← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 211

Sashe 10

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu irin uban lodin shanayene (Cows) suke ƙetarawa ta gefen wani katafaren kogi mai girman gaske, kogin yana da matuƙar girman da ya keta har ta maƙotan garuruwa, ta gefensa shanayen suke wucewa, da alama kiwo zasu tafi, shanayene masu matikar yawan da sun kai a kallah 1000 da ɗoriya, haka suka rinƙa wucewa, buguma buguman cikinsu ne a tagaba, harda boƙolaye ƴan kasar Cameroon a cikin shanayen. Bayan bujumayen sun wuce ne kananan cikinsu suka rufa masu baya, suma kananan suna da uban yawa ba kaɗan ba, ga shanayen da kyan gani sosai, ɓul ɓul da su, sun samu kiwo mai kyau, jikinsu tas, ɗaiɗaikun cikinsu ne zakaga jikinsu da ɗan baki baki, amma tas suke.

Bayan kananan sun wuce uban tilin garken raguna ne suka biyo masu baya, raguna ne irin masu tsawo da dogayen kunnuwar nan, kala biyu ne jikinsu, akwai mai brown da fari akwai kuma mai baki da fari. Suma ragunan suna dayawa sosai, zasu iya kai 300 haka, kuma maza ne da mata.

Bayan sun gama wucewa sai awakai suka bi bayansu, suma suna da yawa gasu manya manyan, sun ji kiwo sun ƙoshi. Bayan su sai jakuna da basu wuce guda 20 ba.

Dukka waɗan nan uban tilin dabbobin da suka wuce wata yar kyakkyawar yarinya ce riƙe da sanda take daga karshensu tana kaɗasu, yar ƙarama da ita, ba ta wuce 8 to 9 years ba a duniya, ita ce ta kaɗo waɗan nan uban tilin dabbobin har da bujumayen saniyoyin nan, duk suna a ƙarkashin kulawarta.

(Ni kam abin ya bani mamaki, yarinyar da idan ta shiga cikinsu ko alamarta ba za'a gani ba wai a ƙarƙashin kulawarta suke?🤔 abin da mamaki da kuma burgewa. Kai wayaga PRINCESS TEEMA a cikin shanaye?🤔😅 Tab da na yi suma goma wlh, kai ni ai tsakanina da su in gansu a soye🥱😅🌝 na ci na kora Maltina mai sanyi!. Kar fa ku ce tsoronsu nake ji, sam bana tsoronsu💪 ni kanwar Mammar Kamran ce, 💪 jarumta a jininmu take😅 tsaro zai sa ba ma zan je in da suke ba ba tsoro ba, fatan kun gane?🌝)

Sanye take da takalmar kiwo a kafafunta, ga zanin da ta ɗaura sai ta baka dariya, ɗaurin zanin ma bata gama iyawa ba, na ciki ya fi na waje tsawo ta ɗaura kayanta, rigar kayan fulani ne a jikinta, sai dressing natan ya kara bawa mutun dariya, barema wannan uban kwadaram ɗin takalmi da tasa na kiwon, kai ba ɗan'kwali, wasu kumbusa kumbusan kitso ne a kanta guda huɗu, da yake tana da tsawon gashi sosai sai jelar kitson ya sauko mata har bayanta, ga gashin nata baƙin kirin da shi sai tsantsi.

Kyakkyawar gaske ce sosai yarinyar, sai dai idanunta a tsaitsai a tsakar ka suke, da alama bata da kunya, dan akwai bushewar idanu sosai kam, ga ɗan bakinta ɗan ƙarami da alama zai yi rashin kunya da surutu dai'dai gwargwado. Ta cancaɗa wani irin mahaukacin kwalliya da idan ka gani sai dariya ya kashe ka, wannan idan ka ga kwalliyar nan da daddare sai ka sume ko ka ruga a guje a zatonka aljana ka kallah, amma ita a haka gani take tafi kowa yau, ji take kanta ya yi kato saboda ta yi kwalliya, ji take babu kamarta a duk faɗin rugar Lamiɗo, har wani taku take yi irin na wadda ta fita daban yau.......😅

Sai Æ´ar wakarta take rerawa cikin harshen fullanci tana cigaba da bin dabbobin tana kuma kaÉ—a sanda, idanunta tas suke kamar farin cikin kwai, ga idanun kam sai dai muce masha Allah, dara dara da su.

Cigaba da tafiya da dabbobin ta yi har suka keta ta cikin wasu gonakin suka bar kusa da wannan kogin. Da ɓacewarsu a arear wajen ba jimawa sosai wata kyakkyawar matashiyar yarinya fara tas tare da wani dattijo suka zo giftawa ta wajen kogin, da alama duk a tare suke.

Cikin nutsuwa suke tafiya suna hira, daga ganinsu kasan baban da Æ´a ce ba sai ka tambaya ba, dan suna kama sosai, sai dai yarinyar ta fishi hasken fata sosai, tana da tsawo sosai kamar shi, a shekaru ba zata wuce 14 to 15 years ba, kyakkyawa ce ajin farko. Zanin dake jikinta irin na wancan yar yarinyar da ta kaÉ—a dabbobin nan ne, sai dai ita tana sanye da hijabi mai É—an girma zuwa gwiwarta, da alama tana da nutsuwa sosai, dan yadda take magana da baban nata cikin girmamawa da yin kasa da murya a kan nasa ne zai tabbatar maka da nutsuwarta.

"Bappa zan sha ruwa". Yarinyar ta faÉ—a cikin sanyin murya, tana murya mai daÉ—in gaske wanda zai dace da rera kira'ar Alqur'ani mai girma. Cikin harshen fillanci ta yi maganar!.

"Tom Mahnoor jeki sha sai ki sameni a wajen Mahreen, ki kula sosai fa". Ya bata amsa tare da wucewa gaba, haƙiƙa muryarsa sak irin tata yake, sun yi kama.

Nufar gangaren da zai sauketa izuwa bakin kogin ta yi, dan a saman tudu suke, shi kuma Bappa kwairaga ya bi bayan Æ´ar yarinya mai kaÉ—a dabbobin nan.

Cikin nutsuwa take sauka izuwa bakin kogin, daga ganin wannan kyakkyawar innocent face É—in nata da akwai damuwa a kanta, tana da fuskar tausayi sosai.

Bakin ruwan ta tsugunna tare da kai kyawawan fararen tafukan hannunta ta É—ebi ruwan ta kai baki, da yake ruwan gudu ne yana da haske sosai, ba'a tsaye ruwan yake ba, yana gudu ne.

Bayan ta sha dai'dai yadda take buƙata sai ta miƙe tsaye, bin kogin da kallo ta fara yi tare da sanya hannayenta ta riƙo ƙugunta. Can ta hango wani abin jibgi kamar kaya a can gefe a bakin kogin.

Ɗan zaro ido ta yi tare da kurawa wajen idanu, bata iya ganin menene sosai daga in sa take tsaye, hakan yasa ta yi tunanin bari ta ƙarisa wajen ta ga menene?. Ai kuwa babu tsoro ba komai ta nufi wajen cikin nutsuwa. Tun bata gama ƙarisawa ba ta ja wani uban birki tare da gwalalo ido waje sosai kamar zasu faɗo ƙasa. A ɗari ta ɗan ja baya tare da wage cool voice ɗinta tana kwalawa Bappa kira.

Da ƙarfi ƙarfi take kwala mashi kiran, amma ina, kasancewar tana da sanyin murya sai voice ɗin nata baya fita sosai sam.............

Da yake dajin yana amsakuwa hakan yasa kiran nata ya dira a kunnen Bappa dake ƙoƙarin rabon faɗa tsakanin............

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 19/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘STEP TWO....✍️📚🔥

Da yake dajin yana amsakuwa hakan yasa kiran nata ya dira a kunnen Bappa dake ƙoƙarin rabon faɗa tsakanin Mahreen da wata ƴar matashiyar yarinya da zata iya finta a shekaru, a kallah yarinyar zata kai shekaru goma sha biyu haka, amma Mahreen ta tsaya sai gwabza faɗa suke yi har zani ya faɗi saura pant kawai.

Sandar kiwon nata ta rarumo zata bugawa yarinyar a tsalar ka Bappan da ya iso wajen yanzu ya yi maza ya riƙe sandar yana faɗin. "Haba gajin Bappanta (Auta kenan shi ne gaji da fillanci), meyasa zaki bugeta da sandar nan har haka?".

Gashin idanu a tsastsaye kamar wadda tasa na kanti, idanu a bushe kwalam ba alamar kunya, Bappan yana idasa maganarsa ta sanya mashi kuka kamar ba ita take jibgar ƴar mutane a yanzu ba, sake mashi sandar ta yi tare da yin zaman ƴan bori a kasan wajen, kan kace me ta fara birgima a kasan kamar mai shafan aljanu, yi take yi tana kukan shagwaɓa ita a dole Bappa ya kyaleta ta cigaba da jibgar ƴar mutane kamar ita ta haifota izuwa duniya.

Yarinyar kuma da ta samu Bappa ya kwaceta ai sai ta danna a guje, dama ta daku a hannun Mahreen É—in, ta germe mata a shekaru, amma saboda bala'in Mahreen É—in nan sai da ta daka yar nan lilis kamar an aikota, har kuka sai da yarinyar ta yi, tana kukan ne kuma dama zata kara kwala mata sanda a kanta dan iyashege.

Sai rarrashinta Bappan yake yi, da alama shi ya ɓatata da shagwaɓa da kuma faɗa, dan baya yi mata faɗa da nasiha a kan idan tana faɗa da mutane ko tana shagwaɓa, sai dai ya biye mata ya yi ta rarrashi, yanzu ma faɗi yake yi tom ta tashi ta dage shi da sandar shi tun da ba zata hakura ba, ai kuwa make kafaɗa ta yi tana faɗin ita dole ya barta ta kwalawa yarinyar can sandar, idan ba haka ba yau ba zata ci abinci ba.

Ita kuwa yarinyar da Allah yasa Bappa ya kwaceta ta ruga da gudu wajen shanayen kiwonta, sai da ta kusa isa wajen ta juyo tare da faɗin. "Mahreen mai kwalliyar mahaukata na faɗa ɗin ki lilili ki liƙeni ki mai dani cikin uwata ki fitar dani ta bakin allura idan kin isa ba iya duka kawai ba! Na faɗa kin yi kwalliyar aljanu karya na yi ne? Fuska a dame kamar fura........"
Chapter 10 · 0% Book details