← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 211

Sashe 177

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan hoto da kika ga na ajiye a yanzu tabbas shi ne wan da ya mun wannan ciki, shi ne uban cikina, and then kamar yadda na faÉ—a maku ranar da ke da maman Hanif a parlon to gaskiya ne, sai dai ban faÉ—awa maman Hanif cewa bayan mun yi rayuwa da shi a gida daga ni sai shi ya kaini wani gida wanda ina zaton familynsa ne a ciki ba, ni ban san su waye su ba, amma a yadda naga hotonsa da wani babban mutun yana manne a jikin bangon parlonsu to ina zaton daddynsa ne, dan sun yi kama da na jikin hoton sosai, ni kaina na yi mamakin ganin yana mugun kama da Jahiz É—inku, ina ji a jikina ba Jahiz bane, amma idanuna sun gaza iya karyata mun hakan.....".

Shiru ta ɗan dakata tana cigaba da goge kwallan dake zubo mata, abu ɗaya take tunawa ya sanyata irin wannan kukan, ba komai bane kuma face disvirjin ɗinta da ya yi, ba zata taɓa manta wannan azaban da ta sha ba, shiyasa a dik lokacin da ta tunasa sai ta yi kuka dan sai ta tuna wannan ranan.

"Aunty Khadijah da ya kaiki gidan me ya faru?". Zee da hawaye suka gama wanke mata fuska ne ta jefa mata wannan tambayar.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da É—an yin gyaran murya dan ta samu damar cigaba da yin magana da kyau.

"Akwai wata mata wadda ita ce ya sanya ta zubar mun da cikina, ina tunanin mom ɗinsa ce, basa kama da ita kam sam, amma a nawa tunanin ne mom ɗinsa ce, baturiya ce fara tas da ita, ita ta kawo likitoci kala daban daban suka yi yunkurin zubar mun da cikin, bana son in gaya maki irin azaban da na sha, bana son ki ji bakar wahalar da na ɗanɗana a sanadin ƙoƙarin zubar da wannan ciki da wannan mata ta yi mun........."

Dakatawa ta yi a wannan gaɓa ta rushe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Matsowa kusa da ita sosai Zee ta yi, ita ma tana kukan amma hakan bai hanata ta rarrashi ƴar uwar tata ba.

"Zee dan Allah ki barni na yi kuka sosai, zuciyata zafi take yi mun, idan ban yi kuka ba zata iya buga mun". Ta yi maganar cikin muryar kuka da yake fita haɗe da shessheƙa.

"A'a Aunty Khadijah, ba dan ni ba, ba dan kowa ba, dan babynmu dan Allah ki yi shiru kuma ki daina damuwa kin ji? Wlh tallahi ina son koma menene a cikin cikin nan naki, ina kaunarsa fiye da kaina, dan Allah kada ki yi sanadiyar salwartansa".

Still tana kukan ta ce. "Zee tun da kika ga dik wannan wahala da na sha, dik wannan azaban da na É—anÉ—ana, dik waÉ—an nan turawan likitoci da aka kira domin cire wannan cikin sun kasa iya fitar da shi, har jini na zubar amma cikin bai fita ba, daga nan yakamata ki san cewa ta Allah bata mutun ba, ba a haifi wanda Allah zai ce e shi kuma ya ce a'a ta yi wu ba, ba haifa ba kuma ba za'a haifa ba, Allah ya ce É—ana sai ya zo duniya, ba'a yi abin da zai tare shi ya hanasa zuwa ba, dan haka ki kwantar da hankalinki, idan namiji ne a cikina to Ahmad sai ya zo duniya, idan macece kuma to Zainab sai ta zo duniya da izinin Allah, kuma wlh sai Allah ya saka mun ya kuma nunawa duniya waye su". Ta kai karshen maganar tana kifa kanta a saman gwiwonta saboda wani irin kululun bakincikin da ya tokare ta.

(My peoples kun san me nake tunani?🤔😅 Idan da gaske cikin uncle Jahiz ɗinmu ne me kuke tunanin Akka zata yi ma ɗan autan nan nata?😅 Ni dai ina tunanin yaseen sai ta yanke bananarsa🤣🤭 a yanketa kawai muga ta tsiya ato🤸)

"Haka ne Aunty Khadijah, amma dan Allah ki daina damuwa kin ji?".

"Hmmmm Zee dole na yi bakinciki na kuma damu, sun cutar dani sun kuma wahalar da ni, mom É—insa ta azabtar dani wajen yunkurin cire mun ciki, tasa aka daina bani abinci a gidan, ta tsaneni kamar ta kasheni, kuma dik abin da take yi ba mai ce mata uppan a cikin gidan, shi ma yana sane da komai amma bai tanka ba saboda baya son na haifa mashi cikin, baya son É—an shege".

"To Aunty Khadijah kin manta da akwai Allah ne da har kike ɓarnar hawayenki a banza?".

Kai ta É—ago tare da fara girgizawa. "Ban manta ba Zee, amma kukance ta gaza dakatawa, na gaza iya mantawa da su a rayuwata!!".

"To amma ya aka yi kika samu hotonsa mai kyau haka?". Zee sarkin tambaya da son ta ji komai dallah dallah.

"Ba iya hoto É—aya nake da shi ba, ina da su dayawa, kuma a É—akinsa na É—aukesu". Ta bata amsa tana aikin goge hawayen da suka ki dakatawa daga zuban da suke yi.

Janyo jakar Zee ta yi tare da buɗesa, ciro hotunan ta yi wajen kala shidda, dik hotunan sanye yake da kayan ƴan kwallo a jikinsa, guda biyu ne kawai yake sanye da kananan kaya. Zuba mashi idanu Zee ta yi tana mamakin irin kyansa da zubin kyakkyawar halittarsa, a yadda ta ga face ɗinsa tabbas za'ayi mutun mafaɗaci mai kuma kafiyar balain, sai dai kuma a yadda yake ɗin nan da wuya ya yi rashin imani har haka, to meyasa yake son zubar da cikin nasa? Yasan baya son cikin ya bari ta ɗauka? A jikin ɗayan hoton nasa ga shi nan riƙe da wani ɗan matashin yaro da ba zai wuci 7 years ba mai balain kama da shi, ko dai shi ma ɗan sa ne?. Ta jefawa kanta tambaya.

Da wuya ma in wajen iyayensa ya kaita! Kila wani waje ya kaita dan a zubar mata da cikin, idan baya son asirinsa ya tunu to dama meyasa bai ɗauki matakin hana cikin shiga ba?! Kai gaskiya akwai matsala, kila labarin nan sun yi wa Khadijah hauhauwa ne yasa watakila bata fahimci ainahin kan abubuwan da suka faru ba, ita dai Zee a nata tunani dole akwai abin da ya tsaɓa ba daidai ba a cikin wannan al'amari. Amma kuma tasan yanzu ko ta gayawa Khadija ba yarda da ita zata yi ba, ba zata taɓa yarda akwai abin da ya saɓa ba, dan ta yi nisa a son ɗaukar fansa, wutar fansa ce kawai take ruruwa a cikin zuciyarta.

Wai taya ma aka yi suka zo Abuja? Mu koma baya na kwanaki da suka suÉ—e. Kamar da na gaya maku wannan restaurant É—in yana ta farko farkon shigowa cikin garin Abuja ne.

To wannan mota da ta É—aukesu dai garin Abuja ta nufa da su, sai dai bai kai ga shiga cikin gari ba cikinsa ya fara murÉ—a mashi, hakan yasa ya yi parking a bakin hanya ya fito daga cikin motar, cikin daji ya nufa dan a tunaninsa bayan gari zai yi, bai san cewa mai sama ne ya yi kira ba, kuma dole a amsa.

Allah mai iko mai yin yadda ya so, dik abin da zai yi kuma baya shawara da kowa, zai karɓi rayuwar bawa a lokacin da ya so, idan ya ga dama a rana ɗaya zai iya bawa uwa wani yaron ya kuma karɓi wani daga cikin ƴaƴan nata, mutuwa bata sallama, wani ma yana cin abinci yake tafiya, akoma ina a koma yaushe mu rinƙa tunanin ba zamu bar wajen da muke a raye ba, yawan tunan mutuwa zai sa mu yi aikin alkhairi sosai, Allah baya kuskure, komai ya yi dai'dai ne, mutuwa baya sallama.

Shi dai wannan bawan Allah yana shiga cikin daji da nufin ya yi bayan gari kawai rai ta yi halinta, babu ciwo babu komai, su Khadijah kuwa ya barsu cikin mota suna ta zuba barci, kafin ya fita motar kuma dama sai da ya kulle ko'ina, rashin samun wadatatcen iskan numfashin ya farkar da su daga barci, dama kuma da alama maganin da aka shaƙa masu ɗin karfinsa ya kai time na karewa.

Hakan yasa suka farka, sai suka rasa ta yadda zasu yi su fita, kun san rashin samu iska ba karamin cutar da rai yake yi ba, dan haka sai suka fara rasa ina zasu sanya ransu, suka fara neman mafita ido rufe.

Wani abin suka samu suka fara bubbuga glass ɗin motar da shi, amma abin ya gaza fasa glass ɗin. In short dai har Zee ta fara galabaita tana ƙoƙarin sumewa, ita kuma Khadija da alama jinin cikin jikinta yana da karfin da yasa ta iya juriya fiye da Zee.

A takaice dai suna cikin halin mutuwa ko rayuwa Allah ya kaÉ—o masu wani bafulati mai kiwon shanu, Allah yasa kuma ya zo ya jingina da jikin motar tasu yana jiran dabobin nasa su gama sallaka titin. Dama ance mutuwar wani tashin wani.

Bubbuga glass É—in da karfi Khadija ta yi hakan yasa ya ja hankalinsa a in da ya juyo garesu, da alama ya saba ganin irin haka, dan kuwa yana ganinsu bai yi mamaki ba, bai kuma É—aga hankalinsa ba, sai ma É—aga sandarsa da ya yi ya makawa glass É—in motar ta gaba, nan take glass É—in ta tarwatse, dik yadda aka yi ya saba da irin hakan.

Yana fasa masu glass ɗin iska ya risƙesu suka fara jan numfashi da karfi karfi. Bai bar wajen ba har sai da ya taimaka masu suka fito daga cikin motar, sai dai kash baya jin Hausa su kuma basa jin fillanci, hakan yasa basu iya sanin komai dan gane da shi ba, shi ma kuma bai iya sanin komai dangane da yadda aka yi suka zo nan ba, ya so ya gaya masu cewa ai irin wannan satar mutane suke yi su shigar da su kudu su sayar da su, amma sai ya rasa ta ina zai gaya masu su yi taka tsantsan, sun yi sa'a ba'a kai ga fita arewa gabaɗaya da su ba.
Chapter 177 · 0% Book details