganar tana nuna su da É—an yatsar hannunta manuniya.

"And among the two of you who should I going to talk?, answer me as soon as possible because I have something a lot to do!". Ta kai karshen maganar tana tsayar da kallonta a kan dogarawan da suke bayan nasu.

Abokin nasa zai sake yin magana cikin fushi da fusata dan a ganinsa ta raina mashi wayo, kun san jinin sarauta basu É—aukar wasa.

Dakatar da shi yarima ya yi ta hanyar É—aga mashi hannu, sannan ya furta. "Ni ne yarima gimbiya Sarina".

Nisawa ta É—an yi tare da nuna abokin nasa da manuniyar yatsarta haÉ—e da dawo da kallonta a kansa, cike da class take magana, babu hayaniya sai zallar jiji da kai, yadda zaku san e ba wawiya bace, wayayya ce mai ji da kanta.

"Okey ban san kai ya kake da shi ba, even do dai bana son É—aga idanu na sake ganinka a cikin parlourn nan, coz ba kai kazo neman auren ba, shi da ya zo neman auren ma i don't have time for him ma bare friends or familynsa, you have to go out now!". Tana kai karshen maganar ta maida kallonta a kan dogarawan nasa.

"Sai na furta maku ku fita ku bani waje ne kuma?". A tsiyace sosai ta yi masu magana, cikin nuna ƙasƙanci a garesu.

Daga dogarawan har abokin nasa shi suka zubawa idanu suna kallo, ta bakinsa kawai suke jira su ji.

Wani irin murmushi ya saki wanda da ka ganta kasan e lallai ƙaƙalota ya yi, dan kuwa murmushin takaicice, ya ji haushin abin da ta yi masu, a ɗan tsagaice ya furta. "You can go outside by her permission, I don't have to say anything, coz my words and hers will all go together"

Zaro idanu abokin nasa ya yi, da mamaki yake kallonsa, kenan yarima ya goyi bayanta a kansa? Lallai to da matsala, wannan yarinya maras kunya da idanunta a tsaitsaye a tsakar ka, bata jin kunya ko nauyin zagin babban ne yarima yake tunanin ita ta dace da rayuwarsa? Har yake ƙoƙarin nunawa tun yanzu ta fi mashi kowa? To da matsala gaskiya.

"Adam har da ni yau kake cewa zan iya fita waje bisa umarnin wata ba sai ka ce komai ba? Ni ne fa?".

A É—an takaice ya ce. "And so?! Ko dai ba zaka fita É—in bane?". A dake ya yi maganar.

Tun da dogarawansa suka ga haka sai suka kama kansu salum alum suka fice, da farko sun so su ce mashi ya yi hakuri ya barsu saboda mai martaba mahaifinsa ya ce in dai ba toilet ya shiga ba to su tabbatar duk wani motsin da zai yi suna a tare da shi, su bashi kula na musamman, amma ganin harda abokinsa tun na yarinya da suka taso a tare ya dakawa magana maras daÉ—i a kanta sai suka shafawa kansu lafiya suka yi ta kansu.
Chapter 144 · 0% Book details