Sashe 92
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idanunta ne suka cike tab da kwallah, ta ji matuƙar tausayin Sharifat ɗin matuƙa, mayar da idanunta ta yi ta datse su, zafafan hawayen da suka cika idanun ne suka fara bin gefen ƙuncinta da ɗuminsu, ta rasa mafita, idan ta juya gefe guda babanta, idan ta juya zata aiwatar da aikinta dan ta ceci baban nata kuma sai ta tuna Sharifat dake da tsohuwar soyayya a zuci, in ta ja Ramish ya mutu ya Sharifat ɗin zata yi? Tasan zata cutu matuƙa. In ta juyo ta wani gefen kuma Abbie bawan Allah ya nuna mata kauna, shi take tunawa, duk sai ta ji tamkar ta kashe kanta kawai ta huta, ta gaji da wannan azaba, kullum bata cikin nutsuwa, zuciyarta cike da ciwo matuƙa, kullum tana cikin tashin hankali da fargabar asirinta zai tonu!.
Kallon Dr Raj Bilal É—in ya yi. "Dr i think Ummie ce ta azabtar da yarinyar nan, dan a sambatun da ta yi lokacin farkawarta tana ambatar aji tausayin maraicinta a kyaleta, kaga kuwa hakan na nufin wani daga cikin gidan nan ne ya yi mata wannan aika aikan!"............. Tab tashin hankali, wato shi Bilal ma zargin Ummie yake yi a kan ita ta fasawa Leesharh kai? E lallai kuwa, Leesharh tana zarginsa a kan yana tare da masu nikaf, dan yanzu ta gane cewa wlh shi ta gani a gidan masu nikaf, wlh shi ne ba kama ba, domin kuwa farfaÉ—owar da ta yi jiya kafin ta sake suma ta ga kayan da ya sanya ya je gidan masu nikaf shi ya sanya a jikinsa jiyan, ya fito a sak yadda ta gansa, sannan yana da zanen kunama a wuyarsa, kuma ta ga zanen, kai wlh shi ne ya je wajen masu nikaf, kunga ita tana zarginsa a kan da sa hannunsa wajen kashe Ramish, shi kuma yana zargin Ummie wajen cutar da ita, tab akwai cakwakiya, idan kuwa haka ne an samu babbar matsala ba kaÉ—an ba!
Amma meyasa duk zafin rai da zafin kai irin na Bilal ɗin daga kallonta a karon farko ya yi mata saukin kai? Meyasa ya zaɓi ya taimaka mata bayan su da basa yarda wani ya raɓesu? Su da basu yarda da kowa ba?! Har ma yake zargin Ummie a kanta! Meyasa ya ɗauketa da mahimmanci lokaci guda haka?. Sannan kuma ta wani ɓangaren idan har yana son cutar da Ramish meyasa zai taimaka mashi a lokacin da suka zo kashe shi? Meyasa ya shiga damuwa sosai na rashin lafiyar Ramish ɗin? My people's akwai matsala fa, wannan cakwakiya ta kusa sanya ƙwaƙwalwata ta ɗauke ɗif na wucin gadin.
Mu koma baya kaɗan dan jin abin da ya faru. Abin da baku sani ba Bilal ne ya shiga ɗakinta dan ya yi magana da ita ya ganta kwance cikin jini, shi da tun da Allah ya yi Sharifat a cikin wannan gidan bai taɓa taka kafafunsa ya shiga ɗakinta ba sai jiya wai yana son ganin Leesharh, shi ne ya je, idan baku manta ba a lokacin ta baro part ɗinsu ba jimawa masu nikaf suka kirata, to ya biyo bayanta kenan, yana shigowa ya sameta kwance a ƙasa cikin jini, kanta a fashe saboda bugasa da bango da ta rinƙa yi, a hanzarce ya ɗauketa cak zuwa room da Ramish yake kwance, a nan ya sanya Dr Raj ya bata taimakon gaggawa, da yake kanta ta rinƙa bugawa sai yasa jinin nata ya yawaita zuba, a jiyan ta farfaɗo ta sake sumewa, dan ciwo a kai ba karamin abu bane. Wannan shi ne abin da ya faru, tsayuwa tsayin daka a kanta Bilal ɗin ya yi har sai da Dr Raj ya kasa danne hakurinsa ya ce mashi wai ko ya san yarinyar nan ne da ya tsaya tsayin daka a kanta haka?
A'a ya amsa da shi tare da É—aurawa da cewa kawai tausayi take bashi.............. To mu koma kan labarinmu tun da mun ji ya aka yi Bilal ya taimaki Leesharh!.
Siririn tsaki Dr Raj ya ja tare da sanya hand gloves a hannunsa ya kwaso wasu allurai da nufin ya haÉ—a ya yi mata, dama jiran farfaÉ—owarta suke yi ya yi mata allura.
"Dama kai Yah Bilal ka yarda da Ummie kenan? Ai ko dan waÉ—an nan shashashun friends É—in nata da suke zuwa gidan nan ita ba abar a yarda da ita bane, tsab zata iya cutar da Æ´ar mutane, kasan dai babu wata maikaciya a gidan nan da zata yi wa wannan yarinyar irin wannan rauni, dole Ummien ce mana".
Shiru ya yi kamar mai nazarin wani abin. Kamar daga sama idanunsa suka sauƙa a kan Ramish, a hankali ya ga yatsun hannunsa suna motsawa, a lokacin kuma Dr Raj yana ƙoƙarin yiwa Leesharh allura, ai tana jin za'ayi mata ta waro idanunta waje, da a tunaninsu barci ma take yi shiyasa suka tsaya suna hiran Ummie a wajen, ashe basu san ta ji komai ba.
Tana buɗe idanu sai kan alluran hannun nasa idanunta suka sauƙa. A ɗari ta yunkura zata tashi, dan tana tsoron allura kam sosai.
Da kallon mamaki Dr ya bita tare da daure fuska sosai kamar ba shi ba, dama dan dole Bilal ya sanyasa kula da lafiyarta.
"Gyara na yi maki". A dake ya yi maganar, irin babu wasa a tartare da shi É—in nan.
Jin ya yi magana yasa Bilal dawo da kallonsa a kansu, sai gani ya yi Leesharh ta manne da bango dan bata son ayi mata alluran, ga shi kuma ba zata iya miƙewa ta gudu ba, jikinta dukka tamkar an ɗaure mata shi da igiyoyi.
Motsawa gaɓɓan jikin Ramish suka cigaba da yi, nan take bugawar zuciyarsa ta fara aiki daidai wa dai'da, sautin numfashinsa ya fara dai'daituwa, hakan yasa duk suka kai kallonsu a kansa jin na'urorin dake wajen bed ɗin nasa sun fara ƙara. Cikin zafin nama Bilal ya fara isa wajensa, shi ma Dr ajiye alluran hannunsa ya yi suka nufi ɗan uwansu. Ajiyar zuciya Leesharh ta sauke, dan a tunaninta sun fasa yi mata alluran ne.
Suna isa Dr ya fara aikinsa, shi kuwa Bilal cikin ƙaguwa da tsananin kaunar ɗan uwan nasa ya fara ambatar sunansa a hankali a cikin kunnensa. Kamar daga sama a hankali ya ji Ramish ɗin ya amsa da. "Yes blood".
Wani irin annashuwa ne ya bayyana a saman face É—insu, wani irin sanyi suka ji, tsabar daÉ—i Dr bai san time É—in da ta furta. "Yes, oh my god, Allah Alhamdulillah, Alhamdulillah!".
Shi kam Bilal matsowa ya yi ya rungumi Drn, dan ya rasa ina zai tsoma kansa saboda murna. Sautin muryar Ramish É—in yasa suka raba jikinsu da juna suna sauraron me zai ce dasu. Girgiza kai ya fara yi a hankali, idanunsa a rufe ruf ya fara faÉ—in.
"Bilal don't let this people's to go anywhere, kill them all, the hut me to much.............." Bai ƙarisa maganar ba tari ta kwacemashi wanda ya yi sanadiyar waro idanuwansa da suke kamar wuta waje. A hanzarce ya mayar da idanun ya datsesu, saboda wani irin haske da ya kashe mashi idanu, ya jima idanun a rufe ruf shiyasa, ga idanun sun kumbura sosai sun yi jajir kamar ba waɗan nan idanu kyawawa irin na King ba.
Da sauri suka yi kansa, Dr yana ce mashi ya yi shiru kada ya yi magana, shi kuwa Bilal yana gaya mashi ai bai bar mutanen sun tafi ba, ya kamasu dan haka ya kwantar da hankalinsa ya yi shiru kada ya sake yin magana dan kada ya ja wani ciwon ta tashi kuma.
A hankali ya sake gwada buÉ—e idanun nasa. A wannan karon ma haske ne ta kashe mashi idanun, sai dai bai rufesu ba, ya barsu a buÉ—e har lokacin da haske ya É—an washe, sannan ne ya fara iya ganinsu Bilal É—in.
Yana ɗaura ganinsa a kan Bilal ɗin ya sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, har cikin ransa ya ji wani irin sanyi ta ratsa shi na ganin ɗan uwan nasa, Dr Raj fa shi ne ƙaninsa da suke uwa ɗaya, amma ga dukkan alamu ya fi kaunar Bilal, bai yi farincikin ganin Dr kamar yadda ya ji wani irin sanyi lokacin da ya ɗaura idanun a kan Bilal ba.
Hannunsa dake É—aure da drip ya buÉ—ewa Bilal É—in. Da sauri ya kai hannunsa saman hannun Ramish É—in suka haÉ—a hannu, saman shoulder É—insa Bilal É—in ya damko tare da É—an jijjigasa alamar ya cigaba da kasancewa da jarumtarsa, jinjina kansa Ramish É—in ya yi alamar In Sha Allah jarumta a jininsu take, Dr Raj dai ya zama É—an kallo, ya tsaresu da idanu kawai yana kallonsu.
Ita ma Leesharh tv ta mayar da su, wani irin abu ta ji a kan Ramish ɗin, kura mashi idanun sosai ta yi tana kallon yadda yake magana ƙasa ƙasa da Bilal, wani irin jiri ne ta ji ya wani ɗebeta, ta rasa gane irin wannan wahalallen cakwakiya, kenan shi Ramish yana bala'in kaunar wanda yake neman rayuwarsa fiye da ɗan uwansa da suka fito ciki ɗaya ba tare da saninsa ba? Anya kuwa hakan zai yiwu? Ko da yake mutun fa ko ya mutu sai an ɗauresa, Allah dai yasa mufi karfin zuƙatanmu.
Nan take Dr Raj ya hau kiran ƴan uwansu a waya yana sanar da su ɗan uwansu ya farfaɗo kuma ya farfaɗo ba tare da wata matsala ba, sai dai jikin ne da za'a cigaba da kula da shi har ya ƙara warwarewa. Murna a wajen su Yah Rizwan ba'a magana, Abbie yana jin wannan labarin ya baro office ɗinsa ya dawo gida, kan kace me gida ya cika tab da family, su uncle Rahab duk sun zo, Sharifat sai kuka murna ake yi masoyi ya farfaɗo.