← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 211

Sashe 69

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habawa ai a ɗari commander Zafar ya fito daga part ɗinsa, ban da Hoorain babu wanda yake nema, nemansa yake kamar hauka a kan ya zo ya jagoranci ɓangaren da suke kula da makamai bari shi kuma ya kula da zakunar mayakansu da zasu fara yin gaba wato masu harbi da kifiya kenan, akwai abokin Hoorain ɗin wanda kuke ganinsu kullum a tare mai suna Ansar, shi kuma commander ya ce mashi ya haɗa kan dakarun da zasu fita da dawakai, ya ce su haɗa dawakai guda 400 ma ya isa, dan ma sun ga ba ƙananan mayaka bane suka kawo masu hari, sannan kuma suna dayawa sosai suma, gasu da manya manyan kayan yaki sosai.

Kan kace me masarauta ta ruÉ—e, dan ma suna da tsari sosai.

Yah Jawad yana ƙoƙarin shiga part ɗin King Aunty MieMie tana shigowa, a tare suka ƙarisa ciki, ba wanda ya iya yi wa ɗan uwansa magana, saboda dukkansu hankalinsu baya jikinsu, yana wajen mahaifin nasu. Ba komai ya ja haka ba face sun san dayawan lokuta idan aka kawowa masarauta hari fa mayakan kwantan ɓauna suke yi su nufi in da sarki yake, shi suke fara kashewa kafin su yi ƙoƙarin ruguje komai, shi ya ɗaga masu hankali sosai, sannan abu na biyu sun san kafin a kawowa masarauta hari fa dole sai an santa ciki da waje, dole akwai ƴan leƙen asirin wasu masarautun a cikinsu ba tare da sun sani ba, so sun san da wuya idan waɗan da suka kawo masu harin a yanzun nan ba'a gaya masu in da King Zuhair yake ba ta yadda kai tsaye zasu hari wajen da yake ɗin dan su fara kashe shi.

Ai kuwa suna shiga suka wani irin jan burki ba shiri, dukkansu zaro idanu waje suka yi tamkar idanun nasu zai faɗi ƙasa. Ba komai suka gani ya sanyasu jan wannan birki ba face yadda suka sami King a tsaye cikin uniform na mayaƙa, ya yi tsayuwar jarumta tamkar wani zaki, ga Momma a tsaye kusa da shi tana ƙoƙarin taya shi shiryawa, da alama ita ta sanya mashi kayan, sai jan mashi gemu take yi tana yaba shi tare da yi mashi kirari a kan ba'a taɓa samun wanda ya ci nasara a kan modarawa ba tun farkonsu har izuwa yau, su ɗin jarumai ne na bugawa a jarida, dan haka ta sani da izinin Allah koma su waye suka kawo masu hari da izinin Allah sune zasu yi nasara, sai kara kuranta mijin nata take yi, ko a jikinta, babu karaya ko tsoro a tattare da ita, tsabar zafin zuciya da karfin hali irin nata ta yarda mijinta ya shiga filin daga duk da yake sarki, dan ita gani take in bai shiga filin dagar nan ba za'ayi nasara a kansu tun da ƴaƴan cikinsu basa nan, ita fa Momma ta yarda da jarumta King, tasan sarai zai iya, su Mama dai sun ki yarda a kan ya shiga fili, tun ɗazun suke yi mashi magiya a kan ya hakura a matsayinsa na sarki ya haura sama ya kalli yakin daga sama, momma ta ce a'a dole ya fita saboda al'ummarsa, shi ma ya ce a matsayinsa na adalin sarki dole ya fita saboda al'ummarsa, ya ce kowa dake cikin kingdom ɗin nan mutun ne kamar shi kuma kowa yana son ransa kamar yadda shi ma yake son nasa, dan haka kamar yadda yake son kansa da lafiyarsa, matansa da ƴaƴansa suke sonsa suma al'ummarsa haka suke son kansu da kuma matansu da ƴaƴansu suke sonsu, dan haka dole ya fita ya gwabza dan ya samu hujjar kare kansa a gaban Allah a kan amanar talakawa da ya bashi....... Gaskiya King Zuhair adalin sarki ne over wanda samun irin sa zai yi matuƙar wahala a duniyar yanzu!!.

Akka ma tace ya fita ta bashi goyon baya, kun san jinin Modarawa yake gudu a jikin Akka, ita da Momma ba sarewa ko karaya a lamuransu, basu san menene ja da baya ba, akwaisu da taurin zuciya kam sosai da sosai.

Tun ɗasun suka rinƙa dragging da su mama and Mummy a kan sun ce su basu son ya fita, hankalinsu a tashe har kuka Mummyn Gimbiya Chuchu ta yi, amma daga karshe ma ce masu ya yi su fice mashi a ɗaki fita babu fashi tun da su basu san hakkin bayin Allah da yake rataye a kansa ba, dan haka su fice mashi a part, shi ne yasa suka fita Akka ma tace tana zuwa ta wuce part ɗinta, ya rage daga shi sai momma dake ta kara mashi kwarin gwiwa shi kuma yana ta bata wasiya a kan koma bai dawo a raye ba, sam bata wani ɗauki wasiyar tasa da mahimmanci ba, dan tana ji a jikinta zai dawo garesu, su fa Modarawa wlh basa taɓa yin tunanin faɗuwa, kullum tunanin sune da nasara suke yi.

Da sauri Yah Jawad ya ƙariso wajen nasu da nufin shima ya dakatar da daddyn nasu daga fita filin, ita kuwa Aunty MieMie da yake jinin King ɗin ne a jikinta habawa juyawa ta yi sai part ɗinta ta fara shirin yaki ita ma, dan na gaya maku mayakiya ce sosai a baya, har mutunmutuminta aka sassaƙa a kofar masarautar tasu, so jaruma ce sosai da sosai, haka ta hau shiryawa dan ta takewa babanta baya zuwa wajen yakin, a nan ta sami mijinta ma yana shirin yakin, kai kingdom of power gabaɗaya babu ragwaye, gabaɗayansu a shirye suke, a koyaushe suna shirye su afkawa yaki bayin Allah, jininsu a tafashe yake!!.

Kallon Momma dake ta zubawa King kirarin kara mashi kwarin gwiwa fuskarta ba yabo ba fallasa Yah Jawad ya yi kafin ya ce. "Momma ba zaki hana dad fita ba?". A ruɗe ya yi maganar!!. Bawan Allah bai taɓa ganin dad ɗinsu a filin yaki ba, dan lokacin da ake gwabza yaki shi da Jaish suna Dubai basu dawo ba, shiyasa hankalinsa ya tashi sosai.

"A kan me zan hana shi Jawad?". Ta jefa mashi tambayar tare da É—auke hannunta daga kan gemun King É—in tana dawo da kallonta a kan Jawad É—in, while shi ma King kallonsa yake yi da waÉ—an nan idanun nasa kamar shi ya arawa gimbiya Zunaira su.

"Momma yaki fa? Haba bai kamata dad ya fita yaki ba! Duk yawan mayakan da muke da su basu isa ba sai dad ya fita?".

"Jawad ina son ku sani su kansu mayaƙan dake cikin kingdom ɗin nan nauyinsu ya ratayane a kan daddynku, matsawar daddynku adalin sarki ne to fa dole hankalinsa ya tashi ya shiga filin daga domin kare al'ummarsa, duk wasu adalan sarakuna haka suke, kuma mu jininmu basu san sarewar gwiwa ba! Dan haka ka kawo wata zancen ba wannan ba!!". Cewar Momma, murya a ɗan kausashe ta ƙarisa maganar.

Tana rufe baki King bai bari Yah Jawad ɗin ya sake yin magana ba ya ce mashi. "Kaje ka haɗa mun kan ƴaƴana dukka ka sauke mun su izuwa under ground, sannan umarni ne ka tsaya da su a wajen, duk da mayakan da zasu basu tsaro ban yarda ba, dan mutun bare ba abin yarda bane, ana iya haɗa baki dasu ko a sayesu a cutar mun da family, dan haka ka tsaya da su kada kaje ko'ina,". Fuska a ɗaure ya yi maganar, hakan yasa Yah Jawad bai ja da maganar ba, dan kuwa bai ga alamar wasa a tattare da dad ɗin nasu ba, in a serious note ya yi maganar, dan haka sai ya karɓi umarni ya juya ya fita kawai.

Shi da Jaish mafa sun taɓa renon Commander Zafar, jarumta a jininsu yake, suna da karfi sosai, amma su wajen Ramish and Bilal suka koyi wannan training ɗin kafin commander!.

Yana fita ya nufi part É—in Akka, a nan ya samesu gabaÉ—ayansu except Auta, harta Mammiensu da su Mummy sun haÉ—u a wajen.

Yana zuwa ya ce da su su tashi su tafi, Chuchu na ganinsa ta taso da gudu ta nufesa tana faÉ—in. "Yah Jawad Aunty Sarina ta ce mun yaki za'ayi kuma Auta ban ganta ba, na shiga uku dan Allah Yah Jawad ka nemo mun ita, na je part na Momma bata nan, na je É—akinta bata nan, na duba ko'ina ban ganta ba, kuma ni yau since morning fa bamu haÉ—u da ita ba".
Wani irin zaro idanu ya yi tare da mayar da kallonsa kan su Fanan É—in. Tabbas bata cikinsu, a É—ari ya fara tambayarsu ina take?.

Cikin girmamawa su Fanan ɗin da suka sha duka a hannunsa ɗazun suka amsa mashi da suma basu ganta ba, ɗazun sun ci duka sosai a hannunsa, lilis ya yi masu kamar an aiko shi, su Sarina iyayen rashin kunya sai da idanu ya rena fata, an daku, shiyasa suka nutsu suka kara bashi girma suna girmamashi dan dole ƴan ƙaniya.

Jin cewa kowa ya ce bai ganta bane yasa ya ce yana zuwa bari ya dubata ko tana barci a wani É—akin. Da sauri Chuchun ta ce. "Yah Jawad zan bika". Girgiza kai ya yi. "A'a Jannat ki zauna a cikin Æ´an uwanmu, dan kinga yadda Kingdom É—in nan yake a rikice ban lamunta ki bini ba, ki zauna ina zuwa yanzu zan tambayo Hoorain ko ya ganta ne, in dai bata cikin nan kinga ta fita waje kenan, idan ta fita kuma dole Hoorain zamu nema, dan shi ne mai alhakin kula da ita a duk lokacin da ta fita". Ya kai karshen maganar tare da nufar waje.

Kuka ta sanya mashi tana yi mashi magiya a kan dan Allah ya tafi da ita, tana son ta raka shi ta riga kowa ganin Æ´ar uwarta autansu. Tsawar da Mammie ta daka mata a kan ba zata bishi ba ta wuce ta dawo ne yasa ya juyowa tare da dakatawa daga tafiyar da yake yi.
Da farko bai da niyar juyowa ya saurareta saboda baya son fita waje da ita, amma da Mammie ta yi magana sai ya ji yana son fita da ita, dan haka da ya juyo sai ya miƙa mata hannu kawai.
Chapter 69 · 0% Book details