← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 211

Sashe 58

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba musu ta yarda, ya wuce gaba ta bi bayansa. Har cikin toilet ɗin ya rakata, sai da ta shiga ya juya ya fita. Yana fita bai kai ga karasawa tsakiyar ɗakin bama ta fito a guje, saboda ta je neman kwano ta ɗebi ruwa a cikin bokitin da ta gani a wajen pampom kusa da wash hand base, tana zuwa kusa da wajen ɗin wata ƴar baby dake wajen ta ce mata welcome to wash hand base side, wannan ne abin da ya ruɗata ya ja ta fita a dubu, dama idan ba ka saba da su ba dole ka rinƙa tsorata, unexpect ka ji an yi maka magana a cikin toilet kuma kasan kai kaɗai ne a ciki ai dole mutun ya razana tun da ba ya saba bane, da ta saba ne lafiya lou...... Gaskiya Daular Black Tiger duniya ne, wato duk in da zaka je a cikin toilet ma akwai na'ura mai yi maka welcome haɗe da gaya maka side ɗin da kake a cikin toilet ɗin, wannan ko baka san komai dan gane da toilet ɗin ba kamar dai Sweetien ba sai ka nemo mai yi maka bayanin komai ba, na'urorin cikin toilet ɗin zasu gaya maka komai, kuma idan ka taɓa abu a toilet ɗin ka tambayi menene wannan menene kuma amfaninsa tsab zasu yi maku bayani menene da kuma amfaninsu, ba a iya yiwa mutun welcome na'urorin suka tsaya ba, har da yiwa wanda ya shigo bayanin komai idan ma bai sani ba. Kowa ni side da na'urorinsa har da wc.

A guje ta fito waje, jin motsin ta fito waje yasa ya juya, yana juyowa ta faɗa jikinsa bata ankara ba. Wani irin shock ya ji tun daga tafin kafarunsa har tsakiyar kai, haƙiƙa yana rungumar ƴan'mata da dama, su Floris duk yana rungumarsu, dan su basu ɗauki hakan a bakin komai ba, amma bai taɓa jin abin da ya ji yanzu da Sweetie ta faɗa jikinsa ba, duk sai ya ji kasala ta sauko mashi a jikinsa.

Ita kuwa a hanzarce ta raba jikinta da nasa tare da komawa gefe ta tsaya tana zare idanun kamar ball, ita wannan Daula masifa ce a gareta, ta gaji da fargaba da faduwar gaba, tashin hankali ne zai kasheta, ita ko da iya waɗan nan ƴan iskan na'urorin dake cikin toilet ɗin aka barta mutuwa zata yi da tsoronsu, ba sai an kara mata wani azaban ba, gida ne babu setting a ganinta, wai na'urorin dake magana ne yasa take ganin gidan babu setting, a haka ma bata taɓa cin karo da robot na gidan ba, da sai yaya kenan? Da kila cewa zata yi bata duniya, ko da yake yanzu ma bata yarda a duniya take ba, dan ita rayuwar Forest kawai ta sani.

"What happened kika fito a guje haka?". Da kyar ya iya tambayarta, cikin kasalalliyar murya ya yi maganar.

"I am very afraid of going to the toilet" "afraid of what your feeling?". Kamar baya son motsa baki yake maganar, dan ta kashe mashi jiki faÉ—awa jikinsa da ta yi.

"There is something in the toilet that talks, I'm afraid of that".
Ya fahimci me take tsoro a yanzu, dama kuma yasan in dai baka saba da waÉ—an nan na'urorin ba dole ka tsorata idan sun yi magana, dan magana suke yi unexpect, da zarar ka doshi waje zasu yi maka welcome tare da ambatar sunan wajen, kunga ai dole bawa ya tsorata.

"Okay, let's go, I'll accompany you, then do what you have to do and we'll come back".

Kasancewar tasan iya alwala zata yi sai ta aminta da ya rakata É—in. Haka suka juya a tare tana gaba yana biye da ita izuwa cikin toilet É—in, yana tafiy a kasale. Tsayuwa ta yi a cikin bata san komai ba, ko iya kunna ruwa a panpo bata yi ba, roba ma ta fara nema ta yi alwalar.

Ganin haka yasa ya tambayeta me take nema?.

Abin da zata saka ruwa a ciki ta bashi amsa, ƙarisowa cikin ya yi, panpon dake dai'dai da tsawonta wajen kusa da bath pan ya kunna mata tare da cewa ta matso taga yadda ake kunnawa ko dan anjuma. Ƙarisawa wajen ta yi, tana zuwa sai da wannan na'ura ya yi mata welcome, a yanzu kam bata tsorata ba, dan yanzu tasan akwai su a wannan toilet ɗin ma, dama ɗazun rashin sanin suna nan ne yasa ta tsorata.

Kunna mata ya yi tare da É—an jan gefe ya bata waje, tsayuwa yayi ya tsareta idanu, komai nata makurar burgesa yake yi. Ai ba batun tsarki kawai ta hau yin alwala, da kallo ya bita yana mamakin abin da take yi É—in.

Bayan ta kammala ta ce mashi su tafi. Kaman zai tambayeta me ta yi kenan, sai kuma ya ce bari ya zuba ido ya gani, dan yawan tambaya ya kansa mutun baya cin moriyar gani ko kuma jin labari, dan haka bari dai ya bita ya ga me zata aikata.

Cikin room ɗin suka koma, saman bakin bed ya zauna ya tsareta da ido, ita kuma ta tsaya turus kamar wata sakarya. Sai da ya tambayeta me ya tsayar da ita ne ta gaya mashi kaya wanda zasu kai mata har ƙasa sosai da kuma abin rufe kai take so. Dressing room na ɗakin ya nuna mata, dan kuwa yasan tun da aka kawota wannan ɗakin to ba makawa akwai abubuwan da zata iya yin amfani da su.

Cikin ta nufa, duk wasu drawers dake cikin É—akin akwai na'urar da zata gaya maka wani irin kaya ne a cikin drawers É—in bayan ta yi maka welcome, ba sai ka sha wahalar buÉ—e drawers É—in ba na'urar zata gaya maka kaya iri kaza ne a ciki, kana dosowa wajen zata yi maka welcome sannan ta sanar da kai.

Sam a wannan karon bata tsorata da jin maganar na'urar ba, dan ta fara sabawa da abubuwan al'ajabin dake cikin wannan Daula. Duba abin da zai yi mata dai'dai ta yi sallah ta fara yi, da kyar ta iya samun doguwar rigar da zata kai mata har ƙasa, ta laluɓi hijabi har ta gaji bata samu ba, ko gyale ma babu a wajen bare hijabi, kaya ne kawai da suka saɓa da addinin musulunci cike a wajen shagon kayayyaki, ganin babu hijabi ko gyalene yasa ta laluɓi wata doguwar riga ta ɗan lulluɓa ta fito cikin ɗakin.

ÆŠan waro idanu waje ya yi yana kallonta, bata san ina ne gabas ba, dan haka sai ta tambayesa ina ne east? Da hannu ya nuna mata a tunaninsa wani abin take nema, bai san ma sallah ba bare yasan gabas ake duba ayita. Gyara tsayuwarta ta yi ta fiskanci gabas É—in.

Mamaki ne ya bayyana a kan fuskarsa na ganin ta tada kabbara ta fara sallan da ita kanta bata san na wani lokaci take yi ba a yanzu. Shiru ya bita da kallo har ta idar da raka'a huɗu ta sake miƙewa ta fara wani, shima raka'a huɗun ta yi ta sallame, a lissafinta azahar da la'asar na jiya kenan, haka ta yi mangariba da isha, sannan ta yi asubar yau, bata san azahar ta sake yi ba, da ta sallame asuban sai kawai ta yi addu'oi tare da rokan Ubangiji da ya yafe mata jinkirta sallah da ta yi da kuma haɗesu da tayi. Bayan ta shafa addu'ar ne ta miƙe ta nufesa, sam bata jin tsoronsa shi kam, dan shi da Floris ne kawai masu sakar mata fuska.

Gefensa ya nuna mata a kan ta zauna, cikin É—ari É—arin jiki ta zauna, sai binta da kallon mamaki yake yi. Kasa hakura ya yi har sai da ya tambayeta me ta yi yanzun nan kenan?.

Sallah ta bashi amsa a takaice. "Sallah?". Ya mainaita kalmar mai haÉ—e da alamar tambaya.

Kai ta gyaÉ—a mashi tare da cewa e. "Menene shi sallah É—in?". "Gaishe da ubangijinmu". Ta bashi amsa a nutse

Ubangiji ya maimaita kalmar. "To ai mu ba haka muke gaishe da Ubangijinmu ba".

Cikin nuna halin ko in kula ta ce. "To ya kuke yi kenan?". Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "Anjuma zamu je church ai, idan mun je zakiga yadda muke yi, zan roki yaya ya bari mu je tare da ke sai ki gani, ko da yake ma ai dole ki je tun da kike nan, dole ki girmama ubangijinmu ki je church".

A takaice ta ce mashi. "Mu bama zuwa church, a gida muke sallah, ni musulma ce ba Christa ba". "Musulma kuma? Menene musulman?". Ya tambaya yana É—an kai kallonsa saman room É—in.

Bata san ta yaya zata bashi amsa ba sai kawai ta yi shiru. Shi ma kawar da zancen ya yi da cewa. "In ba damuwa zaki iya bani storynki? Ina son sanin wacece ke?"

Tunani ita kuma take yi a kan maganar da ya yi na cewa dole ta je church, kuma haka zancensa yake, in dai tana cikin birnin nan to fa dole ta zayarci church É—insu yau da yamma, wannan dokace, suna da ranakun yin ibadunsu, a sati sau uku suke ibadan nasu, ranar Wednesday, Friday da kuma Sunday, a cikin waÉ—an nan ranaku suke ibada, Friday da Wednesday da yamma suke ziyartar church É—in, Sunday kuma da safe. So yau zasu je da yamma kenan, lallai akwai kura, Sweetie ta zuwa church, kuma ya zame mata dole yin hakan ba yadda zata yi, tabÉ—ijam!!

Kai ta gyaɗa mashi a kan babu damuwa zata bashi labarin nata. Go ahead ya bata a kan ta fara bashi ɗin, yanzu fa ya dawo daga school ko abinci bai ci ba ya tare a wajenta, to Allah dai yasa da gaske har cikin zuciyarsa yake tausaya mata ba haɗa baki aka yi da shi za'ayi mata wayo ba, kafin ta gama bashi labarin nata bari mu leƙa wani ɓangaren mu gani...

______________________🔥💘

PARIS____________FRANCE

55 RUE DU FAUBOURG SAINT-HONIRE

_______ELYSEE PALACE🔥💘

Elysee palace wato president house ne na kasar Faransa, kun dai san yadda gidan shugaban ƙasa yake ba sai na tsaya ɓata lokaci na wajen yi maku bayani ba, Daula ce guda, duniya ce guda, to mu shiga cikin gidan ba ɓata lokaci.
Chapter 58 · 0% Book details