← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 211

Sashe 39

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya Ronnie ya sauke tare da yin fito da bakinsa, ita dai Sweetie sai kuka take yi ba tare da kowa ya lura da ita ba, duk hankulansu na kan wasa.

Ronnie ji yake yi tamkar ya tashi ya taya Oxil faɗar nan, har wani tsuma jikinsa yake yi, sai ciza lallausan laɓɓansa yake yi, shi ala dole bugun da Oxil yake yi wa Feros ta yi mashi kaɗan........... Kash ana ƴan iska a cikin birnin Dark world wlh, kun ji mun Ronnie fisabilillahi my people's wai jibgar da ake yi wa Feros ta yi mashi kaɗan, Allah gamu gareka, Allah ka shirya mutanen birnin nan........😅

An gwabza wasa iya wasa, sun jibgi juna iya jibga, daga karshe Oxil ya yi nasarar kayar da Feros kasa a in da ya kasa tashi har commissionern wasannin wato master Devil ya ƙirga daga ɗaya zuwa goma bai miƙe ba, ya sha jibga ba kaɗan ba, shi ma Oxil ɗin dai da kyar ya sha, da kyar da suɗin goshi ya iya yin galaba, ya ci wuya, shi ma sai ya yi jinyar kansa, dan ya daku.

Ganin bai tashi bane yasa commissionern ya kama hannun Oxil tare da ɗagata sama a zuwan shi ya yi nasara. Nan take masoyansa suka fara ihu suna fito kamar zasu tashi wajen. Ronnie har da miƙewa da sauri ya raba Sweetie da jikinsa, cikin sauri ba tare da ya bi ta kanta ba ya wuce ya shiga wajen wasa, rungumar Oxil ɗin ya yi kafin ya sakesa suka fara taka rawa kamar me.......... Ashe dai Ronnie ya iya rawa.

Rawa sosai suka taka kamar west ɗinsu zai ɓalle shi da master Devil, da alama master ma yana team na Oxil ne, shi ko Oxil girgiza kai kawai ya tayasu, dan ba zai iya rawa ba, jiki duk ta yi tsami. Kiɗa mai dukan sautin gaske Dj Jack ya sakar masu, ba karya sun taka rawa, suna yi Ronnie yana fito da karfin gaske, da alama wannan winning ɗin da Oxil ya yi fa ya yi masu matuƙar sugar. Suma masoyansa sun takarawan nasarar da ya samu.

Sai da suka taka rawansu mai isarsu jama'a suna yi masu fito sannan ne Ronnie ya dawo wajen zamansa, sai a lokacin ya lura da Sweetie ta sha kuka har ta ƙoshi, ɗazun duk bai gani ba hankalinsa na'a kan wasan, burinsa kawai Oxil ɗinsa ya yi nasara. Rarrashin ta ya hau yi tare da tambayar meya sameta me aka yi mata take kuka?.

Shi kuwa master umarni ya baiwa wasu jaruman mayaƙa da su ɗauki Feros su sanya shi a wajen da suke datse wuyar wanda ya faɗi wasan wato head lock kenan. Ai kuwa basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen aiwatar da hakan, bayan sun kaisa wajen ne master ya ce Oxil ya je ya ƙarisa aikinsa, Allah sarki Feros da bai gama dawowa cikin hayyacinsa daga dukan da ya sha a hannun Oxil ɗin ba zai bakunci lahira.......Abin ya taɓa mun zuciya sosai.

Babu imani bare tausayi Oxil ya ɗaga wuƙa ya datse mashi wuya da ita, habawa sai jini ke feshi kamar fanfo. Fito jama'a suka sanya suna jinjinawa Oxil a zuwan ya yi jarumta ya yi abin kirki.

Wani irin azabbabbe kuma razanannen ihu Sweetien ta kurma na ganin ya fillewa ɗan uwansa wuya da wuƙa a gaban dubbannin jama'ar birni kuma sai jinjina mashi suke yi babu wanda ya ce ya yi ba dai'dai ba. Ihu ta kurma saboda razana kan kace me numfashinta ya ɗauke diff, bata taɓa ganin irin wannan bala'i ba a rayuwarta, a kullum fatanta idanunta su buɗe taga Kamran, ga idanun sun buɗe kuma ta fara cin karo da tashin hankalin da ta gwammaci makantarta ma ya fiye mata alkhari.

Ganin ta kurma ihu kuma ta sume ne yasa Ronnie ya kalli Floris kafin ya dawo da kallonsa kan Delisha. "Wai me yake damun yarinyar nan ne? ÆŠazun na ganta tana kuka, yanzu kuma ta suma, to me aka yi mata?". Ronnie ya tambaya da mamaki a saman face É—insa, wato dai shi wannan tashin hankali duk ko a jikinsa, kun ji ma wai tambaya yake yi me aka yi wa Sweetie ta suma?. Allah mai iko.

Jama'a sai ihu suke yi suna murna, su kuma team na Feros idanunsu sun yi jajir masu saurin kuka har sun fara yi, abin nasu dai babu tsari sam, ina laifin wanda ya faÉ—i wasan a bashi horo na mai tsanani, amma a kashe shi abin ya munana, ku duba kuga Feros fa ko dawowa cikin hayyacinsa bai yi ba suka cire mashi wuya, a gaskiya Black Tiger bakin azzalumi ne na karshen kasasheshe, irin wannan zalinci haka, Allah dai ya kawo karshen wannan irin mulki taka ta zalinci, Allah ya kawo wanda zai cire wannan RAWANIN ZALINCI ya É—aura CROWN OF JUSTICE, PEACEFUL AND FREEDOM.

Ganin da gaske ta sume ne yasa Ronnien ya miƙe ya ɗauketa cak, da alama Ronnie shi aka bawa gadin Sweetie, da alama ya roƙin alfarman a barsa ya karɓo Spender daga hannunta cikin sauki, dan yadda yake yi matan nan da biyu, dole akwai abin da suka shirya mata na dabara.

Kai tsaye É—akinta ya mayar da ita, da kansa ya É—auko ruwa ya yayyafa mata. A haukace baiwar Allah ta farka, ihu take tana faÉ—in shikenan ya mutu, ya mutu, sun cire mashi kai. Rungumota Ronnien ya yi tare da hawa rarrashinta.

Cigaba da sambatunta ta yi da alama ta fita a hayyacinta. A cikin sambatun nata ne ta yi suɓul da baka ta ce. "A irin wannan ɗanyar zalincin da kuka aiwatarwa ne kuke tunanin zan gaya maku in da spender yake har ku mulki duniya? Da kuwa Allah ya kamani, da karshena ba zai taɓa yin kyau ba, tun da ni zan taimaka a azabtar da bayin Allah, wlh ko ina tare da ainahin Spender ba.........." Dakatawa da maganar ta yi sakamakon wani irin azabbabben mari da ta ji saukarsa a ƙuncinta.

Ai tuni ta dawo cikin hayyacinta, kwalalo idanu waje ta yi dan taga waye ya mareta, ina idanunta sun ƙasa iya gane mata komai da kowa, face ɗakin empty babu kowa, tabbas ta jita a jikin mutun, amma ta ƙasa iya ganin fuskarsa, kuma ba makancewa ta yi ba, kawai fuskar ne ya ɓacewa ganinta saboda marin da ta sha ɗin.

Tsoro iya tsoro ne ya dira a ranta, hawaye kuwa yadda kuka san an buÉ—ewa ruwa hanya haka suke gudu a saman face É—inta, jikinta nan take ya fara kerma ya kuma É—au zafi sosai, addu'oi ta fara jerowa wanda ita kanta bata san wasu iri take yi ba, sai a lokacin kuma ta tuna da cewa bata yi sallah ba.

Wani irin banko kofar ɗakin da aka yi aka shigo ne yasa ta ƙara tsorata, ji take kamar bugawa zuciyarta zata yi ta mutu kawai. Faɗi take yi a ranta koma me zai faru ko kasheta zasu yi wlh ba zata taɓa gaya masu in da spender yake ba, dan wannan alkawari ta ɗauka, (ta ɗaukawa waye?) a wani ɓangare na zuciyarta kuma addu'a take yi Ubangiji Allah yasa Kamran ya riƙe kayan da suka bashi da amana, Allah kuma yasa kada su kama Kamran ɗin and Pretty, in dai basu kamosu ba, to wlh ba zata gaya masu in da spender yake ba, idan kuma sun kamosu ko dan Pretty dole ta faɗa........... Ni kam nace akwai tashin hankali kenan, wato dama Sweetie tasa abin da suke nema kenan? Tab lallai yarinyar nan ta wuci tunanin mai tunani, gata makauniya, ƴar karama kuma shiru shiru ashe ta san abubuwa da dama! Lallai yau ake yinta kuwa, fatanmu dai shi ne Allah yasa kada su azabtar da ita baiwar Allah, ko me da me ta sani baiwar Allah, tabbas tun da tasan labari a kan Spender ta kuma san da cewa yana da karfi iko na musamman, sannan tasan ana nemansa ruwa a jallo to tabbas da wuya idan bata san tarihinsu ba. Allah dai yasa kada ta ji wahala ta basu spender su cigaba da zalunci, karfin ikon Black Tiger ya ƙaru, yanzu ma yaya bare ya samu Spender?. Tab akwai cakwakiya.

Amma ina da tambaya, ya aka yi Sweetien tasan abubuwa da dama Pretty bata sani ba? Ko dai ita ma Prettyn ta sani ne? Waye ya sanar da Sweetien dukka wannan abin?. And meyasa duk yadda da suke da Kamran bata sanar da shi komai dangane da hakan ba? Kuma dai ta yarda da shi sannan tana sonsa! Sannan meyasa kai tsaye mun É—insu ta bawa Kamran auren Pretty ba Sweetie da take babba mai hankali da nutsuwa ba? Daga karshe a tsakanin su ukun nan wato Sweetien, Pretty and Kamran a hannun wanenen Spender yake takamaime? Waye yasan hakikanin in da yake? Akwai babban buhun bala'i kam a cikin wannan birnin tab.

Ba kowa bace ta banko wannan kofa ta shigo face Delisha, sai wani huci take yi, daga ganin yadda take tafiya zaka fahimci sam bata ƙullo mutunci ba, rashin mutunci ne cike a face nata haɗe da mugunta.

Tana zuwa ta fimciko Sweetien daga jikin Ronnie da tun É—azun da ya zabga mata mari ya kasa motsawa daga in da yake...... Me dalilinsa na zabga mata mari to?.

Ya kasa yin wani kataɓus har Delisha ta fincikota tare da janta kamar kayan wanki ta nufi waje da ita. Sai bayan sun fita ne Ronnie ya iya sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin muryar ya furta. "Kin yi kuskure". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya sauko ƙasa daga saman gadon....... To fa ta yi kuskure? Wacece ta yi kuskure? Kuma kuskuren me? Mu je dai zuwa.

Waje ya nufa wato ya bi bayan Delishan kenan, da alama duk jikinsa ta yi sanyi, tafiya yake yi kamar wadda aka zarewa laƙa.

Kai tsaye sama ya sake haurawa yana tafiya kamar zai faɗi ƙasa.............

___________________________🔥🤍

GIDANSU KHADIJAH.💔😥

Satin Zainab guda a asirbiti tana fama da jinya, yanzu Alhdulillah jiki ya fara kyau, ita kuwa Hauwa da maman Haidar sai cin karensu suke yi babu ɓaɓɓaka.
Chapter 39 · 0% Book details