← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 197 OF 211

Sashe 197

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yake takunsa ɗaya ta ninka nata uku sai ya yi saurin cin mata, ya hangota tana ƙoƙarin komawa cikin gida. Ƙara zafafa tafiyar tasa ya yi dan ya cin mata ya samu ya bata hakuri, sai dai bai kai ga hakan ba ya hango guyson yana nufota. Dakatawa da bin nata ya yi yana danasanin kalaman da ya furta na cewa bai san wata Zunaira ba.

Jiki a mace ya juya da sauri ya bar wajen dan ma kada guyson ya kalle shi. Bai zame ko'ina ba sai cikin É—akinsa. Yana shiga ya turo kofa ya rufe har da sa key dan ma kada su Ansar su biyosa, yasan sarai sai sun zo bashi hakuri dan a tunaninsu fushi ya yi ya tafi, basu san bayan masoyiya rabin rai ya bi ba.

Kifa kansa da jikin kofar É—akin ya yi yana jin kamar ya koma ya yi mata magana koda a gaban guyson É—in ne, zuciyarsa ta É—acaca ainun. Burinsa kawai a yanzu ya sanyaya mata rai koda kuwa bayyana mata soyayyarsa ce zai sa hakan to zai yi, zai bayyana mata.

Call ne ya shigo cikin wayarta dake hannunsa hakan yasa ya É—aga kansa daga jikin kofar. Kawo wayar saitin face É—insa ya yi dan yaga wanene mai kira.

Uncle Taheer shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Wani irin ɗaure fuska sosai ya yi tamkar akwai mai ganinsa, nan take kishin maza ya motsa, har zai buga wayar da ƙasa saboda kishi sai kuma ya danne ya fasa dan kada ya kara laifi a kan laifi, yanzu ma flower tasa fushi ta yi.

Call É—in ta yanke wata ta sake shigowa, dogon tsaki ya ja tare da wucewa ya nufi saman bed É—insa dake shinfiÉ—e tsab gwanin birgewa.

Kwanciya ya yi a lokacin call ɗin ya yanke, sai ya fara ƙoƙarin yi mata bincike a waya kamar ta aikesa, wayar babu password ba komai, hakan ya bashi damar shiga ciki.

Sai dai wasu sassa daga cikin wayar ta sanya masu password, da alama akwai abin da take ɓoyewa.

_____________🌹💘_____________

A nata ɓangaren kuma ta sha madarar mamakin ganin Guyson ya biyo bayanta, daga shi sai short na Jessy and singlet a jikinsa, kamar dai wanda ya kwanta ya fara barci ma, yadda yake tafiya zaka fahimci jikinsa a mace.

Nan take ta fara Æ´an kame kame tana tunanin me zata ce mashi, sai dai bata wani É—aga hankalinta sosai ba, dan tasan Guyson mutun ne mai saukin kan da a tunaninta ko da ya san gaskiyar abin da ya fito da ita ma ba zai É—aga hankalinsa ko ya yi mata faÉ—a ba.

"Zunaira me ya fito dake waje a cikin dare nan?". Ya jefa mata tambayar yana É—aure fuska.

Zaro idanun waje ta yi, da mamaki ta ce. "Yah Omar yau kuma kai ne kake kirana Zunaira?".

"Meya fito dake waje a daren nan nace?". On a serious note ya yi maganar, babu wasa a tattare da shi.

"Babu komai". Ta faɗa a tsorace, dan bata taɓa ganin ɓacin ransa haka ba, shi kullum cikin murmushi yake.

Tsawa ya daka mata cikin ɗaga murya ya ce. "Meya kawoki ɓangaren warriors?! Mama kika fita yi?!"

Yadda ya yi maganar ya ɗaga hankalinta sosai, har ta ji zuciyarta ya karaya da son Hoorain, wannan ma guyson mai bala'in saukin kai ne ya ganta a hanyar part na warriors ma kawai ku dubi yadda yake yi mata tsawa abin da bai taɓa yi ba, to ina ga kuma yasan abin da ya fito da ita? Kuna tunanin ba zai ɗauketa da mari ba kafin ya san hukuncin da zai yi mata?. Guyson ma ya yi haka ina kuma ga su Ramish, Jaish da su Bilal? Me kuke tunanin zai faru in suka sani?.

Ganin ta yi shiru bata amsa mashi bane yasa ransa ya ƙara ɓaci da har ya ɗaga hannu zai dalla mata mari. Kuka ta saka mashi tare da zurawa a guje ta nufi cikin gida, da sauri ya juya ya bi bayanta.

Tana shiga part na Akka ta gudu ta ɓuya, shi kuma ya wuce part na Momma, dama daga nan ɗin ya fito, yaga lokacin da ta shigo part ɗin ta ɗauki hijabi a room ɗinta, a lokacin yana tsaye a parlourn reast area yana waya da su Omaid, shiyasa har ta fita bai dakatar da ita ba, da ya gama wayar kuma ya manta da batun sai ya koma cikin bedroom ya kwanta a saman bed ɗin Momma, har ya fara barci sai ya tuna da yaga ta fita ta kofar baya, hakan yasa ya bi bayanta.

Nemanta ya fara yi a dikka É—aku nan dake cikin part É—in Momma, shiru bai ganta ba, part na mummyn Chuchu ya nufa, nan ma tsab ya bincike ko'ina bata ciki. Wayarsa ya dawo ya É—auka a cikin room na Momma ya fara kiran numberta.

3 miss calls ya yi mata Hoorain bai yi picking ba, hakan yasa ya fita ya nifi part É—in Akka dan ya duba wajen, in bata nan sai ya dubata wajen King.

Kwance ya iskota saman bed É—in Akka ta shige cikin bargo ta yi barcin karya. Ajiyar zuciya ya sauke alamar ya ji sanyi a ransa na ganinta da ya yi, da a tunaninsa bata dawo ciki bane. Kamar zai tasheta dan ta gaya mashi abin da ya fito da ita, sai kuma ya fasa a zuwan da safe zai tambayeta ta faÉ—a mashi.

Sumbatarta ya yi a goshi kafin ya juya ya bar É—akin. Yana fita ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya tare da gyara kwanciyarta, sai tunanin maganganun jarumin nata ya dawo mata cikin kwakwalwata, Allah sarki bata san lokacin da hawaye suka fara gangaro mata ba, sai take ganin kamar ita kaÉ—ai ce take dakon sonsa.

Hawaye sharɓa sharɓa a face ɗinta barci ya yi awon gaba da ita. ASUBA TA GARI.

Washe gari da safe wasu zaƙwaƙuran masu iya lalle sosai daga kasar Sudan suka yi diran mikiya a kingdom of power domin yiwa amarya da ƴan uwanta lalle. Su ƙawatasu da kyau.

Abin mamaki shi ne a É—akik Jawad Chuchu ta kwana kwance a saman jikinsa amma babu wanda ya sani, Rizwan dake jinyarsa tun da ya fita a daren jiya bai jara dawowa ba, dan ya shiga cikin É—akinsa da nufin ya yi wanka ya canza kaya, sai ya ji gajiya ta ka mashi ya ce bari ya kwanta ya huta, daga kwanciya wani irin barci mai azabbabben nauyi ya yi awon gaba da shi, har yanzu kuma wajen karfe 9 bai farka ba. Cakwakiya kenan baku tunanin da sa hannun mammie a wannan barcin kuwa?.

Sannan abin mamaki shi ne su Aneesa basu nemi Chuchun ba, suka kwanta suka yi barcinsu, su Inno mariya kuma dama basu san ta fita ba, abin dai da mamaki gaskiya.

___________________🌹💘____________

Zaune Aunty MieMie take a saman egg chair dake cikin ɗakin King, yanayin chair ɗin design of egg aka yi su, sun yi matuƙar haɗuwa ga wani lallausan sofa a cikinsu mai daɗin zama.

King yana zaune a bakin bed É—insa yana shan coffee É—in da momma ta kawo mashi, ya dake a cikin alkyabbarsa ga haÉ—aÉ—É—en naÉ—in rawanin da ya sha, ya fito a balarabensa sak, madaran kyau iya kyau

Hankalinsa a kan Aunty MieMie da ta tsaresa da ido alamar damuwa a face É—inta, fada zai fita amma ta tsayar da shi wai tana son yi magana da shi, dole ya bata lokacinsa dan yana ji da ita.

Sai dai kuma ya zauna ta kasa yin magana, ta tsaresa da kallo kawai tana tunanin ta ina zata fara yin magana.

Gajiya da shirun nata ya yi ya ce. "Daughter wai lafiya? Maganar me kike son mu yi kika tsayar da ni?".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa, cikin girmamawa ta fara magana kamar haka.

"Daddy maganar Jawad da Jannat nake son mu yi da kai dama, amma ka gama shan coffee É—in sai ya fi".

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

50

"Daddy maganar Jawad da Jannat nake son mu yi da kai dama, amma ka gama shan coffee É—in sai ya fi".

Shiru ya ɗan yi yana kallonta, damuwa ce sosai a tarrare da ita, dan in baku manta ba da ita da Chuchu mamarsu ɗaya, so kunga ai ba zata so kaunarta ta auri wanda bata so ba, zata so farinciki har karshen rayuwar ƴar uwartata, sannan ita ta yi auren nan tasan ya yake, ba abu ne na rana ɗaya ko biyu ba, tamkar rai ne da shi shi ma, sai randa kwanakinsa ya kare yake katsewa. Rayuwa da wanda baka so akwai ciwo matuƙa.

"Daughter just tell me kawai is better, coz ba zan iya cigaba da shan coffee É—in ba bama until i know what's wrong with u i saw ur face like you're in a bad mood".

Nisawa ta yi tana jin wani irin É—aci a ranta, ita da take matsayin sistersu ma kenan ina ga su kuma masoyan? Ai sai Allah ne kawai zai iya sanin me suke ji a cikin ransu, dan baki kam ya yi kaÉ—an ya bayyana yadda suke ji.

"No my dad, take the coffee first sai na fi samun farincikin yin maganar da kai".

"Really?". Ya faÉ—a cikin zolaya yana É—aga mata gera. Dan dole yasa murmushi ya subce mata ba tare da ta shirya ba, dama kuma abin da yake son gani a face É—in nata kenan yasa ya ce really haÉ—e da É—aga mata gera.
Chapter 197 · 0% Book details