Sashe 146
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai kafin ya yi mata magana har ta shige room É—in Mammienta, dan wani uban sauri take zubawa, tamkar bata gansa ba ta wucesa da sauri, da alama kasancewarsa shiru shiru mai sauki kai sosai yaja suka rena shi.
Dan a dik jikokin Akka babu mai saukin kansa, ga fara'a, kunga ai basa gigin kawo wa Jawad iyashege, da Jawad ne wlh kome ta kwaso, ko da wuta take tafiya sai ta tsaya ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa, amma da yake wannan gajeran dangarta ne sai ta wucesa fuuuu kamar kunfa.
Da ya so ya bi bayanta izuwa É—akin mammie É—in, sai kuma ya fasa ya nufi nasa part É—in a zuwan zai yi mata magana idan suka sake haÉ—uwa.
Shi kuwa yarima wani irin murmushi ya saki na abin da ta yi mashi, sai dai da alama murmushin takaici ce, a face ɗinsa bai nuna ya damu ba, daga ta cikin zuciyarsa kuma tamkar ya murɗe wuyarsa ya mutu yake ji saboda wani irin ɗacin takaici da ya ji, ba'a taɓa yi mashi irin wannan cin mutuncin da ta yi mashi ba, ace dik izzarsa da isar nan tasa Sarina ta walaƙanta sa har haka?! Abin da kunar rai gaskiya.
Waje ya nufo shi ma ba tare da ya É—aga idanu ya kalli kuyangun da suka kawo mashi abincin ba. Yana fitowa ya nufi motarsa tare da bada umarnin su tashi motoci su tafi.
Da ido abokinsa ya bisa da shi yana addu'ar Allah ya kara, dan ko ba'a gaya mashi ba ya san rashin mutunci Sarina ta yi mashi, da yake abokinsa ne sai ya iya gane hakan y
a face É—insa!.
A dai'dai lokacin kuma ita ma Fanan ta fito a tare da nata yariman daga É—ayan part É—in, sai murmushi yake yi ita ma tana murmushi kuyangu biyu suna take mata baya, shi ma dogarawa biyu suna take mashi baya.
A haka ta rakosa har wajen mota, sai kwasan gaisuwa sauran dogarawansa dake jiransa a wajen suke yi a wajenta. Cikin mutunci ta rinƙa amsa masu.
A jikin motarsa ya jingina bayansa, cikin sanyin murya ya furta. "Na ji matuƙar ɗaci da takaici na rashin samunki a matsayin mata da na yi Fanan, amma ba komai kana naka Allah yana nashi, na gode da karranawa kuma na ji matuƙar daɗi, ina yi maki fatan Allah ya haɗa kanku ke da wanda kike so ɗin ya kuma baku zaman lafiya".
Kanta a ƙasa ta furta. "Amin ya Allah, ina godiya sosai da addu'a, ni kai'na na ji babu daɗi da zuciyata ta riga fara son wani ba kai ba, ina yi maka fatan samun mace tagari tamkar yadda kake nagari mai tsoron Allah".
"Amin Fanan, amma ba zan gaji da faÉ—in na yi babban rashi ba, na kuma ji ciwon hakan sosai a zuciyata, kuma na tabbata zan cigaba da jin zafin hakan na har abada, na so ki sosai Fanan, tun da na É—aura idanuna a kanki sonki ya shigeni, amma babu komai na barki lafiya, please keep smiling like the way you're, murmushi tana yi maki kyau sosai". Yana kai karshen maganar ya matsa daga jinginar da ya yi da jikin motar.
Wani dogari ya yi saurin zuwa ya buÉ—e mashi kofar motar, a back seat ya zauna idanunsa a kanta.
Kanta a sunkuye tana kallon ƙasa ta jinjina mashi kai tare da furta. "In Sha Allah ko dan kai zan cigaba da kasancewa da murmushina, nagode sosai da ka fahimceni, ina yi maka fatan alkhairi".
Kawar da kallonsa daga kanta ya yi cikin jin kunar rasata da ya yi, dogarin ya rufo kofar motar, sauke glass ya yi a in da ya ce mata ya gode, daga haka bai kara furta uppan ba aka tashi motocin nasu. Tana tsaye a wajen tana kallonsu har suka danna hancin motocinsu waje da gudu.
Shi ma idanunsa a kanta har suka bar gidan, motocin yariman Sarina na fita ne nasu ya take masu baya.
Ajiyar zuciya ta sauke na ganin sun fice, godiya ta É—aga hannu ta yi wa Allah da ya sanya ta rabu da wannan yariman lafiya, yarinyar kirki, ita dai bata bi shawarar Mammienta ba, ta fito fili ta gaya mashi gaskiyar dake cikin zuciyarta na cewa tana son Jaish, ba faÉ—a ba komai, suka gaisa cikin mutunci, ya isar mata da kudurinsa a kanta, bata katse shi ba har ya gama jawabansa, sannan ne ta fara da bashi hakuri kafin ta É—aura mashi da sauran bayanai.
Da yake mai ilimi ne shi É—in sai ya fahimceta ya kuma yi mata uzuri, suka yi hira cikin mutunci da mutunta juna, ta yi ta bashi hakuri yana ce mata ba komai wlh, ai bai sani ba ne, da ya san tana da wanda take so ma ba zai zo ba, dan haka ita ma ta yi hakuri.
Cikin fara'a da girmama juna suka rabu abin gwanin birgewa saɓanin Sarina da nata saurayin.
______________________🦋💘
Har cikin É—aki ta bisa tana faÉ—in Allah ba zata rabu da shi ba, sai dai ko da ta shigo cikin room É—in baya nan, babu shi a É—akin.
Duba shi ta fara yi dan dai ita tasan taga shigowarsa, yana shigowa ta biyo bayansa, sannan ace baya ciki, to ina ya shiga?.
Balconynsa ta fara leƙawa, wayam baya nan, a hanzarce ta zo ta nufi toilet dan wauta. Wayam baya ciki, yanzu da yana ciki ma haka zata shiga dan yarinta na mata gizo a kai.
Bincikarsa ta fara yi babu kakkautawa, tsabar shiririta har da leƙa kasar gado, tana yi tana hawaye, ni kam na ce Jawad mage ne da zai shiga kasar gado ya ɓuya fisabilillahi idan ba shirme irin ma Chuchun ba.
Ta ko'ina sai da ta leƙa except bayan curtains kawai, ta sha wahala bata gansa ba, sai ta haye saman gadonsa, ta kwanta tare da rungumo pillow tana cigaba da kukanta tamkar wadda aka daka.
Kamar daga sama taga an kashe wutar ɗakin, ai a fujaje ta miƙe zaune a tsakiyar gadon tana rarraba idanu kamar an tare ɓera ga tarko, ɗakin ya yi duhu sosai saboda curtains gabaɗaya a sake suke. Zaro idanu ta fara yi, kumatu a kumbure ansha kuka a ƙoshi ta furta.
"Yah Jawad bana so, dan Allah ka kunna wutar, ka dai san duhu tsoro yake bani ko?". Tana magana hawaye suna kara tsananta gudu a saman face É—inta. Muguwar matsoraciyar duhu ce, bata kaunar rashin haske ko kaÉ—an! Tana iya sumewa ma idan duhu ya yawaita.
Shiru bata ji motsin kowa ba, kamar zata saki fitsari a wandonta ta sake faÉ—in. "Yah Jawad dan Allah ka bari ka ji, wlh ina jin tso........."
Bata kai karshen maganar ba sai ji ta yi ya rungumeta ta baya, ta tsorata sosai sai ta wage baki zata fasa mashi ihu. Da sauri ya rufe mata shi da hannunsa, a kunne ya raÉ—a mata kalmar sarkin tsoro yi mun shiru.
Ƙoƙarin kai mashi dukan wasa ta yi tana ƙoƙarin kwace kanta daga riƙon da ya yi mata. Jawota mai gabaɗaya ya yi ta faɗa jikinsa yana faɗin. "Sorry my beb kin ji?".
Harara a duhu ta banka mashi, tana shasshekar kuka ta furta. "Dan Allah ya Jawad ko wutar lamp ne ka kunna, kaga ina jin tsoron duhu sosai, ko dai ka manta ne?".
Kai ya girgiza mata alamar a'a bai manta ba, ƙasa ƙasa ya ce. "Tun da kina jikina bai kamata ki ji tsoro ba".
Kai kawai ta gyaÉ—a mashi alamar haka ne, amma bata furta kalma ba, ta yi shiru tare da kwantar da kanta a kirjinsa.
"My beb kin san me nake tunani kuwa?".
Ba tare da ta É—ago ko ta yi magana ba ta girgiza mashi kai kawai alamar a'a bata sani ba.
"Tunani nake yi ko dai na yi wa dad batun aurenmu ne? Wlh na gaji da ɓuye masu da nake yi, ina buƙatar kasancewa da ke a kullum ba tare da wani shamaki ba".
Tana dai lafe, kasa kasa a shagwaɓe ta ce. "Da zanfi kowa farinciki kam my melody".
Da sauri ya ce. "Da gaske kike yi? Kin yarda na bayyanar da soyayyarmu na kuma nemi aurenki?".
Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e, wani irin farincikin da ya ji ne har bai san lokacin da ya matseta a jikinsa sosai ba, har sai da ta furta washe ne ya farga ya ɗan sassauta mata riƙon yana sauke ajiyar zuciya.
Shiru suka yi na ɗan lokacin, shi ya afka tunanin ɗan uwansa Jaish wanda da shi yake kwana da shi yake tashi a cikin ransa, kullum tunaninsa ina ɗan uwan nasa ya tafi? Ga shi har yana shirin yin aure bai dawo ba, yau tsawon watanni kenan. Abin ya yi mugu mugun taɓasa, dik ya zabge sosai, dan ma Momma tana tsawatar mashi haɗe da rarrashinsa a kan ya kwantar da hankalinsa ɗan uwansa yana nan dawowa nan ba da jimawa ba, amma dik da hakan ya kasa samun nutsuwa, kullum yana cikin fargabar labarin da zai ji a kan ɗan uwan nasa.
Ita kuwa rufe idanu ta yi babu jimawa barci ɓarawo ya saceta, dan daren jiya ta biye mashi, bata yi barci ba suka rinka zuba hira, da safe kuma ta tafi school, shi ne yasa barci ya tarun mata sosai.
Saukar numfashinta irin na mai barci da ya ji ne ya fargar da shi tare da dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da matsawa kaɗan, a hankali ya kwantar da ita, ya janyo pillow ya sanya mata a wajen kanta, ya kuma janyo bargo ya lulluɓeta. A gefenta ya kwanta shiru, jikinsa dik a mace na tuna Jaish da ya yi, ji yake yi tamkar ya sanya hannu bisa kansa ya zunduma ihu ko zai ji sassauci a ransa.
A ɓangaren Auta da uncle Taheer da suke cikin gonar dad kuwa, sai janta da hira uncle Taheer yake ta faman yi, yana son su saba da ita sosai, ita kuwa ta tasa waya a gaba tana ta danne danne.