← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 211

Sashe 114

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To amsa kiran me? Magana zata yi da wani? Leesharh ta kasa gane cewa yanzu fa time ɗinta ne, ta kasa fahimtar cewa yanzu fa sai dai ita ta juya masu nikaf ba dai su su juya taba, yanzu Allah ya ara mata dama, tana da damar da zata iya ce masu idan basu yi mata kaza ba ita kuma ba zata yi aikin ba, ba su da zaɓi kuma ba yadda zasu yi da ya wuce dole su yi abin da take so, dan kuwa ita kaɗaice zata iya yi masu wannan aiki, dole su lallaɓata idan suna so, amma duk bata gane hakan ba, bata gane cewa yanzu ita fa abin su lallaɓane idan suna son aiki, ba wai su rinƙa yi mata barazana ba, da yake tun farko da tsoronsu a ranta, sun rigada sun sanya mata tsoro azzalumai sai ta ƙasa gane komai.

Shiru ta luluƙa duniyar tunani, bata san da shigowar Sharifat ɗakin ba sai tsinkayo muryarta ta yi tana faɗin. "Bloody me ya sameki a kumatu? Waye ya mareki? Kuma ya baki zo kiran da Abbie ya yi maki ba?".

Ƴar firgita ta yi alamar mutum yana cikin tunani, a hanzarce ta shiga sharce gumin dake saman face ɗinta.

Da mamaki É—auke a fuskarta Sharifat ta ce. "Bloody lafiya kike kuwa? Gumi fa naga kike yi? Ko dai gudun Acn ne ya yi maki kaÉ—an ko baki da lafiya ne?".

Duk tana ruɗe, hannunta har yana kerma wajen fita daga kan massages ɗin ta kashe wutar screen ɗin, murmushin dole ta ƙaƙalo tare da faɗin. "Brat babu komai fa, kawai ina tunanin mamata ce, Abbie kuma kin san har yau bana iya gane wasu hanyoyi na cikin gidan nan, na fita zanje wajen nasa sai na rasa hanya".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da zama a kusa da ita. "Allah sarki my bloody, da na yi zaton wani abin ne ya sameki, kada ki damu ki rinƙa yi wa mama addu'a Allah yasa tana cikin rahmarsa".

Da amin ta amsa tare da ɗan runtse idanunta, tunanin Jasrah ce ya faɗo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, Allah sarki baiwar Allah, yadda Sharifat take bata shawara a kullum, yadda take nuna mata girman Allah a kullum sak yadda Jasrah take yi mata, suna yi mata kamanceceniya, ga shi bama su san juna ba bare ta ce suna da alaƙa ta jini, haka kawai Allah mai halitta sai komai nasu yana zuwa kusan iri ɗaya, wani lokaci idan Sharifat ta yi magana sai ya yi mata tamkar Jasrah ce a wajen take magana, tana yawan yi mata addu'a a kullum, dan tasan yanzu ƴan watanni ne da basu wuci biyar zuwa shidda ba suka rage a yanke mata hukuncinta, a ratayeta a kashe, innalilahi wa inna ilahir rajiun.

A wani ɓangaren na zuciyarta kuma wani tunani ne ya faɗo mata, shiru ta yi tana tuna lokacin da mahaifiyarta take magagin mutuwa ga wuƙa a saman tsakiyar ruwan cikinta, ya fasa fatarta ya shiga har can ciki, faɗi take. "Leesharh ki yafe mun, ki yafe mun duk abin da na yi maki, nasan na cutar dake na ɗauki alhakinki, duk abin da kika yi a duniyar nan ba laifin kowa bane laifina ne, na yi danasani a lokacin da na rigada na san lokacin ta kure mun, amma dai ina sa ran zaki yafe mun, idan kin haɗu da Abbanki ki ce ya yafe mun, haƙiƙa na cutar da ku, sai magana ta karshe kuma shi ne........". Wani irin zabura ta yi tare da furta.

"Hakan ba zai yiwu ba mama, ni ba zan taɓa yarda da waɗan nan kalaman naki ba".

Tsoratar da Sharifat ta yi tare da miƙewa zata gudu ne yasa ta farga ashe a duniyar gaske ta yi maganar ba'a duniyar mafarki ba, hakan yasa ita ma ta miƙe tsaye tana faɗin innalilahi wa inna ilahir rajiun.

Ta lura idan bata yi hankali ba watarana tunanin mahaifiyarta zai iya sanya a ce mata tuburar mahaukaciya.

"Bloody zaki sa na gudu, tunanin me kike yi haka har zancen zucin naki ya fito da karfi?".

Komawa ta yi ta zauna tana wani irin sauke numfashi kamar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi, dafe saitin zuciyarta ta yi tana huro iska daga bakinta, bata iya amsawa Sharifat amsarta ba saboda ruɗewa.

"Bloody yakamata ki dai'na yawan tunani, kinga a yanzu tunani ya fara sanyaki kin fara surutai da karfi a bayyane, na ce maki addu'a zaki rinƙa bin mama da shi, ni tashi mu je mu yi breakfast ma, amma kafin nan ki rakani na kaiwa su Yah Ramish abincinsu, mu dawo mu yi namu breakfast ɗin, Abbie kuma yana kiranki a kan result ɗinki ne, dan ya ce yana son week ɗin nan ki fara zuwa school".

Shiru ta É—an yi kafin ta amsa da. "Ni dai Brat ba zan je wajensu Yah Ramish ba, sannan ni breakfast É—in ma mu yi namu a nan ba sai mun je main parlourn ba, sai ki rakani wajen Abbie É—in daga haka na amsa kiran nasa".

"Oh oh oh yanzu na gane dalilinki na kin zuwa amsa kiran Abbie kika wani fake da cewa baki gane hanyar ba, dama naji ne kawai amma ban yarda ba, wai bloody sau nawa zan gaya maki ki dai'na ɓoye mun abin da Ummiena take yi maki? Dama na yi tunanin yadda ta baro room ɗin Abbie ɗin nan da wuya idan baku ci karo ba, ban yi tunanin zata fita a lokacin bane shiyasa nakiraki nace ki zo, nasan ita ta hanaki shiga ko?". Ta kai karshen maganar tare da komawa ta zauna.

Girgiza kai ta fara yi. "A'a ni Ummie bata yi mun komai ba, kuma bata hanani shiga ba, ban ma haɗu da ita ba, kawai dai hanyar ce ta ɓace mun". Ta yi maganar kai a ƙasa.

"Bloody kenan, watanninki almost 6 a gidan nan amma ki ce wai hanyar zuwa É—akin Abbie daga nan ne ba zaki gane ba? Anyway yanzu dai zo mu je mu kaiwa su Yah Ramish abinci, kin ma san me nake tunani ne?".

Girgiza kai ta yi alamar a'a, a cikin zuciyarta kuwa ta furta Alhamdulillah da Allah yasa zata canza masu topic na hira.

"Addu'a nake yi Allah yasa Yah Bilal ya kamu da sonki, kinga ina son Yah Ramish sai kawai a haɗa aurenmu, matsalar ma ke ɗin nan wawiya wawiya ce, sai ki rinƙa cewa kina jin tsoronsu, ba fa abin da zasu yi maki, dan kuwa su ɗin basu dukan mata, Yah Ramish ya ce me abin duka a jikin mace? Wai idan ya ce zai daki mace mutuwa zata yi, shiyasa baya farawa, nima idan na yi masu laifi harara ta kawai suke yi a wuce wajen, dan haka ki dai'na tsoronsu kema kin ji?".

Kai kawai ta gyaÉ—a mata alamar to, amma batun ta dai'na jin tsoronsu kam babu shi bai taso ba, dan fa dole a ji tsoronsu, zaratan samari irin haka ai dole hantar ciki ta kaÉ—a idan ta gansu.

"Yauwa my gurl, ki rinƙa tsara kwalliya idan zamu je wajensu, Ummie na ta ce in dai ina son shawo kan Yah Ramish har ya fara ɗaga idanu yana kallona to sai da hakan, dan haka kema ki ɗaura ɗamayar sace zuciyar Yah Bilal saboda mu auri yaya da kaɗin zan yi farinciki da hakan".

Okey nan dai da shi kawai ta bita, dan kuwa dai ba É—aukar shawarar nan tata zata yi ba, ita kaÉ—ai tasan abin da ya kawota gidan, ba auren É—an gida ta zo yi ba, dan haka babu ruwanta da su, yanzu ma jiran ranar da masu nikaf zasu É—auketa kawai take yi, dan tasan dole zasu É—auketa kamar yadda suka kawota, ta san suna kewaye da ita, duk wani motsinta suna samun information a kai, ga shi yanzu ma daga saya mata waya jiya har sun sani sun kuma samu number.

"Yanzu gaskiya ki yi wanka ki canza kayan nan mu je kai masu breakfast, sai mu zauna mu ɗan yi hira a wajensu, dan ma dai Yah Rizwan baya nan, shi ne abokin hirana, su sauran basa magana, sai dai ki zauna shiru kina kallon film". Ta kai karshen maganar tana miƙewa tsaye.

Okey nan dai shi ta sake amsa mata da shi tare da miƙewa ita ma, har ga Allah bata so binta part ɗinsu ba, dan ita bata son hanya ma yana haɗata dasu ba batun zuwa in da suke ba ma tukun nan.

Sharifat fa wayayyiyar yarinya ce sosai, idanunta a buɗe suke, gata da iya soyayya dan mayyar kalle kalle film ɗin turawa ce, kada ku manta na gaya maku tana da yawan karance karance da bincike bincike, ta iya bada shawarar yadda za'a sace zuciyar namiji, amma ita kuma ta kasa sace zuciyar Yah Ramish ɗin nata, ko kallon ma bata ishe shi ba, dan shi ɗin wani irin bahagon mutum ne ba mai iya mashi sai Bilal and mamarsa, ko King Zuhair wani lokaci hakuri yake yi kawai ya kyalesa, ita maman nasa kawai ya san girma da darajar mahaifiya ce yasa baya musa maganarta komai ƙankanta, hakan yasa ake ganin kamar ita ce kawai take iya mashi, ba wani nan, kaunarta yasa hakan.

Shi kuma Bilal shakuwar da take a tsakaninsu da tsananin kaunar juna yasa idan ya ce yana son Ramish É—in ya yi abu to yana yi dan kauna, suna iya sadaukarwa juna da abubuwa sosai, hakan yasa ake ganin kamar Bilal É—in yana iya mashi, kaunace kawai shi ma.

Toilet Sharifat ta nufa, wanka ta yi, yau da kanta ta ciro masu kaya masu shegen kyau, Italians gown ta fitar masu, kayan daidai yake da shape É—in jikinsu, yana É—aya daga cikin kayan da suka sayo lokacin da Bilal ya kai su shopping.

Ita ma Leesharh wanka ta yi suka tsara shirunsu, yau Sharifat É—in ce ma ta yi wa Leesharh kwalliya, wai duk dan ta sace zuciyar Bilal, ni kam naga ikon Allah, ita ta kasa iya sacen zuciyar nata masoyin amma tana tsarawa wata yadda ita kuma zata saci zuciyar wani, abin dariya wai yaro ya tsinci hakwara.
Chapter 114 · 0% Book details