← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 211

Sashe 156

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har lokacin da ya dawo tana kwance bata ko motsa ba a yadda ya ganta. Ɗan zuba mata idanu kaɗan ya yi kafin ya ƙariso gefenta ya kwanta, ji yake yi kamar ya tasheta ta yi sallah, sai kuma ya tuna irin wahalar da ta sha, hakan yasa ya kyaleta tare da gyara kwanciyarsa. A hankali ya lumshe idanunsa, dan shi ma barci yake ji, agajiye yake sosai.

A fujaje ta miƙe tana ƙoƙarin barin gadon, kamar wata zararriya ko wadda aka tsoratar, ashe kenan ta farka idanunta biyu, kwarai ta farka ta yi sallah ne ta sake kwanciya.

Idanunsa a lumshe amma ya ji yadda ta miƙe daga kwanciyarsa kamar shi ɗin dodo ne, hannu yasa zai kamata idanunsa a rufe.

A guje ta yunkura zata sauka ƙasa, ya yi sa'a ya dapko shoulder ɗinta, a hankali ya waro idanunsa, caraf suka haɗa ido, dan kuwa shi take kallo da ya riƙota, ɗakin akwai ɗan duhu duhu, gari bai gama waye ba, amma kuma iya ganin juna.

A hankali ya mayar da idanunsa da suka yi ja saboda barci ya lumshesu ba tare da ya saketa ba.
"Ina zaki je da sanyin nan?". Kamar baya son yin magana ya yi ta.

"Zan je in yi wa Nenne aiki ne, shara da wanke wanke da........."

Ɗaukewa ta yi diff da yin maganar saboda waro idanun nasa sosai da ya yi a kanta, dawo da kallonsa a kan hannnunta da ya riƙe dake ta fama kerma ya yi, slowly kuma ya dawo da kallon nasa saman tsoratacciyar face ɗin nan nata, ya sani sarai tsoronsa take ji, kuma ba zata iya kwanciya da shi a mattress ɗaya bane yasa zata sauka ta gudu waje, ga sanyi kamar me ko me zata je ta yi a wajen, har yanzu yayyafi ake ɗan yi ko ta yaya zata yi shara? Ya jefawa kansa questions.

"Daga yau kada na sake ganin kin fita daga ɗakin nan da sassafe, sai karfe 8 dai'dai zaki rinƙa fita". Kamar wanda yake cikin maye ya yi maganar, dama ya jima yana bakincikin yadda take fitowa da sanyin safiya tana yi wa Nenne aiki kamar wata jaka, to yau dai Allah ya bashi damar hanata, a ransa ya kuduri niyar ba zama ta sake yi wa Nenne aiki a gidan nan ba, idan ya wuce aikin gyaran ɗakin bappanta da sharar tsakar gida ba zata sake yin komai ba, idan Nennen ba zaman aure ta zo yi ba sai ta kara gaba bappan ya auro wadda zata zo ta yi zaman aure, ta kula da gidan da abin da zai ci.

To fa akwai cakwakiya, Jaish zai hana Mahnoor yi wa Nenne aiki! Kuna ganin akwai zaman lafiya kuwa idan ya yi hakan? Dan dai kunsan Nenne dole ta dawo gidan, dole ArÉ—o zai kaÉ—ota ta dawo, me kuke tunanin zai faru? Akwai rikici fa my people's, abubuwa zasu É—auki zafi kenan.

Shiru ta yi kirjinta yana dukan uku uku, tara tara.
"Koma ki kwanta". Ya yi maganar tare da sakin shoulder É—in nata ya juya ya bata baya.

Kamar zata yi kuka, cike da tsoro ta koma ta takure jikinta waje guda, Allah tsoron kwanciya a saman mattress É—in take ji, dan ma É—an kwana biyun nan ta É—an saba da shi, ai da ko kallonsa ba zata iya yi ba.

Shi kuwa barci sosai kamar zai yi yaya, amma hakan yana iya jiyo dik wani motsinta, ta manne da jikin bango kamar ance zai cinyeta,.sai mutsu mutsu take yi, dik ta ishe shi ta hana shi runtsawa, ba abin ya juya ya dallah mata mari ba, amma tana mugun bashi tausayi sosai.

Cikin muryar barci ta furta. "Noor ki dai'na mutsu mutsun nan kina damuna, barci nake ji". Yadda ya yi maganar sai ka rantse da Allah shagwaɓa yake yi mata, dan barcin dake kansa.

Ai bata san lokacin da ta saki baki, ido da kuma hanci tana kallon bayan wuyarsa ba, tunani take yi akan ya aka yi ya yi shagwaɓa irin na Mahreen? Ko dai dama shi ma ya iya ne? Bata san barci yasa shi yin hakan ba.

Wani irin daÉ—i na musamman ta ji na cewa ya yi mata magana cikin nuna kauna da kulawa.

Hakan yasa ta kwanta shiru dan kada ta takura mashi, kafin wani É—an lokaci barci ya yi awon gaba da su.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

FRANCE🔥🌹

Zaune yake a tsakiyar bed É—insa ya tasa wata haÉ—aÉ—É—iyar tsadaddiyar laptop É—insa a gabansa, ya kura mata idanu tamkar mai nazarin wani abin.

Shirye shiryen tafiya duniyar wata yake yi saboda wani binciken nasa a kan aikinsa da zai je, da farko yaransa biyu zai tura, sai kuma ya fasa zai tafi da kansa. Tun last week ya tashi launch rocket, so yanzu lokaci ya yi da ya kamata ya tura life support system, kun san kafin ka tafi duniyar wata kana da buƙatar fara bincikar yanayin sararin samani first, sannan a tashi launch rocket ita ce hanya ta farko da zata fara yi maka clearing hanya, sai system da zai duba maka yanayin yadda karfin hazo, karfin sanyin da yake sararin samaniyar duniyar watar da dai sauransu, sannan sai ka tura life support system wannan zai tantance rai zai iya dinfarar wajen a wannan lokacin ne ko kuwa zai iya samun matsala idan ya je?.

Idan ya tabbata zaka iya zuwa a wannan lokacin to ba tafiya kai tsaye zaka yi ba, sai ka sake tura navigation system mai karfi wanda zai duba maka yanayin motsin abubuwan da suke sararin samaniyar. Kun san sararin samaniya fa sai Ubangijin da ya halicceta ne kawai yasan adadin abubuwan dake wajen, so unexpect zaka iya cin karo da wani abin da baka raɓa zata ba, shiyasa ake tsawaita bincike kafin mutun ya tafi, aiki ne fa babban zuwa duniyar watar nan, ba wai ɗaga jirgi kawai za'ayi a tafi ba, planet ɗin zuwa can ma na daban yake.

Daga nan sai ka haɗa energy generation, amfaninsa shi kuma shi ne zai taimaka maka wajen tare maka karfin hasken rana ta yadda ba zai yi maka illah ba, haka zalika yana ɗan taimakawa wajen tare maka sanyin dake duniyar watar, kun san fa wata bala'in sanyi ne mai ratsa ƙashi da ɓargo na wuce misali a wajen. Mataki na gaba shi ne safety and emergency za'a haɗa, wato irinsu medical supplies, domin kula da lafiyarka idan Allah ya nufa ka sauka a duniyar watar, ana iya samun mura ko wata ciwon ta kamaka saboda tsananin sanyin dake wajen da kuma sauyin yanayi, kun san dai dik wasu system da za'a sanya dan su tare maka sanyin wata ba zai taɓa yiwuwa ba sai dai su rage maka, dan ba wanda ya isa ya tare abin da Allah ya kaddamar da shi, so akwai sanyi sosai dik da waɗan nan systems ɗin.

Sai kuma su oxygen dan babu iska a sama ko kaɗan, ainahin sama duniyar wata ake magana, babu iska a wajen, dole sai da irinsu oxygen ɗin nan dan shaƙar numfashi a rayu.

Sannan yazama wajibi a bawa wanda zai je wajen ƙwaƙƙwaran training na musamman, dan ya iya kare kansa da dik abin da zai iya cin karo da shi, dole ya cire tsoro a ransa, abin fa ba ƙaramin aiki bane wlh, sai masu dakiya, juriya da kwarin gwiwa.

So ya nutsa cikin dube duben da yake yi a kan abubuwan da suka tura ɗin, daga wajen aikin nasu yaransa dake kula da wannan ɓangaren suka turo shi rahoton da system ɗin da suka tura sararin samaniyar ta basu, shi ne yake dubawa, ya ce yau ba zai fita ba sai dare, shi ne ya buƙaci da su turo mashi ta nan ya duba.

Door room É—in nasa ne ta buÉ—e kanta da kanta, bai É—ago ya kalli door É—in ba, dan yasan guarantee familnsa ne.

Daddynsa ne ya shigo, yana cikin shigar cargon short and singlet fara tas, hannunsa É—auke da two cup of cortado, dik dangin su coffee ne, sai dai shi cortadon zaku ga suna yi mashi design of heart a saman shi, shi ma wanda dad ya kawo yanzu har da design É—in, kamar wasu masoya, ya zo ya É—aura cup É—aya a saman bed kusa da Smart, ya zago ta É—ayan side É—in, ya haye saman bed É—in ya zauna tare da janyo pillows ya É—aura saman laps É—insa, a bayansa ma ya sanya pillow É—aya.

Tun da ya shigo room É—in idanunsa a saman laptop na Smart, da alama yasan aikin da yake yi.

Sipping na cortadon nasa kaÉ—an ya yi tare da cirewa. "Son take urs". Ya faÉ—a yana kara sipping, still idanunsa a kan laptop É—in.

"Daddy who told you that I woke up from sleep?". Calmly ya furta hakan.

"My heart! you forget that our hearts are connected?".

Shiru ya yi yana jin kaunar daddyn nasa tana kara ratsa shi sosai, wato har yasan ya farka ma tsabar soyayyar dake tsakaninmu.

Kai mashi cup cortadonsa sai tin É—an bakinsa daddyn ya yi, a hankali ya buÉ—e ya É—an yi sipping kaÉ—an, yana cigaba da latsa madannan laptop É—in. Mayar da cup É—in bakinsa dad É—in ya yi ya cigaba da sipping a hankali cike da class, shi kuwa cup É—in Smart yana gefe bai ko kalli in da yake ba suka cigaba da shan na dad É—in, idan ya yi sipping É—aya sai ya kawowa Smart É—in ma ya É—an yi.

Suna yi suna hira cike da so da kauna yana kuma yin aikinsa har suka shanye cortadon dad tas ba tare da sun sani ba, ganin ya kare yasa da gangan dad É—in ya kawo mashi saitin É—an bakinsa da nufin ya yi sipping.

Dama kun san hankalinsa yana a kan aikinsa, dan haka sai ya yi sipping na iska babu komai a ciki cup ɗin. Ɗan turɓune fuska ya yi tare da juyowa ga daddyn nasa.

"Daddy!". Ya faÉ—a yana binsa da kallon kauna.

"Son". Shi ma ya faÉ—a yana binsa da hararar wasa.
Chapter 156 · 0% Book details