← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 211

Sashe 62

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shigowa ɗaya daga cikin bodyguards ɗin dake wajen ne ya janyo mashi chair baya ya zauna. Shirye yake cikin wandon jeans white color, rigar jikinsa round neck t-shirt ce milk color, kasancewar akwai sanyi matuƙa sai ya ɗaura wata haɗaɗɗiyar white jacket, ya sanya hular jacket ɗin a kansa, kyawawan fararen ƙafafunsa suna cikin black socks and luxury booth mai kyau fari, wuyarsa da wani ɗan siririn chain mai bala'in tsada, hannayensa ɗaya ɗaure yake da danƙareren agogo diamond, ɗayan kuma ɗaure yake da chains na hannu na zallar madarar zinari masu bala'in tsada, kai guy ɗin nan ɗan wanka ne na bugawa a jarida, akwai iya ɗaukar wanka ga shegen tsabta kamar me, ya haɗu iya haɗuwa. Kara ɗaure tiger face ɗin nan nasa ya yi kafin ya ɗan motsa lips ɗinsa a hankali furta. "Good morning mum".

Ta tsare shi da kallo kamar zata mayar da shi cikin cikinta saboda tsananin so da kauna, kai daga ganin yadda take kallonsa zaka san tana bala'in kaunar É—an nata fiye da tunaninku.

"Morning my baby, how was your night?".

Shiru ya yi bai sake amsawa ba. Umarni dad ya bawa bodyguards a kan su zuba mashi abinci. Abincin gidan nan fa idan aka girka shi kafin a kawo shi saman dining table sai an yi scanning ɗinsa, sai na'ura ta tace shi an tabbatar babu wani abin cutarwa a cikinsa, duk dan saboda tsaro, ga shi abincin different kala suke dafawa, sai ayi girki sama da kala 10 lokaci guda........ Ni kam nace koma me zaku yi da zarar wa'adin da Allah ya ɗebawa bawa ya cika dai mutuwa dole ce babu tantama kuma babu wanda ya isa yasa a fasa mutuwa.......... Irin wannan tsaro haka! Dama kunsan shuwagabannin ƙasa fa haka suke, komai nasu daban ne, komai zasu ci kuma sai an bincikesa tsab.

Hannu ɗaya ya ɗaga masu alamar baya buƙatar cin komai tare da miƙe tsaye. Wata black zazzafar luxury glass ya ciro daga aljihunsa ya sanya a idanunsa, nan take ya kara wani masifaffen kyau.

Tun da ya shigo wajen Heleena ta tsare shi da ido, da alama tana tsoronsa sosai, dan yadda ta zauna ta nutsu daga jin kamshin perfume ɗinsa ya nuna basa shiri sam sam, dan kuwa ita ɗin bata da kunya ko kaɗan, idan ta tashi rashin kunyarta bata ragawa kowa a cikin gidan sai shi ɗin, idanunta a tsai tsaye a tsakar ka na rashin kunya, ko daddy bata raga mashi, duk abin da ya zo bakinta take faɗa masu ba tace magana, shi kaɗai take mahaukacin tsoro, kuma tun da yake da ita sau ɗaya ya taɓa dallah mata wani marin da yasa sai da ta sume aka kaita gadon asibiti, daga nan take bala'in tsoron ma su haɗa hanya, dan kuwa ya sauke mata aljanun iskancin da suke kanta na rashin kunya, duk abin da take yi idan ta gansa zata bari ta nutsu sai ya wuce.

Mum ce ta ce ina zai je bai yi breakfast ba?. A takaice ya ce mata yana da meeting ne da wasu yaransa. Daga haka ya sanya kai zai wuce. Miƙewa mum ɗinma ta yi ta bi bayansa. Ɗaure fuska sosai Heleena ta yi, da kallo ta bisu. Riko hannunsa mum ta yi suka fice daga room ɗin kamar wadda zata je ta gaya mashi wani abin, amma nan raka shi wajen motarsa zata yi kafin ita ma ta wuce nata office ɗin, tun da ba zai yi breakfast ba ita ma ba zata yi ba kenan, akwai shaƙuwa da kauna sosai a tsakaninsu.

Suna futa a filli Heleena ta furta. "I already knew that you didn't love me at all". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye cikin ɓacin rai, ba komai ya ɓata mata rai ba kuma face yadda suke a gidan, shi Smart idan ya yi magana ɗaya iyayen nasa basa jayayya da shi, ita kuma idan ta yi magana sai sun ja da ita, yanzu ta ce ba zatayi breakfast a gida ba sun ce basu yarda ba dole ta yi a gida, shi kuma daga ya ce ba zai ci a gida ba sun yi shiru basu kara magana ba, sai ma fasa yin breakfast ɗin su ma da suka yi, to hakan ne yake ɓata mata rai, sai ta rinƙa ganin kamar suna nuna mata banbanci da shi......... Ni kam na ce Heleenar nan yadda take jin haushin nan tsab idan aka kawo mata contract na kashe smat zata karɓa, gaji yarinya ai sonki ma akeyi da aka matsa maki ki ci abinci amma baki gane ba.

Kai tsaye harabar gidan mum ta fita tana riƙe da hannunsa. Suna fitowa ji kake dip! Dip! Dip gudun manya manyan jami'ai ƙosassu masu ji da lafiya kuma madaka katti, dukkansu jami'an dake gidan fararen turawa ne masu jajayen kunnuwa.

Da hannu ya nunawa jami'ai guda biyu su fito mashi da motocinsa fita zai yi ba tare da ya yi magana ba, da alama magana tana yi mashi wahala. Ko da yake irin wannan kyau da Allah ya yi mashi dole ya ja aji sosai, dan yasan shi É—in one in million ne.

Hira mum É—insa take yi mashi ba tare da ya amsa mata ba, yana dai jinta kawai, sai bashi labari a kan wajen aikinta take yi, daga karshe ta ce mashi ko dai zai kaita wajen aiki ne yau?. A takaice ya ce mata no mum. Bata ja da shi ba kawai ta ce a fito mata da jerin gwanon nata motocin.

Haka kuwa aka yi, wata dankareriyar mota aka fito mashi da shi, motocin jami'ai kala huɗu ne suka take mashi baya, mota ɗaya na swat ne, mota ta biyu na special emergency unit wato SEU ne, su ɗin tamkar wuta suke, aiki da cikawa, baku ji sunansu bane? Emergency suke, abu yana faruwa faka faka zasu dira a wajen su yi handle na komai and they solve everything, so motarsu ce ma a gaba kafin nasa, dan su tabbatar mashi da tsaro, jama'ai ne da suke na musamman. Mota na uku kuma jami'an SSS ne a ciki, suma jami'ai ne masu zafi, duk waɗan nan jami'an sun take sojoji a iya aiki, jarumta, ilimi haɗe da zafin nama, jami'ai ne na musamman masu aiki da ƙwaƙwalwa mamar computer, sannan suna aiki da karfin damtse kamar me.

Smart Tiger a da can baya baya taɓa yarda a take mashi baya, dan a cewarsa ai shi ya fi sojoji da ƴan'sanda power to bai ga abin da zai sa su take mashi baya ba tun da ko wani abin ya faru ma sai dai shi ya karesu ba dai su karesa ba, sai dai ya agaza masu, dan haka shi bai ga amfanin su take mashi baya ba, ragwaye ne a cewarsa, wannan dalilin yasa daddynsa a matsayinsa na president ya ƙaddamar mashi da jami'ansu na musamman waɗan da suka take sojoji da ƴan'sanda a tafasar jini da iya aiki, shi ne yasa ya yarda suna take mashi baya, dan ba kananan jarumai bane, nan ma fa sai da mum ɗinsa ta saka baki ne ya yarda su rinƙa take mashi baya su ɗin ma, idan ba haka ba yaki yarda, ya ce suma ƙananan kwari ne, daddynsa kuma yana jin tsoron kada wata ƙasa ta yi kwantan ɓauna ta sace mashi yaro shiyasa bai yarda yana barinsa ya fita shi kaɗai ba. Duk da hakan kuma wlh smart sai ya fita shi kaɗai ɗin, shi fa gani yake shi ɗin zaki ne a cikin namun dawa, gani yake yi babu wanda ya isa ya ce zai kawo mashi wargi, kuma haka ne, yasan abin da ya taka, ba ƙaramin kwaro bane shi ɗin.

Mota ta huÉ—un kuma jami'an NDLEA, motocin biyu suka yi gaba, sannan nasa a tsakiya, sai biyu suka rufa mashi baya.

Juyowa ya yi ya É—an yi hugging na mum É—in tasa, sannan ya manna mata sumbata a kumatu bayan ya raba jikinsu, ita ma sumbatar kumatun nasa ta yi tare da É—aga kafafunta tana son shafa kansa, sai dai bata iya yin hakan ba, dan ya fita tsawo sosai. ÆŠan sunkuyo mata kaÉ—an ya yi ta shafa kan nasa. Sannan suka yi sallama tana sakar mashi lallausar murmushi.

Motar tasa ya nufa, ita ma ta nufi nata jerin gwanon motocin ta shiga. Da gudu securitys suka buÉ—e masu kofofin motocin nasu, gidan baya ya shiga, ita ma mum a nata motar hakance, gidan baya ta shiga.

Wani katon bature fari tas ne yake tuƙa nasa motar, ita ma mum haka. Jerin motocinsa ne suka fara dallawa waje a tsananin guje, sun ɗan jima da tafiya kafin motocin mum ya tashi, dan ta tsayar da su tana waya da dad da ta barosa a cikin gida, sai da ta gama da shi sannan ta ce su wuce.

Gudu suke shararawa da motocin nasu kamar zasu tashi sama har suka fita arear Elysee palace dake jibge da securitys ta ko'ina kamar zasu tashi arear, duk in da suka gifta da sunan zasu wuce sai securitys É—in wajen sun É—aga hannu sun sara masu cikin girmamawa.

Kai tsaye Avenue Montaigne Suka nufa, unguwa ce ta manya manyan kai bana ƙananun kwari ba. Duk gidajen dake arear sun amsa sunansu gidajen gaske. Manya manyan luxurious highrise buildings ne kawai a arear, idan ka shiga wannan arear kauyanci ma kawai zai hanaka motsawa daga in da kake

Ya ilahi ya lillahi, my people's ku zo ku ga aljannar duniyar da babu irinta a nan, tun daga kan titin da zata sadaka da cikin gidan wasu irin mahaukatan securitys aka suba a wajen, securitys ne wanda ko giftawarsu ka gani a cikin Tv sai hantar cikinka ya kaÉ—a, jiga jigai ne masu lafiya, sai safa da marwa suke yi a wajen, ga wani uban zare jajayen idanunsu da suke yi suna muzurai kamar mutun ya ruga a guje, yadda suke tsaye suna kewaye ko'ina a wajen bana jin kamar zasu iya barin ko tsuntsuwa ne ta gifta ta tsakar sararin samaniyar harabar wannan gida.
Chapter 62 · 0% Book details