Sashe 110
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan rasuwarta da kwana uku ne Maman Hanifa tana zaune a parlour, ta buga uban tagumi tana tunanin rayuwa. Fitowa daga cikin É—akinsu Khadija ta yi, ta zo wucewa zata shiga kitchen, idan baku manta ba dama kitchen É—in a parlour yake.
"Zo nan Khadija". Ta faÉ—a tana kallonta sosai, da alama tana zargin wani abin.
Ba musu ta juyo ta zo, dan koba komai maman Hanif tana nuna masu so, tana kuma tausaya masu.
A saman sofa ta zauna kusa da gwaggon nata. "Gwaggo gani nan". Da kyar muryarta ya iya fita har ta furta hakan, saboda kukan da ta rinƙa sha, ga kukan cikinta da take ɓuya a cikin toilet kullum dare ta ɗirka, ga kukan rasuwar kakar tasu, ga shi bata san a wani hali kawunsu mai kaunarsu Sadiq yake ciki ba, hakan yasa yanzu sai dai ka kalli bakinta ka fahimci me take faɗa, muryanta kam sam baya fita.
"Khadija me nake ganin nan? Ya naga jikinki haka?". Maman Hanif ta faÉ—a da mamaki a saman face É—inta!.
Wani irin dukan uku uku kirjinta ya bada, nan take ta nemi nutsuwarta ta rasa, tsuru tsuru ta yi da idanu, duk da muryar tata baya fita zaka iya fahimtar muryar tata tana sarkewa, da kyar ta furta. "Me kika gani gwaggo? Me jikin nawa ya yi?".
Sarai maman Hanif É—in ta lura da ruÉ—ewar da ta yi daga tambaya, hakan yasa ta ji zuciyarta ya tsinke, addu'a ta yi a cikin ranta Allah yasa ba abin da take zargi bane ya faru da Æ´ar É—an uwan nata, da sun shiga uku sun lalace.............. Ai kuwa sai dai ki fara kukan kun shiga ukun, dan kuwa abin da kike zargi ne in ji ni princess Teema!.......ðŸŒðŸ˜¥
Zuciyarta a tsinke ta ce. "Khadija naga jikinki ne wani ɗanye ɗanye ban gane ba, kamar mai ƙaramin ciki kamar kuma period ne, menene yake faruwa?". Ta jefa mata tambayar kirjinta na dukan uku uku, fargabar abin da zata tono ne yake neman kasheta.
"Gwaggo nima ban sani ba". Ta faɗa tamkar zata rushe da kuka, wani irin ƙululun bakinciki mai matuƙar bala'in tsaci ne ya tokare mata maƙoshi, wani lokaci ji take yi kamar ta kashe kanta kawai ta huta, Zee ce take ce mata ko ta kashe kanta bata huta ba, hasali ma a lokacin da ta kashe kanta a lokacin ne babin wahalarta mai lasisi zai buɗe, dan kuwa duk wanda ya kashe kansa dai yasan makomarsa, to gara mata azabar duniya da ta lahira, tun da Allah ya ƙaddara basu da rabon duniya to su tsaya su nemi lahira kawai kada su yi biyu babu, wannan maganganu na Zainab suke sanyawa ta daure ta fasa kashe kan nata. Ban da haka wani lokaci har wuƙa take ɗauka ta ce zata kashe kanta!.
"Anya kuwa Khadija? Ko dai mu je asibiti ne? Dan gaskiya alamar mai ƙaramin ciki ne a tattare da jikin nan naki".
Zaro idanun nata da rama suka kara masu girma ta yi, nan take wani irin faÉ—uwar gaba ya dira mata, da kyar ta haÉ—iyi yawun wahala a wahalce, sannan ta ce. "A'a gwaggo ni bana jin komai wlh".
Shiru ta É—an yi kamar mai tunanin wani abin, can kuma sai ta ce. "To shikenan ta shi ki je".
A hanzarce ta miƙe har kamar zata kifa ƙasa, duk saboda saurin ta bar wajen kada ma gwaggon nata ta sake jefo mata wata tambayar da ƙwaƙwalwarta ba zai iya jura ba.
Da kallo ta bita har ta shige cikin kitchen ɗin, ajiyar zuciya ta sauke, a fili ta furta. "Ya tabbata baki da gaskiyar Khadija, wlh akwai abin da kike ɓoyewa, ya Allah gamu gareka, ka dubemu da idanun rahma, ya Allah kada ka sa abin da nake zargine yake a gaske, ya Allah ka kare mun mutumcin dangina". Tana magana idanunta ne suka ciko tab da kwallah, zuciyarta yana yi mata wani irin suya, yau da bata yarda da Allah da Manzonsa ba da ta shiga uku ta lalace, irin wannan jarabawa sai mai karfin imani zai iya ɗauka, duk rintsi duk wuya my people's kada ku kaucewa Allah, kowace irin hali zaku shiga kada ruɗu da tashin hankali yasa ku manta Allah ne kaɗai zai iya fitar da ku.
Duk abin da ya faru a kan idanun Zee dake bakin kofa tana ƙoƙarin fitowa ya faru, zata fito ne ta taya Khadijah ɗin aiki ne dama, jin suna magana da maman Hanif ɗin ne yasa ta tsaya tana sauraro, wani irin bugawa da zuciyarta ya yi na jin abin da gwaggon nasu take zargin ƴar uwarta da shi.
Da karfi ta dafe saitin zuciyarta tare da furta. "Ciki? Kuma Khadija gwaggo kike zargi? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, na shiga uku ni Zain........." Bata kai karshen maganar ba ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, idan baku manta ba dama tana da ciwo a zuciya baiwar Allah, sai hakan ya fama mata ciwon ya ja mata wata bala'in. Kuma haƙiƙa ta yarda da zancen gwaggon nasu ne ya ja mata wannan matsalar, dan dama ta jima tana zargin Khadija na ɓoye mata wani babban al'amari dangane da ita, sai dai bata kai abin har ga ciki ba gaskiya, amma da gwaggon nasu ta yi magana sai ƙwaƙwalwarta ta tariyo mata komai da ya rinƙa faruwa a tsakaninta da Khadija.
Na farko tun da Khadija ta dawo bata ga ta yi fashin sallah ba wato period, sannan sau da dama tana kamata a cikin toilet tana kuka, idan ta tamnayeta sai ta ce ta tuna baba da mama ne, kuma tasan karya take yi mata, dan bata saba yinsa ba, idan ta yi dole a ganeta, amma duk da haka bata nuna cewa ta gane karya take yi mata, sai ta yarda kawai a wuce wajen, to yau ga gaskiya ya bayyana innalilahi wa inna ilahir rajiun wannan wace iriyar bahaguwar ƙaddara ce?.........................
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI â¤ï¸ðŸ”¥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 29/10/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
💘ZANGO NA BIYU....âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
E30
A guje maman Hanif ta miƙe ta yi kanta, sunanta take ambata babu kakkautawa cikin tsananin tashin hankali take!.
Jin tana ihun sunan Æ´ar uwar tata yasa Khadija É—in fitowa daga cikin kitchen É—in da gudu a kuma ruÉ—e, haka zalika ita ma Hauwa a guje ta fito daga nata É—akin.
Kansu Khadija ta yi tana ambatar sunan Zee ɗin, ita kuwa Hauwa ganin cewa Zee ce ta suma ba wata masifar da ta zata bace sai ta ja birki ta tsaya a tsakiyar parlourn tana binsu da kallon walaƙanci.
A ruÉ—e Khadijar ta bar kan nasu ta juya da nufin ta je ta É—auko ruwa su zubawa Zee É—in, tana juyowa suka yi karo da Hauwa dake tsaye a tsakiyar parlourn tana yi masu kallon rashin mutuncin.
Bangajeta Hauwar ta yi har sai da ta yi baya ta faɗi ƙasa, hakan yaja hankalin maman Hanif ta juyo da kallonta a kansu.
Yunƙurawa ta yi ta miƙe tsaye, a tsiyace haɗe da walaƙance ta ce. "Ke amma dabbace ko? Ƙwaƙwalwar ki ta jakuna ce da alama".
Da yake jahilar ce bata ma san zafin abin da Khadija É—in ta faÉ—a ba, sai bata wani ji zafin maganar ba, amma saboda a cewarta Khadijar ta rainata da zata yi mata magana ba respect haka sai ta cire hannu zata dalla mata mari.
Kaucewa ta yi marin bai sameta ba, cikin fushi ta É—ago kai, dama ga cikin nata ya mayar da ita mafaÉ—aciya. Kanta ta yi da nufin ta daddallah mata maruka, dan kuwa duk yadda kake kai zuciya nesa sai Hauwa ta kureka, duk yadda take dannewa ta kawar da kai yau sai da ta kure ta, sam bata so wani abin ya sake haÉ—asu ba, amma Hauwa muguwar Æ´ar shisshigi ce.
A hanzarce maman Hanif ta riƙeta tana faɗin. "A'a Khadija ki rabu da ita, jeki ki kawo ruwa mu zubawa ƴar uwarki kin ji?".
Wani irin hucin da ta fara fitarwa ne zai sa ku gane lallai yau ranta a matuƙar ɓace yake, ta zo har wuya.
Zata wuce Hauwar ta danko rigarta ta wajen shoulder É—inta tana faÉ—in. "Dawo nan dan ubanki! Da kenan faÉ—a da ni zaki yi ko? To bismillah, ba kin san abin da uwarki ta sani ba? Ai dole ki ce zaki yi faÉ—a dani ina matsayin uwarku a cikin gidan nan". Ita fa Hauwa a dole dole so take yi su yi faÉ—a ta samu wani abin ta buga mata yadda zata raunatata.
Aikuwa a wannan karon Khadija tana juyowa ta É—auketa da wani irin gigitattacen mari mai rai da lafiya. Ihu ta saki kamar wata mai motsi a kai, cukumo wuyar rigar Khadija É—in ta yi da nufin ta lakkaÉ—a mata dukan tsiya.
Kunsan dai tana fama da kanta, ba wani karfin kirki bane gareta, ba ci a ƙoshi ga ciki, hakan yasa Hauwar ta jefar da ita ƙasa, tana ƙoƙarin hayewa kan ruwan cikinta ta yi mata dukan kawo wuƙa.
Aikuwa maman Hanif ta ce ba'a haifi uwarta ba, dankota ta yi, hankaÉ—ata ta yi sai da ta tafi ta kifa a kusa da sofa two seater. Bin bayanta ta yi ta hau jibgarta kamar ba gobe, dama ta jima da takaicin Hauwar nan a ranta, kullum idan ta ganta sai ta ji tamkar ta kasheta kowa ta huta, to yau dai Allah ya yi ta samu dama jibgar banza.
Dukar takaici ta rinƙa kaimaya ta ko'ina tana sauke numfashi mai kama da huci, ihu mai sauti Hauwar ta fara fitarwa dan jama'a su kawo mata ɗauki, kunsan akwai ɗaiɗaikun ƴan zaman makoki a waje da suka yi saura.
Jin ta dameta da ihu zata iya tara masu jama'a yasa ta dunkule hannunta ta dakarkare ta danna mata naushi a bakin nata.