Sashe 133
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunani ta fara yi a kan idan Yah Jaish ne ya zo fa? Ta shiga uku ta lalace! Ita da kanta ma kenan, ina kuma ga shi? Kamar ba yanzu ta gama ce mashi ba mai hukunta shi ba, ta yi mashi daÉ—in baki, ashe dai ita da kanta ta san bakar zuciyar Æ´an uwanta, tasan idan hakan ya faru ta ja mashi babbar aiki ne da kaf kingdom of power babu wanda zai iya tare mashi, a gaskiya ta tafka babban kuskure wanda sai a yanzu ta fahimci hakan, addu'arta É—aya shi ne Allah yasa Yah Guyson É—in ta ne idan ma É—aya daga cikin Æ´an uwanta ne, shi ne kawai a gabaÉ—aya familyn nasu wanda tasan zai iya fahimtarta ya kuma rufa mata asiri ba zai gayawa kowa ba, bayan shi wlh ko Gimbiya Chuchu da suke tamkar chewing gum ba barinta zata yi ba, sai ta sanar da King, dan ita ma bata wani sonta da Hoorain É—in, bata son ganinsu a tare.
Sake buga kofar da aka yi ne yasa suka dawo cikin hankalinsu, dawo da kallonsa daga kan kofar izuwa kanta ya yi, while ita ma shi take kallo, sun rasa mafita, yadda suka tsaya a tsakiyar É—akin sai sun baka tausayi ga kuma abin dariya na yadda suke kallon juna sun rasa mafita.
"Zan ɓuya a cikin toilet ɗinka kai kuma sai ka duba wanenen ka ji?". Ta yi maganar ƙasa ƙasa kamar mai yin raɗa.
Kai kawai ya gyaɗa mata, da alama jikinsa duk a mace, bashi da wani kuzari, dan kuwa shi ba ƴan uwanta ne ma suka damesa ba, idan sun kamashi karkari dai bai wuce su kashe shi bane kawai, shi damuwarsa yadda Abbonsa ya ja mashi kunne a kanta, ya yi mashi faɗa, sai a ce mashi yau an kama shi da ita a ɗakinsa a irin wannan daren? Ya kuke tunanin commander zai ji a ransa? Shi ɓacin ran mahaifin nasa ne baya so, gara mashi su kasheshi idan suna so amma kada Abbon nasa ya sami labarin hakan, yasan zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba.
Wato commander yana balai'n kaunar É—an nan nasa É—aya tilo a duniya, shiyasa duk abin da zai zama mashi matsala a rayuwarsa yake saurin taka mashi birki a kan abin, kunga yasan kasancewarsa kusa da ita zai haifar mashi da matsala ne yasa tun wuri ya daka mashi warning a kan, amma bai ji ba, ko da yake ba laifinsa bane bawan Allah.
Tun da yake bai taɓa sallake ko A a maganar da Abbonsa zai gaya mashi ba, yana yi mashi biyayya sosai, yana gudun ɓacin ransa sosai, da ya yi abin da zai ɓata mashi rai gara mashi ya yi kwana biyar a ɗaure babu ruwa babu abinci, a kanta ne farkon fara tsallake maganar commander, a hakan ma kullum yana cikin danasani tare da ƙoƙarin nesanta kansa da ita, amma ya ƙasa.
Kofar É—akin ya nufa ita kuma da sauri ta shige cikin toilet.
"Wanene?". Ya faÉ—a muryarsa tana sarkewa. Ya yi tambayar cike da tsoro da fargabar muryar wanda zai bashi amsa. Kirjin maza yau sai dukan uku uku yake yi dan tsoron kada ace Abbonsa ne, Allah sarki shi commander ne ma kawai a ransa.
Daga wajen ya amsa da. "Lafiya yau ka kulle kofar Hoorain?".
Wani irin sauke nannauyar ajiyar zuciya ya yi, to fah ya zai yi kenan? Abin da yake gudu dai da alama shi ne yake shirin faruwa.
"Babu komai Abbo". Ya bashi amsa tare da sanya hannunsa dake ɗan ɓari saboda tashin hankalin da ta jefasa a ciki, da kyar ya murza key ɗin ya buɗeta.
Commander ne a tsaye cikin wannan irin tsayuwar tasa ta manyan jiga jigan jaruman, hannunsa riƙe da kayan abinci cikin wani babban tray.
Hannunsa dake ɓari ya kai ya karɓa mashi abinci yana faɗin. "Sannu da zuwa Abbo".
Miƙa mashi abincin ya yi a tare suka ƙarisa cikin ɗakin commander ya rufe kofar. A saman gefen bed ɗinsa ya zauna yana faɗin. "Hoorain wani irin kamshin perfume ne wannan?".
Wani irin dukan uku uku ya ji kirjinsa ta bada, Abbonsa akwai kaifin ƙwaƙwalwa, wai yanzu har ya iya tantance cewa akwai wani kamshi na daban da ya shigo ɗakin?. Kai shi ma dai ya iya sa ido gaskiya.
"Kamar wani kamshi fa?". Ya yi tambayar cikin dakiya, yadda kuka san bai san me commander yake nufi ba.
"Na ji kamshin perfume irin na mata ne a ɗakin, kuma tamkar kamshin perfume ɗin princess Zunaira ko Jannat, su ne suke amfani da irin wannan turaren". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya sauƙo ƙasa saman dadduma ya zauna.
Tun da ya fara magana kirjin ɗan nasa take harbawa pat, pat, pat da karfi karfi, addu'arsa ɗaya kada ya titsiyesa a kan sai ya ji dalilin zuwan wannan kamshi ɗakin, bawan Allah duk yana cikin firgici da tashin hankali, Auta tana neman jefashi cikin bala'i, da yake bai taɓa aikata hakan ko da sunan wasa bane sai tsoron nasa ya tsananta.
"Zo nan na baka abinci yau barci da wuri nake ji". Abbon nasa ya katse mashi tunanin da yake yi.
Wani irin ajiyar zuciya da ya sauke ne yasa Abbon nasa É—agowa ya zuba mashi idanu.
"Hoorain ya na ganka tamkar a ruÉ—e haka? Lafiya kake kuwa?".
Da sauri ya furta. "E a'a e". Ya yi maganar ma murya na sarkewa alamar rashin gaskiya, wlh bai iya karya ba, ga shi wane shi ya ce zai faÉ—i gaskiya a yau, zai jawa kansa bala'i ne, amma kuma ya rasa ta ina zai fara yin karyan dan kare kansa, shi ne yasa ya ruÉ—e yake ta faÉ—in eh kuma a'a.
"E a'a kuma?". Ya sake jefa mashi tambaya.
A karo na biyu ma cewa ya yi e a'a e ya sake yi.
Zuba mashi idanu sosai ya yi yana son karantarsa. Ganin hakan yasa sai ya yi saurin miƙewa, a ruɗe ya nufi toilet duk dan ya kaucewa zargin da yake gudun Abbon nasa ya fara jefansa da shi.
Da kallo ya bisa har ya shige cikin toilet É—in, bai kawo komai a ransa ba, sai ma tunani da ya yi a kan ko dai toilet da yake son shiga ne ya rikitashi har haka? Ko da wasa bai bashi wani zargi maras kyau ba, dan yasan da wuya Hoorain ya aikata wani abin rashin gaskiya, yasan irin tarbiyar da ya bashi.
Jim kaÉ—an ya fito daga cikin toilet É—in ya dawo ya zauna, sai a lokacin kuma ya rage kayan jikinsa, ya kuma cire wannan hula tasu, ya zauna a gaban Abbon nasa, zaman cin abinci da kyau.
Abinci commander ya zuba masu da kansa, a tare suka fara ci suna tattaunawa a kan rayuwa, haka suke yi kullun, commander yana bala'in kula da É—an nan nasa, baya yarda Hoorain ya ci abinci har sai ya zo sun ci a tare, shiyasa baya barinsa ya ci shi kaÉ—ai.
Duk abinda suke yi tana jiyosu daga cikin toilet ɗin, sun yi matuƙar burgeta, uba da ɗa ne kamar wasu abokai haka abin da birgewa matuƙa.
Hira commander yake ta zuba mashi amma hankalinsa baya a tattare da shi, yana can ya tafi duniyar tunanin yadda za'ayi ya mayar da ita cikin gida.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...âœï¸ðŸ”¥ðŸ•Šï¸
Sosai hankalin King ya fara tashi, sai yanzu yake danasanin saba mata da zuwa kowani É—aki ta kwanta da yake yi, kun san tana kwana da Chuchu ko su Sarina idan ta yi ra'ayi, sannan tana kwana wajen Momma, har part na Jaish tana kwana da shi idan tana so, yau dai King ya yi nadamar hakan.
Bai sanar da mommarta ba, ya nufi part ɗin Akka domin dubata a can, a jikinsa yake jin bata cikin arear wajen, saboda bata taɓa wuce wajen su Mommarta ba, in ta ɗan yi nisa ne room na Jaish, yasan bata zuwa wajen mama and mummy, amma haka ya je can ya duba, duk dan kawar da zargi.
Duk wasu É—akuna da suke part É—in na Akka sai da ya shiga, wayam babu kowa, yau ko su Sarina ma basu kwana a part É—in ba, har É—akin uncle Jahiz dake cikin part É—in sai da ya duba, wayam bata a ciki, uncle Jahiz É—in ne kawai kwance yana zuba barci cikin kwanciyar hankali.
Tsayuwa ya yi a main parlourn part É—in yana tunanin ina ta shiga a wannan dare? Baya son shiga É—akin barcin Akkar dan kada ya tasheta ko wani abin makamancin hakan.
Tunani ya fara yi ta ina zai fara nemanta a daren nan? Ina ma taje? Yasan dai babu wanda ya isa ya shigo part ɗin nan nasu har ya ɗauketa ya fita da idan ba dai aljani ba, domin masu tsaron wannan part ɗin ko ƙuda idan zasu gani ba zasu barshi ya giftasu har ya wuce ciki ba, so idan ma bata nan to wlh da kafafunta ta fita ko kuma wani daga cikin family ya fita da ita!!.
A hankali ya juya zai bar part ɗin, amma sai ya ji zuciyarsa ta ƙasa yarda da hakan, ya kasa samun sukunin aikata hakan, damuwa mai tarin yawa ce take cunkushe a cikin zuciyarsa take ƙoƙarin taso mashi izuwa maƙoshinsa.
A hankali ya juya ya nufi ainahin bedroom na kwanar Akka, bai so shiga ba, amma haka ya tsinci kansa da leƙa wajen dan ya samu damar cewa babu in da bai duba ba a gidan.
Ba karamar madarar mamaki ya sha ba na ganinta kwance a kusa da Akkar, idanunta a rufe alamar barci take yi, shi dai yasan bai taɓa samunta a wannan part ɗin da sunan zata kwana ba, tana shiga, amma banda batun kwana kam.
A hanzarce ya ƙarisa cikin ɗakin domin ya tabbatar ba kaunarta ce take sa take yi mashi gizo ba.
Kamar zai kunna wutar ɗakin domin ƙara tabbatarwa, sai kuma ya fasa dan kada Akka ta farka, wutar lamps ɗin ma sun wadatar ya iya hango face ɗinta.
Tana kudundune a cikin bargo, sai zuba barcinta take yi abinta. Ina ai duk da haka bai yarda ba sai da ya hau saman bed ɗin ya taɓata dan dai ya kara tabbatarwa da kyau.