← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 211

Sashe 11

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habawa a wani irin zabure ta yunƙura, an fasa yi wa Bappa shagwaɓa, aljanun dukan sun motso, Mahreen mai karɓawa wata ƴancinta ma bare kuma ace ita aka tsokano? Ita fa take tsayawa ta yi dambe da duk waɗan da suka taɓo Mahnoor, dan ita Mahnoor ɗin sam bata da faɗa, tana da sanyi, idan anyi mata ba daɗi sai dai ta samu waje ta zauna ta sha kuka, to Mahreen take tsaya mata a buga dambe, tsabar faɗarta yasa yanzu aka dai'na tsokanar Mahnoor mai idon mujiya a kauyen, ai ganganci ne ma ka taɓo Mahreen ka yi tunanin zata barka, wlh komai daren daɗewa ba zata manta ba kuma bazata hakura ba, duk randa kuka haɗu sai ta rama, gata da iya faɗa, duk ta yagushe maka jiki da faratun hannunta, kamar wata mage, idan kuna faɗa tsalle take yi ta haye jikin mutun ta shakesa kamar mage, ta yi ta yagushe maka fuska, bazata taɓa bari kuma ka yakiceta ba, sai ta yi ta zullewa har sai ta yi maka lahani, duk kuma abin da zata yi Bappa baya taɓa ganin laifinta, shiyasa ko ta jibgi ƴaƴan mutane ba'a kawo kara wajen Bappa ko Nennenta, dan kuwa basu karɓar laifinta, gara ma Bappa zai bawa waɗan da suka kawo karan tata hakuri ya ce yarinya ce, ranar kam ma da ta fasawa wata baki sai da Bappa ya basu kyautar ɗan marakin saniya kafin suka hakura, sun ce sai sun ɗauki fansa sai sun rama, hakan yasa dole ya basu wai aje a yanka a gasawa yarinyar nama ta ci bakin nata ya koma normal, sai da ya yi haka suka hakura, ita kuma Nenne idan kika kai mata karar Mahreen uban masifa zata hau surfa maki ta ce ƴarta kawai aka sakawa ido a kauyen nan, yarinya kamara zasu cinyeta da baki!.

Mahreen akwai shagwaɓa sosai dan Bappa ya shagwaɓata sosai ba karya, sannan akwai faɗa dan faɗarta ma gado masifar ta yi daga wajen Nennenta, in tana masifa fa har wani rufe idanu take yi hannu na rawa ya yi sama ya yi ƙasa, ƙugu na rawa kamar ana kaɗa burugalin burga nono, haka take riƙe ƙugu tana sama tana ƙasa, ta in da take shiga ba tanan take fita ba, sai dai bata shiga harkar kowa ne, haka kawai bata kama mutun da faɗa, idan kunga tana faɗa to tabbas taɓota aka yi, idan kuma aka taɓota wlh wannan faɗar bata karewa cikin sauki, idan yarinyar bata gudu ko ta miƙa wuya ta bada hakuri ba, wlh sai Mahreen su kwana suna gwabza faɗa ba zata gaji ba, so bata faɗa sai an tsokaneta ko kuma an taɓa mata ƴar uwarta Mahnoor, nan ne zaku ga balbalin bala'i in mai tafasa in jita. Yarinyar nan ta yi suna a wannan kauyen fiye da tunaninku, manya da yara kowa ya santa, gata da ɗan banzan farinjini, bata isa ta gifta wani guy ɗin saurayin bai ce mata hllo ƴan mata ba.........😎🌝

Su fulanin daji kunsan suna auren wuri gaskiya, kamar Mahreen ɗin nan takai ayi mata miji idan an samu, wadda bata kaita bama ana yi masu miji har ma aure, shi dai Bappa ya bar ƴaƴan nasa ne a cewarsu yana jiran ƴaƴan yayansa maza da suka tafi kiwo na tsawon shekaru biyu, sun tafi yawon kiwo har ƙasashen makota, dama kun san suna yin haka, to su yake jira idan sun dawo zai aura ma ɗaya Mahreen sai a haɗa da Mahnoor dake da nata saurayin shi ma na gida ne, yana son haɗa aurensu lokaci guda ne yasa bai aurar da Mahnoor ɗin ita kaɗai ba.

Da sauri Bappan ya riƙota. "Haba gajin Bappa, ki kyaleta mana tun da dai ta gudu, ai ta ji tsoronki ne yasa ta gudu, tun da tana tsoronki yi hakuri ki ɗaga mata kafa". Ya faɗa cikin sigar rarrashi.

"Da gaske bappa ta ji tsorona?". Ta faɗa tana zaro idanu. Duk wannan faɗuwa ƙasa da ta yi tana birgima tana kuka ashe babu hawaye ko tsilo a face ɗinta, ashe ihunta kawai take kwararawa babu hawaye, kai wannan yarinya sai shirin Allah. Amma dai wani lokaci tana da gaskiya wajen kwatawa kanta ƴanci har ma da ƴar uwarta.

"Kwarai kuwa gajin Bappanta, ta ji tsoronki sosai ma kuwa".

Wani irin tuntsirewa da dariya ta yi tare da fara yin tsalle tana faÉ—in. "Shikenan Fatu ki je na yafe maki tun da kin ji tsorona, yeee ta ji tsoro a bata kunun zakin da ya yi sati ta sha ta bugu ta hau aiki".

Mahnoor dake tsaye tun É—azun tana kallonsu ne ta ce. "Mahreen Allah ya nuna mun ranar da zaki dai'na faÉ—a, Bappa kazo muje ka ga wani abu a bakin ruwa, sai kiranka nake yi baka amsa ba".

Yana ƙoƙarin yin magana Mahreen ta rigasa da cewa. "Adda Mahnoor zan daina faɗane kawai idan suka dai'na zagin kwalliyata".

ÆŠan girgiza kai ta yi kafin ta amsa mata da. "Ai Mahreen ba zagin kwalliyar taki suke yi ba, na sha faÉ—a maki saboda basu iya haÉ—aÉ—É—en kwalliya irin taki É—in bane yasa suke zaginsa, da zaki koya masu irinsa tsab zasu dai'na zagin su fara yin irinsa...."

Ƙara zaro fararen idanun nata ta yi. "A'a gaskiya wlh ba zan koya masu ba munafukai kawai". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai.

"Bappa zo mu je ka ga wani abin, ke kuma Mahreen ki dawo da dabbobin nan kusa, sun yi nisa sosai".

To ta amsa mata tare da sanya kai da Æ´ar gudunta ta wuce tana murmushin da ya kara mata kyau sosai, ta ji daÉ—i Æ´ar uwarta ta ce tafi kowa iya kwalliya a kauyen........ E da gaske wannan yarinyar akwai shiga rai, nima dai ta shiga rai na.

Wucewa Bappa ya yi izuwa in da Mahnoor ke tsaye, a cikin ransa yana addu'ar Ubangiji Allah ya shirya mashi Mahreen ɗin nan nasa, Allah ya rabata da shegen son faɗar nan, fargaban da yake yi kada wata yara ta taɓo wadda zata yi mata duka, ba zai iya jure a daketa ba, yana kaunarta sosai, duk wadda ta taɓa mashi lafiyarta sai sun buga shariya a wajen Arɗo da shi, so shiyasa yake yi mata addu'ar Allah yasa ta dai'na faɗar ma tun kafin a kai ga haka.

Daga ɗan baya baya Mahnoor ta tsaya bata iya ƙarisawa bakin kogin ba. Shi kuwa Bappa da ganin kamar mutun ne a wajen yasa ya yi saurin ƙarisawa wajen dan ya ganewa idanunsa.

Zuba mashi ido sosai Bappan ya yi yana kallon yadda fuskarsa take da kuma yadda yake kwance a bakin ruwan, rabin jikinsa duk a cikin ruwan, kyakkyawa ne sosai, farine tas da shi, soft skin ɗin nan nasa sai wani sheki yake yi, ga fatar tasa luwai luwai kai ka ce bai taɓa fita rana ba. Yanayin yadda yake kwance a bakin kogin ba ƙaramin mamaki ya bawa Bappa ba, abin ya ɗaure mashi kai. Ita kam Mahnoor ta tsorata sosai, ta koma baya tana faɗin. "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun ". A cikin zuciyarta, dan a nata tunanin aljani ne ba mutun ba, dan kyakkyawan gaske ne, ga wannan dark black curly hair nan nasa ya kwanto mashi har saman goshinsa, da yake ruwan kogin ya jiƙa gashin nasa, sai ya manne mashi a fuska, duk da idanunsa a rufe, hakan ba zai hana ka gane cewa yana da manya manyan idanu ba, ga lips ɗin nan nasa ya yi pink color sosai kamar na mata, ɗan ƙarami da shi, yana da dogon hanci sosai, hancin nasa kuma bai yi irin dogo zur ɗin nan ba, a'a ya yi ɗan dai'dai mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ya kuma yi dai'dai da face ɗin nasa, ya kara kawata kyansa ba kaɗan ba.

Kwata kwata bai yi kama da Nigerians ba, suit ce mai bala'in kyau da tsada a jikin sa, launin ask color ce, daga ta ciki kuma, long sleeve shirt ce fara tas. Duk da yana kwance, hakan bai hana ka ga cikakkiyar tsuransa ta kiran karfi da lafiya tare da jini a jika a tattare da shi ba, ga dukkan alamu yana da alaƙa da manya manyan mutane, duba da irin tsadaddun kayan da suke jikinsa, watch dake hannunsa ma kawai abin kallo ne, diamond watch ce mai matukar kyau da ɗaukar hankali, kafarsa na sanye cikin wata dankareriyar half cover ash color mai bala'in kyau, neck tight dake wuyarsa ta manne mishi a wuyar tasa ta samar lallausan fatarsa, saboda ruwa da ya jika shi, yana da tsawo sosai, ga faɗin kirji tamkar wani zaki.

Tsugunnawa a kusa da shi Bappa ya yi babu ko tsoro tare da sanya hannunsa a bakin kofofin hancinsa dan ya ji shin yana numfashi ne ko baya yi.

Ko kaÉ—an baya numfashi kamar ma babu rai a tattare da shi, duba da yanda ya yi wani yellow sosai, ga kuma face nasa da alamar kumbura a tattare da shi. ÆŠagowa Bappan ya yi cikin harshen fillanci ya ce "Mahnoor É—in Bappa ki kaÉ—o mun jakin guda É—aya bari na É—aura shi a kanta mu je gida".

"Bappa kada ka ɗauke shi, aljanine fa, ni ban taɓa ganin mutun mai shegen kyau irin haka ba". Ta yi maganar tana zaro idanu.

Cike da ɗa zolaya ya ce. "Kin taɓa ganin aljani ne? Kuma waye ya ce maki aljani yana da kyau? Ko dai kin taɓa ganin kyakkyawan aljani ne ban sani ba...?"

Kara ja da baya ta yi, jikinta har ya fara kerman tsoro, ita dai bata taɓa ganin kyau irin nasa ba, sannan ga shi kwance a cikin ruwa, sai hakan ta kara sanyawa fuskansa ya yi wani iri a gareta. "A'a bappa, ban taɓa ganin aljani ba, amma dai ban taɓa ganin mutun irin wannan ba".

A takaice ya ce mata. "Nima ban taɓa ganin mutun irin wannan ba kam, ina dai ganin masu irin yanayinsa, amma ina da yaƙinin ba aljani bane, mutun ne wannan In Sha Allah, kada ki damu je ki kaɗo mun jaki bari na nemo wani ya tayani kama shi mu ɗaura a saman jakin".
Chapter 11 · 0% Book details