Sashe 205
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ya fara girgiza kai yana faÉ—in. "A'a ranki ya daÉ—e, tsabar girman Zunaira a cikin zuciyata yasa nike tunanin ta ina zan fara bayyanata, girmanta ya wuci tunanin dik mai tunani, amma in ba damuwa zan fi so mu haÉ—u sai na bayyana maki ya take ko?".
Wayyo soyayya, wani irin daɗin da bata taɓa jin irinsa bane ta ji ya ziyarceta, cikin sanyin murya ta ce. "Da gaske Hoorain ina da girma da kima a cikin zuciyarka?".
Kai ya jinjina haÉ—e da faÉ—in. "Sosai kuma, fiye da tunaninki, baki ma ya yi kaÉ—an ya zayyana girmanki, sai dai kawai na faÉ—i iya abin da zan iya faÉ—a na bar sauran".
Bata san lokacin da idanunta suka ciko da kwallah ba, miƙewa tsaye ta yi, a hanzarce ta fara ƙoƙarin danne hawayen firincikin nata, ƙasa ƙasa ta ce. "Hoorain mu haɗu a bayan side ɗin uncle Abbas, na tabbata babu mutane a wajen kuma babu wanda zai ganmu ko yasan muna tare a wajen".
Cike da farincikin hakan ya amsa da to, sannan ya miƙe da sauri ya sauko ƙasa daga saman gadon. Hular kayan yakinsa ya ɗauka ya sanya tare da ɗaukar wayarta. Ita kuma ta katse kiran ta nufi waje da sauri, yau ranta fes Hoorain ya ce tana da girma da kima a idanunsa, wannan ma bai bayyana mata cewa yana sonta ba, idan ta ji haka ya kenan?.
Kai tsaye bayan side na uncle Abbas ta nufa, dik wanda ya ga face É—inta sai ya tabbatar da yau tana cikin farinciki na musamman, ta baro su mama suna ta kai ruwa rana a kan dole fa sai mummy ta yarda cewa Æ´arta MieMie azzaluma ce kuma ba tsakani da Allah take son su Aneesa ba, tana nuna banbanci, ita kuma mummy dik hakurinta yau sai da ta yi faÉ—a, ta ce wlh MieMie ba muguwa bace, ku kun san mama fa tsabar masifa ce ta yi mata yawa da shegen son rashin zaman lafiya, amma Aunty MieMie ba munafuka bace.
________________________________
Ta rigasa ƙarisawa wajen, dan haka tana zuwa sai ta tsaya tare da harɗe hannayenta a saman kirjinta tana jiran isowarsa, dik ta zaƙu da ya iso suga juna a cikin ido.
Ga wajen babu kowa, very clear, silent and ventilation, ba wanda yake zuwa ta wajen ma, dan ba zaka taɓa tunanin akwai wajen tsayawa a yi hira a nan ba.
Cike da jarumta yake takowa ya nufo wajen, tun daga nesa ta hangosa yana nufota, wani irin sanyi take ji yana ta kara ratsa mata zuciya, sai ta ji kamar ta ruga ta je ta rungumesa su ƙariso a tare. Amma sai ta danne ta zuba mashi ido yana tahowa.
A gabanta ya kariso ya tsaya, cikin girmamawa ya ce. "Sannunki da isowa ranki ya daÉ—e".
Fuska a ɗauke da ƙayatattcen murmushi ta amsa da. "Yauwa kai ma sannunka da zuwa".
Jinjina kai ya yi yana ta kallonta kamar zai cinyeta da ido. Cike da zaƙuwa ta katse masu shirun da suka yi da cewa. "Faɗa mun ya ka ɗauki Zunaira a cikin zuciyarka".
Nisawa ya yi, haƙiƙa ya ga zaƙuwa da son jin amsarsa a cikin idanunta, murmushi da take saki yasa ya ji wani abin a ransa tamkar ya fasa abin da ya yi niya, ya ji tausayin innocent face ɗinta kaɗan, yarinya yar baruwanta mai farar zuciya.
A hankali ya tako two step ya matso kusa dab da ita sosai kamar zai rungumuta, har sai da abin ya É—an bata mamaki.
Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Yadda na ɗauki Zunaira a cikin zuciyata shi ne in ɗauki fansa a kanta, in kuma kasheta har lahira!!,". Tashin hankali!!.
Yana kai karshen maganar ya sa hannu ya janyota jikinsa tare da rufe mata bakinta da hannunsa ɗaya, tana ƙoƙarin ce mashi bata gane bane ya janyo waist ɗinta ta faɗa jikin nasa, zaro idanu ta yi ba halin ta yi magana dan ya rufe mata baki, ƙoƙarin kwatar kanta ta fara yi dan ta tsorata, amma ina ta kasa.
Matsawa da iya ya yi a in da ya mannata da jikin last wall na uncle Abbas, ya matse mata baki sosai ya haɗeta da bangon da karfi, sannan ya zaro wani ɗan madaidaicin wuƙa daga waist ɗinsa, babu tausayi babu imani ya caka mata a cikinta, ya kuma kara mannata da bangon da karfi dan ya ji daɗi wukar ta shiga cikinta sosai, ya toshe mata baki da kyau ta yadda wane ita ta iya fitar da komai kanƙantar sauti daga bakinta.
Zaro idanu ta yi tana kallonsa har cikin ido, while shi ma kallonta yake yi har cikin ido babu ko kyaftawa. Nan take idanunta suka rikiɗe suka yi jajir kamar jini, wasu irin hawaye masu zafi kamar wuta ne suka fara bin ƙuncinta, dik jikinta ɓari yake yi, da alama ba ƙaramar azaba take ji ba, dan daga yanayin hawayen dake fita daga idanunta sai ya ɗaga hankalin mutun.
Babu ko É—igon tausayi a idanunsa, yana kallon cikin idonta yasa hannun ya kara murza wukar a cikinta da kyau ta yadda zata kara shan azaba kafin rai ya yi halinsa. Kamar yadda yake murza wukar a cikinta haka yake kara matse mata baki haÉ—e da matseta a bangon............Tashin hankali, innalilahi wa inna ilahir rajiun. For what reason Hoorain zai kashe Auta? Meta yi mashi? Fansar wa zai É—auka a kanta? Laifin me ta yi mashi da har zai É—auki fansa?.
Ko tausayinta bai ji ba ya cigaba da matseta tun tana iya fitar da numfashi kaÉ—an kaÉ—an har sautin numfashin ya daina fita daga kofofin hancinta, idanunta dake tsaye cikin nasa ne suka fara rufewa a hankali hankali har suka rufe gabaÉ—aya, nan take jikinta dikka ya saki alamar rai ya yi halinsa, innalilahi wa inna ilahir rajiun.
Ganin ta mutu da gaske ne yasa ya saki bakin nata tare da sanya hannu ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa, jini ne yake zuba daga jikinta tamkar ruwa ya faso hanya, ga kayan jikinta white color ne hakan ya yi sanadiyar bayyanar jinin sosai.
Wani É—an siririn hanya dake ta wajen ya bi da ita, da yake in baku manta ba na gaya maku yasan dik wata hanyar sirri dake cikin masarautar, hakan yasa ya fita da ita ta kofar da babu wanda ya gansa.
Dik in da ya wuce jininta ne yake ta zuba, hanyar da ya bi ya fita kuma babu wanda yake zuwa ta wajen, ba zama ka taɓa zaton da akwai kofa a can ba, Allah sarki King yana can yana fama da jama'a an kashe mashi bugun zuciyarsa a nan bai sani ba.
Amma batu na gaskiya Hoorain ya cuci Auta, ina da tabbacin da tana raye sai ta yi fatan da wani ne ya kasheta ba shi ba sai ya fi mata daɗi, na tabbata ba zata ji zafin wukar da ya caka mata har ta mutun nan ba kamar yadda zata ji zafin kasancewar shi ya yi mata hakan, tana ganin cikin kwanciyar idanunsa har ya yi halinsa, kai abin ya yi muni over, mutumin da take mutuwar so fa? Innalilahi wa Inna ilahir rajiun, ya ta ji a ranta lokacin da ya caka mata wannan wuƙa?.............I cant stop my tears wlh, abin ya taɓa zuciyata matuƙa.
Cikin daji ya kutsa da gawarta, babu ko tunanin ya Æ´an uwanta zasu ji? Ya iyayenta zasu ji? Ya Chuchu zata ji? Bare ma Guyson ya zai ji a ransa bawan Allah?
Haka ya bar cikin mutane, ya yi nisa da in da za'a iya jin ɗuriar mutane ma, sannan ya samu kogi ya jefa gawar tata a ciki, ya cire kayan jikinsa ya wanke jininta da ya taɓa shi gabaɗaya a wajen, sannan ya shanyasu, sai da suka bushe ya mayar jikinsa ya kuma koma cikin kingdom of power, da alama fa Hoorain he come for taking revenge ne or something like that.
Baku tunanin idan Hoorain ya aikata hakan kenan commander Zafar ma amanarsu King yake ci tun da dai Hoorain É—ansa ne? Yanzu lokacin gwabzawa ne, yanzu fa zamu shiga ainahin cakwakiyar, kada ku bari book 3 ya wuceku, a nan zamu damalmale dik wani rikita rikita da cakwakiya.
Yana dawowa cikin masarautar ya koma cikin É—akinsa ya kwanta tamkar bai fita ko'ina ba, zuciyarsa fes, sai farinciki yake yi da alama burinsa na farko ya cika.
Ni ce dai princess Teema taku ta amana mai abin ban mamaki, yanzu zamu fara buɗe babin surprise, zan bawa kwakwalenku caji fa..........😂
_______________🌹💘________________
A can cikin gida kuwa, sai hidima ake yi, Chuchu dake kwance a saman gadon Akka ta ci kuka har ta ƙoshi ne ta ji wayarta dake kusa da ita ya yi kara alamar shigowar sako. Akka ta rarrasheta har ta gaji amma taki yin shiru, kunsan yanzu ba lafiya ce da Akka ba, so komai a hankali take binsa, da taga Chuchu taki ta yi shiru ne sai ta ce to bari ta je ta kira King ko mummyn Chuchun su zo zu rarrasheta kila zata yi shiru, shi ne ta fita.
Kamar ba zata duba wayar ba sai kuma ta jawosa, ganin sunan Auta a saman screen É—in wayar ta turo sakon ne yasa ta buÉ—e tana cigaba da hawaye.
Da kyar ma ta iya cire password na wayar ta fara karanta saƙon kamar haka.
"Aunty Chuchu ki zo ki sameni a wajen back side na uncle Abbas akwai maganar da zamu yi".
Shi ne abin da aka rubuta a sakon. Kai my people's Auta kuma? Da ni da ku dai mun san Auta ta mutu ko ba haka ba? Kuma mun san wayarta baya a hannunta time da Hoorain ya kasheta, wayar tana hannunsa, kenan shi ya rubutawa Chuchu sako ko waye? In shi ne me zai yi wa Chuchu ɗin da ya buƙaci yana son ganinta? Tashin hankali kenan! Ko ita ma kasheta yake son yi?.