Sashe 21
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana kwance a saman gado, bata jima da gama yin waya da Rizwan ba, da ga ita sai kayan barci, da alama a part É—in ta kwana, har yanzu kayan barcin jiya ne a jikinta, bata yi wanka ta canza ba, haka zalika bata fito ta ci abinci ba, tana kwance shiru tana fuskantar celling É—in É—akin. A tunanin Aunty MieMie ma barci take yi shiyasa bata zo ta ce mata ta tashi ta yi breakfast.
Jin motsin mutun yasa ta sauko da kallonta izuwa bakin kofar room ɗin, a tunaninta ma Aunty MieMie ce. Tana sauke idanunta a kanshi ta wani irin zabura tare da miƙe zaune a dubu, nan take ta yi ƙasa da kallonta tare da fara ƴan kame kame, tsabar razana har kerma jikinta ya fara yi.
Tura kofar room É—in ya yi ya rufe, sannan ya tako a hankali ya nufo in da take.
Kara tsorata ta yi da ganin ya tura kofar kuma ya tunkaro ta, muryarta na karma yana sarkewa ta fara faɗin. "Yah Jawad dan Allah ka yi hakuri, na shiga ukuna, Momma, mummy kuzo ku ceceni, Aunty MieMie kizo Yah Jawad zai kashe ni, dan Allah Yah Jawad idan wani laifin ma na ya yi maka ka yi hakuri, wlh ba zan sake ba, dan girman Allah........." Ka sa ƙarisa maganar ta yi dan ganin ya zauna a saman bedside drawer tare da zuba mata idanu, tana magana muryarta na sarkewa, ga shi ta datse idanu gam tare da sanya hannunta ta tare fuskar tata duk wai dan kada ya taɓata.
Jin ya zauna a kusa da ita ba tare da ya taɓata ko ya yi mata magana bane yasa ta ɗan buɗe idonta guda ɗaya a hankali dan ta saci kallonsa. Ganin yana zaune shiru ya kura mata idanu ne yasa ta mai da idon nata ta rufe tare da fara yin tunanin to ko dai ya zo bata hakuri ne? In kuwa haka ne wlh ba zata saurare shi ba, kuma ba zata sake jin maganarsa ba, daga yau ta dai'na kula shi.
Shiru shiru almost 10 mins bai ce da ita uppan ba, da ta gaji da datse idanun nata ne sai ta buɗesu tana kallon ƙasa, taki yarda ta ɗago su yi ido huɗu, tunane tunane kala kala ne a ranta.
"Jannat". Ya ambaci sunanta a wani irin low voice sosai. Kin amsawa ta yi kuma taki É—ago kai, ko É—an motsawa ma bata yi ba tamkar ba ita ya kira ba.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Yanzu Jannat ko wata aka ce maki na shiga É—akinta da nufin na keta mutuncinta zaki yarda?".
Still bata motsaba kuma bata amsa ba.
Cigaba ya yi da cewa. "Jannat kenan da gaske zaki yarda da cewa zan iya shiga É—akin wata ma ba ke ba?".
Har yanzu dai shiru bata amsa ba. "Shirunki ya nuna mun cewa kin yarda kenan ni ne?". A wannan karon kai ta gyaÉ—a mashi alamar yes she's agreed!.
Ɗan zaro idanu ya yi tare da bayyanar mamaki a face ɗinsa. Hannayensa ya kai ya riƙo nata cikin nasa. Wani irin zabura ta yi tare da yin baya a ɗari tana ƙoƙarin kwace hannayen nata. Bai saketa ba sai ma ƙara ƙanƙame ƴan hannayen nata ya yi, ƙasa ƙasa kaman mai raɗa ya furta. "Jannat menene hujjarki na cewa tabbas ni na shiga ɗakinki? Ki gaya mun! Idan na ji hujjar taki na kuma gamsu da ita zan karɓi laifin da bani na aikata na, zan yarda da cewa ni na aikata".
In a low voice sosai ta fara magana kamar wadda aka sanya dole. "Wlh Yah Jawad kai ne! Kai ne ka shigo mun ɗaki, face ɗinka ne, jikinka ne, komai nake n........." Bata iya kai karshen maganar ba sakamakon sauke kallonta da ta yi a kan hannayensa dake riƙe da nata. Ɗan zaro idanu ta yi tare da juyar da nata hannayen ta riƙo nasa, kurawa hannun nasa idanu sosai ta yi, har da ɗan ɗagosu tana kara dubawa da kyau, duk bata gamsu ba sai da ta fara jujjuya hannun nasa.
Kura mata idanu ya yi yana binta da kallon mamaki, abin ya ɗan ɗaure mashi kai. "Lafiyarki kuwa Jannat?". Ya faɗa tare da zame hannayen nasa daga riƙon da ta yi masu.
Da sauri ta É—ago da kanta haÉ—e da kallonta izuwa garesa, a É—an ruÉ—e ta furta. "Yah Jawad ina tabon cizon da na yi maka na fasa maka fatan hannu? Izuwa yanzu wlh wannan cizon ba zai yiwu ace ya warke ba, dan na fasa fatar wajen har ta yi jini, ko da jinin ya tsaya da zuba ba zai yiwu a ce babu tabo ba". Tsabar ta ruÉ—e har ta kare maganar tana kallon cikin kwayar idanunsa, yau ba sunkuyar da kai, da alama bata san ido cikin ido suke kallon juna ba saboda ruÉ—u.
"Jannat ni babu wanda ya cijeni bare tabo ya zauna, a yaushe aka yi hakan? Yaushe kika cijeni?".
Still har lokacin tana kallon cikin tsakiyar kwayar idanunsa, mamaki ne ya kara bayyana a saman fuskarta, ta kara shiga ruɗani ta furta. "Ranar da ka shigo ɗakin nawa ne ina ƙoƙarin kwatar kai'na na cijeka har na fasa maka fatar hannunka, wlh kuma ya yi jini sosai".
Wani irin sanyi ya ji ta ratsa shi, Allah ba azzalumin bawansa bane, ga shi cikin sauki ya kawo mashi mafita ta yadda zai wanke kansa, Allahu Akbar, gaskiya ne Ubangiji baya barci, kai ko gyangyaÉ—i baya yi bare barci, Allahu Akbar, Allahu Akbar. Ya faÉ—a a cikin zuciyarsa.
Miƙewa tsaye ya yi tare da fuskarta gabas, ya zube gwiwowinsa a ƙaya ya gabatar da sujjudur shukur tare da miƙa ɗinbin godiya ga Ubangiji. Bayan ya miƙe ya koma ya zauna, cikin hanzari ya riƙo hannayenta a cikin nasa, cikin tsantsan farinciki tare da murmushi a saman face ɗinsa ya furta. "Allahu Akbar my Jannat, Ubangiji ya wankeni daga zargin da kike yi mun, na gaya maki ba ni na shiga ɗakinki ba, jannat ko ƴar wani can da ban ba zan iya keta mata mutunci ba bare ke da kike kanwata, jinina, farincikina, wannan ke kin sani ba tarbiyar gidan nan bane".
Ɗan sakin jiki ta yi da shi kaɗan, izuwa yanzu ta fara yarda da cewa e ba shi bane, amma kuma da yake shi sheɗan munafuki baya son yaga ana zaman lafiya sai ya rinƙa zuga zuciyarta yana sanya mata wasi wasi a kan idan ba shi bane to wanene? Ga kamanninsu ɗaya, komai nasu iri ɗaya ne da wanda ya shigo ɗakin.
"Yah Jawad amma idan ba kai bane ya aka yi komai naku kai da wancan É—in iri É—aya? Na kasa yarda da hakan wlh".
Ƙara matsowa ya yi dab da ita, har lokacin tana kallon cikin idanunsa, mamaki da al'ajabin abin yasa ta kasa kawar da kallonta daga kansa, ta kasa iya tunano ko abu guda ɗaya da ya banbanta Jawad ɗin da wanda ya shigo ɗakinta, babban tambayar da yake cikin zuciyarta ma shi ne, idan ba shi bane to wanenen? Ita dai tasan shi ba twin's bane bare ta ce ko ɗan uwansa ne.
"Tunanin me kike yi kuma Jannat?".
Ƴar razana ta yi tare da ɗan kyafta idanunta kaɗan, ta sake kura mashi ido tana kallonsa. A hankali ta zame hannunta ɗaya daga riƙon da ya yi mata ta kai hannun nata saman kumatunsa, ta dage ne tana son nemo banbancin dake tsakanin shi da wancan, tun da dai taga babu tabon cizon da ta yi wa wancan a hannunsa.
Zuba mata idanu ya yi yana kallonta, shafa kumatun nasa ta fara yi har izuwa saman lallausan sajensa, ita kanta da taɓa fatarsa a yanzu sai ta ji yana da banbanci da na wancan, wancan fatarsa tauri gareta kamar jikin samudawa, shi kuma Yah Jawad jikinsa da laushi sosai. Sam bai yi ƙoƙarin katseta ba, ya zuba mata idanu yana kallon yadda take ta shafa mashi kumatu har izuwa hannunsa.
Shiru ta luluƙa duniyar tunani, nan take kuma ta ji kanta na sara mata, ta gaza gane me yake shirin faruwa da ita ne, wani irin jiri ne ya fara ƙoƙarin ɗibarta, kanta ya kulle ruf.
Sarai ya lura da ta shiga halin ruɗani sosai, hakan yasa ya ɗan jawota jikinsa, murya ƙasa ƙasa sosai ya ce. "Baki yi addu'ar barci lokacin da zaki kwanta ranar ba ko?".
Kai kawai ta gyaÉ—a mashi alamar e. Cikin nutsuwa ya yi mata faÉ—a a kan wasa da addu'a, sannan ya bata labarin da Momma ta bashi na abin da ya gani, daga karshe ya rufe mata da cewa ta zage da yin addu'a sosai, kada ta kuskura ta yi wasa da addu'a, idan ba haka ba wlh akwai babbar matsala sosai.
Kasa iya amsa mashi ta yi, ta kwanta a jikinsa shiru, izuwa yanzu ta yarda ba shi bane ya shiga ɗakin nata, saboda ta gano ko fatar jikinsa da wancan ma ba ɗaya ba ne, ga ba tabon cizon da ta yi mashi. Tsoro da ruɗa ne ya ƙara kamata yasa ta ƙara shigewa jikinsa, yau ta shiga uku taga Yah Jawad guda biyu take faɗa a ranta......... Ni kam na ce ai dama dole ki tsorata, irin wannan ruɗani haka? Mutun ɗaya ya zama biyu, kin ma yi ƙoƙari da baki suma ba bayan jin wannan labarin.
Turo kofar da Aunty MieMie ta yi ne yasa shi saurin kai kallonsa wajen. ÆŠan zaro idanu ta yi tana kallonsu, hararar wasa ya wurga mata lafin ya ce. "Ya da shigowa É—akin mutane ba neman izninsu?".
Dakuwa ta ware yatsunta biyar ta watsa mashi da hannu kafin ta ce. "Me kazo yi a nan? Kazo kana tsara yar mutane ko? To zo ka wuce".
Da sauri Chuchun ta yi ƙoƙarin barin jikin nasa jin voice ɗin Auntyn tasu. Ƙanƙameta ya yi ya hanata barin jikin nasa. Cikin zolaya ya furta. "Aunty MieMie gaskiya zaki takura mun, yanzu me kika zo yi a nan?".
"Zo ka fita nace ko na kira Akka, ke kuma Chuchu zo ki wuce ki yi breakfast ki yi wanka, uncle Dr yana zuwa ya dubaki, dan ina son gobe ki je school".