Sashe 103
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"I never thought there is a woman who will make me fall in love at this moment, I was so surprised, one time like a dream you stole my heart, wow my Mammien is special, ta iya zaɓe gaskiya, dole na yi mata gagarumin kyau"........ Duk ya ruɗe ne, ya susuce kalaman kauna kawai yake ta zuba mata.............Hakiƙa a wannan wajen ɗai zuciyata ta karaya my people's, dukkansu suna bala'in kaunarta, ya zasu yi a lokacin da zasu san cewa mace ɗaya suke so? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, waye zai hakura kenan? A gaskiya Mammie bakar muguwace kuma silent killer ce ta gasken gaske wlh, wato da bata da hanyar da zata bi ta kashesu ne yasa ta haɗa masu tarkon da ciwon zuciya zai kashesu gabaɗaya, domin kuwa dole ɗaya ya hakura ko kuma dukkansu biyu King ya hanasu dan ya raba gardama, kai koda an bawa ɗaya ya aureta ba zai taɓa jin daɗin zama da ita ba, saboda zai rinƙa jin raɗaɗin cewa ya auri abin da ɗan uwansa yake kauna, dole zuciyarsa ta yi ta yi mashi zogi, kai Allah ka rabamu da masu bakar zuciya irinsu Mammie.
Sai sakin cool murmushi take aikin yi, tana mayar mashi da amsa cikin jin kunya. Sun jima suna hira kafin ta ce mashi zata je Momma na kiranta, dama zumuɗin son zuwa ta gansa ne yasa bata fara zuwa kiran Mommar ba. Okey ya amsa mata da shi sannan suka miƙe a tare.
Da hannu ya nuna mata ta yi gaba mana, ba musu ta wuce gaba ya rufa mata baya.
Suna fitowa parlour suka isko Mammien and Aliyah suna zaune, har ƙasa ta tsugunna ta gaida Mammien, sai wani uban washe masu baki na munafurci take yi.
Gera guda ya É—agawa Mammie tare da cewa. "Mammie bari na raka Queen É—ina in tabbatar ta shiga ciki lafiya ina dawowa mu yi magana". Cike da kaunar Mammien ya yi magana.
Kara faÉ—aÉ—a murmushinta ta yi tare da amsa mashi da okey ya kula da ita dai sosai kamar da gaske take yi.
Gaba chuchun ta yi da sauri dan kunya da ya lulluɓeta, bayanta ya bi yana yi mata dariya wai tana kunyar Mammie.
Suna fita Aliyah ta dubi Mammie ta ce. "Aunty ina na ji kincewa Mama Jawad ne yake son Jannat? Ko dai ba Jannat ɗin bace wannan? Dan ni ƴaƴan King ɗin nan ruɗar da ni suke yi, kamanninsu kusan ɗaga, duk da shi suke kama da kuma wannan hegiyar tsuguwa mai idanu manya manya kamar na mujiya, wlh banson tsohuwar nan, haushi take bani". Ta kai karshen maganar tana kwaɓe fuska kamar an naushi kashi.
My people's nace mu gayawa Aliya gaskiyar wacece Akka ne ko dai mu yi shiru Akka ta bayyana mata wacece ita? Ana bala'i a kingdom of power, wai tana son King ya aureta amma bata son Akka, kam balai'n can, e lallai kin ɗauko dala ba gammo hajiya Aliya, dan kuwa Akka kam mai sonta ma bata so shi ba bare marasa sonta, ai duk bala'in ki a tafin hannun Akka ki ke, ita ɗin wandon robace dai'dai da ƙugun kowace maras kunya, ita gobara ce daga kogi wanda kasheta sai dai lillahi, dakalin majina a hau a zame, kai Akka bala'i ce, Akka duniya ce, zaki sameta daram yarinya, zata cire maki hayakin da kanki yake fitarwa, su Mama jiga jigan mata ma ya suka kare da ita bare ke tsutsar masai?.
Wani irin É—aure fuska Mammie ta yi kafin ta ja dogon tsaki. "Ita ce Jannat É—in dai, Jawad yana sonta ni kuma na cusawa Rizwan kaunarta, kinga mun jefi tsuntsu biyu da dutse É—aya, daga karshe dukka zasu yi mutuwar kasko, kinga babu wanda zai ce da sa hannuna, ina da tabbacin dukkansu biyu King ba zai basu aurenta ba, dan kuwa shi King adalin mutun ne, idan yasan suna son mace É—aya zai hanasu dan ya kwatanta adalci, kinga ciwon zuciya ce zata nakastasu". Ta kare maganar tana sakin wani É—an iskan dariya kamar wata mai motsi a kai.
Wani irin shu'umin murmushin ta saki. "Shegiya Aunty gaskiya kin iya plan, amma nasan mama ce ta shirya komai, dan ke baki da irin wannan ƙwaƙwalwar........"
Cak ta tsaya da dariyar tare da É—aure fuska ta wurga mata wani matsiyacin harara wanda yasa ta haÉ—iye maganar. Zata yi magana kenan Rizwan ya shigo bakinsa a É—auke da sallama.
Tsabar iya munafurci a wajen mammie har da wani cewa. "Kai har ka fara kamshin ango, wai ma me ka sayawa amaryar ne cikin katon echolac haka?".
Hegeya Aliya ita ma har da wani sakin murmushin munafurci tana faÉ—in. "Yah Rizwan wlh har wani kyalli face É—inka ta fara yi, e ango, wai yaushe ne ma abin?".
Zama ya yi kusa da Mammien yana murmushi, aka ce rashin sani yafi dare duhu, Allah sarki da kansa ya zauna kusa da makashiyarsu shi da marayan kanin nasa.
"Mammie bafa yanzu bane auren, zan barta ta kammala junior secondary school kafin nan na yi wa daddy magana......"
Bata bari ya ƙarisa zancen ba ta tari numfashinsa da cewa. "A'a ban yarda ba, zuwan nan naka za'ayi komai a gama, ni da bani da burin da ya wuce ku yi aure shi ne kuma Allah ya kawo lokacin kana ƙoƙarin ka kawo mana wani zancen da ba shi ba? Shekara nawa ina dakon jiran wannan rana? Ko so kake na mutu da tsumayin zuwan ranar aurenka a raina". Fuska a ɗaure ta yi maganar.
Aliyah ce ta capki zancen da cewa. "Gaskiya kam nima ban yarda ba, kawai ka shigo mun da Auntyta". Tana magana tana turɓune fuska yadda kuka san da gaske suke yi bayin Allahn nan, amma tsagwaran iya makircine da munafurcin ne kawai, idan ka faɗa tarkonsu ba zaka taɓa tunanin ba sonka suke yi ba hegu.
Fuska ɗauke da ƙayatattcen murmushi ya ce. "Kai mammie Jannat fa yarinya ce, zan bari kafin ta kammala dai zata kara girma, kinga hakan zai fi".
Girgiza kai ta fara yi. "A'a ban yarda ba, idan wani ya yi saurin shigowa ya ɗauketa fa? Kasan ƴaƴan sarakuna nawa ne suke rububinta? Jannat fa ba mace kamar sauran mata bane, ta fita daban, shiyasa na zaɓa maka ita dan kaima na daban ne, dan haka ka gayawa daddynku, zai ma fi kowa murna, jumma'ar nan a ɗaura aure kowa ya huta".
"Haka kike so our Mammie?". A hanzarce ta gyaÉ—a kai. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce. "An gama, bari zuwa dare zan sami dad a part É—insa, kafin nan kinga daddy ma jirginsu zai dira, kinga shikenan sai ayi komai ko?".
Murmushin makirci suka saki a tare ita da Aliya.
"Kwarai kuwa, ai ka yi kyan kai, ka je ka kwanta ka huta, na san a gajiye kake, saboda nasan tun É—azun hira ake yi da surukata kuma Æ´ata".
Ƙara fadaɗa murmushinsa ya yi tare da miƙewa. "Our Mammie kamar kin sani, yanzu ma ban gaji da hira da ita ba, itace dai ta ce mun zata koma, shi ne yasa na kyaleta sai zuwa anjuma da yamma zan sameta a cikin gidan".
"Eyyye wato kai baka kunyata ko?".
Kai yasa ya nufi part ɗinsa yana faɗin. "Mammie kunyarki na me zan ji? Ke fa kika zaɓa mun ita, ai daga nan kunya ma ta kare, bari dai na yi barci na tashi zan zo ki tayani zabawa ɗan uwana rabin jikina mata, dan kin iya zaɓa".
"Kai ai Jawad baya son batun aure, gara ma kada ka yi mashi yanzu, ka kyalesa sai gaba"... ......Munafuka ta faɗi hakan ne dan kada ya je ya ce zai yi wa Yah Jawad maganar aure har su fahimci mace ɗaya suke so, ba'a yanzu take son su fahimci hakan ba, ta fi so sai ranar auren ko kuma sai an bawa Rizwan ɗin Jawad ɗin ya san da hakan, daga nan komai na kwaɓe, shiyasa ta yi saurin dakatar da shi.
Da yake yana bala'in kaunar kanin nasa, kada ku manta shi kaɗai garesa, kunga kuwa dole ya kaunacesa, sam baya son ɓacin ransa, sai ya ce. "A'a ba sai ya ɓata rai ba, na kyalesa ya yi rayuwarsa, idan ya kara girma shi da kansa zai buƙaci yin auren". Yana kai karshen maganar ya shige ciki abinsa. Ya manta Yah Jawad ya taɓa ce mashi ya samu matar aure.
Wani irin murmushin mugunta suka yi tare da miƙewa a tare suka wuce room ɗin Mammie, dan su je su cigaba da kullah tuggunsu kada ya jiyosu.
___________________🕊ï¸ðŸ’˜
A can cikin gida kuwa, sai can dare King Zuhair ya dawo, kai tsaye master room É—insa ya shige. Momma na jin labari ita da Akka suka yi maza suka garzaya izuwa room É—in nasa.
Tsaye yake a tsakiyar room ɗin, ya harɗe hannayensa ta bayansa, daga ganin yanayinsa zaka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali, damuwace a kewaye da shi, kamar ma zai faɗi kasa sabdoa ɓacin rai, ba dan Allah ya tsare yana da taurin zuciya ba da ba abin da zai hana shi faɗuwa.
Tun daga ganin yanayinsa su Momma suka san ba lafiya ba, hakan yasa suka haÉ—a nutsuwarsu waje guda. Akka ce ta fara tambayarsa menene yake faruwa?.
Wani irin yawu mai É—aci ya haÉ—iye tare da furzar da wani irin isaka mai tsananin zafi daga bakinsa, sannan ya ja dogon numfashi, a hankali ya sauke. A hanzarce Momma ta É—auko mashi ruwa, hannunta har yana É—an kerma wajen balle marfin bottle water.
Tana mika mashi ya sa hannu ya karɓa, tun da ya kafa a bakinsa bai cire ba sai da ya shanye tas, karbar robar Momma ta yi. A hankali ya fara sauke numfashi mai tsananin zafi!.
A karo na biyu Akka ta sake tambayarsa meyake faruwa?.
Ajiyar zuciya ya sake saukewa, da kyar ya iya furta. "Akka babu Spender, sun É—aukesa daga gareni"....... Tashin hankali, ai wani irin jirine ya É—ebi Akkan, tafiya ta yi luuuu zata faÉ—i ya yi zafin namar tarota ta faÉ—a saman kirjinsa. Ita kanta momma ta shiga tsananin tashin hankali na wuce misaltawa, har wani juya mata kanta ta ji yana yi.