← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 211

Sashe 179

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baku tanbayeni ina su Sarina ba? Tuni sun nutsu tsit tamkar babu su a cikin ɗakin, sun saki baki suna aikin kallonsu Ramish da basu taɓa gani a zahiri da wayonsu ba, sai dai a hoto da kuma lokacin da suke yara, basu taɓa yin expert ɗin ganinsu ba, wow abin ya ƙayatar matuƙa.

Ramish ransa ya ɗan sosu ganin kowa yana nan banda mamarsa, ita kaɗai ce taki zuwa, dama dai kun san ba shiri take yi da momma ba, so bata leƙo ba, ya ji babu daɗin hakan, ya so ace kamar yadda momma da mummy suke zaune cikin girmama juna da mutunta juna ita ma haka take da su, amma masifarta ya yi yawa.

ÆŠunguma suka yi gabaÉ—ayansu Ramish yana É—auke da guyson suka koma parlon, a nan suka isko Dr Raj, Bilal kuma ya É—auki Auta, King Zuhair bai san sun zo ba, yana can suna ta aikin shirya tafiya yakin da su Hoorain zasu yi masarautar Queen Zarina, Allah sarki ni dai fatana Allah tasa kada Hoorain ya faÉ—a tarkon Queen Zarina da ta kafa masu.

Dik in da Ramish ya motsa sai Sarina ta bishi da ido, ashe a hoto ma bashi da kyau sosai, hoto ta rage mashi kayansa, ashe a zahiri ya fi kyau, haka take ta faÉ—e a ranta. Fanan kuwa tunanin Jaish ne ya addabama rayuwarta, faÉ—in take yi da yananan yanzu da shi ma yana cikin Æ´an uwansa.

Aneesa kuwa da kamar aljana take sarai ta san da labarin zuwan su Ramish da ko King bai sani ba, wai ko a ina take samun waÉ—an nan labaran da ko iyayensu basu sani ba sai kuga ita ta sani? Anya mamarta bata tsafi kuwa? Anya basu da aljanun gado kuwa? Yarinya kamar wata yar ruwa!.

Sannu da zuwa ta yi wa yayyun nata cikin girmamawa, sannan ta tafi shirin Birthday É—in guyson É—insu.

Ita kuwa Sarina da murna ya hanata yi masu sannu da zuwan ma guduwa ta yi izuwa wajen Mammiensu dan ta kai mata labarin abin da yake faruwa. A nan ta isko uncle Abbas yana gayawa Mammie aftar ɗaurin auren Rizwan da chuchun ranar Friday on Sunday tawagar mayaƙansu zasu dinfari masarautar Zarina domin shafe babinta a doron duniya. Allah sarki bai san tamkar a kunne Zarina yake wannan magana ba.

Sai addu'a da fatan nasara take yi masu a zahiri, daga ta cikin zuciyarta kuma addu'ar rugujewarsu kawai take yi. Cike da murna Sarina ta shigo cikin room É—in, daidai lokacin uncle Abbas zai fita kenan bayan sun kammala yin magana.

Cike da so ya dubeta tare da cewa. "Daughter murnar me kike yi ne haka?".

Bakinta da yaki rufuwa ne saboda murmushi ta ce. "Daddy murna nake yi su Yah Ramish sun zo".

ÆŠan zaro idanu ya yi. "Ramish kuma? Kai inaga dai baki ji da kyau ba, nasan baki sansu ba, so baki ji sunanyen waÉ—an da suka zo É—in da kyau bane, amma ba su bane".

"Allah daddy su ne, ai na san su a hoto".

Fuskarsa É—auke da mamaki ya ce. "Su Ramish dai? Kai abin da mamaki, jiya fa na yi waya da shi har nake ce mashi yaushe zasu zo ya ce mun babu rana, har ce mashi na yi Akka bata da lafiya dik dan ya zo, amma ya kekashe ya ce mun kila nan da one year haka idan yaga yana da lokaci zai zo, shi ne yanzu zaki ce mun shi ne? Kai basu bane".

"Wlh daddy shi ne, ka je part na momma zaka gansu, harda Yah Bilal da Yah Raj".

Kallon mammie dake tsaye a gaban mirror ya yi. Ita ma shi take kallo.

"To ka je ka duba mana ko dai su É—in ne da gaske". Cewar Mammie.

Jinjina mata kai ya yi tare da wucewa ya fice. Da gudu Sarina ta kariso gabanta tana faÉ—in. "Mammie yau kam mijina ya zo, yau kam na gansa ido da ido, sai dai kuma fa ko kallona bai yi ba, kuma Aneesa da take kanwarsa ma ta yi mashi sannu da zuwa bai amsa ba, wai Mammie kin gansa kuwa? Allah ya haÉ—u sosai like wow, ya yi kama da dad fa, kai ni ban ma san me zan ce ba". Dik tana ruÉ—e yau ta gansa, dik ta rikice sai surutai take yi.

"Ke waye ya gaya maki Ramish ne na ajiyewa ke? Waye ya ce maki shi ne mijinki?". Cewar Mammie dake binta da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa.

Cak ta dakata da murmushin da take yi, sai ta ji maganar wani irin, ba Ramish aka ajiyewa ita ba to me Mammie take nufi?. Ta jefawa kanta tambayar da bata da amsarsa.

"Ni ki wuce ki bani waje zan yi wani abin ne". Mammaien ta sake faÉ—a, da alama ranta bai so zuwan su Ramish gidan ba sam. Kamar zasu katse mata wani abin ne.

"Mammie ba kin ce babban yayanmu zan aura ba? To ai Yah Ramish shi ne babba, ko dai Yah Bilal ya fishi ne?". Cike da damuwa ta yi tambayar, dan ita fa a gaskiya ta faÉ—a daga kallon farko da ta yi wa Ramish, ta ji sonsa a ranta.

"E haka nace, amma ba Ramish bane, ki fice mun a É—aki da wuri zan yi aiki".

ÆŠan zaro idanu ta yi. "Mammien babban yayanmu kika ce zan aura, sannan kuma kika ce ba Yah Ramish ba, to wanene? Dad yana da wani yaro ne bayan Yah Ramish?".

"Bashi da wani yaro bayan Ramish, amma ba shi zaki aura ba, ni bai yi mun ba, zaki iya fita yanzu". Cikin faÉ—a ta yi maganar.

ÆŠan tsuke fuska ta yi tare da buÉ—e baki da nufin ta sake tamnayarta, hannu ta É—aga mata alamar bata son sake jin wani magana kuma. Dan dole ya hakura ta nufi waje sake sake cike tab a ranta, ta rasa ma me zata tuna dan nemanwa kanta mafita, ta dai kamu da son Ramish daga kallon farko.

A ɓangaren su Momma kuwa, Yah Ramish ne ya yi wa guyson wanka kaman yadda ya saba, dan kuwa Momma ta ce tun da sun zo ba zata yi mashi ba, sai dai su da suka shagwaɓa shi da hakan su karita da shi, part ɗinsa Ramish ya wuce da shi har da cewa Mommar e sun ji a basu kayansu su je su yi mashi wanka dama sun saba.

Mummy kuma ta fito mashi da sabbin haÉ—aÉ—É—un kayan da ta saya mashi, kyautar birthday É—insa ma kayayyakin wanka na gayu masu bala'in tsada ta saya mashi, ta ce ya cigaba da É—aukar wanka yana tashin kan kowa, komai dozen dozen ta saya mashi.

In short sun kammala shirya shi, shi fa kowani irin wanka ya É—auka tashin kai yake yi, ya yi masifar kyau, su Chuchu dik sun É—auki wanka, sai da aka gama haÉ—uwa a part É—in mummy za'a fara gudanar da abubuwa ya saka masu kuka a kan babu Yah Jawad, Yah Rizwan, and Yah Jaish a wajen, shi ba zai yanka cake ba har sai sun zo.

Kallon su Ramish momma ta yi, domin kuwa aikin neman Jaish yanzu ya koma hannunsu, ya rataya a wuyansu, ɗan duƙawa Ramish ya yi ya mashi raɗa a kunne, nan take ya ɗan saki murmushi sannan ya ce. "To ina Yah Jawad and Yah Rizwan kuma?".

Kallon room É—in Ramish ya yi, ganin babu su a wajen ne yasa ya kalli Bilal dake kusa da shi.

Shi ma Bilal É—in kallon Dr Raj ya yi ba tare da ya furta uppan ba.

"Momma ina Jawad da Yah Rizwan?". Cewar Dr Raj.

"Jannat jeki ki kira Jawad yana room É—insa, ke kuma Zunaira jeki ki kira Rizwan a part É—in uncle Abbas". Cewar mommar.

Da sauri suka miƙe, Chuchu ta sha kwalliya sosai, ta yi kyau cikin doguwar rigarta Turkish gown.

Part É—insa ta nufa, sallama ta yi ti a parlonsa, babu kowa sai kuyangun da suke yi mashi hidima, suna ta aikin gyaran parlourn.

Suna ganinta suka zube ƙasa domin kwasan gaisuwa.

"Yah Jawad yana ciki?". Ta gefa masu tambayar ba tare da ta amsa gaisuwar tasu ba.

"E yana ciki". Suka bata amsa har suna haÉ—e baki wajen magana, cikin girmamawa suka yi maganar.

Wucewa ciki ta yi ba tare da ta sake bi ta kansu ba.

A bakin door room É—in ta yi sallama. Shiru ba'a amsa ba, sake kwala sallama ta yi, shiru.

Sau uku tana yi ba'a amsa ba, kamar zata juya ta koma, dan in baku manta ba ya ce ta dai'na shigo mashi cikin ɗaki, ta rinƙa tsayawa a iya parlour, to sai take jin kamar ta juya.

Har ta juya sai kuma ta ji wani irin nishi kamar gurnanin zaki, tamkar wanda aka shakewa numfashi bata fita, bata taɓa jin irin wanann nishin ba, hakan yasa ta yi saurin juyowa, a ɗan tsorace ta tura kofar ɗakin, fargaba kamar zai kasheta, a tsorace take da abin da idanunta zasu gane mata.

Kara tsorata sosai ta yi a lokacin da ta hangosa kwance a saman bed É—insa yana wani irin numfashin da karfi karfi, ya kudundune cikin bargo gabaÉ—aya har kansa, ba zaka ce akwai mutun a gadon bama idan ba ka ji numfashin nasa ba.

Ai a miliyan ta ƙarisa wajen, bama ta san lokacin da ta haura saman gadon ba, tuni ta ruɗe, sunansa kawai take ambata Yah Jawad, Yah Jawad.

Amma ina bayan wannan numfashin babu wani abin da yake yi kuma.

Hannu tasa da karfi ta yaye bargon. Wani irin baya baya ta yi a razane na ganin irin yadda yake kwance, kamar babu rai a jikinsa, ga kuma wani irin numfashi da yake fita wanda sai ka yi zaton ba daga jikinsa yake fita ba.
Chapter 179 · 0% Book details