Sashe 65
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lallai Mahnoor kin girma, yanzu ni ce zan aikeki ki ce mun in aiki Mahreen? E lallai kuwa, yanzu ai da uwarki ce ta aikeki ba zaki ce mata hakan ba ko? Shekiyar idanunki manya manya kamar na mayun nan kina kallona da su in zo in kwakwale maki su in zubar, wlh tun wuri ki wuce ki je ki É—auko mun jakar nan ko in zo wajen in shakeki sai kin mutu"............ Hasbunallahu wani'imal wakil. Wai menene amfanin mugunta ga É—an uwankan a duniya my people's? Kun ga dai wannan zallar madarar mugunta ce Nenne take ji da shi, idan ba mugunta ba fisabilillahi ita da kanta tana bala'in tsoron Jaish É—in nan, dalilin tsoronsa har ta koma gidan babanta, amma tsabar mugunta zata ce Mahnoor ta shiga in da yake ta É—auko mata jaka fisabilillahi, ai wannan zalinci ne, meyasa ita ba zata iya shiga ba hegiya.
Mahreen da take jiyo duk abin da suke faɗa ne ta fito riƙe da jakan bappan a hannunta tana faɗin. "Nenne Adda Mahnoor fa tsoron aljaninna ɗin nan take yi, ni ne kawai bana jin tsoronsa, ga jakar nan na kawo maki......"
Wani irin uban harara da ta wurga mata ne yasa ta tsaya ta kasa ƙarisowa in da take da jakar.
"Wuce ki mayar da jakar nan ta shiga ita ta je ta É—auko mun, ai Mahnoor na ce ta É—auko mun jaka ba Mahreen ba uwar goninta".
Turɓune fuska ta yi tamkar zata sanya mata kuka.
"Ko kukan jini zaki yi yau sai dai ki yi, kuma idan baki wuce kin mayar da jakar nan ba wlh in na damkeki a cikin gidan nan sai buzunki".
Sanin cewa bappansu bayanan kuma tasan halin Nenne nasu sarai ne yasa ta juya tana turo baki ta wuce mayar da jakar.
"Sai na sake gaya maki abin da zaki yi ne?". Ta jefawa Mahnoor dake tsaye idanunta cike tab da kwallah tambaya. Allah ya sani my people's kun sani Mahnoor tana bala'in tsoron Jaish, tsabar tsoronsa da take ji ma ko bappanta yana cikin É—akin bata shiga, amma saboda bakin mugunta irin na Nenne wai sai ta shiga, ga shi Bappa baya nan ma bare ta ji confidence na shiga.
Wasu zafafan hawaye ne suka fara bin ƙuncinta, ji take yi kamar shikenan yau ta mutu, abin gwanin ban tausayi sosai. Jikinta har kerma ya fara yi, Allah sarki haka ta nufi cikin ɗakin tana karanto duk addu'ar da ya zo bakinta saboda tsoro.
Wani irin shu'umin murmushi na mugunta Nenne ta saki, cikin ranta ta furta. "Ai tun da na gano kina jin tsoron wannan aljani wlh kullum sai na haɗaki hanya da shi, shegiya shi ne ma zai zama ajalinki, ko bani da aika cikin ɗakin bappanku sai na ƙaƙalo ko na karya ne na aike ki ciki sai dai ki mutu in zaki mutu, dama ni fatana kenan ki mutu kowa ma ya huta annoba kawai".
Dai'dai zata shiga É—akin bappan Mahreen ta fito ta nufi waje tana turo baki alamar ta ji haushin Nenne, Mahnoor tana son cewa Mahreen É—in ta juya ta koma ciki dan ta rakata, amma ba hali, dan Nenne na tsaye ta tsareta da ido.
Ciki ta shiga tana kuka, kamar ranta zai fita, har zufar dole ta fara haɗawa. Ganin idanun Jaish ɗin a rufe alamar yana barci ne yasa ta yi saurin ƙarisawa wajen da jakar yake a in da yake maƙale a jikin wata itace da ya sanya a jikin bangon wajen. Jakunkuna kala uku ne a wajen.
Hannunta nata kerma da kyar ta iya ciro wanda Nenne ta aiketa, juyawar da zata yi caraf suka yi ido huÉ—u da shi, yanzu ya farka daga nannauyar barcin da ta É—aukesa tun safe.
Ai a dubu ɗari ta kwala ihu tare da jefar da jakar a ƙasa ta fasa waje a guje tana ihu.
Tana fitowa Nenne ta damkota ta hau jibga da bata ga jakar a hannunta ba, dama kiris take jira ta naɗa mata duka, dan kwana biyu bata daketa ba, saboda Mahnoor yarinya ce mai kiyaye dokoki, komai a nutse take yi, da wuya ka samu ta yi wa wani laifi, tana taka tsantsan da komai, komai aka sanyata a hanzarce take yi, hakan yasa Nennen bata samu ta rinƙa jibgarta, dan bata yi mata laifi, shiyasa take ta neman laifinta komai ƙanƙantarsa ta ci zalin yarinya ta zalunceta a banza.
Ai kuwa jibgarta ta fara yi da karfi, kuka ta fara yi tana faÉ—in. "Dan Allah Nenne ki yi hakuri, wlh ya buÉ—e idanunsa ne yasa na gudo, wayyo Allah!". Gwanin ban tausayi.
Ina ai Nenne bata saurareta ba, kai mata duka da hannun take yi ta ko'ina tana faÉ—in. "Har na aikeki ki ki yi mun abin da nace, dan kinga ina yi maki dariya ko? Ni sa'ar wasarki ce? Yau sai kin gaya mun na haifeki ko ban haifeki ba?". Tana magana tana haki saboda muguntar da take yi.
"Wlh Nenne kin haifeni, dama ni a uwa na É—aukeki, dan Allah ki yi hakuri".
Ina ai cigaba da dukanta Nennen ta yi tana faÉ—in. "A'a baki É—aukeni a uwa ba, da kin É—aukeni a uwa ai da kin yi mun abin da nace, kuma wlh ko zaki mutu yau sai kin je kin É—auko mun jakar nan, ki wuce ki É—auko mun jakar nan in ba haka ba wlh sai na takaki har hancin cikinki sai sun zubo waje".
Kamar daga sama tana tsaka da jibgarta ta ɗago idanunta sai a kan kofar ɗakin bappan, hakan yasa suka yi ido cikin ido da Jaish ɗin da yake tsaye ya dafa bango da hannu ɗaya ya kuma ɗan rage tsawonsa saboda ciwo da cikinsa yake yi mashi. Ya ɗaura hannunsa ɗayan a saman cikinsa alamar cikin yana yi mashi tsananin ciwo, ihun da Mahnoor ɗin take yi ne yasa shi lallaɓawa ya fito waje, dan sun takura mashi, sun toshe mashi kunne, ya fito ne yaga su wanenen suke matsawa rayuwarsa?.
Ai kuwa tana sauke idanunta a cikin nasa idanun by mistake, wani irin mahaukacin ihu ta zunduma, a dubu É—ari ta saki Mahnoor É—in, kada kuso ku ga yadda ta wantsala waÉ—an nan siraran kafafun nata kamar na shamuwa ko balbela za'a ce ne, wasu sirara da su ga uban tsawo, ai a É—ari ta watsa a guje sai waje tana ihu kamar wata zararriya, sai faÉ—i take. "Yau na shiga uku na, yau na yi ido huÉ—u da aljani shikenan zan rasa hankalina da ganina, shikenan zan dawo aljana nima".
Ai bata zame ko'ina ba sai gidan ArÉ—o, sai ihu take a kan hanya, ta ja matasa da dama suka rufa mata baya da nufin su kamata, dan a tunaninsu ta rasa hankalinta ne take wannan ihun a kan hanya, shiyasa suka bita dan su ji me yake faruwa.
Ita kuwa Mahnoor tana ganin Nennen ta saketa ta yi waje da gudu ne yasa ta fara waige waige tana son ganin me ya sanya Nennen ta saketa? Ita dai tasan idan Nenne ta fara dukanta sai ta gaji take rabuwa da ita, komai magiyar da zata yi mata bata haƙura har sai san da ta gaji, to yau me ya faru ta saketa?.
Ai kuwa unexpect ita ma ta haɗa ido da shi, yana tsaye, yadda yake bin su Gimbiya Sarina da kallon walaƙanci haka yake binsu da irin wannan kallon, irin wannan kallon nasa yana mugun karyawa mutun zuciya, dan kallo ne mai kama da mugun harara, ta gefen ido yake wurgawa mutun irin kallo, ko ya kake idan aka yi maka irin wannan kallon walaƙancin sai ka ji ka shiga wani irin yanayi, sai ka zargi kanka ko baka da gaskiya ko kuma ka yi laifi ne, irin wannan kallo wlh sam bashi da daɗi idan aka yi wa mutun, duk sai yasa gaji kai ba komai bane a duniya, to haka dama yake kallon su Sarina, ya kware a iya irin wannan kallon walaƙancin, kuma Sarina da Fanan yafi yi wa irin kallon, dan ya tsane yaran nan bare ma Fanan da ake son ƙaƙaba mashi ita, ya tsaneta, tsanar kuma ta samo asaline daga kan Mammiensu, tsanar da ya yi mata ne ya shafesu suma.
Ai kuwa suna haɗa ido ta kwala ihu, a guje ta nufi waje. Karaf suka ci karo da bappa dake shigowa cikin gidan hannunsa ɗauke da ɗan ƙaramin buhu da ya zuba kayan fruits a ciki. Baya baya ta yi ta faɗi ƙasa.
"Subhanallah Mahnoor lafiya kika fito a guje haka?". Cewar bappa.
Kasa iya amsa mashi ta yi, fuskarta jaga jaga da hawayen dukan da Nenne ta yi mata.
Mahreen dake biye da shi a baya ne ta yi kan Mahnoor É—in tana faÉ—in. "Adda Mahnoor meyasameki? Naje gonar bappa ne fa na gaya mashi Nenne ta saki zuwa wajen aljani, dukanki Nennen ta yi ne?".
Kai ta girgiza alamar a'a Nenne bata daketa ba. Kama hannunta Mahreen ɗin ta yi a in da ta taimaka mata ta miƙe tsaye. Hannu tasa tana goge mata hawaye. "To waye ya dakeki?". Ta sake jefa mata tambaya.
Da kyar ta iya saita nutsuwarta tare da cewa. "Babu wanda ya dakeni, aljanin ne ya tashi ya fito waje shi ne ya bani tsoro".
Da sauri bappa ya ce. "Yauwa masha Allah to mu koma ciki bari naje na bashi abinci, dan nasan yanzu abincin kawai zai buƙata, saboda yasha maganin cin abinci".
Ba musu suka wuce gaba riƙe da hannun junansu, ya rufa masu baya.
Jaish dai yana tsaye a in da yake, bai motsa ba, ya kasa iya komawa ciki ne saboda rashin karfi, dama da kyar da suÉ—in goshi ya iya fitowa wajen, yanzu kuma ya kasa motsawa ma daga in da yake, ga wani irin azabbabben yunwa da yake ji, ji yake tamkar ana yayyanke mashi Æ´aÆ´an hanjinsa saboda azabar yunwa, a wannan yanayi da yake ciki wlh kome ya samu zai iya ci bawan Allah, maganin cin abincin bappa ta fara aiki gadan gadan.