← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 211

Sashe 120

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummynsa ce take ta kiransa a kan ya zo gida da wuri akwai ɗan ƙaramin party da suka shirya, yau iyayen Heleena sun zo daga ƙasar England, shi ne suka shirya party, ba komai ne kuma ya kawo iyayen Heleena ɗin ba face sun zo ne domin ayi maganar aurensa da Heleenar....... Babbar magana, har sun bani bazawarar dariya 🤣

Abin da baku sani ba shi ne, Heleena zaman Smart take yi a cikin gidan, tun da ta yi wayo ta san menene soyayya, ta san kanta take fama da son shi, ta kafe shi take so, tana bala'in tsoronsa sannan tana haukar sonsa, iyayenta sun san da zancen, shi ma mummynsa ta sani, shi da daddynsa ne kawai basu san da zancen ba, dan su fa idan daddy ya san abu to tamkar shi ne ya sani, idan kuma shi ya san abu to tamkar daddyn ne ya sani, yadda kuka san twin's wlh, kuma wai uba da ɗa, ko da yake shaƙuwa ce ta yi yawa.

Mum ta ƙasa iya gaya mashi Heleena fa shi take jira, shi take so yasa ma ta yarda har yanzu take tare da su, tana tsoron gaya mashi ne kada ya tayar mata da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali, tasan a duniya ya tsani mutum maras kunya, ita kuwa Heleena badan badan bama sai ace ita ta kawo rashin kunya duniya, tsabar bata da shi ko ɗigo, shiyasa ya tsani ganinta kamar ba gobe, sam basa shiri.

Sun gama shirin komai shi da daddynsa kawai ake jira su zo a tattauna a tsayar da magana, daddy ma yana office yana ta tikar aikinsa bisa gaskiya da amana, yana ta ganin call É—in mum É—in amma yaki É—agawa, dan yasan ita fa idan bata je office É—inta ba bata da aiki da ya wuce ta zauna ta É—aura kafa É—aya bisa É—aya ta yi ta danna masu kira a kan su dawo suma su haÉ—u su jibge a gidan suna kallon juna, ba aikin fari bare baki da zasu yi mata, kawai su zauna suna ta ganin juna, ai mummy duniya ce.

To da suka gane mata ne sai basu wani cika É—aukar call É—inta idan bata je office ba.

Wani call É—in ne ya sake shigowa cikin wayar a karo na biyu, sai dai ba call É—in mum bace.

Bluetooth dake kunnensa ne ya isar mashi da saƙon cewa ga number dake kiransa. Jin bana mum bane yasa ya yi picking.

Yana ɗaga kiran daga ɗayan ɓangaren a ruɗe wani fasashen murya ya fara faɗi. "Sir remain s few minutes, the bomb went off". Ba tare da ya amsa ba ya miƙe tsaye, cikin nutsuwar nan tasa ya nufi waje wayar na'a hannunsa.

Kai tsaye wajen wata F-15E Strike Eagle ya nufa, É—aya ne daga cikin jiragen da air force suke amfani da shi, shi ba air force bane amma yana amfani da irin jirgin a duk lokacin da yake son isa waje cikin gaggawa, dan jirgin tana da mugun gudun gaske.

Yana saƙo kafarsa waje wasu irin jiga jigan zaratan maza ne suka fara aikin sara mashi, tamkar zasu bauta mashi saboda biyayya.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya bar headquarters ɗin nasu cikin wannan eagle ɗin.

Bai jira a ko'ina ba sai a lotus forest, gabaɗaya wajen harta bishiyoyin dake kewaye da wajen snow na mamayesu except wajen da jirgin nasa ta sauƙa. Wajen ana tsabtace shi ba'a barin snow a nan.

Already an rigada an shirya komai shi kaÉ—an ake jira, jami'ai ne da dama cike a wajen, dukkansu fararen fata ne tas.

Suna ganinsa a guje suka nufosa, jami'a,i zasu kai goma karti da su, haka suka nufosa, wasu daga cikinsu suna riƙe da bomb hand gloves, wasu kuma bomber jacket.

A tsananin zafafe suka fara sanya mashi bomber jacket and hand gloves É—in, sauri sosai suke yi domin bomb É—in saura Æ´an mintuna ya tashi.

Cikin nutsuwa yana taku a hankali ya nufi wajen, ji jami'an suke yi tamkar su janyoshi da sauri su ƙarisa da shi wajen, dan rayukan ƴan uwansu ne yake a haɗari, kuma shi kaɗai zai iya cetansu, sai dai ɗan banzan jan ajine da shi na masifa.

Wayarsa ce ta fara kara, call É—in mum ne, dan ya tsokaneta sai ya yi picking, bai bari ta fara jefa mashi tambayoyi ba ya ce. "Mum i am near the bomb, I will remove it from some of our officers, so i will call you later".

Habawa ai mum tana jin wannan labari ta miƙe tsaye, duk da tasan wanenen shi ɗin a kan aikinsa, amma ita wannan batu na bomb yana ɗaga mata hankaki sosai,........ Ni kam na ce dan ma baki san har nuclear ɗan albarkar ɗan nan naki yake haɗawa ba kenan! Da kin sani sai yaya kenan?.

A ruÉ—e ta fara faÉ—in. "My baby, take care of yourself, don't let something to happen to you, take care".

Katse kiran kawai ya yi tare da tura wayar a aljihunsa, dama dan ya tsokaneta ya yi hakan.

Jami'ansa tsabar ƙaguwa da son ya zo ya ceci rayukan ƴan uwansu har kamar su kai hannu su janyo shi izuwa wajen bomb ɗin, tsabar isa da jan aji shi kuma ya tsaya yana waya. Abin abin takaici

Nasan zasu ce wani bomb ne akewa haka? To dai sai gobe zaku ji komai........🥱🤪

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 31/10/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

E32

Jami'ansa tsabar ƙaguwa da son ya zo ya ceci rayukan ƴan uwansu har kamar su kai hannu su janyo shi izuwa wajen bomb ɗin, tsabar isa da jan aji shi kuma ya tsaya yana waya. Abin abin takaici.

Kowannensu zuciyarsa sai bugawa yake da sauri sauri, a cikinsu akwai jami'in da duk jarumtarsa kuka ya fara yi, idanunsa sun cika tab da kwallah, saboda akwai yayansa a cikin jami'ai shidda da suke sarkafe da rigar boma boman, shiyasa ya fara kuka, dan Smart ya ɗaga masu hankali, baya abu da sauri dan iskanci, saboda yasan shi kaɗai ne zai iya, dole a jirasa idan ana da buƙata.

Gabansu ya ƙariso, shi kansa ya girgiza da ganin jami'an nasa, gabaɗayansu ɗaure suke da rigar bomb, jami'ansa da ƙasar America ta kama ne, da Smart ɗin ya buƙacesu a hannunsu ne suka yi masu wannan abin, duk suka sarƙafesu da boma boman da koda minti goma aka baka ka kashe bomb ɗin har ya tashi ba zaka iya sanin me yakamata ka taɓa a jikinsu dan kashe su ba.

Ga shi su dukka shiddan aka É—aurawa, bayan haka dukkansu time na tashin bomb É—in nasu lokaci guda ne, kafin ya cire na wasu na wasu zai iya tashi, wannan dalilin ya É—aga hankulan sauran jami'an da suke wajen, shiyasa kuka ga wancan jami'in ya fara kuka, sai dai dukkansu sun san in dai Smart ya ce zai cire, to Æ´an sakanni sun isheshi, dan yana haÉ—a boma boman da suka fi waÉ—an nan haÉ—ari.

A gabansu ya tsaya dukkansu suna zaune saman chairs da sauran jami'an suka kawo masu. Tsabar suna cikin haÉ—ari ma a jiragen Rockwell B-1B Lancer aka turo su, sun ki sanyasu a normal jirgi, saboda gudun fashewar bomb É—in.

Calmly ya furta. "Jack come and remove all the camera's that have installed for them".

Zaro idanu suka yi, fuskokinsu ɗauke da mamaki, kallon kallo suka fara yi wa junansu, gaskiya Smart ya cika ɗan baiwa, sun duba jikunan jami'an nan nasu tas su basu ga wani abin ɗaga hankali a tattare da su ba, shi daga zuwa ya ga an sanya masu camera a jiki, wato dole dai America tana son kama shi da komai kanƙantar abar zargi, kunga idan ya cire ko ya kashe masu wannan bomb na jikin nasu cikin ƙanƙanin lokaci, in America ta ga da gaske shi ya cire ta hanyar waɗan nan camerorin to fa zasu ce wlh duk yadda aka yi yana haɗa irin boma boman, tarko suka haɗa mashi.

Cikin sauri suka fara ciccire masu camera's ɗin, shi kuma yana nuna masu in da suke, irin ƙanaƙnanan cameran nan ne waɗan da ake ɓatar dasu a jikin botrin riga, sai ka cika mai kaifin basira zaka iya zaƙulosu.

GabaÉ—aya bombs É—in saura five minutes su tashi, jikin wasu jami'an har kerma yake wajen cire camera's É—in, dan tsoron kada ya tashi da su. Shi kuwa yana tsaye yana aikin shafa lallausan hair É—insa.

Bayan sun gama cirewa ne ya ɗan rage tsawonsa ƙaɗan ya fara aikin kashe bombs ɗin, bai yi yunkurin cire masu ba, kasheta ya yi kawai, dan cirewa zai ja lokaci.

Na karshe da ya zo cirewa saura one minute ta tashi, boma boman da kafin ka ciresu a matsayinka na kwararema sai sun ɗaukeka sama da ten minutes, amma shi ya ciresu dukka in less than five minutes tsabar ya kware a iya haɗasu, kuma yana da tsananin nutsuwa ne, irin wannan aikin kuma dama tana buƙatar nutsuwa sosai, ga misali ma kun gani, jami'ansa da yake suna cikin tashin hankali kunga ai basu ga camera's dake jikinsu ba, shi kuwa kunga ai yana zuwa ya gani.

Umarni ya basu a kan su kwashi jami'an izuwa hospital ɗinsu na headquarter. Allah sarki har sun cire rai da rayuwa, dan basu taɓa tunanin za'a cire masu wannan bombs ɗin ba, sun jigata sun sha bakar wahala, kafin ya sanya daddynsa ya yi magana da America ta sakar masu jami'an wlh sun azabtar da su ba kaɗan ba, da kyar ma suka samu aka sakesu.
Chapter 120 · 0% Book details