← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 211

Sashe 158

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai isa ko yatsa ya ɗaga mashi ba matuƙar yana a tare da Black Tiger, kuma yasan Black Tiger ɗin yana kaunarsa sama da komai a duniya, yanzu tunani yake yi ta yadda zai yi ya rabasu, ya ɗauke hankalin Black Tiger ya ɓatar da Ronnie daga empeir ɗin, idan ya so sai ya ja shi zuwa wata ƙasa ta daban cikin daji ya hallaka shi ba tare da sanin kowa ba, a tunaninsa kenan.

Yau tun safe da ya shigo wajen training ɗin tunanin da yake ta yi kenan, ya kasa bawa yara horo, ya zauna saman kujera shiru kamar mai tilawar karatun Alkur'ani mai girma a cikin zuciyarsa, alhalin mugun abu yake ƙullawa, kowa dai yasan master bakin mugune, sannan idan yasa kai tsab zai iya yin abin da ya fi haka, to masoyan Ronnie sai ku tayasa addu'a, zamu ga tsakanin master and black tiger wanene ainahin shegen shu'umin a cikinsu, shin master zai iya wasa da hankalin Black Tiger har ya sace Ronnien kuwa ko yaya? Akwai game babba a tsakaninsu gaskiya, mu je dai zuwa.

Wannan matashi da ya fara miƙewa mai suna Udesh ne ya nufi saman wata iriyar step mai shegen kyau, haurawa ya fara yi cikin jarumta, gini ne aka yi mai tsawo kuma ɗan siriri haka, sai aka yi step na hawansa, a can nesa ma aka yi irinsa, sai aka sanya wani irin murɗaɗɗen sarka mai karfi dogo kamar igiya, dik wanda ya iya hawa saman sarkar daga wannan ginin ya yi tafiya a kan sarkar har zuwa wancan ginin bai faɗo kasa ya ji ciwo ba to fa ya gama haye matakin farko na horo, sai mataki na biyu.

Tun da suka ga Udesh ya nufi wannan gini zai hau wannan sarka suka karaya, da kuwa su a yanzu suke koyar tafiya a kanta, suna tsoron su faÉ—o su karya wuya ko wani sassa na jikinsu.

Sai a lokacin hankalin master ya dawo kansu, wani irin tsawa ya dakawa Udesh É—in wanda ya sanya shi saukowa a dubu. Master yasan basu kai ga iya tafiya a kanta ba, kada su je su faÉ—o su mutu yawan mayakansu masu tasowa su ragu, shi fa bama ransu yake yi wa ba, damuwarsa yawan mayakansu zasu ragu ku kunji mun bakar zuciya fisabilillahi!.

Cikin hanzari ya dawo cikin Æ´an uwansa jikinsa na kerma, dan suna bala'in tsoron master, yana zuwa ya zauna shiru, saura matasan kuma kowa ya kama abokinsa suka cigaba da gwada gwanji da karfi ta hanyar faÉ—a da juna, dama abin da master ya sakasu kenan.

Sake sauke ajiyar zuciya ya yi a in da ya cigaba da tunanin ta yadda zai ɓatar da Ronnien.

A can cikin Black Tiger empire kuma, zaune Floris take a parlour tana buga game É—in triangle ita da É—aya daga cikin Æ´an'mata marayu da Black Tiger yake rai'na, yarinyar ita ma kyakkyawace jinin Dark world. Ko ina Ronnien yau kuma Floris take buga game da wata ba shi ba? Da alama ya tafi school.

Ainahin Black Tiger empire, fitowa Sweetie ta yi daga cikin wani haÉ—aÉ—É—en luxury bedroom mai bala'in kyau, rufeta dama aka yi a cikin room É—in, kullum sai ta gwada buÉ—e kofar amma sai ta jishi a rufe, yau dai tana gwadawa sai ta yi sa'a taga ya buÉ—e.

Sanye take cikin jelly dressing, sai dai rigar ya É—an yi kata tsawo sosai, dan ya sauka har kasar gwiwanta a maimakon ya tsaya a saman gwiwan wajen cinya, haka zalika wandon ma ya É—an yi mata yawa, ya fi tsawonta.

Kanta babu ɗan kwali, saboda kayan basu da shi, golden white hairnta a watse kamar wata mahaukaciya, da alama tana cikin damuwa sosai, dan sexy eyes ɗin nan nata a kumbure alama ta ci kuka sosai, ta rame matuƙa kamar ba ita ba, idanun nan sun kara kwala kwala kamar ball, olive eyes ɗinta sun ƙara ratsa olive green sosai, lokacin da suke jarirai idanunta forest green ne, Pretty ce ke da olive, a hankali hankali suma girma idanun nata suna riƙiɗewa har suka koma sak na Prettyn ba maraba.

Dark purple lips É—inta suna bushe karau tamkar bata shan ruwa, sun zama kamar basu ne masu sheki da É—aukar hankali idan Kamran ya ga na Pretty ba, dik ta canza tamkar wadda aka É—auki lokaci ana azabtarwa.

Kana ganinta zaka fahimci a ruɗe take, ga tsantsar tsoro a face ɗinta, kamar wata zararriya haka ta fara waige waige tana neman hanyar fita daga wajen, tsarin ginin ya sha gaban tunanin wayayyun mutun ma bare ita girman forest, komai wayenwan mutun idan ya shigo wannan waje sai ya ɓata hanya ya kuma zama cikakken ɗan kauye, ga ɗakuna da a kallah zasu kai biyar a wajen, dik kuma design na komai iri ɗaya a cikin wajen, hanyoyi har huɗu ne a ciki, tashin hankalin ma bata san a hawa na nawa take ba, abin da baku sani ba hanyar da Ronnie yake shiga idan zai je wajen Black Tiger sai ya hau elevator sannan ya kai ga babban parlournsa, daga nan sai bedroom ɗinsa, so bata san a wani hawa ma take ba.

Zubawa kujerun dake parlourn idanu ta yi, da zallar madarar gold aka yi su, gabaɗaya kujerun design of ɗawisu aka yi head ɗinsu, yanayin kayin kujerun ne sak gashin bindin ɗawisu, sun yi matuƙar tsaruwa sosai. Wajen zama kuma luntsuma luntsuman sofa foam ne masu lumar da mutum.

Ganin cewa tsayawa ganin kujerun nan da tsaruwan parlourn ba zai kai ta ko'ina bane yasa ta nufi hanyar da ta gani yana fuskantar in da take tsaye.

Sauri sauri gudu gudu ta nufe shi. Wani irin haÉ—aÉ—É—en door room ta gani a wajen, bata yi wani tunanin ba kawai ta tura ta afaka ciki, a tunaninta kofar fita ce.

Wani irin juyi da kanta ya yi mata ne yasa ta sunkuyar da shi ƙasa ba shiri, ji ta yi tamkar wadda aka kwaɗawa katon guduma a tsakiyar kanta, dum ta ji duniya ya yi mata.

A hankali ta fara É—ago sexy eyes É—in nan nata ta fara kallon tun daga kan tafukan kafafunsa da suke farare tas tamkar madara, from his legs fingers ta fara kallo, gasu dogaye masu bala'in kyau, wani bakin gashi siÉ—if kwance saman kowani yatsarsa zuwa kusa da faratunansa.

Bata san lokacin da ta fara É—ago idanunta izuwa sama ba, skin É—insa sak Koreans guys skin, ba karamin girgiza ta yi ba na ganin har ta kai kallonta saman santala santalan cinyoyinsa da wani siÉ—if É—in gashi ke kwance luf bata ga kaya a jikin nasa ba.

Ƙoƙarin kawar da kallonta ta yi daga kansa dan gudun kada ta ga abin da kanta ba zai iya ɗauka ba, amma ta ƙasa, haka idanunta ya cigaba da kallonsa har izuwa saman denim short white color dake jikin nasa. Bata daddara ba ta cigaba da ɗaga idanunta tana kallonsa, ƙara zaro idanun waje sosai ta yi a lokacin da ta sauke su a saman gurayen layukan dake zane a saman plat tummynsa.

Bata ƙarisa tsinkewa ba sai da ta kai kallonta saman lion chest ɗinsa mai bala'in faɗi kamar wani zaki, ga ɓul ɓul ɗin breast ɗinsa a cike, babu riga a jikinsa, tamkar shi ya yi wa kansa halittar jikin nan nasa, gorgeous, sexy body ne da shi.

Wani irin bala'in tsoro ne ya dira mata a ranta, sai ta ji anya zata iya ganin face É—in mai wannan jikin kuwa? Dan kuwa master Devil da take jin tsoron gani saboda murÉ—ewar jikinsa da kuma tsawonsa ma to bai kai wannan jikin ba, da alama wannan shi ne ubansu a kyan jiki a gabaÉ—aya kingdom É—in.

Abin mamakin kuma dik wannan murÉ—ewar tasa wuyarsa tana da tsawo, bata yi tsawo zalau ba, tana da kauri sosai, har wasu gurayen layuka ne a wajen masu kyau da É—aukar hankali, tun daga kan jikinsa zaka gane mamallakin jikin makura ne wajen haÉ—uwa.

Wani irin ja da baya ta yi har sai da ta yi tangal tangal zata faɗi ƙasa a lokacin da ta ƙarisar da kallonta a saman face ɗinsa, ya subhanallah, ni kai'na sai da na ja da baya, saboda ban taɓa ganin halitta mai kyansa ba, wow nace, na kara cewa Masha Allah, na sake haɗawa da kam balai'n can, Allah mai yin halitta a duk yadda ya so, amma dai wannan guy ɗin makura ne. Kamar wani rafani za'ace ne ko me, ban ma san da ya zan kwatanta maku kyan guy ɗin nan ba.

Namiji iya namiji, ga tsawo da cikar halitta. Pink lips yake da shi kamar na mace, yana yin tsarin lips ɗinsa kawai abin kallone ga ɗaukar hankali, ga idanu nan dara dara, farin ciki idanun nasa ya yi milk milk haka, kwayar kuwa olive ne irin na su Sweetien, sai dai shi nasa ya ɗan yi wani iri kamar anyi mashi mix da hazel haka, kumatun nan nasa sai dai muce masha Allah, ɓul ɓul, a haka bai yi magana ba, bai motsa kumatun nasa ba ma zaku iya ganin alamun kyawawan dimple a kumatun nasa, dik yadda zan gaya maku haɗuwar guy ɗin nan ba zaku gane ba, dan baki ma ya yi kaɗan ya bayyana kyansa, wane alƙalamina a wannan gaɓar.

Lafiyayyen matashi mai shekaru 30 a duniya, handsome! Sexy! Gorgeous, end of discussion a kyau, sai dai kuma his heart is totally bad, fine guy with black heart!!.

Yana tsaye a tsakin bedroom ɗin, daga shi sai danim short, hannunsa na riƙe da king scepter ɗinsa da kuma wani ɗan karamin circle abu mai haske kamar madubi, ba kuma madubi bane, idanunsa suna a kan wannan hasken, ya saita scepter ɗin nasa a saman abin, ya bada wani irin haske na musamman, da alama magic yake yi.
Chapter 158 · 0% Book details