← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 211

Sashe 175

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsorace ta amsa mashi da e, ta tsorata sosai na ganin ya zaro mata idanu, dan ma yanzu idanun nasa suna washewa, sun rage ja sosai.

Ai bai san lokacin da ya rabata da jikinsa da nufin ya miƙe tsaye ya je ya samu Nennen ba, saboda ransa in ya kai miliyan to ya ɓaci, ai wannan rashin imani ne, wannan uban kayan har da zanin gado zata sakata wanki, shi a ganinsa ma kamar Mahnoor bai kamata ace ta iya koda shara bane a yanzu, a ganinsa yarinya ce sosai, rashin imanin ya yi yawa, to shi dai yanzu ba zai ɗauki hakan ba tun da ta zama mallakinsa.

A tsorace ta riƙo hannunsa, idanunta sun ciko da kwallah sosai, sai dai bata bari sun zuboba saboda alkawarin da ta yi mashi zata dai'na yin kuka.

A ruɗe ta ce. "Hamma ina zaka je? Dan Allah kada ka je ka gayawa bappana, wlh Nenne zata kasheni da duka, ta ce idan na gayawa bappa tana sakani aiki in bappa ya yi tafiya sai ta kwantar dani tasa wuƙa ta yanka mun wuya". Tana magana tana ƙoƙarin yadda zata yi ta hana hawayen idanunta zuba, bata son ta saɓa maganarsa.

Allah sarki ya fahimci tana matuwar tsoron Nenne, ga idanunta sun nuna razana da firgici a kan hakan, dik sai ya ji ya kara tausaya mata, ya kuma kara jin tsanar Nennen nan, dama ashe ba iya tashinta da sassafe kawai take yi ta yi ta mata aiki kamar jaka ba, ashe muguntarta ya wuce haka, har da yi mata duka da kuma yi mata barazanar yanka ta da wuƙa, kai Nenne yar duniya ce wlh.

Jikinta har kerma yake yi. Ganin hakan yasa ya zauna da kyau ya juyo suna fuskantar juna. Hannunsa dikka biyu yasa ya ɗan rufe mata idanu, nan take hawayen da suka cika mata idanun suka zubo, da tafukan hannunsa ya goge mata su, ta yi ƙasa da kai tana jiran ta ji me zai ce.

Jawota jikinsa ya yi na ganin jikin nata na kerma.
"Noor". Ya ambaci sunanta.

Bata iya amsawa ba saboda tana cikin halin razana.

"Menene ni a gareki?".

Tambayar tasa yasa ta É—ago kai ta kallesa. Jaddada mata tambayar tasa ya yi ta hanyar amfani da idanunsa.

Ba tare da ta kawar da kallonta daga kan nasa ba ta amsa da. "Kai Hammana ne kuma mijina".

"A yanzu da ni da bappa or Nenne waye yake da iko dake?". "Kai ne kafisu iko da ni". Ta bada amsa a dame, burinta kawai kada ya gayawa bappa Nenne na wahalar da ita, baiwar Allah tana tsoron a yankata da wuƙa.

Jinjina kansa ya yi kafin ya ce. "Daga yau ko tsinke kada ki sake kawarwa a cikin gidan nan idan ba kin tamnayeni ba, zan yi magana da bappa a kan hakan, dik wanda ya sanyaki aiki ki ce ya jirani sai na dawo idan ma bana nan, ki ce sai na dawo zan baki izinin yi in ya mun, idan ya sa hannu a jikinki zai dakeki ki bar masu gidan ki zo in da nake ki sameni, kada ki sake tsayawa wani ko wata yasa hannu a jikinki da sunan duka, ban yarda ba kuma ba zan yarda ba!". Cike da ɓacin rai sosai ya yi maganar.

Da to ta amsa mashi, ta lura sarai yana cikin ɓacin rai, ta ji daɗi sosai na yadda ya nuna matuƙar damuwarsa a kanta, har da nuna ɓacin ransa har haka a kanta, abin ya yi mata daɗi sosai.

"Hamma ka yi hakuri ka ji?". Ta faÉ—a kamar zata yi kuka.

"Laifin me kika yi mun da zaki bani hakuri sarkin bada hakuri? Ke baki gajiya da bada hakuri ne?".

"Hamma ai dik mai bada hakuri Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce ba zai taɓa taɓewa ba, ko ka yi laifi ko baka yi ba idan ance ka yi ka bada hakuri kawai a wuce wajen, manzon Allah ya albarkaci masu irin wannan ɗabi'ar, kuma yana yi masu kyakkyawar zato, to kaga nima dole na yi ƙoƙarin koyan bada hakuri ko dan na samu albarkan Manzon Allah".

Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ji zuciyarsa ta yi sanyi na kiran mashi sunan Manzon Allah da ta yi, a ransa ya ji cewa shi kam ya yi dace gaskiya, har wani irin kifiyar sonta ne ya caki farfajiyar zuciyarsa, jawota jikinsa ya yi tsabar farinciki, ya rungumeta da kyau yana sanya mata albarka.

Ita ma ta ji matuƙar daɗi sosai na ganin cewa maganganunta sun sanya zuciyarsa ta yi sanyi ta kuma sa ya fita daga cikin farinciki, lallai ya cika cikakken musulmi, domin kuwa dik musulmin da za'a ambaci manzon Allah bai ji zuciyarsa ta yi sanyi ta kuma shiga wani irin yanayi mai daɗi ba to gaskiya ya binciki imaninsa wlh, musulmin kwarai ko a wani hali yake aka ambaci fiyayyen halitta dole ya ji wani irin daɗi kamar wanda aka tsoma a cikin gidan aljanna, habawa ai manzon Allah ya yi ne, kai ni fa ko ni na kira sunansa da kai'na wani irin shaukin nishaɗi na musamman nake ji, sai na rasa ma ya zan kwatanta wannan farinciki nake shiga, wlh ina son Manzon Allah, Allah dai ya kara mana kaunarsa over to over. Tsab zamu sadaukar da ranmu a kansa, jininmu fansa ne a kansa wlh.

Ita ma rungumesa ta yi tana murna yau ta sanya ya fita daga cikin ɓacin rai cikin ƙanƙanin lokaci, sai take jin kamar ta yi kuka saboda daɗi.

Gyarawa ya yi ya kwanta tare da ita a jikinsa, ya jawo masu bargonsu ya lulluɓa masu, ya manta da ya ce tazo ta ci abinci.

Farinciki samun mace ta gari mai addini ga iya magana da sanyin hali yasa ya manta da batun cin abinci, dama can shi baya jin yunwa.

Shiru ta kwanta a jikinsa, hannu ya ɗaura a saman waist beat ɗin nan nata yana taɓasu kamar an aikesa. Ita barci ya fara ɗauka saboda rashin isasshen lafiya, shi kuma ya jima yana jinta a ransa, yana jin kamar ya kai hannu ya taɓa tula tulanta dake damunsa a saman kirjinsa, dik ya gama shafe mata beat, bai san ta yi barci ba, da tuni ya yi abin da ya yi niya wato taɓa mata tula tulanta.

A tunaninsa idonta biyu, sai da ya ambaci sunanta zai ce ta tashi su ci abinci ne sai ya jita shiru. Sai a lokacin ya ji sautin saukar numfashinta a hankali hankali irin na mai barci. Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, a hankali kamar mai juya kyau a saman tray ya É—an juya da ita.

A saman mattress ya kwantar da ita, sai yazamana suna fuskantar juna, kamar wani ɓarawo yake yin sanɗo a abu. Hannunsa ya kai ya kashe fitilar tasu, dan ko da ta yi barci kunyar taɓa mata tula tulanta ya ji. Wai ni kam anya Jaish bashi da alaƙa da jinin mu ƴan arewacin Nigeria kuwa? Ni dai nasan mune muke da kunya sosai haka.......🌝😅🤭

Kai Jaish yana goge mun hadda har da wani kashe fitillah É—an ikka.

Abin dariya abin tausayi, hannunsa sai kerma suke yi, shi kuma ya zage sai ya taɓa, zuciyarsa sai ingiza shi take yi. Kamar mai kakkarwar zazzaɓi haka hannunsa suke yi a lokacin da ya nufi tula tulanta da su, sai zuba barcinta take yi cikin kwanciyar hankali.

Wani irin azabbabben shock ya ji lokacin da ya sauke hannunsa a kansu, bai ma san lokacin da ya ɗan yunkura zai miƙe zaune ba, sai kuma ya kasa yin hakan, dan dole ya koma ya kwanta, bai kuma cire hannunsa daga kansu ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan datse idanunsa, a cikin duhunma bai yarda ba sai da ya kara da datse idanu saboda kunya.

Shafasu ya fara yi a hankali hankali kamar mai tsoron taɓasu. Wani irin duniya na daban ya afka, jinsa yake yi yana shawagi a sararin samaniya. Ya afka duniyar sama jannati.

A hankali ta waro idanunta waje, ta tsorata lokacin da ta ji an taɓa mata su, sai dai bata nuna tsoron nata ba, dan tasan shi ne, kunya ne sosai ya kamata, da farko bata yi niyar nuna alamar ta farka ba, amma sai ta kasa, dan shafasu da yake yi yasa tana jin shock har cikin ranta, ya hanata sukuni ne yasa ta waro idanunta waje, ta rasa ina zata sanya ranta, sai ta ji kamar yana yi mata cakulkuli ne.

Shi kuwa ya shagala da shafesu yana jin daÉ—i bai ma san ta farka ba, ni kuwa zan ga da safe da wani ido zasu ga juna har ma su ga bappa. Ana show a Jimeta Yola yaseen.

Kasa hakura ta yi, ta kasa dannewa har sai da ta yi motsin da ya fahimci ta farka, a hanzarce ya cire hannunsa ya kuma juya mata baya a dubu, abin gwanin ban dariya.

Ganin ta katse mashi jin daÉ—insa ne sai yasa dik ta ji babu daÉ—i, ta ji ta damu sosai, tunani ta fara yi meyakamata ta yi mashi a halin yanzu.

Bangaren zuciyarta ne ya amsa mata da. "Ki mayar mashi da jin daÉ—in nasa kawai, idan ba haka ba kuma zaki shiga tsinuwan Mala'iku".

Shiru ta yi tana saƙa maganar a ranta, sai taga babu wani hanya face hakan, amma tana jin kamar ba zata iya ba, tunawa da ta yi Jumma ta ce mata zata iya yin komai sai dai idan bata fara bane yasa ta yardanwa kanta zata iya, dama ta ce wa Jumam ba zata iya bane yasa ta gaya mata hakan.

A hankali ta ambaci sunansa Hamma. Ba tare da ya juyo gareta ba ya amsa mata da na'am. Shiru ta yi tana tunanin meyakamata ta yi? Da ta yi tunanin idan ta ambaci sunansa zai juyo gareta ne, sai taga bai juyo ba, ba haka ta so ba sam.

Shi kuwa dik kunya ce ta isheshi yasa yaki juyowa. Shahada ta yi ta matso ta kwantar da kanta a saman faffaÉ—ar bayansa, jikinta har yana É—an kerma saboda tsoron me zai je ya zo. Tamkar mai ciwon baki ta sake ambatar sunansa.
Chapter 175 · 0% Book details