Sashe 67
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai ta yi aman har ta galabaita, idanunta suka yi jajir kamar jini, ta sha wahala sosai. Ganin aman ya dakata ne yasa malamin nasu ya yi saurin nufar shagon mai provision ɗin na bayansu ya karɓo mata ruwa. A harzarce ya zo ya fasa ruwan ya bata.
Da kyar ta iya karɓa ta fara wanke bakinta da shi, da kyar ta iya miƙewa tsaye, bata sake ce da shi ko uppan ba ta nufi hanyar gida, tana tafiya tamkar wadda ta sha wani abin, sai layi take yi kamar zata faɗi ƙasa. Bin bayanta ya yi yana yi mata sannu har suka isa bakin titi, sai tambayarta yake yi dama bata da lafiya ne? Me yake damunta? Har da ƙarawa da an kaita asibiti ne ko ba'a kaita ba?.
Ita dai ko sannu bata sake ce mashi ba, haka ta samu da kyar ta tsallaka titin ta nufi hanyar gida. Binta ya yi yana cigaba da yi mata magana bata kula shi ba har ta shiga cikin gida ta barshi tsaye a waje.
Hauwa kawai ta isko a parlourn, tamkar bata ganta ba ta wuce ta nufi É—akin nasu, har lokacin kuma tana layi kamar wadda ta sha wani abin.
"Ke Khadeejerh lafiya kike kuwa?". Cewar Hauwa uwar shisshigi a lamuran mutane. Ai yadda kuka san da bango take magana haka Khadeejerh bata kulata ba, cigaba da tafiyarta kawai ta yi har izuwa cikin É—akin nasu, ta banko kofa ta murza key.
Tana shiga bata kula Zainab bama ta wuce cikin toilet ɗinsu. Wani aman ta je ta sakeyi saboda yadda cikinta yake murɗa mata sosai, har lokacin tana jin warin turaren mutumin yaki sakar mata hanci, shiyasa ta sake zuba wani aman. A ruɗe Zee dake kwance a saman gado ta diro ƙasa, ita ma ba wani karfin kirki bane a jikinta amma haka ta bi bayan Khadeejerh ɗin da gudu izuwa cikin toilet ɗin.
Ganin tana ta amai ne yasa ta ƙara ruɗewa, a rikice take tambayarta meyasameta, ta yi maganar tare da ƙarisowa ciki ta riƙeta. Bata iya amsa mata ba sai amanta da take yi, sai da ta yi mai isarta, sai da zuciyarta ya ɗanyi sanyi sosai sannan ta wanke bakinta tare da cewa Zee ta saketa ta fita bari ta yi wanka.
Cikin kuka Zee ta ce. "Amma Aunty Khadeejerh ki gaya mun me yake damunki tukun nan in fita".
"Kije É—aki idan na fito zamu yi magana". Ta faÉ—a da kyar. Tana kuka ta nufi wajen ba tare da ta sake yin wata magana ba.
Wanka ta yi tare da É—auro towel ta fito. A zaune a bakin gado ta isko Zee É—in, wucewa ta yi ta nufi wajen jakar kayan da Zee É—in ta dawo da su daga asibiti, dukkansu basu da kaya sai wanda Sadiq ya kwasowa Zee É—in daga tsohon gidansu ya kai mata asibiti lokacin da take kwance, kayansu duk yana tsohon gida.
Wata doguwar riga ta ciro ta sanya a jikinta, tsawon bai kai mata har ƙasa ba kam, amma ba laifi ya ɗan yi mata daidai, sai dai ya matseta sosai, dan ta fi Zee ƙiba kaɗan.
Gadon ta zo ta haye ta kwanta, zannin gadon ta ɓangaren da take ta yaye ta lulluɓa da shi, nan take ta fara rawan sanyi alamar zazzaɓi. Ganin haka sai yasa Zee bata iya sake tambayarta me yake damunta ba, sai ta yi shiru kawai, daga karshe ma lallaɓawa ta yi ta dawo kusa da ita suka kwanta a tare, kafin wani ɗan lokaci barci ya yi awon gaba da su ba tare da sun ci abinci ba bayin Allah, ga Zainab bata sha magungunarta ba, basu yi waya da Sadiq ba haka barci ya yi awon gaba da su.
______________________🔥💔
KINGDOM OF POWER.
Dai'dai Gimbiya Chuchu zata shiga bedroom na Akka ta ji an rufe mata idanu ta baya. Murya a sanyaye ta ce. "Yah Jawad me haka ne wai?". Zame hannayen nasa ya yi tare da cewa. "Waye ya ce maki ni ne?".
Juyowa ta yi suna fuskantar juna tare da ciro wayarta daga kunnenta. "Ba wanda ya gaya mun kai ne face kamshin perfume É—inka".
Kashe mata ido É—aya ya yi tare da cewa. "Da waye ake waya to? Naga kina kan call". Dawo da kallonta kan screen É—in wayar ta yi. "Yah Rizwan ne".
Jinjina kai yayi ba tare da ya sake yin magana ba, gera kawai ya É—aga mata alamar ta cigaba da yin wayarta mana.
Mayar da wayar kunenta ta yi tare da cewa. "Yah Rizwan zamu yi magana anjuma, zan yi hira da Yah Jawad yanzu". Bata jira amsarsa ba ta katse kiran.
Tana katse kiran ta ɗago da kallonta a kansa, while shima kallonta yake yi, suna haɗa idanu suka sakarwa da juma murmushi. Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tana cigaba da murmushi.
"Me kuke tattaunawa ne da Yah Rizwan ɗin namu?". Ya jefa mata tambayar yana ɗago haɓarta, dan ta sunkuyar da kai ƙasa. Haƙiƙa ya ji matuƙar daɗin yadda ta bashi mahimmanci, ta bar abin da take yi ta ce wannan lokaci nata nashi ne yanzu bana yin magana da kowa ba ne, ya ji matuƙar daɗin hakan, bawan Allah bai san soyayya take yi da yayan nasu ba!. Hmmm akwai gagarumin matsala ranar da ɗaya ya fahimci ɗaya yana sonta, sai Allah ne kaɗai yasan irin bala'in tashin hankalin da bayin Allahn nan zasu shiga, waye zai hakura ya barwa ɗan uwansa? Ko dai dukkansu biyu hakura zasu yi ne? Anya ma a cikinsu akwai wanda zai iya hakura kuwa? Dan fa dukkansu suna yi mata zazzafar so ne fiye da tunaninku!! Gaskiya Mammaiensu nan bakar azzaluma ce, zata azabtar da su cikin ruwan sanyi ta hanyar sanya masu ciwon zuciya, bayin Allah marayun Allah masu kaunar junansu zata shiga tsakaninsu ta rabasu, wato idan Allah ya haɗaka da mai bakar zuciya fa kai kam ka shiga uku wlh, Allah dai ya kyauta ya shiga tsakanin nagari da mugu!.
"Hira kawai muke yi da shi, ya ce mun zai zo a satin nan saboda Akka sannan kuma saboda au........." Wani irin kunya ne ya rufeta ta kasa iya ƙarisa gaya mashi sannan kuma saboda aurensu, kasa karisa maganar ta yi, ta yi shiru.
"Awww sai a zauna ayi ta hira da su Yah Rizwan ni ba za'a zo É—akina a tayani yin hiran ba ko?". Cikin zolaya ya yi maganar.
A ɗan shagwaɓe ta ce. "Kai Yah Jawad kai fa Momma ta hanani zuwa room ɗinka, ta ce kada na sake shiga ciki, ko naje kai maka wani abin na tsaya a iya parlour kawai".
Ɗan leƙo face ɗinta ya yi. "Eyeee momma zata shiga tsakaninmu kenan? Ni ba zan yarda ba gaskiya, ni dai ki rinƙa zuwa ko a parlourn ne ma mu zauna ki yi mun hira dan ki rage mun kewa". Ɗan zaro idanu ta yi tare da cewa. "Yah Jawad kai kuma wani irin kewa zaka ji? Kana ganin yadda face ɗinka take wani shining daga gani kullum hira kake yi a waya da Auntynmu da zaka auro......" Ta kai karshen maganar tare da sanya hannu ta toshe bakin nata tana ɗan murmushin.
Damko west É—inta ya yi yana faÉ—in. "Waye ya gaya maki ina da budurwa da nake yin hira da ita?". Wage baki ta yi da karfi ta furta. "Akka ga Yah Jawad nan zai......"
Ai bai bari ta ƙarisar ba ya toshe mata bakin nata da hannun ɗaya, sanin cewa in dai Akka tana cikin room ɗinta to ba abin da zai hanata fitowa ne yasa ya yi saurin zame hannunsa daga bakin nata ya fara ƙoƙarin cicciɓarta sama su bar wajen.
Tsabar tsiya irin nata sake cewa. "Akka ki zo ki ceceni a hannun Yah........." Ai dan dole ƙaniyarta ta dakata bata ƙarisa maganar ba saboda abin da ya yi mata a wannan karon, ya ɗauketa cak da hannayensa, ga shi tana son ƙira mashi ruwa hakan yasa ya rufe mata baki da ɗan bakinsa tun da ba hannu.
Dama ta ce tun da ta gane baya son Akka ta gansu a tare ta ce zata fara rama abin da ya yi mata, to ga shi ta fara ramawa kuma ta samu kyautar sumbata, karon farko kenan a rayuwarta, dan ma Allah ya taimaketa mutumin kirki ne ai da kiss ma mai gabaÉ—aya zai yi mata ba iya sumbata ba, to na dai yi shiru.
Nutsuwa tsit ta yi tare da datse idanunta gam, kai tsaye room ɗinta dake kusa da na Akka ya shiga da ita, a tsakiyar ɗakin ya sauketa yana kawar da kallonsa daga kanta izuwa kofar shigowa, dan ya ji motsi a waje wanda yake kyautata zaton Akkar ce, dan yasan dama in dai tana nan wannan ihun sunanta da Chuchun ta yi zata jiyota shi, idan ta ji kuma tabbas zata fito waje, haka kuwa aka yi, ita ɗince ta fito duba waye ya kirata...... Yah Jawad yana wasa sosai, Momma ta ce ya ɓoye soyayyarsa kada ya bari kowa ya sani, amma yana wasa da hakan sosai, har ɗaukar Chuchun yake yi a tsakar rana ido na ganin ido, sam baya gudun ya haɗu da wani a cikin family.
A hanzarce ita kuma Chuchun ta raɓa gefensa zata wuce ta gudu ta bar ɗakin. Riko hannunta ya yi tare da dawo da kallonsa a kanta. A hanzarce ta yi ƙasa da kanta, dan wani irin kunyarsa ta ji, sunbatar tasa ta tsaya mata a rai, ga shi unexpect ya yi mata shi, a lokacin idanunta suna a kan face ɗinsa, sun ga juna ido cikin ido a yayin da ya sauke ɗan bakinsa a saman nata, duk abin ya tsaya mata a rai, yanzu ba zata iya haɗa ido da shi ba.
"Ina zaki je kuma Jannat?". Yana magana yana kallon face ɗinta, shi ko kunyar abin da ya aikata ma bai ji ba. Ƙasa ƙasa kamar wadda bata son yin magana ta ce. "Wajen Mommana".
ÆŠan É—ago habarta ya yi dan su kalli juna, sai dai taki yarda ta É—ago idanunta su ga junan. "FaÉ—a mun waye ya gaya maki ina da budurwa kafin ki tafi?". A hankali ya yi maganar kamar wani mai faÉ—awa wani gulmar wani.