← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 211

Sashe 79

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka shirya, su Sharifat sun yi kyau a cikin black abayn da suka sanya, sunyi rolling mayafan abayan a kansu, kayan ya fi karɓar Sharifat sosai, saboda ita farace tas, Leesharh kuma kunga ai chocolate ce, kalar fatanta ya ɗan saje da kayan, sai bata wani haska sosai can ba. Ga shi suna son saka kaya iri ɗaya, Yah Rizwan ne kafin ya tafi Tunisia suka je ya saya masu kayayyaki komai iri ɗaya, shiyasa suke saka kaya iri ɗaya yanzu. Abbie yana jin daɗin ganinsu a shiga iri ɗayan kenan, idan ya ga Leesharh na murmushi har wani sanyi yake ji tana ratsa ransa, ya rasa dalilin hakan, amma ya danganta hakan da cewa, dan yana jin daɗi ya sanya marayun Allah farinciki ne, bai san abin ya wuci haka ba, tabbas yana matuƙar jin sanyi a ransa idan ya ganta,
Hakan na matuƙar ƙonawa Ummie rai, sanadiyyar haka har shaiɗan ya samu matsuguni a cikin zuciyarta in da yake saƙa mata cewa tabbas Abbie son Leesharh da aure yake yi, idan kuma Ummie ta yi sake to nan ba da jimawa ba zata ji diran kishi ƴar cikinta a cikin gidan, wannan dalilin yasa ta kara tsanar Leesharh ɗin fiye da tunaninku.......... Tashin hankali, tab lallai gidan Abu Abdussalam zai kama da boma bomai ma kuwa, jama'a kun ji wata lukutar masifar da Ummie take tunani? Tana son tasa su Bilal su yi wa karnikansu kilishi da namar jikin Leesharh, ai idan suka ji Abbie zai kara aure ko da babbar mace ma zai aura akwai yaki ba kaɗan ba bare Leesharh da Sharifat ma ta fita a shekaru, lallai ummie ta zo da babban al'amari, amma kuma fa tun da ta fara tunanin hakan kila akwai kamshin gaskiya, dan fa mai ɗaki shiyasa wajen da yake yi mashi yoyo, ta san halin mijin nata in and out, lamarin abin dubawa ne.

(Ni kam nace da kuwa abin zai bada citta, kash wayaga Leesharh ana buga kishi da Ummie🤔 wayaga ta ce kai Ramish zo kayi driving ɗina muje shopping 🤣 yau zan kwana cikin farinciki dan za'a samu mai saukewa ƴan gidan dukka jijida kansu na jinin sarauta, haba idan Leesharh ta aure mana Abbie da takalma zamu rinƙa shiga parlon muga uban da zai hana mu🥱 mu kaka yaro kneel down😎🤣 uhmm babu ruwa dai.)

A motar Bilal Sharifat da Leesharh suka shiga dan zuwa masallacin, sai bata labarin yadda gidan king Badeen yake Sharifat take yi, tana ta kwaÉ—aita mata son ta ce zata bita gidan, amma ina ta ce ai koma menene a gidan ba zata je ba, ita ai bata fatan ta sake haÉ—uwa da su Omaid a rayuwarta.

A haka suka nufi masallacin, Æ´aÆ´an larabawa sai kallon Leesharh suke yi, dama last week ma da suka zo da ita Sharifat taga idanu a kansu kam har ta godewa Allah, tun bata magana har ta gaji ta kira securitynsu guda É—aya ta sanar da shi cewa kallon da jama'a dake cikin masallacin nan suke yi masu ya isheta, dan haka a taka masu birki.

Haka kuwa aka yi, securitys suka ja masu layi tare da daka masu warning, sai ya zamana a sake suke satar kallonsu, basu fitowa kai tsaye su kallesu bare a kamasu su sha hukunci.
To wannan satin ma haka suke ta faman kallon Leesharh É—in, tabbas ba dan komai suke kallonta ba face kyanta, gata dai chocolate color, amma kuma za'a iya cewa duk Æ´an'matan dake cikin musque É—in ta fisu kyau nesa ba kusa ba, shi ne abin yake ta basu mamaki, basu yi zaton za'a samu kyawawa a bakake fata ba, da sun É—aukemu kamar a kanmu aka sauke muni gabaÉ—aya.

Motocin Abu Abdussalam yana shigowa cikin masjid É—in sai da gabaÉ—aya jiniya ya karaÉ—e ko'ina, yau Bilal bai jira Abbie É—in nasu bane, kawai ya É—auko su Sharifat sun yi gaba, sai yanzu su Abbie suka iso, motocin a jere sun kai guda 10, daga gida zuwa masallacin kawai, Allah sarki Ramish yau jumma'a na biyu kenan za'ayi sallah ba tare da shi ba, abin tausayi, a gaskiya masu nikaf É—in nan bakaken mugaye ne, sun dagula mashi jini sosai da makirin maganin nan nasu, da kyar aka iya shawo kan jinin aka sarrafata, yanzu dai ikon Allah kawai ake jira, kila ya farfaÉ—o ko akasin haka, su Dr Raj kam dai sun gama nasu aikin.

Mata kenan, mu ɗin ƴan albarka ne, kowa da abin da yake yi a cikin masallacin kafin a tada hiƙama, wasu ƴan'matan suna latsa waya a cikin masjid ɗin ma, sam ba zasu hakura ayi askar ba, ayi karatun Alkur'ani a bar wayar sai an koma gida kuma, kwana shidda a week ana tare da waya ana latsawa, amma tana ɗaya, a ranar ma ƴan awannin biyu zuwa uku kawai ake da buƙata ka ware dan samun falala da lada, amma a'a, sai dai anyi abin da ba shi ba, ya Allah ka rabu da sharrin waya ka haɗamu da alkhairinta, kasa ya kasance mune zamu moreta ba itace zata moremu ba.

So wasu suna latsa waya, wasu sun haɗu suna ta hira maras amfani, wasu suna riƙe da Alqur'anin basu buɗe ba suna ta kallon mutane, kuma wlh wannan ɗabiar dayawan mata ne, haka suke yi, meyasa zaku bari sheiɗan ya hanaku samun wannan garaɓasa mai girma da daraja haka? Please mu daina bari shaiɗan yana zugamu yana hanamu aikata aikin da ya dace damu, yasa muna zuwa muna aikata aikin da bai dace da mu ba, kowani wayewan gari ki tabbata kin tuna mutuwa fiye da yadda zaki tuna rayuwa, hakance zata baki damar gina lahirarki mai kyau, Allah ka bamu dacewa.

Alqur'anin mai girma Leesharh ta ɗauko daga wajen ajiye Alqur'anai, tana ƙoƙarin dawowa mazauninsu Sharifat ta nuna mata da hannu a kan ta ɗaukomata ita ma, komawa ta yi ta ɗauko.
A tare suka buɗe suratul Maryam suka fara karatu, Sharifat ta yi mamaki sosai na jin yadda Leesharh ta iya karatu sosai, da kamar zata tambayeta a ina ta iya karatu nan, sai ta fasa ta ɓoye mamakinta suka cigaba da karatu har liman ya fara ƙoƙarin tada kabbara, sannan suka miƙe suka fara kikkimtsawa yin sallah.

Tun daga masallaci bayan sun idar da sallah Sharifat ta ce da Abbie daga nan a wuce da ita kawai, ita ko gida ba zata koma ba, saboda murna yau an barta ta je, tana fin wata biyar haka wani lokaci bata samu daman ko leƙa waje ba idan ba school ba, shiyasa idan aka bata damar zuwa gidansu uncle Rahab ko dai gidan kakan nasu mai gabaɗaya ba ƙaramin daɗi take ji ba.

Saka Bilal Abbie ya yi a kan ya kai masa ita can, sannan ya yi umarni da motocin securitys da dama su raka su. Haka kuwa aka yi Bilal ya wuce da ita, ita kuma Leesharh Abbie ya ce tazo ta shiga nasa motar. Sosai Sharifat ta ɗan yi mamaki, dan kuwa Abbie ba zaka taɓa ganin wani a cikin motarsa ba, ko ita da take ƴar cikinsa sau biyu ta taɓa binsa a cikin motarsa, yau rana tsaka kawai ya ɗauki Leesharh, abin da mamaki.

Shiru ta ɗan yi shaiɗan ya fara raya mata anya babu kamshin gaskiya a zargin Abbie da Ummie take yi na yana son Leesharh da aure kuwa? Dan kuwa yana yawan lallaɓa Leesharh ɗin sosai, wani abin idan ya yi ma sai ka zaci Leesharh ɗin ce yarsa ba Sharifat ba, abin da mamaki kam.

Dannewa ta yi ta shiga motar Bilal, shiru ta yi tanata saƙe saƙe har suka bar gidan, dama Ummie ta sha gaya mata tana zargin Abbiensu da soyayyar Leesharh a ransa, har ta ce mata ta daina janta a jiki, ita kuwa taki fir, ta ce ai Abbie ba zai taɓa yin haka ba, yana da ɗa mai 25 years a duniya ai ba zai ce zai ƙara aure ba, bata san a nata wautar bane hakan, dattijo mai yaro mai shekaru wajen 40 ma ya kara aure bare Abbie, nawa yake?....... Ni dai na ce akwai tashin hankali gaskiya ba kaɗan ba a gidan nan my people's, bala'in can kai jama'a!!.

Ummie ma fa ta zo masallacin, dan haka tsarin gidan Abu Abdussalam yake, sai dai ita ma a nata jerin gwanon motocin ta zo, haka zalika da zata koma, bata lura yau Leesharh ta shigar mata motar miji ba, da yau anyita kuwa.

Bayan sun koma gida ma a elevator ɗaya Abbie ya haura sama da tare da Leesharh ɗin, ya riƙe hannunta ɗaya da hannunsa ɗaya, ya kuma riƙe wannan sandar girman tasa da hannu ɗaya, yana dake cikin alkyabbar nan nasu na larabawa, kansa ya sha naɗi da rawani ya fita sosai. Sai kamshi haɗaɗɗe ne yake tashi a cikin elevatorn.

Suna haurawa parlourn sama suka fito, Abbie ya wuce part ɗinsa yana cewa Leesharh bye bye, ita ma nata room ɗin ta shiga. Tana zuwa ta haye saman gado ta kwanta tana tunanin rayuwa, yau da Sharifat bata nan sai gabaɗaya ta ji gidan babu daɗi, hakan yasa ta miƙe ta fara tunanin me zata yi dan ya ɗebe mata kewar Sharifat kafin zuwa dare.

Sai a lokacin ne tunanin wayarta ya dawo cikin kwakwalwata, dan ba abokiyar hira sai tunane tunanen banza, a haka ta je ta afka tunanin wayarta ko nace barazana ga rayuwarta. A hanzarce ta miƙe ta ɗauko wayar dan ta kunna ta gani, sai a lokacin ne ma ta tuna da abin da ya kawota gidan, babanta ya faɗo cikin ranta, nan take zuciyarta ta karaya jikinta ya yi sanyi sosai, har kerma hannayenta suke yi wajen kunna wayar tata.

Yana kawo wutan screen ya ɗauke saboda babu chargi, a hanzarce ta miƙe ta koma saman sofa dake kusa da switch, chagern Sharifat ta ɗauko ta sanya wayar.
Chapter 79 · 0% Book details