← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 211

Sashe 194

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rashin sani ya fi dare duhu, Aneesa bata san cewa ita Chuchu ba Rizwan take so ba Jawad take so, amma ta sadaukar da soyayyar da take yi mashi ga ƴar uwar tata, ita ma Chuchun bata san Aneesa na mutuwar sonsa ba. Ita kuma Fanan bata san Jaish yana can yana shuka flowers ɗinsa da ƴar matarsa ba, har ma flowers da yake shukawa sun kusa girma su yi su haifi ƴaƴa kun gane ai?. Ita kuma Auta bata san cewa ita ma Hoorain yana mutuwar sonta ba, nata son ma ai wasa ne a gaban nasa, dik dai suna cikin rashin sani bayin Allah, haka zalika iyayen nasu ma suna cikin rashin sani, suna ƙoƙarin kwaɓe abubuwa dik a rashin sani. Komai na ƙoƙarin kwaɓewar da daga baya sai anyi danasani.

Miƙewa Auta ta yi jikinta dik a mace, da kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa. Kayan barci ne a jikinta wando da riga pink color, ta yi matukar kyau, ta ɗaura silk scarves a kanta. Bedroom sillpers ta zura a ƴan kyawawan kafafunta zata nufi waje.

"Ina zaki je Auta?". Cewar gimbiya Chuchu.

"Aunty Chuchu zan je shuka flowers nawa ne". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe kamar zata yi kuka.

ÆŠan zaro idanu Chuchu ta yi, dan tasan wannan kalma ta shuka flowers suna amfani ne da shi idan sun ga masoya, haka suke gulmar Sarina da samarinta a waya, haka suke gulmar King and momma ma, dan tsabar rashin kunya, idan King ya zo part É—in Momma da daddare in dai Auta bata yi barci ba sai ta gudo wajen Chuchu, idan Chuchu ta ce me ya kawota É—akinta a wannan lokacin, sai ta ce daddy ne ya zo suna shuka flowers É—insa mana, wato daddy ne ya zo zuba love da momma, kuma dik kalle kalle fina finan turawa ya lallata Auta da Chuchu har suka yi wa soyayya farin sani haka, har da bashi wani suna wai shi shuka flowers, dik dan kada a gane sun san love kenan, da sun ce shuka flowers wa junansu sun san me suke nufi. Hmmmm wai a haka uncle Jahiz yake cewa Auta da Chuchu basu san komai ba, sai ya samesu a tare suna magana a nan ne zai gane wanene su.

Sai ma idan sun kalli love film, sai su zauna suna faÉ—in haka zasu yi wa mazajensu idan suka yi aure, ba abin da basu sani ba yara biyun nan da kuke gani.

"Auta wani flower kika shuka da har kike zuwa bashi ruwa ni ban sani ba?". Cewar Chuchu. Tana magana yana kara zaro idanunta da suke jajir saboda kukan rashin lafiyar Jawad da take fama da shi.

Wlh Æ´aÆ´an King sun san kan duniya, kai ka ji wai wani flower ta shuka har take zuwa bashi ruwa? Kai jama'a ana abubuwa a RAWANIN ZALINCIN wlh.

"Kai Aunty Chuchu zan gaya maki idan na je na dawo".

Allah sarki Aneesa da Fanan sun yi nisa cikin kogin tunanin masoyansu da suke dakon soyayya basu jin me su Auta suke faɗa, wlh son maso wani akwa wahala matuƙa, su kaɗai suka san raɗaɗin dake a cikim zuƙatansu a halin yanzu, kai Allah dai ka barmu da masu son mu, amma wlh ina tausayawa Fanan da Aneesa, especially ma Fanan..........😥💔

"Dan Allah Auta kada ki tafi ki barni ba tare da kin taimaka mun na gansa ba, in har ban sanyasa a idanuna yau ba zan iya mutuwa kafin da safe". Tana magana idanunta na cikowa da zafafan hawayen da suka fi wuta ƙuna.

Nan take Autar ta ji wani irin muguwar tausayin ƴar uwar tata ya kara kamata, ita ma sai da idanunta suka kawo kwallah, dan tasan zafin so ita ma tun da flowers ɗin Hoorain yana shuke a cikin zuciyarta, sai dai Hoorain ɗin yaki yarda ya rinƙa bawa flowers ɗin ruwa ya ginasa da kalamai masu zafi.

"Aunty Chuchu ba zan bari ki cutu ba, In Sha Allah a daren nan zaki gansa, bari na tuna mafita, idan wani abin ya sameki ni ya zan yi kenan?".

ÆŠan sunkuyar da kai Chuchu ta yi tana kokarin shanye waÉ—an nan zafafan hawayen nata kada su zubo. Wayarta dake gefenta ne ya fara ruri yana neman agaji.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kai kallonta a kan wayar. Yah Rizwan shi ne sunan da bayyana a saman screen É—in.

Da sauri ta yi picking dik dan ta ji a wani hali Jawad yake ciki, tun jiya rabonta da shi. Da kyar ta iya saita nutsuwarta haÉ—e da gyara voice É—inta, a sanyayye ta ce. "Hello Yah Rizwan".

Daga ɗayan ɓangaren ya amsa da. "My Jannaty barka da dare". Yadda ya yi maganar zaka iya fahimtar yana cikin tsananin damuwa matuƙa, da alama jikin Jawad bata yi sauki ba, bawan Allah ya shiga tashin hankali na wuce misali, Allah sarki dik suna kan rashin sani, kuna tunanin da Rizwan yasan dalilin rashin lafiyar ɗan uwansa ko zai mutu ba zai hakura da ita bane? Wlh sai dai sonta ya kashe shi amma tabbas zai hakura ya bar mashi, amma kash ba daman sanin hakan domin kuwa Mammie ta datse dik wannan hanya, ba ta yadda zasu sani sai bayan aure haka ta tsara masu hegiya.

"Yah Rizwan ya jikin Yah Jawad?". Ta faÉ—a waÉ—an nan hawaye suna gangaro mata a guje kamar ruwa ya fasowa kansa hanya.

A hanzarce ta kai hannunta ta toshe bakinta dan kada sautin kukanta ya fita. Da sauri Auta dake tsaye tana kallonta ta koma ta zauna a bakin bed É—in tare da sanya hannu ta fara goge mata hawaye tana girgiza mata kai alamar ta yi shiru.

Sai a lokacin su Fanan suka farga da abin da yake faruwa, a ruÉ—e suka kewayeta suna tambayar ko lafiya take kuka.

Daga ɗayan ɓangaren ya ce. "Jannat jikin ɗan uwana sai dai nace maki Alhamdulillah kawai, dan Allah ki tayani da addu'a, idan wani abin ya same shi bana jin zuciyata zata iya ɗaukar hakan, ba zan iya jurar ganin ko ciwon kansa ba bare har ya kwanta irin wannan ciwo mai tsanani haka da ko motsi baya yi, wlh ji nake kamar ana caka mun wuƙa a kahon zuciya". Ya kai karshen maganar yana huci tare da furzar da iska mai zafin gaske kamar dai iskan bakin mai fama da tsananin zazzaɓi, da alama akwai zazzaɓin a jikinsa bawan Allah.

Ai kasa yi mashi magana ta yi, ta ji batun da ya ƙara ɗaga hankalinta matuƙa, sai take jin kamar ba fa a duniya ta ji wannan zancen ba, a take ta ji ta kasa iya tantance a duniya take ko akasin haka, kanta da ya yi wani irin sara mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wayar ya yi ƙasa zai faɗi ba. Da sauri Auta ta tare wayar tare da katse kiran ta ajiye a gefe.

Hankalinsu idan ya yi miliyan to ya tashi, a ruÉ—e Fanan da Aneesa suke jera mata tambayoyin me yake faruwa ko dai wani ne ya mutu?.

Ta kasa iya buɗan baki ta furta uppan. Suna goge mata hawaye wani yana sake ɓulɓulowa kamar indororon ruwan sama. Auta ce ta riƙo hannunta ta miƙar da ita tsaye, dan ita ce kaɗai tasan matsalar.

"Aunty Fanan, Aunty Aneesa muna zuwa, idan mun dawo zata gaya maku menene yake faruwa, amma dai ku sani ba wani abin bane da ya wuce tana damuwa ne a kan rashin lafiyar Yah Jawad, dan haka kada ku É—aga hankulanku, bari dai mu dawo sai ta gaya maku da bakinta". Tana kai karshen maganar ta ja hannunta suka nufi hanyar fita.

Kafin su Fanan su yi wata magana tuni ta fice da sauri, da alama da gangan ta yi wannan sauri dan kada su dakatar da ita, ta kuwa yi sa'a har ta fita basu kai ga yin magana ba.

Suna kaiwa wajen É—an corridor dake tsakanin room É—in da parlourn sai Auta ta dakata tare da juyowa suna fuskantar juna.

"Aunty Chuchu ki yi shiru ki goge hawayenki, yanzu ki laɓe a nan zan shiga cikin parlourn mu gaisa da su Inno sai nace masu ina zuwa, idan na zo fita zan shammacesu in kashe wutar parlourn, kina ganin duhu ki yi sauri ki fita, bayan minti ɗaya zan sake kunna wutar, da yar dan Allah sai kin kalli Yah Jawad yau.

Zaro idanu Chuchu ta yi, a ruÉ—e ta ce. "Idan suka tuhumeki a kan wani dalili zaki kashe wutan fa me zaki ce? Kin dai san halinsu da bin kokkofi". Da kyar ta iya faÉ—ar hakan saboda kukan da ta sha.

"Ke dai Aunty Chuchuna kada ki damu, na san yadda zan yi da su, ke dai ki tabbatar kina ganin duhu kin laluɓa kin fita da sauri".

Hmmm Auta da ta yi wa King da kansa ma wayo ta je ta kalli Hoorain da daddare waye ba zata yi wa wayo ba? Dik wani fitar sirri dan kada a ganota yarinyar nan ta san hanyar yinsa, dik dan zuwa ganin Hoorain a sace, kunga kuwa ai fin haka ma zata aikata, yaran King dik sun shuka flowers É—insu har suna zuwa bashi ruwa King bai da labari, shi uncle Jahiz ma har da wani cewa basu girma na, bai san manyan Æ´an love bane, sai ranar da dubu ya cika akwai zare idanun kam.

"Tom shikenan Auta ta my lovely baby, Allah ya bar mun ke yar kanwata rabin rai'na ". Yadda take Maganar zai nuna maka tsabar farincikin da take ciki ne yasa har ta ruÉ—e take ta surutai, Allah sarki zata je ta ga flowernta ta zuba mashi ruwa.

Wucewa gaba Auta ta yi tana faÉ—in. "Ke dai yanzu ba lokacin godiya bane, bari idan mun dawo zamu yi murna a tare, yanzu dai ki shirya".

Da okey ta amsa kawai. Da sauri Auta ta fito cikin parlourn. Dattawa kuyangu mata guda biyu ne a cikin parlourn, É—aya tana zaune a saman sofa tana kallon tv, É—ayar kuma tana ta aikin haÉ—e haÉ—en magungunan gyara a cikin kwarya.

"Barkanku da dare Inno mariya". Cewar Auta Æ´ar basaja.
Chapter 194 · 0% Book details