Sashe 43
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadija ce ta amsa mata da. "Kina ji ko Hauwa kike ko wa? Koma ya sunanki dai ina son ki tsaya a iya matsayinki, kada ki sake ki shiga harkarmu wlh, idan kuma kika ki wlh sai na sa kin gane Annbi isa ba É—an Allah bane manzon Allah ne". Tana kai karshen maganar ta ja hannun Zee suka wuce cikin É—akin.
"E lallai Khadija kin girma, wuyarki ya yi kwari ya isa yanka kenan!". Cewar Hauwa.
Zee ce ta capki zance da cewa. "Tun da ya isa yanka ai sai kizo ki yanka ai!".
Daga hanka suka banko masu kofa da karfin gaske, irin su suka sani nan. Taɓe baki maman Haidar sarkin tsoro ta yi, dan ita fa tsoron masifaffu take yi kada su naɗa mata duka ato, ta ji daɗi ma da Khadija ɗin ta amsa mata magana cikin mutunci har ta ce mata gwaggo, dan haka gara ta kama girmanta ta cigaba da samun suna ce mata gwaggon, dan yanzu ta lura yaran nan suna ji da tashen girman, tsab zasu dakata ta yi laushi, gara ta shafawa kanta lafita ta ja mutuncinta.
Hauwa kuwa da yake ƴar balaja'u ce sai ta fara surfa masu masifa, a can ƙarƙashin zuciyarta kuwa tana tunanin ta yadda zata yi ta yi maganin yaran nan, dan ita ma ta lura Khadija tana ji da tashe girma a yanzu, tsab zata iya cewa zata yi faɗa da ita, idan kuma faɗar zasu yi wlh tsab Khadija zata lakaɗa mata shegen duka, dan Khadija fa sai dai muce masha Allah, Zainab akwai rashin kunya ba karfin kirki, Khadija kuwa shiru shiru amma in ka kureta karfi ne da ita sosai, haka suke, dama kunsan mai hakuri fa kada ka kuskura ka kuresa wlh, in ka kuresa abin baya kyau sam sam.
Suna shiga É—aki Khadija ta ce. "Zainab kin yi sallah ne?". Kai ta girgiza mata alamar a'a. "Okey yi alwala ki yi sallah kizo ki gaya mun me yake faruwa ne a gidan nan?". Da okey ta amsa mata tare da wucewa cikin toilet, wanka ta fara yi da ruwa mai zafi sosai kafin ta É—auro alwala ta fito.
A saman gado ta isko Khadija É—in tana duba magungunar da aka bata a asibiti. "Zainab wannan uban tulin magunguna kuma na waye? Naga har da na zuciya duk na waye haka?".
Kamar zata yi kuka ta ce. "Magunguna na ne, yanzu ma zan zo in hau shan su".
Zaro idanu ta yi kafin ta ce. "Dukka uban magungunar nan? Ji wannan manya manyan kamar shanu ce zata sha? Dukka kuma zaki sha?". Ta yi tambayar fuskarta É—auke da mamaki.
Kai ta gyaÉ—a mata alamar e, abin gwanin ban tausayi.
"To me ya sameki har zaki zuba waÉ—an nan magunguna a cikinki? Meyake damunki?"
"Bari na yi sallah sai na gaya maki me ya faru". Nan take idanun Khadija suka ciko da kwallah, rayuwa kenan, yau sun dawo yin rayuwa su biyunsu Allah sarki gwanin ban tausayi.
Sallah Zee ta yi, bayan ta idar ne ta yi addu'a sosai, ta ɗauki lokaci mai tsawo a wajen jero addu'oin nata kafin nan ta shafa, sannan ta miƙe ta dawo saman gadon ta zauna. Khadija da ta ƙura mata idanu tun ɗazun tana kallonta cike da tausayi ne ta ce. "Dan Allah Zee kada zuciyata ta fashe ki sanar da ni meyake faruwa? Ke kaɗai nake jira, a ƙage nake wlh".
Ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙarisa hayewa saman gadon da kyau, sannan ta riƙo hannun ƴar uwar tata, nan ta fara bata labarin abin da ya faru tun fitar ta gida lokaci da mamarsu ta cakawa babansu wuƙa har izuwa yanzu da suke zaune.
Ya ilahi ya lilliahi, kuka Khadijan take yi sosai da sosai, hawaye a saman face nata gudu suke yi kamar ba gobe, jikinta har rawa ya fara yi saboda tsananin tashin hankali, babanta ya rasu, mamarta ta ci life in prison, innalillahi wainna ilaihir rajuun, wannan masifa ko makiyin ka ba zaka so ka yi mashi fatan shiga makamancinsa ba.
Rungume juna suka yi suka hau murzan kukansu, wannan hawaye nasu Allah ne kaÉ—ai yasan ranar da zata dakata daga zuba a idanunsu, ya ilahi ya lilliahi. Allah sarki babu mai rarrashinsu, haka suka ci kukansu har ya ishesu suka rarrashi kansu da kansu, Zainab sarkin zuciya sai shessheka haÉ—i da ajiyar zuciya take ta faman saukewa.
Sai da suka ɗan ji dama dama ne Zainab ta ce. "Ina ke kuma kika je? Ina kika tafi kika barni ni kaɗai na rinƙa faɗa tsakanin rayuwa da mutuwa? Na sha wahala! Na rasa wa zan yi wa kuka, babu mai rarrashina, babu wanda zan gani na ji sanyi a rai'na, ta ko'ina na juya zafi ne kamar wuta a gareni, sam babu wani sassauci, na ce kawu Sadiq ya kaini wajen mama ya ce shi ma ya je an hana shi ganinta, zuciyata zafi take mun kamar zan mutu, shiyasa kika ga maganin zuciya a cikin magungunana, wlh Aunty Khadija gara mun mutuwa akan azabar nan da na shiga, irin wannan tashin hankali bana fatan ko makiyina ya shiga cikinsa". Ta kai karshen maganar wasu zafafan hawaye suna ganganro mata a saman kumatunta.
Matsowa Khadija ɗin ta yi ta fara goge mata hawaye tana faɗin. "Kiyi hakuri Zainab, na tabbata Allah bai mance da mu ba, na tabbata yana sane da mu kuma zai yi mana sakayya, sannan shi ne kawai zai share mana hawaye, ina son ki sani duk halin da zaki shiga kada ki manta Allah yana tare da ke, kuma shi kaɗai ne zai kawo maki sauyi a lokacin da baki taɓa zato ba, dan haka ki goge hawayenki, addu'a baba yake da buƙata, mama kuma da izinin Allah Ubangijinmu zai dubeta da idon rahama tun da ba da gangan ta kashe baba ba, ban taɓa yankewa daga fatan samun nasara daga wajen Ubangiji ba, nasan shi ɗin mai rahma ne a kan bayinsa, da izininsa zai saukar mana da rahmansa, kuma baya mantawa da bawa ko guda ɗaya, Allah zai kawo mana mafita".
Maganganun Khadija sun ratsata sosai, hakan yasa ta goge hawayenta tare da yin alkawarin zata yi ƙoƙarin ta dai'na zubda hawaye duk da tasan abu ne mai wuya a gareta, dan kuwa wani lokacin idan ta yi kukan ne take samun sauki a zuciyarta.
"Aunty Khadija ina kika je har tsawon wata biyu to?". Ta yi tambayar tana kallonta har cikin ido.
A takaice ta ce "Russia!". Zaro idanu sosai waje Zee ta yi tare da maimaita sunan Russia ɗin. Jinjina mata kai Khadija ɗin ta yi kafin ta ce. "Yeah kamar yadda kika ji hakan ce ƙasar Russia aka kai ni".
"Waye ya kaiki can? And me kika yi a can?".
"Saceni suka yi suka kaini can, ni ban san na yi wata biyu da tafiya bama sai da kika faÉ—a mun yanzu, dan tun da naje ina ga na É—auki kwanaki ko satuttuka a sume, ni ban san komai da ya faru ba".
Ƙara zaro idanu waje Zee ta yi. "Na shiga uku ni Zainab! To amma ya aka yi kika dawo? Sannan kuma basu yi maki komai ba ko?".
Tana ƙoƙarin firfito da magungunar Zee ɗin da ta mayar ɗazun ta amsa mata da. "Waɗan da suka ɗaukeni su suka dawo da ni har kofar gida, kuma ni ba abin da suka yi mun, ban ga alamar sun cutar da ni ko wani abin makamancin haka ba, kamar yadda suka ɗaukeni a kofar gida haka suka dawo da ni, sannan suka bani wancan jakar mai cike da kuɗi suka ce na tafi gida wai na rinƙa cin abubuwa masu kyau da kuɗin da suka bani".
Shiru Zainab ta yi tana tunanin anya hakan zai yiwu kuwa?........ Ni ma dai nace anya hakan zai yiwu kuwa? Su zo har kofar gida su ɗauketa su tafi da ita ƙasa mai nisa haka, sannan su riƙeta na tsawon sati bakwai ace sun sake dawo da ita da kansu kamar yadda suka ɗauketa? Sannan su bata maƙudan daloli ma ba nairori ba su ce ta tafi ba tare da sun yi mata komai ba! Anya hakan abu ne mai yiwuwa kuwa? Kai akwai dai abin da ya saɓa wanda ita bata sani ba. Hmm akwai dai wata a ƙasa, haka kawai ba zasu yi abin da suka yin nan ba.
Katse mata tunani Khadija É—in ta yi ta hanyar cewa. "Zo ki sha magani, dan ina fargabar wani abin ya saman mun ke, ke kaÉ—ai kika rage mun sai Allah da ya haliccimu sai kuma kawu Sadiq, dan haka ba zan barki ki yi wasa da magani ba, zo maza ki sha bari na nemo waya mu kira Kawu Sadiq mu ji ina yake kuma me ya faru ya fita asibiti da sauri haka?". Ta kai karshen maganar tare da turo mata tulin kwalin magungunar a gabanta.
"Aunty Khadija ban fa ci abinci ba, magungunar nan kuma suna da karfi in ji Dr, dole na ci wani abin kafin na sha su". "E haka ne, to ki jirani bari na nemo maki abin da zaki ci, daga nan na nemo mana waya". Tana kai karshen maganar ta zuro kafafunta kasan gadon ta sauƙa.
Kai tsaye wajen jakar kuɗin nata da taho da shi ta nufa, dala ɗaya ta zara, wannan shi ne dare ɗaya Allah kan yi bature, yau dai ga Khadija da dukinyar da babanta ma bai mallaki ko kwatansa ba, wannan maƙudan dukiya da yake cikin jakar nata duk familynsu daga ɓangaren mamarta har na babanta babu mai kwatan wannan dukiya, dan zallar dollars ne a ciki, gasu da uban yawa, Allah sarki a kan dukiya aka kashe babanta kuma Hauwar take son kashesu, dukiyar baban nasu ma da bai wani taka kara ya karya ba, to ita gata da dukiyar da zai isheta rayuwa ita da familyn nata gabaɗaya ba tare da sun juya shi bama ma, su ajiye suyi ta zara kawai zai ishesu har su mutu....... Hmmm tab yau ake yinta, wannan uban kuɗin dukka da suka bata kuma ace basu yi mata komai ba? Kai ina akwai ayar tambaya gaskiya.