Sashe 100
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru bai motsa daga in da yake ba, dama idan jiji da kan mulki jinin sarautar tasa ta motsa sai ayi ta yi mashi magana yana ji amma ba zai motsa ba bare ya nuna alamar ya ji me suka ce, hakan yana É—aya daga cikin abin da yasa bappa yake zargin ko dai shi É—in jinin sarauta ne, ya iya miskilanci da shegen izza na karshe.
Lallashinsa tare da bashi hakuri sosai bappan ya fara yi, dan ya fahimci tabbas ransa ne ya ɓaci, wato fushi yake yi yanzu kenan.
In short bappa ya ɗauki almost 40 min a wajen yana yi mashi magana, amma ɗan tahaliƙin nan yadda kuka san mutum mutuminsa ne aka sassaka a wajen, ko ɗagowa ya kalli bappan yaki, duk da dama can baya yarda su haɗa idanu da shi, amma ko motsawa daga in da yake yaki yi.
Sai da bappan ya gaji dan kansa ya hakura ya rabu da shi, amma ransa bai so hakan ba sam sam, shi da burinsa a kullum Jaish ɗin ya saki jiki da su, ya zama kamar jini ɗaya suke kawai, amma sai ga shi yau Mahreen ta ɓata komai, abin ya ƙona mashi rai matuƙa.
Miƙewa ya yi ya nufi waje, wlh idanun Jaish biyu yana jinsa, kawai ransa ne a ɓace, baya son ya yi wa dattijon nan wani abin da babu daɗi ne yasa ya danne zuciyarsa ya kuma riƙe harshensa, yasan yadda zuciyarsa take tafasa in bai yi da gaske ba wlh tsab zai iya dallawa bappan maruka, ku da kun san halinsa, to shiyasa ya kwanta shiru ya danne zuciyar yana jiran har ta sauƙa, kun ji dalilinsa na share bappan, ya yi kokari matuƙa gaskiya na iya danne zuciyar tasa.
Gona bappan ya koma, kai tsaye wajen Mahreen da Mahnoor ya nufa, sai hira suke yi suna wanki gwanin birgewa. Yau karo na farko a rayuwarsa da ya fara yi wa Mahreen faɗa dan kawai ta sanya ran baƙonsa ya ɓaci.
Tsabar mamakin hakan yasa Mahnoor miƙewa tsaye tana tambayarsa meyake faruwa?. Bai ɓoye mata komai ba ya gaya mata Mahreen ta ja Jaish ya yi fushi sosai, mamaki ne sosai ya kama ta sosai baiwar Allah, ita dai tasa wlh ko Arɗo Mahreen ta yi wa laifi bappan nasu baya taɓa yi mata faɗa, amma yau akan bare da basu san saga ina yake ba yake yi mata faɗa? Lallai wai wani irin kauna bawan Allahn nan yake yi wa Jaish ne? A gaskiya yana kaunarsa over, ku duba ku gani, kun san yadda fulanin daji suke kaunar dabbobinsu sosai, amma a haka bappa yake zubar da dabbobin nan nasa yana yankesu wa Jaish, a gaskiya ya nuna mashi kauna sosai, ya cancanci a jinjina mashi, yau a kansa aka yi wa ƴar gabar goshi, ƴar Auta, kuma ƴar zinarinsa faɗa? Lallai Jaish ya ciri tuta. Wlh haka yaran Momma suke da shegen farinjini da shiga rai, shiyasa ya shiga ran bappa sosai.
Ita ma fushi ta yi da ya yi mata faÉ—an, fuuuuu ta wuce gida abinta, cikin raunin murya Mahnoor ta ce. "Bappa kaga ta tafi gida fa".
Rai a ɗan ɓace ya amsa mata da. "Kyaleta ta tafi ɗin, yau wata da watanni ina ta shan wahala wajen ganin bakon nan nawa ya buɗi baki ya samu lafiya sosai, amma na lura Mahreen tana neman ta lalata mun komai, yanzu idan ta sanya yana shiga ɓacin rai komai ya zo ya lalace ya take son nayi?".
"Ka yi hakuri bappap In Sha Allah zata dai'na". A sanyayye ta faÉ—a. Albarka ya sanya mata tare da juyawa zai koma cikin gonarsa, har ya fara tafiya sai kuma ya juyo. "Nennenku fa ta dawo". Ya faÉ—a fuska ba ya bo ba kuma fallasa.
ÆŠan zaro idanu waje ta yi tare da cewa. "Kai masha Allah, amma ba zata sake tafiy ba ko?".
Wallahu a'alam ya amsa mata da shi tare da wucewa in da ya nufa.
Cigaba da yi wankinta ta yi har izuwa azahar, ta kammala ta je ta shanyasu a farar yashin dake gefen kogin, sannan ta É—auro alwala ta nufin in da bappan nata yake.
Ga mamakinta sai ta iskoshi a tare da Mahreen suna ta zuba hira kamar ba ita ce ta yi fushi ta tafi gida ba, yanzu ta dawo, abinci ma ta kawo masu Nenne ta yi girki mai rai da lafiya yau, sai mamaki bappa yake ta yi, ita kanta Mahnoor ta sha madarar mamaki na ganin Nenne ta yi girki, ta kai tsawon shekaru 5 bata girki kamar matar aure a gidan, Mahnoor É—in ce ke yi, yau rana tsaka ta yi girki abin da mamaki, amma duk basu kawo komai a ransu ba, suka ci suka sha, suka yi sallah, sannan suka zauna yin hira kamar yadda suka saba.
Nasiha bappan ya rinƙa yi masu sosai mai ratsa zuciya, sai kuka Mahnoor ta rinƙa yi saboda nasihar ya taɓa mata zuciya sosai, bappa ya iya yi masu nasihar da ya kan sanyasu su ji duniya ma gabaɗaya ya fice masu daga ransu, bawan Allah ne sosai, uba ne na gari sosai.
Ita kuwa Mahreen da harkar tsoro baya a tsarinta, idanunta a bushe garau ba ko alamar hawaye, kun san ita harkar jarumta ta tasani, sai kace wata renon Commander Zafar, idanu a bushe, komai nasihar da bappa zai yi masu, zai ratsa zuciyarta, amma hawaye? Tab baya fitowa daga idanun yarinyar nan, sai ka yi zaton ma bata da ruwan hawayen a duniya, amma akwaisu, kukan ne kawai ba za'ayi ba.
Sai karfe uku Mahreen and Mahnoor suka dawo daga wajen kiwo, abin mamaki kuma yau Nenne dai bata yi masu tijarar da ta saba ba, salum alum suka yi wanka, suka ɗauro alwala, har da abinci ta basu suka ƙara ci suka ƙoshi, sai ɗari ɗari Mahnoor take yi da ita, dan bata taɓa ganin ta yi masu makamancin haka ba, ita dai tasan tsakaninta da Nenne duka, zagi da kuma hantara.
Sai tunani take yi a kan to ko dai yau lafiya Nennensu take? Abin da É—aure mata kai.
Islamiyya suka nufa kamar yadda suka saba, yau bata hanasu tafiya da wuri bama.
Ko da suka tashi daga islamiyyar sai da su Salisu suka biyosu da nufin su dakesu, duk da yayan nasu ya sami sauki saboda bakar zuciya sunki hakura sai sun É—auki fansa.
A hanya suka taresu, suka sha gabansu sun hanasu hanya. Mahnoor dai hakurin nan da ta saba shi ta shiga basu da wannan sanyayya muryar tata.
Ita kuwa Mahreen Mahnoor na tsaka da basu hakuri kamar wata zararriya ta zunduma ihu tare da bajewa a ƙasa ta fara birgima tana watsi da wulli da kafafunta sama. Zaro idanu gabaɗayansu suka yi, da sauri Mahnoor ta tsugunna a gabanta, murya na rawa ta fara tambayarta me yake damunta?.
Sam bata kulasu ba, ihun ta ta cigaba da yi tana birgima, sai da ta babbatar zuƙatansu sun gama tsinkewa, sannan ne ta wani irin girgiza jikinta yadda kuka san wata bujumar saniyar da aka zubawa ruwan sanyi, kunsan zai karkaɗe jikinsa ya yi wani irin girgiza ai? To haka ita ma ta yi tamkar mai wani motsi a kai.
Zaro idanu suka yi suna cigaba da kallonta, da wani irin murya kamar na Æ´an shaye shaye da suka jima a harkar murya ta gama lalacewa ta ce. "Kai Salisu zo nan gabanmu!!".
Tun da Mahnoor ta ji haka ta gane iskancin da ta saba yi wa waɗan da suka fi karfin ta iya dukansu ne ta yi masu, dama idan ka fi karfinta, ta san cewa zaka iya dukanta sai ta yi masu aljanun karya, a haka take kwatar kanta a koma inane, lafiyar jikinta ne ba zata bari a taɓa mata ba yar albarka.
Da farko Salisu dai an gwada jarumta, nunawa ya yi kamar baya tsoro har da wani É—aure fuska sosai. "Ba zanzo ba, idan ma kai aljani ne to ka fito ina dai'dai da kai, ba kana ganin da safe kasa mun gudu ba? To yanzu aradun Allah babu in da zanje har sai na ci uban yarinyar nan".
Wani irin zaro idanu waje ta yi tare da sake yin wani irin girgiza, sannan ta kara kausasa murya tare da yunƙurawa a haukace zata tashi tana faɗin. "To jiramu gamu nan zuwa!!".
Habawa ai tana yunƙurowa da karfinta a guje Salisu ya watsa sai hanyar gida har wando na faɗuwa, takalma kam ba'a maganarsu, tuni ya watsar da ƴan banza, hege ko waye ya ce mashi barno a gabas take, ai Mahreen ba taya baya bace, kuma she's know how to act well well ƴar albarka, ji yadda ta taso fisabilillah har da wani cewa gamu nan zuwa, oh ni princess Teema ina ganin rayuwa wajen wannan yarinya, ko da yake jikar gwaggo ce fin haka ma idan ta aikata ba abin mamaki bane, dan faɗa dai kun gani da idanunku a jininsu yake, gwaggo ce ko bala'i, ga Nenne ma ta gado.......... Ni kam na ce to da ta tason nan in da Salisun bai gudu ba ya zata yi kenan? Ita dai tasan ba iya dukansa zata yi ba? Amma dai koma me yarinyar akwai bala'in karfin hali tare da sanyawa ranta koma me itace da nasara, bata tunanin ɓacin rana sam sam............ Na ce ba Allah ya haɗa mun ita da Obaid and Omaid, ƴan amin ku ce amin......🤣
Tana ganin sun gudu ta miƙe tsaye tare da buga tsalle tana faɗin. "Gobe ma ku dawo mana, na fiku iya shan kunun tsiya". Tana magana tana karkaɗe kasan da ya ɓata mata jiki saboda kwanciyar da ta yi a ƙasan.......... Oh ni ƴar mamata, har da kunun tsiya ma Mahreen take sha? Allah mai iko!.
Ko sannu Mahnoor bata ce mata ba suka nufi gida, sai addu'ar neman shiriya a wajen Allah Mahnoor É—in take ta yi wa Æ´ar kanwar tata a cikin zuciyarta.