← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 204 OF 211

Sashe 204

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana barin part ɗin kai tsaye part ɗinsu ta nufa, wato side ɗin uncle Abbas kenan, amma kafin ta bar part ɗin momma sai da ta tsaya ta ɗaga rigarta sama ta cuta envelope ɗin dikka a cikinta, ta ɓoyesu, da yake tana da dogon wando a ciki, sai ta cusasu ta wajen waist ɗinta ta kuma sanya waist beads ɗinta a kansu dan kada a gani. Ita da murmushi bai dameta ba, bata yi sai na mugunta sai ga shi yau sai sakin uban murmushi take yi kamar baki ba zai rufu ba, da sauri ta shige cikin side ɗinsu har tana haki.

________________🌹💘_____________

Sai lokacin da aka É—aura auren Chuchu ne Auta ta fahimci wayarta baya a tare da ita, dan haka sai ta fara nemansa, dan zasu yi hotuna, kowa ta fito da wayarta, ga su Jannat Æ´aÆ´an uncle Rahab dik sun zo, kowa sai É—aukar hotuna da Æ´an uwa yake yi da wayarsa banda ita.

Room É—inta ta nufa domin ta nemi wayar tata, yau gabaÉ—aya haka take wata sukuku da ita, dan daren jiya jaruminta wato Hoorain ya bakanta mata, da abin ta kwana a ranta, shiyasa ko kwalliya ta gaza yi wa kanta sai da Aunty Ummi babban Æ´ar uncle Rahab ta yi mata, ba dan haka ba da yau ba zata yi kwalliya ba.

GabaÉ—aya Æ´an'matan sun shirya cikin wasu irin haÉ—adÉ—un Turkish gown mai kama da wedding gown, kasa a buÉ—e sosai daga ta sama kuma ya É—an kamasu zuwa waist É—insu.

Sun yi kyau over, ga shi sun sha lalle, ba ƙaramin kyau suka yi ba, sai kamshi ne yake tashi ta ko'ina. Aunty MieMie ce ta kira masu masu gyaran gashin familyn nasu suka zo suka gyara masu wanan kyakkyawan Arabs hairn nasu.

Binciken É—akin nata ta fara yi tana neman wayar, sam ta manta jiya ta fita da shi. Da sauri ta aro wayar gimbiya Fanan ta fara gwada number tata. Wayar tana ta ringing ba'a É—aga ba.
Tana hannunsa kuma, yana kwance a saman bed ɗinsa yana ta ƙoƙarin gwada buɗe wasu folders ɗin da ta sanyawa password dan ya ga me ta ɓoye a ciki, akwai wajen hotuna ta rufe shi shi ma, sannan ta rufe Whatsapp ɗinta, ta kuma rufe wajen videos na wayar, to me take ɓoyewa?. Shi ne abin da ya dame shi yake son buɗewa.

Ita kuwa idan hankalinta ya kai dubu to ya tashi na rashin ganin wayar nan tata, ta ruÉ—e kamar wata maras gaskiya ko wadda take da wani abin da bata son a gani cikin wayar, da sauri ta hau wargaza bed É—inta, dik pillows É—in ta yi watsi da su kasa.

Sai da ta gama watsa É—akin caf sai ta tuna ashe jiya bama a É—akin ta kwana ba, sai a lokacin tunanin ta fita da wayar zuwa wajen Hoorain ai ya faÉ—o mata, kuma kamar bata dawo da shi ba.

Tuna hakan yasa a hanzarce ta shigar da number Hoorain da ta haddace shi a kanta a cikin wayar Fanan, da sauri ta fara kira.

Lokacin da call É—in ta shigo ya É—aga yaga sabuwar number ce sai ya mayar ya ajiye bai yi picking ba. Ganin bai É—aga bane yasa ta hau rubuta sako dan ta tura mashi.

Salam Zunaira ce ka É—aga please, shi ne abin da ta rubuta ta numbersa ta tura mashi.

Yana ganin sakon sai da ya miƙe zaune a tsakiyar gadon, wani irin daɗi ya ji a ransa ya samu hanyar da zai bata hakuri, da alama shi ma da tunaninta ya kwana, ya gaza samun sukuni.

Yana ƙoƙarin fita daga sms ɗin sai ga kiran nata ya sake shigowa. Cikin nutsuwa ya yi picking tare da kara wayar a kunnensa.

"Assalamu alaikum". Ya faÉ—a a sanyayye.

Ta saba idan sun haɗu ta ɗaga mashi gaisuwa, yau kam sai ya ji bata ɗaga mashi gaisuwar ba, da alama dai da gaske fushi take yi da shi, sai ya ji abin ya kara taɓa zuciyarsa.

"Hoorain dan Allah wayata tana hannunka ne? Ka ganta?". Shi ne abin da ta ce mashi kawai.

Bawan Allah bai iya bada hakuri ba, sai ya rasa ta ina zai fara, hakan yasa ya yi shiru yana tunanin meyakamata ya faÉ—a.

"Hoorain baka ji nane?". Ta sake faÉ—a tana É—an É—aure fuska.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yi kasa da murya sosai, a hankali ya ce. "Am so so sorryyyyyyy ranki ya daÉ—e, ina tuba kuma ina fatan zaki mun afuwa".

"Tuba a kan me kuma Hoorain?". Ta jefa mashi tambaya.

Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "Idan ba zaki damu ba zamu iya haÉ—uwa yanzu?".

To fa yau da kansa yake neman su haÉ—u?.

"Meyafaru kake neman mu haÉ—u? Ko dai yanzu kam ka san wacece Zunaira É—in ne?".

ÆŠan dafe forehead É—insa ya yi, wato dai bata manta ba, lallai yanzu ya tabbatar da maganar ta yi mata zafi ashe.

"Kiyi hakuri ranki ya daÉ—e kuskure aka samu, amma tuba nike".

Allah sarki soyayya, zuciya bata da ƙashi, ai bata san lokacin da murmushi ya kubce mata ba, amma da yake ta yi degree a sanin ilimin soyayya sai ta danne ta ce. "Ni kam ka dai'na bani hakuri dan baka yi mun laifin komai ba, wayata tana hannunka ne in turo a karɓa mun?".

"E wayar tana hannuna, amma dan Allah kada ki turo kowa, ki zo da kanki kin ji? Magana nike son yi dake please, ba dan ni ba, saboda nasan ni ban kai na kiraki ki zo ba"..

Sosai ta ji daÉ—in da yau shi ya nemi da su haÉ—u, bayan tsawon lokaci da ita take zuwa dan ta gansa, abin ya yi mata daÉ—i, sam bata duba matsayinta da girmanta ba, ita dai tun da zuciyarta na son shi ai shikenan kuma.

"Ni gaskiya Hoorain ba zan iya zuwa ko'ina a yanzu ba, bani da lokaci, zan turo a karɓa mun wayar kawai ka gaya mun in da kake".

Wai ita ma zata ja ajin nan, har da wani dake murya irin ya san da gaske take yi.

Bai ji daɗin hakan ba, ya so su haɗu da ita ne, amma ba yadda zai yi, sai ya ce. "Tom shikenan ranki ya daɗe, ina ɗaki amma zan fito wajen garden ɗin da muke zama ta zo wajen ta karɓa maki wayar".

"Tom gata nan zuwa". Ta kai karshen maganar tare da ciro wayar daga kunnenta tana ƙoƙarin katse call ɗin tana sakin murmushi dan ta ji daɗi, dama tun safe take kewarsa sosai, yanzu ta ji voice ɗinsa zuciya ta sanyaya. Sai dai kuma burgagin banza ne take yi na nuna cewa tana son katse kiran, amma har ga Allah ba call ɗin take son katsewa ba, bataki su yi ta wayar daga nan har gobe da safe ba, amma nauyin jansa da hira take ji yasa ta yi kamar zata katse.

"Dan Allah kada ki katse kiran ranki ya daÉ—e". Shi ne abin da ta ji ya sake faÉ—a. Ai bata san lokacin da ta saki wani irin cool murmushi haÉ—e da sanyayyar ajiyar zuciya ba, abin da take so me dama.

Wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta, fasa katsewan ta yi tare da mayar da ita kunnenta.

"To me kake so kuma? Ko da sauran wani magana ne?". Ta jefa mashi tambayar tana murmushi, irin kada ya gane ta damu É—in nan ne yasa ta yi mashi wannan tambaya.

Girgiza kai ya yi kamar yana a gabanta, bai san lokacin da ya ce. "Kawai ban gaji da jin voice ɗinki bane, yau nayi kewarki sosai, na kuma shiga damuwa a kan hakan sosai, meyasa zaki yi fushi dani? Kin san cewa ba zan iya juran fushinki ba? Kin san cewa jiya kwana na yi ban rintsa ba? Dan Allah ki yi hakuri, yanayi ce tasa nike cewa ban sanki ba bawai da gaske bane, bana son su gayawa Abbona wani maganar ne yasa nike faɗan dik abin da na faɗa, amma in har baki son hakan ba zan ƙara ba".

Tun da ya fara magana ta samu wajen bakin bed É—inta da ta gama watsawa ta zauna tana sakin murmushi.

Yana kai karshen maganar ta sauke wani irin daddaÉ—ar ajiyar zuciya wanda har cikin ransa ya ji hakan, shi kansa bai san lokacin da ya sauke nasa ajiyar zuciyar ba.

"Okey na yarda da dik abin da ka faÉ—a, kuma zan hakura, amma yanzu ka gaya mun ka san wacece Zunaira?".

A hanzarce ya ce mata. "Sosai ma na santa".

"Wacece ita to?". Ta sake jefa mashi tambaya.

Shiru ya yi yana tunanin wacece zai ce to? muryarta ce ta katse shi da cewa. "Zan hakura amma har sai ka gaya mun wacece Zunaira a zuciyarka? Sannan ya ka É—auketa?".

Ɗan shafa kansa ya yi yana mamakin wayo irin nata, wato so take ta ji sirrin zuciyarsa kenan, wai ita ma ta yi girman da zata yi mashi wayo, ita da ko soyayyar da take yi mashi ta kasa iya ɓoyewa kada a gane ne take son yi mashi wayo, shi da tsawon shekaru goma kenan yanzu sonta yana ɗawainiya da shi amma ba wanda ya iya gane hakan har sai yanzu da ta fara girma ta kai 13 years, kyanta yana ta kara bayyana abin ya matsawa zuciyarsa ne yasa su Ansar suka iya ɗagosa, amma a haka wai zata yi mashi wayo.

Amma jin yadda ta yi mashi tambayar dik da baya ganinta ya iya gane cewa tana cikin farinciki sosai, dan haka ba zai iya karyar mata da zuciya ya gaya mata akasin abin dake cikin zuciyarsa ba, amma kuma yana tunanin me amsar shi zata haifar? Baya son tashin hankalin Abbonsa.

"Sai ka yi tunanin wacece Zunaira a gareka kafin ka gaya mun ko? Tsabar Zunaira bata da amfani a wajenka ko?".

Siririn muryarta ce ta katse mashi tunanin da yake yi da faÉ—in hakan. Ta faÉ—a kamar zata yi mashi kuka.
Chapter 204 · 0% Book details