← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 211

Sashe 187

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dik ranar da suka haɗu kwana yake yi baya barci, tun farkom dare har karshenta tunaninta zai kasance yana yi, sai idan ya ji zuciyarsa na neman azabtuwa sosai ne sai ya miƙe ya ɗauro alwala ya zo ya fara nafilfili domin ya rage tsawon dare, amma barci kam sam baya rintsawa, tana ransa a kullum, da ita yake wuni ya kuma kwana ya tashi, ya yi mafarkinta a duniya babu adadi, baki ba zai iya zayyana yadda yake ji a kanta ba.

"A lokacin da King ya sanyani kula da ita sai da na ji tankar na zuba ruwa a ƙasa na sha saboda daɗi, ban taɓa son wani abu a duniya kamar yadda nake sonta ba, amma dik nasan a banza ne, nasan sai dai na mutu da soyayyarta a cikin zuciyata". Ya kai karshen maganar yana ɗago da idanunsa da suka rikiɗe a take suka yi jajir.

Sam Ansar bai yi mamakin ganin idanunsa sun rikiÉ—e sun yi jajir ba, saboda yasan wanenen shi, akwai taurin zuciya da iya shanye abu, sai dai kaga alamarta a cikin idanun nasa.

Matsowa Ansar ya yi ya dafa saman shoulders É—insa dikka biyu, cike da tausaya mashi ya fara magana kamar haka.

"Hoorain ka dai'na cewa soyayyar da kake yi wa gimbiya maras amfani ce........".

"Ansar idan ban kirata da maras amfani ba me kake son na kirata da shi kenan?".

"Hoorain wlh soyayyarka a gareta ba maras amfani bace". "Saboda me zakace hakan?".

"Saboda kasani kuma kasan nasan kasani gimbiya ita ma tana sonka, tana sonka kamar yadda kake sonta".

Girgiza kai ya fara yi. "No Ansar, tana dai sona, amma ba kamar yadda nake sonta ba, badan iyaye iyaye bane da sai nace nama fi King sonta, amma ina da tabbacin nafi su Prince Jaish sonta".

"Sannan soyayyar da take mun shima dik na banza ne, ita ma wahala zata sha kawai kamar yadda nake sha, dan sanin kankame dik cikin masarautar nan ita kaÉ—ai ce ma take daga idanu ta kallemu". Zuciya babu daÉ—i ya kai karshen maganar.

"Hoorain zaka yi nasara, wlh trust me, ka É—auki shawarata ka bayyana mata soyayyarka, in har soyayyar gaskiya Æ´an uwanta suke yi mata to dole su baka aurenta a lokacin da zata ce masu babu wanda take so sai kai, idan har baka gaya mata kana sonta ba to ka sani tabbas za'a yi mata miji ne a cikin gida, in kuma hakan ya faru babu abin da zata iya cewa dan bata san kana sonta ba, baka bayyana soyayyarka a gareta ba ba ta yadda za'ayi ta fito cikin Æ´an uwa tace bata son wani sai kai, think about it".

Shiru ya ɗan yi yana nazarin maganganun Ansar ɗin, sai dai kuma baya jin kamar zai iya aikata hakan, saboda shi ya fi Ansar sanin su wanenen Jaish, ba zasu taɓa yarda ko da sunan wasa a bashi ita ba.

"Trust me Hoorain, yanzu haka tana lambun daddynsu, tun ɗazun naganta a can, ka je wajenta, kada ka ɓoye mata gaskiya, ka bayyana mata kana sonta, da izinin Allah zamu yi nasara".

Wani irin daÉ—i ya ji na jin cewa tana lambu, dama tuntuni yake ta fama da kewarta a cikin ransa, yana son sanyata a idanunsa, dama ce kawai bai samu ba, amma kuma dik da haka fa bai É—auki shawarar Ansar ba, ya yarda zai je lambun dan yana son sanyata a idanunsa, amma ba wai zai je ya bayyana mata soyayyarsa a gareta ba.

"Gimbiya bata da dalilin kinka Hoorain, dik in da ake neman namiji cikakke ka kai nan har ma ka wuce, kyan fuska Allah ya baka, kyan zuciya Allah ya baka, kyan jiki Allah ya baka, jarumta da jajircewa, ina ga baya Abbo a kaf cikin kingdom ɗin nan babu wanda ya kaika jarunta, zama assistant commander ba karamin abu bane, na duba gabas da yamma gudu da arewa ban ga wani abin da zai sa a kiƙa ba". Cewar Ansar.

Hmmmmm jinjina kai kawai ya yi, shi kaÉ—ai yasan me yake hangowa. Dafa shoulders É—in Ansar ya yi. "My brother kai dai pray for me kawai, am coming bari in je ko ganinta ne na yi zan ji daÉ—i a rai'na".

"By the grace of god zaka mallaki gimbiya, ina yi maka wannan addu'ar our Lion amount the Lions".

"Thank you block brother". Ya yi magana tare da sake shi, cikin takun jarumta ya wuce ya nufi lambun. A lokacin ta fi awa tana zaune a wajen tana jiransa, har ta fidda rai da zai zo gareta sai kuma kwatsam ta hangosa ya shigo cikin lambun.

Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya a lokacin da idanuwansu suka sauƙa a kan face ɗin juna, shi ma ya ji daɗin ganinta, ita kuwa ji ta yi tamkar ta tashi ta je ta rungumesa saboda tsabar farinciki.

Idan ta kallesa sai taga kamar baya ganinta, amma tin da ya shigo idanunsa suke a kanta, sai dai ya ji babu daÉ—i a cikin zuciyarsa na ganin kamar tana a ciki damuwa sosai.

Ita kuwa tana mutuwar son ganin yadda yake tafiya, yanayin tafiyarsa akwai ɗaukar hankali, sai ka yi zaton baya taka kafafunsa gabaɗaya a ƙasa, in ka kallesa a fisge zaka yi zaton da iya yatsun kafafun nasa kawai yake tafiya, amma sam ba haka bane, kawai jarumta ce da zafi wajen saurin tafiya yasa hakan.

Tun bai gama ƙarisowa gabanta ba ta shagwaɓe fuska tana faɗin. "Hoorain tun ɗazun fa nake jiranka, sai yanzu zaka zo?".

ÆŠan zaro idanu ya yi yana mamakin jin cewa tun É—azun shi take jira, to ai shi bai san da tana jiransa na. Amma sai bai nuna mata bai san shi take jira ba, sai ya ce. "Kiyi hakuri ranki ya daÉ—e".

"To zauna mu yi magana". Ta yi maganar tana nuna mashi saman sofa.

Sanin cewa yau brothers É—inta dik suna nan yasa ya É—an girgiza kai. "A'a ranki ya daÉ—e mu yi maganar a haka ina tsaye".

"Kana tsoron su Yah Ramish ne?". Ta jefa mashi tambayar idanunta a kansa.

"Wani abu makamancin hakan dai". Ya faÉ—a ba tare da ya kalleta ba.

"E sai dai wani abin makamancin hakan, amma dai ba tsoro ba, dan kuwa ni nasan my hero baya jin tsoron komai".

Shiru ya yi kansa a ƙasa bai furta uppan ba.

Shiru ita ma ta ɗan yi tana ta kallonsa. Sarai yasan shi take kallo, har ga Allah tausayi take bashi, yana jin kamar ya zubar mata da kwalla, yasan ta kamu da sonsa sarai, amma kuma yana ji a jikinsa ba zasu taɓa mallakar juna ba.

"Hoorain Yah Jawad É—ina bashi da lafiya, na rasa ina zan je na ji daÉ—in rayuwata shi ne nace kazo mu yi hira dan nasan tabbas zan samu farinciki da nutsuwa idan ina tare da kai, amma kuma shi ne zaka ce ba zaka zauna mu yi hira ba ko?". Ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka.

Ai bai san lokacin da ya juyo saitinta da kyau ya kuma ɗago ido ya kalleta ba, bai taɓa tunanin tana ɗaukarsa a matsayin mai sakata farinciki ba, shi dai ya san tana son shi, bai san soyayyar tasa ta kai har haka a ranta ba, Allah sarki wai bari ta zo wajensa tasan zata samu farinciki, bai yi zaton muhimmancinsa ya kai haka a gareta ba, ai kuwa bai kamata ace ta tafi bai sakata wannan farinciki da ta fito nema ba, sai dai kuma baya son ƴan uwnata su samesu a haka, yasan nan lambun daddynsu ne, kowa yana iya zuwa a kowani lokaci. Amma da ya tuna cewa farincikinta ya fi mashi komai sai ya matso ya zauna saman sofa.

Kasa ya É—an yi da kai yana tunanin to shi me zai ce mata ta yi farinciki ne wai?...... Yau ake yinta, masu abin fa suna magana, wayyo Allah shi da bai san komai ba face sare kawunan mutane a yaki ne zai sata farinciki, ina ga sai dai ya bata labarin kalar takobin da ya fi kaifi da kuma yadda ake sare wuyar mutane, yo in ba shi ba shi me ya sani? Dik tsawon rayuwarsa ya bata ta a yaki, bashi da wata abin da ta fi wannan.

Ya ɗauki almost 10 mins shiru kansa a ƙasa, ita ma ta yi shiru tana ta kallonsa, ko ba komai ta ji daɗi ya zauna, sai bata furta mashi uppan ba.

"Kiyi hakuri gimbiya, In Sha Allah Yah Jawad zai sami lafiya nan ba da jimawa ba". Ya faÉ—a kamar mai raÉ—a, kun san cewa abin da ya faÉ—a É—in nan ita yake ta tunawa har na wannan tsawon 10 mins da ya zauna shirun? Kurma kenan, sam bai iya magana ba.

"Allah yasa, amma kasan me ya sa Yah Jawad rashin lafiya kuwa?".

Kai ya girgiza mata ba tare da furta uppan ba.

"Yah Jawad yana son Aunty Chuchu, ita kuma ta fara soyayya da Yah Rizwan kafin Yah Jawad ya gaya mata yana sonta, to da dad ya tanbayeta waye take so sai ta ce Yah Rizwan alhalin ita ɗin ma Yah Jawad take so ba Yah Rizwan ba, ni kai'na na rasa dalilinta na zaɓar Yah Rizwan, bayan kuma ni da ita ta ce mun Yah Jawad take so, Yah Jawad fa tun tana ƙarama ya ce mun yake sonta, shi kuma Yah Rizwan sai da ta girma, jibi za'a ɗaura aurenta da Yah Rizwan to shi ne Yah Jawad ya fara rashin lafiya da ya ji hakan, ita kuma Aunty Chuchu na ce mata ta je ta gayawa daddy ita Yah Jawad take so ba Yah Rizwan ba, amma ta ce mun ba zata iya ba, ni yanzu ma na rasa me zan yi, shiyasa ina cikin damuwa sosai, dan Aunty Chuchuna ma bata da lafiya kamar dai Yah Jawad". Ta kai karshen maganar idanunta cike tab da kwallar.

Tun da ta fara magana yake kallonta ta kasar ido, kansa kawai ya tuna, ashe a tare suka yi dakon soyayya shi da Yah Jawad, a gaskiya ya tausayawa Jawad ma bare kansa da bai san matsaya ba bai san a wani mataki yake ba a yanzu, dik sai ya ji ya karaya.
Chapter 187 · 0% Book details