← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 211

Sashe 9

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nutsuwa ta sanar da King abin da yake faruwa na Chuchu tana zazzaɓi, amma bata sanar da shi abin da ya faru a daren jiya ba, ta ɓoye saboda dalilin ɗaya zuwa biyu, ba wani dalili bane kuma face ta yi tunanin koma wanenen ya shiga ɗakinta ya yi ƙoƙarin keta mata mutunci to ɗan gidan ne, dole kuma tsakanin Jawad da Jaish ne, ita bata san Jaish baya nan ba, so ta ce dole tsakanin su biyun nan ne, dan sune kawai mazan gidan da suke nan, wannan dalilin yasa ta yi shiru bata yi maganar ba, tana son idan Chuchun ta samu lafiya sai ta tambayeta wanenen ya yi ƙoƙarin yi mata hakan? Idan ta gaya mata sai ta san matakin da zata ɗauka, wannan dalilin yasa ta yi shiru bata yi magana ba.

King ya ce mata yana zuwa ya duba jikin nata, Aunty MieMie da Yah Jawad suka miƙe tare da faɗin bari su dubo jikin nata, mummy dai tana zaune bata ce ko uppan ba, kamar Chuchun ba yarta na cikin ta bace, da alama tana da alkunya da kawaici sosai, tun da taga momma ta tsaya a kan rashin lafiyar ƴar tata sai ta kawar da kanta kamar bata jin zafin a kirjinta, alhalin kuma ta shiga damuwa sosai.

"Raeesa ki zauna akwai maganar da zan yi dake, idan mun kammala sai mu dubo jikin nata kafin na wuce fada". Cewar King, ya yi maganar ne kuma da Aunty MieMie, ita ce sunanta na gaskiya Raeesa, MieMie kawai sunan gida ne da mummyn tasu ta sanya mata, kasancewar ita ce ƴar farin mummyn shiyasa bata kiranta da Raeesan ta sanya mata MieMie, da haka sunan ya bita har izuwa yanzu, Raeesan ma ya ɓace, King ne kawai yake kiranta da sunan, da yake shi da sunansu da ya yanke masu yake kiransu dukkansu, Guyson ne kawai baya kiransa da Omar ɗinsa sai kuma Zunaira da yake cewa Auta, my Saeadati ya ke kiran Guyson, wato farincikinsa kenan, su biyun nan ne yake kiransu ba da sunansu ba.

Komawa Aunty MieMie ta yi ta zauna kamar yadda daddyn nata ya bukata, ita kuma Momma suka tafi tare da Yah Jawad É—in.

Suna shiga ɗakin suka sami Chuchun ta miƙe zaune suna hira da Auta, da alama ma kamar labarin abin da ya faru da ita daren jiya take gayawa Autar, dan ga alamar tashin hankali game da mamaki haɗe da tsoro sun bayyana a saman fuskar Autar.

Suna jin motsi shigowa ɗakin suka kai kallonsu izuwa bakin kofar ɗakin. Ai kuwa Chuchu na yin ido huɗu da Yah Jawad ta kusa haukace masu. Ihu ta fara zundumawa tana ƙoƙarin gudu ta sauka daga gadon, ko ina zata je idan ta sauka?.

Da kallon mamaki bawan Allah shi da mommar suka bita da shi, ta datse idanunta gam tana zunduma ihu, sai ƙoƙarin sauka daga gadon take yi, ita kuma Auta ta riƙeta gam ta hana ta sauka, sai tambayarta lafiya me yake faruwa take yi.

Ƙarisowa cikin ɗakin suka yi, da sauri momma ta riƙeta tana faɗin. "Jannat lafiya? Meyake faruwa ne?".

Banda ihu babu abin da take zundumawa, da alama bata jin me suke faÉ—e. Saman bedside drawer Yah Jawad ya zauna, cikin sanyin murya ya furta. "Jannat lafiyarki kuwa?".

Habawa ai tana jin muryarsa ta kara zunduma wani irin ihu mai sauti, ga shi kuma ta kasa iya yin magana, kamar wadda aka shaƙewa maƙogwaro magana ba zata fita ba.

Kallonsa Mommar ta yi da mamaki fal a face É—inta. Zarginsa ne ya dira mata a ranta, dama su biyu ta É—aurawa ayar tambaya shi da Jaish, to kuwa tun da Chuchun ta gansa ta birkice masu har haka dole a sanya mashi ayar tuhuma.

Bawan Allah shi kuwa da bai san komai ba sai ƙoƙarin rarrashinta ma ya fara yi, dan zuciyarsa tana yi mashi zafi na wannan ihun da take yi, ji yake yi ba zai iya jurewa ba. Ita kuwa Chuchu ta ki bada haɗin kai ta yi magana, banda ihu ba abin da take yi, idanunta ma a datse gam, bazama ta budesu ba bare ta yi ido biyu da shi.

"Jawad jeka kai kam, barni da ita". Momma ta faÉ—a tana hayewa saman gadon. Ba musu ya tashi ya fice, sai dai ransa bai so ba, ya so ya rarrasheta ya ji me matsalarta? Amma bai isa ya ce da momma ta bari ya rarrasheta ba, sai kawai ya bi umarninta ya tashi ya fita fuskarsa a É—auke da damuwa fal. Mommar kuma ta yi mashi hakan ne domin ta tabbatar da zarginta, so take ta ga da gaske saboda shigowarsa yasa Chuchun kuka ne ko dai me?.

Ai kuwa yana fita ta rage sautin kukan nata sosai tana sauke ajiyar zuciya game da shessheka.

"Jannat wai me yake damunki ne? Me yake faruwa ne?". Ta yi maganar tana É—an rungumota. Lafewa a jikinta ta yi, cikin shesshekar kuka ta furta "Momma ni bana son na sake ganin Yah Jawad, please ki ce kada ya sake shigowa cikin É—akin nan"...... Babbar magana!!.

Da mamaki Mommar take sauraron kalamanta har ta kai karshen, tambayarta ta yi me yasa bata son ganinsa?. Shiru ta yi ta ƙasa iya bada amsa, ita dai bata son ganinsa kawai ta sani.

Ganin ta kasa iya faɗar dalilin nata ne yasa Mommar ta fara zargin wani abin, da yake ita akwai ta da kaifin basira sosai, su twin's ma a wajenta suka gado rabin nasirarsu, tunani ta rinƙa yi anya Jawad zai aikata abin da take zarginsa a kai ɗin nan kuwa?. Ni ma dai PRINCESS TEEMA ina tantanma a kan hakan, ga shi shima dai Yah Jawad ɗin ya nuna kamar bai san komai ba, ko dai lumbu lumbu yake yi mana ne?🤔 Amma bari mu leƙa wani bangaren mu dawo, watakila kafin nan zamu samo mafita, dan komai a kulle yake yanzu, kila mu iya warwaresu idan muka dawo!!.

Amma kafin mu leƙa wani part ɗin bari na ɗan yi maku wani bayani a kan tambayoyin da nake sha, yau bari na baje maku amsar a faranti😂 to masu tambayata wanenen star na littafin RAWANIN ZALINCI, and wacece star mace, kun kasa iya gane star mace da star namiji bari na fara da amsa tambayoyinku, dan tun farko farkon book 1 nake samun waɗan nan tambayoyi, yau dai nace bari na amsa. Amsarku a nan shi ne kun manta nace maku littafin RAWANIN ZALINCI zai zo maku da sabon salon da baku taɓa ji ko karanta irinsa bane? Ton idan kun manta na tuna maku! Littafin RAWANIN ZALINCI yana da ɓangarori da dama! Sai dai shi salonsa daban ne, a kowani ɓangare suna da nasu rikicin da cakwakiyar, ba wai rubutu nake yi a kan abu guda ɗaya ba! No kowace ɓangare jigon labarin daban yake, ba family guda bane a cikin labarin, kowace family da nasu cakwakiyar da kuma saƙon da nake son isarwa, in short a kowace family tana da star ɗinta namiji da kuma mace, haka labarin yake, sabon salo ne da na tabbata baku taɓa jin irinta ba! Amma a gabaɗaya littafin akwai star guda ɗaya wanda ya fita daban da kowa, haka ita ma macen akwai guda ɗaya da ta fita daban da kowa, ku cigaba da hasashenku daga macen har namijin kila zaku iya ganesu kafin alkalamina ya afka cikin labarin sosai ta yadda zamu zaƙulosu😅 so a takaice dai RAWANIN ZALINCI yana da ɓangarori da dama, sannan ba family guda nake rubutu a kansu ba, family's ne daban daban, kuma kowani family da cakwakiyarsa na daban, sannan yana da star ɗinsa mace da namiji, sabon salo na kawo maku ai🤨

Sai masu yawan tambayata tun lokacin da nake tubuta littafin TRIPLETS har izuwa kan RAWANIN ZALINCIN a kan rubutun, kuma bari na baku amsa. Ana yawan yi mun tambaya a kan yadda nake rubutu part part daban daban and kowani part da nashi cakwakiyar, sannan familys daban daban, nasamu tarin tambayoyi a kan cewa labarin baya haɗe mun ko kuma akwai wanda take tayani rubutu ne yasa baya haɗe mun kuma bana mantuwa sannan bana ɗauko cakwakiyar familyn nan na sanya a cikin familyn nan dan mantuwa, to ga amsarku, a gaskiya babu wadda ta taɓa rubuta mun ko A a cikin rubutuna, ni da kaina nake zama na ɓata awa huɗu zuwa biyar ina rubuta maku labarin, haka nake raba dare ina rubutu, haka zan sanya ƙwaƙwalwata busy, zama nake yi in kirkiro labarina, na tsara shi yadda zai kasance a cikin ƙwaƙwalwata kafin na fara rubutawa, babu wanda ta taɓa taimaka mun da ko A, wai taya ma za'ayi wani ya yi maka rubutu ne?🤔 Ai ba zai yiwu ba, domin labarinka a cikin ƙwaƙwalwarka yake ba'a ƙwaƙwalwa wani ba, ai ba zai taɓa iya rubuta maka shi yadda zaka rubuta ba, in short babu wadda ta taɓa tayani da ko A, ni nake zama in kirkiro labarina in kuma tsara kayana, sannan in hau rubutu na ni kaɗai har in kammala shi, kamar wata computer nake aiki, ni ko irin true life story da ake karɓa a rubuta ma bana yi, akwai wadda ta taɓa cewa zata bani labarinta na rubuta a cikin grp ɗina, duk wadda take cikin grp na PRINCESS TEEMA ina tunanin taga hiranmu da matar a lokacin da ta ce zata bani labarinta na rubuta nace mata a'a banaso, abin da yasa kuma shi ne, labarin da zan ƙirƙiro da ƙwaƙwalwata sai ya fi bani damar isar da saƙona ga al'umma cikin sauki, duk ta yadda nake so zan tsara labarina da na ƙirkira saɓanin true life story, so ni ba zan iya karɓar labarin wani or wata ma na rubuta ba, na fi son na ƙirƙiro kayata da kai'na ta yadda zan sarrafa shi yadda nake so, na isar da saƙona ta sigar da nake so, na ilmantar da al'umma ta sigar da nakeso, na tafi da komaina ta sigar da nake so, na juya kayana upside down yadda nake so, wannan shi ne, fatan kun gane?! Yau dai kun samu amsoshinku dukka!!. To mu cigaba da labarinmu.

JIMETA..........NIGERIA💘🔥
Chapter 9 · 0% Book details