Sashe 64
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsab bappa ya yi mashi duk abin da ya dace, sannan daga karshe ya ƙara mashi da maganin cin abinci na gargajiya, a lissafin bappan idan ya bashi maganin da zata sanya shi cin abinci zai ci abinci sosai dan ya samu kuzarin jikinsa.......... Ni kam na ce lallai ba shakka bappa ya gama da Jaish tabɗijam, yanzu yunwa da ba kanwar kowa bace zata nukurkushe mana Jaish na mu ta yadda dan dolensa ya nemi abinci ko dan ya rayu. Akwai matsala gaskiya, bappa dai bai kyauta ba da wannan magani na cin abincin gaskiya .......😥💔
Cin abincin ruga ya kama Jaish Innalillahi. Ko da yake Mahreen zata yi mashi gata wajen bashi a baki, idan ya ki ci ma zata iya yi mashi ɗure wannan yarinyar kam........ Duk kuma cikin gata ne!.😎
Barci mai nauyin gaske ne ta É—aukesa. Fitowa waje bappa ya yi, ruwa ya É—ebo ya zo ya yayyafawa Mahreen, abin mamaki a nutse ta farfaÉ—o, tana farfaÉ—owa kuma ta fara rambayar bappan nata ina aljaninta yake?. Da hannu bappan ya nuna mata shi, sannan ya ce. "Jeki ki kira mun hammanku Faisal kin ji?".
Turo baki ta yi, a shagwaɓe kamar zata yi kuka ta ce. "Amma bappa kasan dai bana son hamma Faisal ɗin nan ko?".
"Yi hakuri gajina jeki ki kira mun shi kin ji ko? Daga yau na yarda baki son shi".
Miƙewa ta yi tana turo baki ta nufi waje. Kai tsaye gidansu Faisal ɗin ta nufa. Tana shiga ta gaida Innarsu, sannan ta ce bappa na kiran hamma Faisal, bata jira amsar Innar ba ta wuce ta fice abinta.
Gida ta koma, a lokacin bappa yana hura wuta a kitchen, Nenne kam har yanzu bata dawo ba. Wuta ya hura ya ɗaurawa Jaish ruwan wanka, bayan ya ɗaura ya fito waje, Mahreen kuwa ɗakinsa ta shiga, a kusa da Jaish ta zauna ta tsare shi da idanu, ita dai a duniya aljanin nan nata yana matuƙar burgeta, ya yi mata kyau sosai, bata gajiya da kallonsa, sannan bata son kawar da kallonta a kansa, sai dai yau bata taɓa mashi kumatu ba, domin shakkarsa ya ɗan shiga ranta, ta ji tana ɗan shakkarsa.
Sallama cikin nutsuwa Faisal ya yi a bakin kofar gidan kafin ya shigo ciki. Har ƙasa ya duƙa ya ɗagawa bappa gaisuwa, cikin so da kauna bappa ya amsa mashi tare da ce mashi. "Yau Shehu ne ya tafi kiwon shanun bappanku ko?". Kai ya gyaɗa mashi alamar e.
"Tom dama so nake ka je ka karɓawa Mahnoor kiwon nan ta dawo gida, ta zo ta yi mana girki, ni yau ba zan samu fita ba".
Da to ya amsa mashi tare da miƙewa tsaye ya nufi waje. Ruwan albarka bappa ya fara sanya mashi, da amin amin ya yi ta amsawa har ya fita, bappa yana kaunar Faisal sosai, a yanzu bashi da burin da ya wuce yaga ya ɗaura mashi aure da Mahnoor, haƙiƙa Faisal yaron kirki ne sosai, ga girmama manya da sanyin hali sosai da sosai, baya son yanayina kuma baya yi, bashi da faɗa kamar na sauran matasan ƴaƴan fulani, ko takalarsa faɗa kayi baya kula mutun, yana da hakuri sosai da kawaici haɗe da kunya, idan kunji yana magana ma to sun haɗu da abokiyar faɗarsa ce wato Mahreen wanda dama can ita bata zaman lafiya da kowa, duk wanda ya ce mata kule sai ta ce cas, to da ita kawai zaku ji yana magana mai sauti, sai masoyiyarsa abar kaunarsa wato Mahnoor.
Yana fita ba jimawa sosai sai ga Mahnoor É—in ta dawo, tana shigowa Nenne na shigowa tamkar a tare suke. Ai Nennen tana shigowa nata É—akin ta nufa da sauri saboda tsoron Jaish, tana bala'in tsoronsa sosai. Ita ma Mahnoor akwai tsoron nasa dai, amma haka ta nufi kofar É—akin bappan jiki na kerma, kirjinta sai dukan uku uku yake yi.
A bakin kofa ta tsugunna tare da cewa bappan. "Bappa jamɓandu?. (Bappa ina wuni?)". Yana daga cikin ɗakin zaune a kusa da Jaish da kuma Mahreen ya amsa mata gaisuwar tata sannan ya ɗaura mata da cewa abinci zata girkawa bakonsa mai daɗin gaske.
ÆŠan zaro idanu ta yi kafin ta ce. "Bappa dama aljanu ma suna cin abinci ne?". Kyakkyawar murmushi ya sakar mata kafin ya bata amsa da. "Mahnoor baki yarda da bappanki bane?".
Girgiza kai ta yi tare da cewa. "A'a bappa na yarda da kai".
"To idan har kin yarda dani kuma zan yi magana ki ji to na gaya maki wannan bawan Allahn ba aljani bane, mutun ne kamar kowa, ku dai'na É—aukarsa a matsayin aljani, sannan batun kyansa da kuka damu sosai a kansa ku sani akwai mutane kyawawa sosai a duniya, ba yadda Allah baya halittar bawa, amma na maku alkawari ke da Mahreen in zan sake fita Nigeria zan tafi daku, ko Cameroon kuka je akwai turawa mazauna can sosai bama sai a Nigeria ba, akwai larabawa, to wannan bawan Allahn yana É—aya daga cikinsu, ko bature ko balarabe, ni nasaba ganin irinsu shiyasa ban damuba, dole ma idan zan sake tafiya in tafi daku dan ku kalli irinsu saboda ku rage tsoro". Ya kai karshen maganar yana kallonta.
Ɗan karkatawa ta yi ta leƙo fuskar Jaish ɗin kafin ta sake dawo da kallon nata a kan bappan. "Tom shikenan bappa, na yarda ba aljani bane, amma ni dai ina jin tsoronsa har yanzu, bari na je na dafa mashi tuwo dawa da miyar zogale".
A hanzarce bappan ya fara girgiza mata kai tare da cewa. "A'a Mahnoor ba zai iya cin irin abincinmu ba ai, su basa cin tuwo, kinga yanayinsa ya yi maki kama da wanda zai iya cin tuwo ne?".
Kai ta girgiza mashi alamar a'a.
"Yauwa ai ba zai iya cin irin namu abincin ba, yanzu dai zan yanka mashi zabbi da kaji ko guda goma ko ashirin haka, sai ku gyara ku soya mashi, nasan nama kam zai iya ci tun da suna ci, sai a rinƙa dama mashi fura yana haɗawa kafin ya samu sauki ya koma garinsu".
"Tom bappa, bari na sanya ruwa a wuta dan gyara kajin". Da to ya amsa mata, miƙewa ta yi ta nufi kitchen, shi ma bappa ya miƙe ya fito waje, wajen kajinsu da zabbin nasa ya nufa, haka ya zaɓo manya manya guda ashiri, kaji goma zabo goma, ƙosassu ya zaɓo, sannan ya tsinto kwan zabi dayawa ya dawo da su cikin gidan.
Mahreen ce ta riƙe mashi wuyar kajin ya yankesu dukkansu, Mahnoor bata taɓa yarda ta riƙe mashi kaji ya yanka, saboda tsoro irin nata, sannan tana da raunin zuciya sosai, idan ana yanka kaji tana wajenma har kuka take yi, dan tausayi suke bata, ba zata iya ganin ana yankasu ba, sai ma idan ransu ya zo fita, a wannan lokacin kuka sosai take yi, shiyasa bata tsayawa a wajen da ake yankan, ita kuwa Mahreen sarkin taurin zuciya da rashin tsoro, ai tuni take riƙewa bappa ya yanka, ita ko wukar aka bata tsab zata karɓa ta yanka da kanta, ai wannan yarinya special ɗin specials ce.
Dukka ya yankasu, da shi da Mahreen suka haɗu suka taya Mahnoor gyara kajin, Nenne dai taki fitowa daga cikin ɗakinta, tana kwance tana tunanin wani irin mugunta zata ƙullawa Mahnoor wanda zai sanya bappa ya tsaneta ya dai'na sonta, ya jima tamkar ya kasheta idan ya ganta, abin da kawai ta kwanta take tunani kenan.
Baiwar Allah Mahnoor kuwa tana can tana aikin farantawa mahaifinta rai tana samun lada ba tare da tasan me Nenne ke shirin kullah mata ba.
Sai misalin karfe 3 ta gama soya kajin nan dukka, dan ma Bappa da Mahreen sun tayata sosai, ta gama bappa ya ce ta dafawa Jaish É—in kwan zabbi bari ya duba gonarsa ko akwai nunannun kaya itatuwa ya taho mashi da su a haÉ—a mashi a kayan abincin nasa kila zai É—an iya ci.
To suka ce mashi, wucewa ya yi ya fita ita kuma Mahnoor ta juye ruwan zafin dake saman wuta ta je ta yi wanka. Mahreen kuma ta kwashe namar ta kai shi cikin É—akin bappa.
Mahnoor bayan ta fito daga wanka shirin zuwa Islamiya ta yi fes abinta ta fito, sannan ta ce da Mahreen ta fito daga ɗakin bappan nan ta wuce tazo ta yi wanka ta yi shirin zuwa Islamiya bari ita kuma ta tattare gidan ta share kafin lokacin yin sallar la'asar ta yi sai su yi sallah su wuce islamiya, sam basa jin yunwa dan sun ci namar kajin sosai sun ƙoshi, da yake su kam ma ba bakin nama bane, kullum Friday bappa yana tanka masu ƙaton rago ƙosasshe guda ɗaya, kaji kuwa duk lokacin da yaga dama yana yanka masu, so su nama baja baja suna da shi.
Tsintsiya ta É—auko da nufin ta fara share gidan, dai'dai lokacin Nenne da ta tashi a barci yanzu ta fito waje.
"Ke Mahnoor É—auko mun jakar littattafan bappankun nan bari na duba wani littafin addu'oi a ciki zan kai wa gwaggona". Cewar Nennen, tana maganar tana jefawa Mahnoor É—in wani irin kallon tsana.
Narai narai baiwar Allah ta yi da idanu, tamkar zata rushe da kuka ta ce. "Nenne dan Allah ki yi hakuri Mahreen ta É—auko maki, wlh ina bala'in tsoron wannan mutumin da bappa ya kawo, dan Allah Nennen ki yi hakuri, Mahreen ce bata jin tsoronsa, zata iya..........".
Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon wani irin matsiyacin kallo da Nennen ta wurga mata, shiru ta haÉ—iye sauran maganar tata, nan take idanunta suka ciko da kwallah.