← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 211

Sashe 19

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banda tunanin Pretty babu wani abin da yake cikin ransa, jefi jefi yana tunanin Sweetie, kuma ya fi yin kuka mai tsuma zuciya idan ya tuna Sweetien, yana matuƙar tausayawa rashin idanunta, baya damuwa sosai idan ya tuna Pretty, saboda tana da idon ganin koma inane, amma Sweetie bata gani, idan Pretty bata dawo ba ya rayuwarta zai kasance? Wannan shi ne tunanin da yake cikin ransa a kowani lokaci.

Yana shiga matsanancin damuwa tare da fargaba sosai idan ya tuna cewa Pretty ta bazama cikin dajin nan, fargabansa kada ace wani abin ya sameta, kada ace ta mutu, kuma da alamun wani abin ya sameta É—in, dan duk lokacin da ya tuno sunanta kirjinsa ne yake duka da sauri sauri, gabansa sai ya yi ta mummunar faÉ—uwa, hakan yasa ya fara yanke kauna tare da daina tunanin tana raye ko ta mutu? Yana É—aya daga cikin dalilan da yasa yake horar da kansa da kin cin abinci dan ya mutu ya bi Prettynsa, zuciyarsa ta gama saddakarwa da ta mutu.

Har izuwa yanzu kuma Mamma bata jin kamar zata iya lallashinsa, ji take yi ta barshi dan dole zai sauƙo da kansa idan ya ji azaban wahala, ta manta da cewa ɗan na gada ya fi ɗan na koya, ita ma ta yi kafiya da zafin zuciya bare shi? Ai kuwa yana da kafiya sosai tare da jajircewa a kan sai ya cika muradinsa haɗe da taurin kai da taurin zuciya.

A takaice kenan halin da Mamma and Kamran suke ciki a yanzu. Bari mu leƙa wasu Familyns kuma muga halin da suke ciki.

KINGDOM OF POWER.💪🔥💘

Wasa wasa har kwana uku yau Chuchu bata yarda su haɗa hanya da Yah Jawad, babu kuma wanda ya san da wannan abin sai Momma. Duk yadda Yah Jawad ya so su haɗu taki yarda, ta tattara ta koma part ɗin Mummynta, dan can ne bai cika zuwa ba, idan ta ji zai zo sai ta koma part ɗin Mammiensa ko kuma na Mama, dan part biyun nan ne baya taɓa zuwa sai idan su ne suka kira shi, bai ma san a wani part takamaime take ba.

Ya tambayi Auta sai dai ta ce nashi ita ma bata ganta ba sam sam, kuma wlh tasa san in ta take, amma da yake kun san shakuwar da take a tsakaninsu, bakinsu É—aya sun iya rufawa juna asiri, yanzu haka Autar ma haushinsa take ji haÉ—e da tsoronsa, dan Chuchun ta gaya mata komai.

Abin ya dame shi matuƙa, ko ya kira numberta bata ɗauka, yau kwana uku bata zuwa school, ya shiga damuwa matuƙa, ya rasa ina zai sanya ransa, abubuwa sun haɗe mashi, ga shi idan ya kira number Jaish bata shi ga, yana cikin tashin hankali a kan hakan! Sannan ga wani tashin hankalin da ya faru a Dubai wanda Rizwan ya sanar da shi ya ce kada ya gayawa kowa dan suna iya ka bakin ƙoƙarinsu dan su shawo kan matsalar, sannan yanzu ga shi baya samun damar ganin sanyin idaniyarsa bare ta rage mashi raɗaɗin da yake ji, har zazzaɓi sai da ta kama shi, a halin yanzu ya fi shiga damuwa sosai a kan Jaish, shi ne a ransa, ƙoƙari yake yi ya ɗan samu lafiya ya ji kwarin jikinsa sai ya bi bayansa, dama ƙasar England ya ce mashi zai je, so yasan hotel ɗin da ya sauka ma, dan da ya sauƙa ya tura mashi saƙon a kan ya sauƙa lafiya da sauran bayanai, coz yanzu yana son ne jikinsa ya ɗan warware daga damuwar da suka yi mashi yawa sai ya bi bayansa ya je ya gani shin aiki ne ta yi mashi yawa har ya kashe wayarsa ne ko kuma dai wani abin ne ya faru?.

A safiyar yau ma sai da King ya tambaye shi ina Jaish? Da ya rasa me zai ce mashi sai ya ce ya tafi ƙasar Brazil wajensu uncle Jahiz yau da safen, ya rasa amsar da zai basu ne yasa ya ce masu haka, dan kullum idan suka tambaye shi sai ya ce masu bai dawo office da wuri bane, ya yi dare shiyasa yana dawowa ya kwanta, da sassafe kuma ya sake fita saboda aiki ta yi mashi yawa, kullum amsa ɗaya shiyasa yau ya canza amsar.

Sosai King ya yi faɗa a kan ya za'ayi ya yi yafiya ba tare da ya sanar da su ba? Idan wani abin ya je ya farufa? Allah ya tsare!. Sai hakuri Jawad ɗin ya rinƙa bashi, ya yi ƙoƙarin kiran number Jaish ɗin amma bata shi ga, sai ya yi tunanin ko dai yana cikin jirgi bai sauka bane yasa wayar bata shiga ba, da haka dai ya samu suka rabu da King ɗin.

Yana barin part ɗin King ya kira number uncle Jahiz ɗin nasu, wato ɗan autan Akka kenan kaninsu King. Yana kiransa bai ɓoye mashi komai ba ya sanar da shi gaskiya, sannan ya ɗaura da cewa King zai kirasu dan ya tabbatar da cewa Jaish yana tare da su, idan ya kirasu dan Allah su amsa da e, idan ba haka ba sun san halin King sarai. Da yake uncle ɗin nasu ma irin uncle Abbas ne, yana kaunarsu sosai kuma ya iya goya masu baya, sai ya yarda a kan e lallai za'ayi yadda suke so, amma Jawad ɗin ya yi saurin nemo in da Jaish ɗin yake, cikin raunin zuciya ya amsa da tabbas zai yi duk yadda zai yi ya dira a ƙasar England gobe ko jibi domin ya duba shi, idan ba haka ba za'a samu matsala, da haka dai suka bar zancen suka shiga hirar duniya.

Suna tsaka da yin hiran ne Momma ta kira numbersa, sallama ya yi wa uncle É—in nasu ta hanyar sanar da shi cewa Momma na kiransa bari ya É—auka, okey ya amsa mashi kafin su yi sallama ya É—auki kiran nata.

"Jawad ka sameni a parlourna yanzu". Shi ne abin da ta faÉ—a. Cikin sanyin murya ya amsa mata da okey ga shi nan zuwa.

Katse kiran ta yi shi kuma ya nufi part ɗin nata. Zazzaɓi sosai yake ji a jikinsa, da alama shakuwarsa da Jaish yasa yake yi mashi ciwon wahalar da ya shiga, kun san idan mutun biyu suka shaƙu, in ma mata da miji ne ko ƴan uwa, in dai shakuwarsu ta kai shaƙuwa zaku ga ko basa tare idan ɗaya ya shiga wahala ko tashin hankali sai kuga shi kuma ɗayan ya kamu da wani ciwo, ba dai ciwo mai tsanani can can bane, amma sai ku ga yana ta fama da ciwo, daga ya ce kansa na ciwo, sai ya ce zazzaɓi, mutuwar jiki, ko zafin jiki, haka zai yi ta fama da rashin kwarin jiki har sai randa wancan ya fito daga cikin matsalar da ya shiga, ana samun irin haka sosai a cikin al'umma. So shi dai ga shi yana yi wa Jaish jinya ba tare da ya sani ba.

A parlournta ya iskota zaune cikin kwalliya irin na hamshaƙan gimbiyoyi, da alama ma wajen King zata je, dan kwalliyar ta musamman ce.

Saman carpet ya zauna ta kusa da ita kafin ya ɗaga mata gaisuwa cikin girmamawa. Amsa mashi ta yi fuska ba yabo ba fallasa, sannan ta ɗaura da cewa. "Jawad ina Jaish? Yau kwanansa huɗu kenan ban sanya shi a idanu na ba, kuma sanin kanka ne baya taɓa yin kwana guda cur ba tare da ya zo in da nake ba, na kira numbersa bata shiga, na je part ɗinsa daren jiya misalin karfe 1 ban samesa ba, ɗakin nasa ma ya nuna mun alamar kamar ya kwana biyu babu mutun a ciki, saboda curtains na windows and balconynsa duk sun nuna alamar an kwana biyu ba'a taɓasu ba, kuyangun da suke gyara ɗakin nasa basa taɓa wajen, meyake faruwa? Ina ya tafi?".

Wani irin yawu mai wuyar wuce maƙogwaronsa ya haɗiye da kyar, sannan ya ɗan ɗago da kallonsa izuwa kanta. Ya rasa me zai ce mata, yasanta da kaifin ƙwaƙwalwa, sannan ita ta renesu shi da Jaish ɗin, yana yi mata karya zata ganosu, ta yi masu farin sani, ko da sunan wasa ya yi mata magana ba dai'dai ba tana ganewa cikin ƴan sakani bare da gaske, to yanzu ya zai yi da ita? King ya fita sauki, shi bai cika tsawwalawa sosai ba, ko ya gane ba gaskiya ka faɗa mashi ba yana kawar da kai sai ya yi bincike da kansa, ita kuma sai ta tirkeka ka faɗi gaskiyar da bakinka.

"Shirun da ka yi mun Jawad ya tabbatar mun da abin da zuciyata take raya mun, tun jiya bani da kwanciyar hankali, ina jin faÉ—uwar gaba da fargaba kamar wani abin ya samar mun É—aya daga cikinku, duk na kira Æ´an uwanka a waya suna lafiya, kai kuma muna tare da kai a nan, shi kaÉ—ai ne ban samu damar yin magana da shi ba, kuma shi kaÉ—ai ne idan na tuna shi nake jin faÉ—uwar gabana ya tsananta, ka gaya mun gaskiya me yake faruwa?".

Wani irin nisawa ya yi wadda da ka jita kasan yana cikin mawuyacin hali, muryarsa har wani ɗan sarkewa ta yi, ɗan gyaran muryar ya yi kafin ya ce. "Momma babu abin da ya samu Jaish, In Sha Allah yana cikin aminci tare da kariyar Ubangiji, tafiya ya yi izuwa ƙasar Brazil wajensu uncle Jahiz........"

Bai ƙarisa maganar ba saboda wani irin kallo da ta wurga mashi yasa ya shanye sauran maganar tasa. "Jawad ka manta cewa da Mommarka kake magana ne? Sam babu kamshin gaskiya a maganarka, faɗa mun gaskiyar dai ina sauraro".

Haƙiƙa sai da ya ji kirjinsa ya bada dum dum, dama yasan halinta sarai, ba zaka mata karya kuma kasha lafiya ba, sai ta kamoka, bashi da zaɓin da ya wuce ita dai ya gaya mata gaskiya ko dan ta tayasu da addu'a idan ma wani abin ne ya samu ɗan uwan nasa.

Ya sha madarar mamakin ganin fuskarta bai sauya ba duk da ya gaya mata gaskiyar halin da ake ciki, shiru ya yi yana tunanin ko dai dama tasan gaskiya ne? Ko dai gwadasa kawai ta yi?.
Chapter 19 · 0% Book details