← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 211

Sashe 123

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi shi ma ya yi tare da miƙewa tsaye. "Idan na biye maka tabbas ba zan yi abin da zan yi ba, dama kewarka yasa na fara zuwa dubaka". Ya yi maganar cikin tsantsar kaunar ɗan uwan nasa.

Miƙewa Jawad ɗin ma ya yi tare da miƙa mashi hannu suka yi musabaha, sannan Rizwan ɗin ya nufi waje, Allah ya tsare ya yi mashi, da amin ya amsa tare da ficewa waje.

Komawa ya yi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Duk abin da suka faÉ—a tana jinsu, haka kawai ta ji Yah Rizwan É—in nan ya kara burgeta saboda yadda yake nuna kauna da kulawa ga Yah Jawad É—inta...... To fah e lallai Chuchu ta yi nisa.

Tana tsaka da tunani sai ji ta yi ya shafa face É—inta tare da cewa. "What are u thinking?".

Ƴar firgita ta yi, da sauri ta ɗago da kallonta izuwa kansa, lokacin guda suka sakarwa da juna cool murmushi, sai kuma ta ɗan shagwaɓe fuska. "Yah Jawad ni matsa na fito zafi nake ji".

Ƙasa ƙasa ya furta. "Da gaske?".

Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e da gaske. A maimaikon ya matsa ɗin sai ya kara matsowa kusa da ita. Ƙara turo baki ta yi. "Yah Jawad zafi fa nace maka nake ji".

Kumatunta ya sumbata tare da ɗan yin baya ya miƙar da jikin nasa, ya koma ya jingina da jikin chair ɗin nasa.

Fitowa ta yi tana faɗin. "Sai na gayawa Yah Rizwan cewa lokacin da ya zo office naka ka sakani ƙasan table wai dan kada ya ganni, bari kaga mu koma gida". Tana magana tana kwaɓe fuska irin ita a dole zata yi mashi barazanar nan.

Riƙota ya yi, da murya kamar mai jin barci ya fara faɗin. "Da gaske zaki iya tona mun asiri?".

Kai ta gyaÉ—a alamar e. "Okey bari dai na yi maki wani abin ma dan idan mun koma ki haÉ—a har da shi ki faÉ—a mashi".

"Wani abin kuma?". Ta tambaya tana É—an zaro idanu, addu'a take Allah yasa ba zaneta zai yi ba.

Matso da face É—insa dab da nata ya yi, kamar zai haÉ—e fuskokinsu waje guda, in a whisper ya ce. "Rufe idanunki ki gani".

ÆŠan siririn haÉ—aÉ—É—en hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Yah Jawad to wai ina budurwar taka ne?".

Yadda kuka san wanda yake cikin maye haka ya zama, kamar ya sha wine. A kasalance ya ce. "Jannat wai meyasa kika damu da zancen budurwa ta É—in nan ne? Ko dai kishina kike ji?".

Da sauri ta girgiza kai. "A'a ni bana kishi, kawai ina son in ganta ta fini kyau ne ko na fita?".

"Are you sure that's all?". A hanzarce ta gyaÉ—a kai.

"Okey yanzu kuwa ba sai anjuma ba zan gaya maki wacece ita, amma kafin nan rufe idanunki".

Kamar dai bata yarda da shi ba, kamar tana ɗan tsoron wani abin haka ta ɗan datse idanun nata. Kara matso da face ɗinsa dab da tata ya haɗesu, suna iya jiyo sautin numfashin juna suna kuma iya shaƙa. A hankali ya........

___________________🔥

Sautin tashin kiɗa ne ya karaɗe gabaɗaya kingdom ɗin, an gama shirya komai, an ƙawata komai yadda ya dace, dukiya ta yi kuka a wannan party da aka shirya, daga walima mummy ta mayar da shi yazama party, dan an haɗa ne da na murnar cin nasara da suka yi a yaki.

Sai neman Chuchu Auta take yi bata ganta ba, dukka princess sun ci kwalliya na gani a sake kallah, sun fito reras da su, komai cikin tsari da nuna tsantsar mulki ake gudanar da shi, zakarun mayaƙan da suka fi kowa a cikin kingdom ɗin ne suka kewaye hall ɗin da ake gudanar da partyn, Hoorain yana tsaye daga bakin kofa shigowa cikin tsantsar jarumta,

Auta dake zaune saman stage, ta tsantsara kwalliya, ta fito a ainahin jinin sarautarta kuma princess, in ma mace ko namiji duk wanda ya kalleta sai ya juyo ya sake kallonta, kai kace ba ita bace, tana zaune kusa da Guyson É—inta, ga Gimbiya Aneesa na zaune a gefenta.

A gabaÉ—aya taron jama'ar dake cikin hall É—in nan ba wanda ta kurawa idanu sai shi, ga Guyson É—in nata ma yau yana kusa da ita yadda take damunsa a waya a kan ya dawo amma bata mayar da hankali a kansa ba.

So take ta karɓi single ɗinsa da ya ɗaure mata hannu da shi ranar, amma bata san ta ya zata sake samun damar keɓewa da shi su biyu a keɓaɓɓen waje ba, ranar ma Allah ya tsare zasu samu wannan damar ne, tana da buƙatar sake haɗuwar nasu kuma, to me yakamata ta yi? Dole ta nemowa kanta mafita.

Shi ma ɗin dai tun da ya harɗe hannayensa a saman lion chest ɗin nan nasa ita ya zubawa idanu, ba zaka taɓa iya famintar cewa yana kallonta ba har sai idan kana tare kusa sosai da shi.

Baiwar Allah yau ko damar yi mashi magana bata da shi, idan tana son zamansa lafiya to kada ta kula shi, dan kuwa dai yau idan ta ce zata kula shi zata ja mashi wani bala'in ne, barema yadda uncle Taheer yake wajen ai ba zai bari ba.

Tunanin yadda zata yi ta fara yi. Can sai wani tunani ya faɗo mata. Da sauri ta miƙe tsaye, sai sakin wani irin murmushi take yi ta samu mafita.

"Where are you going?". Guyson da wanka ta bi jiki ne ya yi magana, guy É—in nan yau haÉ—uwa ta musamman ya yi, shigar henley shirt and cargo trouser ya yi, kaya sun bi jiki Masha Allah.

"Yah Omar zan je duba Aunty Chuchu ne, kaga bata zo ba".

ÆŠan wawwaigawa ya yi domin duba Chuchun, a nan yaga tabbas bata a wajen. "Okey sit down let me look at her". Ya faÉ—a a tsanake.

Tamkar zata sa ihu ta ce. "No Yah Omar, ka zauna kawai kada ka wahala bari ni na dubata by my self ka ji?".

Da yake basa son ɓacin ran juna sai ya yi na'am da zancen nata, amma sai ya ce ta samu ɗan rakiya.

Rai a farance ta amsa da. "Already ni ina da É—an rakiya ai, Hoorain zai rakani".

Ya yi mamakin ganin karuwar farinciki a tattare da ita lokaci guda, amma bai kawo komai a ransa ba ya amsa mata da to kada ta jima.

A hanzarce ta nufi step na sauka daga wajen, da ido uncle Taheer dake zaune kusa da mama suna hira ƙasa ƙasa ya bita, yadda kuka san son Autar nan yake, ya cika nuna kishi da kulawa a kanta, da yanzu zai ganta a tare da Hoorain ba ƙaramin faɗa zai yi mata ba, kuma zai ce sai ya hukunta Hoorain ɗin, yana ɗaya daga cikin waɗan da suka hanata yiwa Hoorain magana bayan Jaish kenan.

Miƙewa ya yi da nufin ya bita dan ya ji ina zata je ƴan uwa dukka suna nan? A lokacin King bai kai ga shigowa cikin wajen ba, babu tabbacin ma zai halarci taron, dan yana can suna zama ta tattaunawa da dattawan fada, duk zama ce a kan Spender, duk wani amintaccen dattijo na fadan ya halarci tattaunawar, commander Zafar kam shi ne ma a kan gaba.

"Koma ka zauna ai bamu gama maganar ba". Cewar mama.

Ba dan ya so ba ya koma ya zauna dan su kammala maganar, ya so bin bayanta yaga ina zata je sai ya rakata, amma ya kudurci niyar in har bata dawo ba suka kammala magana sai ya bi bayanta.

Ita kuwa cikin nutsuwa tana taku wanda ya ja hankulan jama'a da dama a kanta, da yake takalma high ta sanya, kuma ƙasar wajen tiles ne, sai yake bada sauti duk in ta yi one step, ga manya manyan ƴaƴan sarakuna, ƴaƴan shuwagabannin ƙasashe da dama, baki dai iya baki sun halarci wannan taro na mummy.

Yadda take tafiya suna binta da kallo hakan ba ƙaramin ƙona ran Hoorain ya yi ba, ya ji babu daɗi, haushin takalmar nata ne ma suka kama shi, kamar ya je ya ciresu ya jefar, amma bai isa ba, bashi da damar yin hakan.

Ya luluƙa duniyar tunanin haɗe da bakincikin yadda maza suke binta da kallo, bai ankara ba sai jin sautin ɗan siririn muryarta ya yi tana faɗin. "Hoorain mu je ka rakani garden ɗin babban yaya". Ta kai karshen maganar tare da wucewa gaba.

Bayanta ya bi, yana taku cike da tsantsar jarumta sosai.

Suna fita daga hall É—in ta fara faÉ—in. "Hoorain yanzu haka zamu iya samun gonar daddy a buÉ—e?".

Yadda suke tafiya gwanin birgewa, gata Æ´ar karama a gabansa, dan Hoorain yana da tsawo da cikar halitta sosai, ya tasata gaba, ita kuma ta ja mashi tafiya irin na mata, dan kuwa yadda take tafiya a hankali hankali sai ya ji kamar ya É—agata sama kawai sai ya fi mashi, yana da zafin nama, ba zai iya jurar irin wannan tafiya tata ba, tafiyar tata kayan haushi ne a wajensa, dan bata sauri.

Shiru ya yi tamkar ba zai amsa ba, sai da ta dakata daga tafiyar da take yi ta juyo da kallonta a kansa, sannan ne ya É—an kawar da kansa tare da buÉ—e baki zai amsa mata kenan suka ji sallamar wani ta bayansu.

A tare suka kai kallonsu kansa. Wani matashin balarabe ne da ba zai wuci 23 years ba, É—a ne ga sarki Egypt.

Hoorain ne ya amsa mashi sallamar. Wani irin ƙasƙantacen kallo ya wurgawa Hoorain ɗin, a gadarance ya ce. "Bada kai nake yi ba malam bodyguard, ko an gaya maka prince kamar ni ina magana da irinku ne? Ni idan ina waje ma waɗan da suka fiku ma basa magana bare ire irenka".

Ɗaure fuska sosai ta yi, maganar ta mata zafi, ta ji babu daɗi sosai, a kan me wannan ƙazamin zai ce wa Hoorain ɗinta bodyguard ya kuma yi mashi magana a gatse haka?.

Ƙarisowa wajensu ya yi yana sakin murmushi, ita ya nufa da nufin ya yi mata magana. Gabansa Hoorain ɗin ya tare ba tare da ya yi mashi magana ba, ya dai hanasa isa gareta ne kawai.
Chapter 123 · 0% Book details