← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 211

Sashe 22

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawo da kallonsa kan face É—inta ya yi tare da faÉ—in. "Dama baki da lafita ne yasa 3 days baki zuwa school?".

Ɓoye fuska ta yi a kirjinsa dan kada Aunty MieMie ta ganta, ƙasa ƙasa ta ce lafiyarta lou, zuwa ne bata son yi yasa ta ce masu bata da lafiya.

"Kus kus É—in me kuke yi?". Cewar Aunty MieMie.

"Kash Aunty MieMie wai ba zaki barmu mu É—an zanta ba, ina ruwanki tsakanin yaya da kanwa, ni ki tafi zata zo". Ya faÉ—a yana juyo da kallonsa a kanta. "Babu in da zanje, zo ka wuce ka tafi ko na kira Akka, ke kuma zo nan ki je ki yi breakfast". Tana magana tana wurga mashi harara, saboda su abokan wasa ne sosai.

Raba jikinsu ya yi, ya riƙo hannunta tare da sauko da ita daga saman gadon. "Zo mu tafi kada ta kira mana wannan masifaffiyar tsohuwar ta jiƙa mun aiki. Ya yi maganar tare da nufar kofar fita hannunsu cikin na juna.

"Tun da ba zaki barni na yi hira da farincikina ba ai sai mu tafi tare ko?". Ya faɗa bayan ya zo raɓawa ta gefenta zai wuce.

Harara ta bishi da shi tana faÉ—in. "Oho dai kaje dai, ko na kira wayar Akka".

"Ni Aunty MieMie ki daina kiran sunan tsohuwar nan, kina sanya na ji kai na na sara mun". Ya karesa zancen nasa a waje, saboda yana tafiya ne bai dakata ba.

Juyawa ta yi ta bi bayansa tana zolayarsa a kan Akka ce maganinsa, kuma sai ta sanar da ita yana tare mata jika a lungu ya kalailameta da kalamai.

Duk zancen da suke yi suna ta raha tare da tsokanar juna sam Chuchu bata a tare da su, ta afka duniyar tunanin ya aka yi aka samu mai kama da Yah Jawad a gidan nan? Wannan abin ya tsaya mata a rai matuƙa. Sam bata san lokacin da suka isa saman dining table ɗin ba, ta luluƙa duniyar tunani, sai da ta ji spoon na abinci yana taɓa lips ɗinta ne ta farga ashe sun iso wajen cin abincin har ma ya zuba masu ya fara bata a baki.

Ɗago idanu ta yi sai saman fuskarsa, wani irin faɗuwar gaba ta ji ya ziyarce, lokaci guda ta fara jin sauyin yanayi a cikin zuciyarta a kansa, taga ya kara yi mata kyau sosai. Buɗe baki ta yi ta fara karɓar abincin, ita kam Aunty MieMie ta kama kanta abinta ta basu wuri.

A can cikin babban family part kuwa, sai shiryawa Auta take yi tana tsantsara kwalliya mai kyau cikin Turkey gown brown color mai matuƙar kyau, ya ji duwatsu sosai a jikinsa, sai kyalli yake yi, kun san yanda kayansu yake ai, daga ta sama ya yi dai'dai da jikinsu, ya bi shape ɗinsu, daga wajen kugunsu zuwa ƙasa kuma a buɗe a bage kamar umbrella. Kayan yana da kyau sosai, yana ƙara fito masu da ainahin kyansu.

Tamkar wadda zata je wani wajen mai muhimmanci, sosai ta tsara kwalliya, ta ɗaure gashin kanta kashi biyu, ta kuma kitsa bakin gashin tare da ɗaure karshen jellar gashin da roba saboda tsantsin gashin zai sanya kitson nata ya warware, ta saki jelar a saman shoulder ɗinta sun zubo mata har saman ciki. Ba karya kam ta haɗu iya haɗuwa, ta ɗauko wani malesian cap mai tsadar gaske ta sanya a kan nata, sai ta ƙara kyau sosai. Flat smooth shoe ta sanya a kafafunta, wanda ko tana taka ƙasa ba zaka ji tafiyarta ba.

A hankali ta fito waje, kai tsaye ta hau elevator ta yi kasa mai gabaɗaya, sai sauri take zubawa tana yi tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Kai tsaye wannan wajen hutawa na musamman ɗin na mussan dake cikin family part ɗin ta nufa, wajen wasu kyawawan tsuntsaye dake cikin keji ta nufa a hanzarce. Tsuntsaye masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali ne suke birjik a wajen, a kallah kejunansu sun kai guda 20 a wajen, tsuntsaye ne different types and colos.

Kai tsaye wajen wasu fararen tattabaru ta nufa, guda biyu ta damko bayan ta buɗe kejin, ta riƙosu da kyau a hannunta, suna ta faman ƙoƙarin kwacewa su tashi sama, amma ta riƙe su gam dan kada su gudun.

Da sauri ta nufi waje, har da ɗage doguwar rigarta dake sharar ƙasa saboda sauri. Wani hanya da ya raɓa da wajen da ake gabatar da gasar tsaren doki duk sati ta nufa, a hanzarce take tafiya kamar zata kifa, tana yi tana waigawa bayanta dan taga shin akwai wanda ya ganta ne? Sai laɓewa take yi a duk lokacin da taga wani warriors ya zo zai gifta, da alama bata ƙullo gaskiya ba.

Wasu jiga jigan warriors ne suke gadin gate É—in in da ta dosa É—in.

Mayaƙa biyu ne a wajen, sun ji horarwar yaki sosai, commander Zafar ya yi aiki a jikkunansu wajen basu horo mai lafiya, sun ginu tamkar wasu dakuna, ga faɗin kirji da baya kamar na zaki, ganinsu da ido kawai sai sun tsorata ka, suna tsaitsaye cikin kayan yaƙinsu, ɗaya daga cikinsu yana sanye da hular yakinsu a kansa, ɗayan kuma ya cire shi, sai hira suke yi da junansu, dukkaninsu larabawa ne tas tas da su, ga kyau sosai da bakar gashi haɗi da saje.

Suna ganinta tun bata iso wajen ba suka tinkarota da sauri. Ƙara ɗaga kafa ta yi wajen yin sauri, dan bata son su tareta a hanya, ta fi son ta isa in da suke. A kusa da bakin gate ɗin suka haɗu. Cikin girmamawa ɗaya daga cikinsu ya ce. "Barkanki ranki ya daɗe, shin kina da buƙatar wani abin ne?".

Shiru ta É—anyi tana tunanin abin da zata ce masu, dan wlh yau ko zasu yi yaya sai ta je gonar É—awisun daddynsu, so take yi ta je ta gani kuma ta É—auki hutona da su, sai dai kash saurinta yasa ta manta ma bata É—auko wayar da zata É—auki hoton da shi ba, kuma har izuwa yanzu bata tuna cewa babu waya a hannunta ba.

King Zuhair ya hanasu kusantar gonar ba tare da shi bane saboda sanin halinsu, basu taɓa shiga cikin gonar ba, ita kuma Auta ta ɗaukarwa kanta alkawarin sai ta shiga taga me a ciki, akwai mugayen namun dawa sosai a ciki, akwai kuma dabbobi masu ban sha'awa sosai a ciki, irin su ɗawisu akwai su dayawa kala daban daban, su kuma ba'a cikin keji suke ba, an sakesu suna yawo a wajen, akwai su jimmina, su kifaye kala kala na gida dana waje waɗan da suke cikin wani haɗaɗɗen glass mai matuƙar ɗaukar hankali, an zuba masu ruwa sai shawagi suke yi abinsu, akwai tsuntsaye kala kala, ga su dila, Zomo, bushiya, a manyan dabbobi da aka killacesu a cikin keji akwai su zakuna, damisai, kuraye, da dai sauransu, duk wasu dawakai da King yake hawa suna cikin wajen an kewaye masu nasu ɓangaren daban ana kula da su sosai, akwai dai tarin abubuwa dayawa a ciki, wasu suna cikin keji, wasu kuma an sakesu suna ta shawagi a cikin katafaren filin tsakiyar wajen.

To ita bata san saboda haÉ—arin da yake a ciki bane yasa King ya hana su ko tinkarar wajen, ta É—auka baya son ta yi hoto da su É—awisan ne kawai, shiyasa ta saci hanya ta zo ba tare da sanin kowa ba.

Ganin ta yi masu shiru ne yasa suka sake tambayarta cikin girmamawa a kan ko dai tana buƙatar wani abin ne?.

Ɗago idanun ta yi ta zuba masu kallo, cikin dabara ta saki tattabara ɗaya ya tashi sama, kukan gulma ta sanya masu a kan lallai su kamo mata tattabararta kafin nan su zo ta gaya masu abin da take buƙata a wajensu. Mutun ɗaya ne ya yi saurin bin bayan tattarabar da ta tashi sama ta bi ta wajen tseren dawakai da suke gudanarwa a cikin masarautar duk sati.

ÆŠayan warriors É—in kuma sai ya hau bata hakuri yana faÉ—in za'a kamo mata shi ta yi shiru. Sake fakar idanunsa ta yi ta saki É—ayar tattabarar ma, kara fashewa da kuka ta yi mai sauti tana faÉ—in É—ayar ma ta sake guduwa lallai lallai ya kamo mata abinta. Sanin ita wacece da kuma girman kaunar da ake mata a gabaÉ—aya faÉ—in kingdom É—in yasa ya bi tattarabar da gudu yana mai gaya mata zai kamo mata amma dan Allah ta yi shiru.

Ai kuwa suna barin wajen ta yi saurin ƙarisawa wajen gate ɗin. Ƙoƙarin tura gate ɗin ta yi dan ta buɗe, amma ta ƙasa saboda karfi da nauyi irin ta kofar, kamar zata rushe da kuka ta sanya dukkanin karfinta tana turawa.

Ko gezau kofar bata yi ba, bakin ciki kamar ta haɗiyi zuciya, sai waigowa take yi tana kallon bayanta dan taga ko suna dawowa. Ta yi iya yinta kofar ko motsawa bata yi ba, tamkar dasata aka yi, fara bin jikin kofar da kallo ta yi, can ta hango wajen key ɗin datse kofar, ashe a rufe take, sai dai tsawonta ba zai kai ta iya taɓa wajen key ɗin ba, dan kofar tana da tsawo kuma key ɗin a sama yake. Ciccikowa da kwallah idanunta ya yi dan haushi, kamar ta ɗaura hannu a kai ta zunduma ihu.

Juyawa ta yi cikin sanyin jiki, har zata nufi hanyar komawa kuma sai wani dabara ya faɗo mata, da sauri ta juyo tare da janyo kujerun da warriors ɗin suke zama a wajen ta kawo shi wajen saitin key ɗin, takawa ta yi ta haye dan ta ƙara tsawo. Ta kuma yi sa'a tsawonta ya kai wajen makullin, da sauri ya kama key ɗin dake manne a wajen ta hau murɗa shi, tana yi tana waigo bayanta.

Tana buɗe key ɗin ta hau tura kofar, Da kyar ta iya buɗesa, a hanzarce ta afka ciki, tana shiga ta datse kofar da wasu keys da suke ta ciki, a kallah key zasu kai uku a jikin kofar ta ciki, sai ta sanya ɗaya wai dan kada idan warriors ɗin suka dawo su zo su fitar da ita, yau ta ci alwashin sai ta kewaye cikin wajen gabaɗaya duk girmansa, waje ne fa mai matuƙar girma sosai, amma wai sai ta kewaye dukka.
Chapter 22 · 0% Book details