← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 211

Sashe 63

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban gida ne sosai mai matuƙar girma da ɗaukan hankali.
Daga yanayin tsarin gidan mutum zai tabbatar da maƙudan kudin da aka zubar wajan tsara shi ba zai ƙirgu ba. Ta ko wani ɓangare gidan ya haɗu sosai da sosai.
Daga wajan gidan akwai wasu flowers da masu kyau da aka ƙawata wajan da su, sai babban gate ɗin gidan mai matuƙar girma da ɗaukar hankali, ga securities ta ko ina da suke shawagi hannayensu ɗauke da bindigu, har zuwa second gate ɗin da yake wajan, wanda tazaran sa da fırst gate ɗin mutum sai yayi kusan 5 minutes a hanya .

Daga harabar gidan babban fili ne me É—auke da shuke shuke masu kyau da É—aukar hankali, sai babban titin da zai kai mutum har zuwa main building. In short wannan gida ya kai filli girman plot 50. Parking space na wannan gida kawai ya kai girman fili plot 10, tsab zai iya kwasan motoci sama da guda hamsin, a haka kuma cike yake tab da zafafan moto. Pentin gidan gabaÉ—aya ya kasance white color ne, my people's wannan gidan ya haÉ—u, Allah ya bamu aljannatul firdaus my people's, ku ce amin!.

Da electric stair case suke amfani, amma akwai elevator ma, sai dai sun fi yawaita yin amfani da electric stair case ɗin, komai na cikin gidan nan ba ƙananan ƙuɗaɗe aka zuba wajen sayansu ba, lallai ba shakka dollars sun yi kuka kuma sun yi mubaya'a a wannan ginin.

Tampatsa tampatsan gate ɗin gidan dukka biyu wasu irin jiga jigan securitys ne suke tsaronsu. Suna dakatawa a parking space na gidan, gabaɗaya jami'an suka sauƙo ƙasa. Bai bi ta kan kowa ba suna buɗe mashi kofar motar yasa kai ya nufi cikin gida.

Wani irin azabbabben daddaɗar kamshi ne yake tashi tun daga ɗan nesa da hanyar nufa cikin parlourn gidan, idan nace zan tsaya zayyana maku haɗuwar wannan gida sai mu kwana mu wuni bamu kammala ba, dan haka ku ƙawata shi a ranku, ni na yi gaba na je na leƙo maku ciki ba zan ɓata lokacina a wajen harabar gida ba.

Shi kaÉ—ai ya shige cikin parlourn, duk sauran securitys da suka rakosa sun tsaya a waje wajen securitys da suka samu a gidan.

Yana shigewa cikin parlourn ya nufi luxurious dining room ɗinsa, wannan gida dai ba gidan kowa bane face gidansa, bashi da mata, bashi da budurwa, hasali ma bai taɓa yin soyayya ba, kuma bashi da niyar yin matar amma yana da tampatsetsan gida irin wanna, bama wannan ne kawai ba, yana da gidaje sosai, sannan shi mutun ne mai yawan kyauta sosai, yana sadaka fiye da tunaninku, idan zai yi kyauta kuma baya zaɓar wa zai bawa, duk wanda ta faɗa kansa kawai bashi zai yi, duk da bashi da sauƙin kai da tausayi amma yana da zuciya mai kyau, ga taimakawa gajiyayyu, kuɗinsa basa tafiya a banza.

Yana zama saman table É—in sai ga wani na'ura mai siffar É—an adam ya shigo wajen. A gabansa na'uran ya tsaya yana jiran umarni.

Ya ɗauki tsawon lokaci yana latsar wayarsa wadda shi kaɗai company ta kerawa irinsa, shi ya bada design da duk wasu abubuwan da yake buƙata da yadda yake so wayar ta kasance, wane mutun ya iya bibiyarsa ta wannan waya, a garƙame take da matakan tsaro na ban mamakin gaske, komai maitancinka a iya computer baka isa ka datsi tsaron dake tattare da wannan waya ba har ka shiga cikinta, dan shi ma guy ɗin shegene a fagen iya computer

So ya jima yana latsa wayarsa kafin nan ya bawa na'uran umarni ya kawo mashi breakfast da ya fi kauna, ya haÉ—a mashi da Espresso strong coffee...... Ko meyasa yaki yin breakfast a gida ya zo gidansa?.

Da sauri na'urar ya juya ya bar wajen. Cigaba da latsa wayarsa shi kuma ya yi.

A hankali sautin ringing É—in wayarsa ta fara tashi, shiru ya zubawa wayar sexy eyes É—in nan nasa masu shegen shining kamar me.

Har wayar ta katse bai ɗauka ba, ƙira na biyu ne ya sake shigowa, a dai'dai lokacin kuma wannan na'ura mai yi mashi aikin ya dawo hannunsa ɗauke da wani jibgegen glass tray mai bala'in kyau. Kayan abinci kala kala ne a saman wannan haɗaɗɗen tray ɗin tare da spoon, knife da sauransu.

Saman table É—in ya É—aura trayn, sannan ya tsaya a gefe yana jiran umarnin ya hau yin serving.

Kira na uku ne ya sake shigowa, a lokacin ne ya yi pick tare da sanya wayar a hand-free ya ɗaura saman table ɗin a kusa da shi tare da ɗauko tsadaddiyar cup dake cikin tray ɗin mai shaƙe da Espresso strong. A hankali ya kai ɗan bakinsa, lips ɗin nan nasa ba'a magana, yana ɗaukar hankali matuƙa.

Kaɗan ya ɗan kurɓa ya cire, a nutse yake bin komai daki daki, cikin class mai jan hankali.

Daga cikin wayar tasa wata ƙatuwar fasashiyar murya ta furta. "Sir the RS52-nuclear was mistakly feared". Cikin tashin hankali mai maganar ya yi ta, yadda yake maganar har word ɗinsa suna haɗewa.

Shiru ya yi bai yi magana ba, kuma bai nuna alamar kamar ya shiga tashin hankali ba duk da ya ji cewa sun yi mistake sun saki nuclear bom ɗin, basu yi setting ɗinta ba aka samu akasi suka saketa, amma hankalinsa a kwance, cigaba da shan espresso strong ɗinsa ma ya yi. Daga cikin wayar wanda ya yi maganar ya sake cewa. "Hello sir I said the RS.........". Bai bari ya ƙarisa sake faɗa ba ya sanya kyakyawan hannunsa ya katse kiran.

Lallai akwai cakwakiya, wannan guy ɗin gaskiya bana ce komai ba, ace maka nuclear ta kwace ta fita amma yana zaune yana sharholiyarsa?🤔 Akwai matsa in dai haka ne, ni dai bari na hau jirgi sai ƙasar Nigeria cikin birnin jimeta Yola mu dubasu mu gani, kila kafin mu dawo ya farka daga barci, dan ni ban yarda cewa baya barci ba, nuclear bom fa ake magana amma yana zaune, kuma shi kaɗai zai iya shawo kan matsalar, to ni dai kada nuclear nan ta yo Nigeria ato, ta tsaya a ƙasar tasu ko kuma ta yi ta yawo a sararin samaniyarsu, na dai gudu abina.

_________________________🔥💔😥

JIMETA🔥

Duk wani karfi dake tattare da shi ne ya kare sakamakon wannan aman, kan kace me ya zube ƙasa ya kwanta, sama sama yake numfashin tamkar ba zai rayu ba.

Bappa dai bai karaya ba kuma bai ji komai ba ya matso ya fara yi mashi sannu. Wani irin fita da karfi karfi numfashinsa ta fara yi tamkar zai sume, bawan Allah dama bashi da lafiya ya zo kuma ya ƙarisar da ɗan karfin da yake da shi a wajen yin amai. A ruɗe bappa ya miƙe tsaye ya nufi waje har yana haɗawa da gudu.

Matasa ya nemo a kan su zo su taimaka mashi ya kai Jaish É—in É—aki ya taimaka mashi da agajin gaggawa kada ya mutu.........

My people's ina son ɗaukar hutu, kuma ina son in bari sai mun kai ƙarshen book 2 ko tsakiya sai na ɗauki hutun, wanne kuke ganin ya fi? In ɗauki hutu yanzu ne ko sai na kai tsaki ko kuma karshen book 2? Ina son in ɗan huta kwakwal ta yi fresh ta ƙaro walaƙanci, 😅 ku tayani da addu'a.......✍️

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 11/10/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

E20

Matasa ya nemo a kan su zo su taimaka mashi ya kai Jaish É—in É—aki ya taimaka mashi da agajin gaggawa kada ya mutu.

Kama shi suka zo suka yi izuwa cikin ɗakin, a saman gado bappa ya ce su kwantar mashi da shi. Duk kyakkyamin nan nasa yana ji yana gani suka kamashi izuwa cikin ɗakin, kamar ba zai rayu ba! Sai ma da suka kama shi ne jikin nasa ya ƙara tsananta ciwo, dan kuwa da alama wannan uban kyakkyamin nasa a jini take, shiyasa yake fama bawan Allah, kun san akwai waɗan da abin a jininsu yake, akwai waɗan da kuma tsabta ce ta ja masu hakan, idan kana da tsabta sosai tana iya ja maka hakan, to shi bayan tsabta ma a jininsa take abin, shiyasa ko ya ce zai bari ma zai sha bakar wahala ne a banza, dan ba abu bane da za'a iya barinta kamar yadda kuke tunanin nan.

Datse idanunsa gam ya yi baya son ganin cikin ɗakin bappan, saboda kyama, ga shi bashi da wani zaɓin da ya wuce ya kwanta shiru, saboda ko motsawar kirki baya iya yi, cikinsa ne yake bala'in murɗa mashi kamar zai mutu.

Magunguna bappa ya hau jiƙa mashi tare da yi wa mutane da suka taimaka suka kamashi izuwa cikin ɗakin godiya. Idanunsa a datse gam yana numfashi sama sama har bappa ya kammala jiƙa magungunar, su kuma samarin suka yo waje, ɗaya daga cikinsu ya ɗauki Mahreen izuwa cikin ɗakin ya kwantar da ita a gefen Jaish ɗin, sannan suka fice daga gidan.

Idanunsa a datse bappa ya fara ɗura mashi magunguna masu uban ɗaci kamar me, abin da bai taɓa sha ba, ko a mafarki bai taɓa mafarkin zai sha irinsu ba, ga shi bashi da zaɓin da ya wuce ya haɗiye a cikin cikinsa dan dolensa, dan kuwa kansa yana ɗage da pillow ne, yadda bappa ya sanya mashi bakin kwaryar a ɗan bakinsa dan dole ya haɗiye, dan bashi da karfim da zai iya ture maganin ko kuma ya iya ture bappa or ya yunkura ya ce zai fitar da maganin, bashi da kuzarin iya motsa kansa ma bare iya amayar da maganin, haka ya ƙara datse idanunsa ya jin maganin tana ratsa maƙogwaronsa izuwa cikinsa, wani irin takaici da yake ji kamar zai mutu, ji yake yi kamar ya tashi ya shaƙe bappan har sai ya mutu, amma dukka babu halin yin hakan.
Chapter 63 · 0% Book details