← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 211

Sashe 30

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yah Omar stop it, i don't want, am a hero, and who tall you that am fighting with her? Am not her mate, about beating she did a wrong think to me that's why i teach her a lesson". Ya kai karshen maganar yana É—aure fuska sosai.

Cigaba da harararsa Guyson ya yi ba tare da ya yi magana ba, dan yawan magana sam shi ba nasa ba ne, bata a tsarinsa.

Dr Raj ne suka shigo a tare da Sharifat cikin sauri, daga shi sai jallabiya a jikinsa, da alama daga masallaci sallar isha ya dawo. Cikin zafin nama ya zo ya kama kafan Obaid ɗin tare da ƙurawa jinin dake zuba ɗin idanu.

"What happened to him?". Ya jefa masu tambaya. Guyson ya amsa da suna tsaye a wajen wannan É—an hanyar kawai sukaga ya haska hasken wayarsa sai jini suka gani a kafar tasa.

Tambayarsa Dr Raj ɗin ya sake yi a kan meyasame shi?. Bai ɓoye mashi ba ya gaya mashi gaskiya. Wani irin ɗaure fuska sosai Dr ya yi, rai a matuƙar ɓace ya fara faɗa a kan cewa duk laifin masu aikin gidan ne da basu goge komai yadda ya dace da har za'a sami wani abin da zai ji ma wani ciwo a wannan wajen, gaskiya dole duk wata mai aiki dake cikin gidan yau sai sun karɓi hukunci na gaske ma kuwa, sai faɗa yake yi sosai ya ɓata rai. Shi kuwa Guyson binsu da ido kawai yake yi, yana jin tamkar jikinsa wannan kwalba ta fasa, Sharifat dake tsaye a gefe ne ta fara cewa yayan nata ya yi hakuri.

Ransa a ɓace ya fara duba kafan ƙanin nasa. Da gudu Omaid ya faɗo masu cikin ɗakin har yana haki, tun ɗazun yake ta neman Obaid ɗin.

Haka Dr Raj ya gyara mashi kafar tasa tare da yi mashi abin da ya dace, sannan ya ce Sharifat ta gayawa Ummie ta tara mashi duk masu aikin gidan nan ta miƙasu ga Discipline master ya basu ajikinsu, dan gobe su ɗauki aikinsu da mahimmanci, shi fa wannan discipline master ɗin wani shirgegen jami'in Special weapons ne, ya kware a iya casa mutane, duk wanda ya yi laifi a ma'aikatan gidan shi ake damkawa ya yi mashi hukunci, duk ma'aikatan gidan suna matuƙar tsoronsa kamar menene, saboda bashi da mutunci, bakin mugu ne, ya iya tabka ba karya, ga wata shegiyar zabgegiyar bulalarsa wadda aka yi ta da fatar macijin mesa, duk in ya hukunta yarinya ko wani ma'aikaci to fa sai wan da aka hukunta ya yi jinya sosai, saboda bulalar bata wasa bace, akwai shiga jiki.

Sosai Sharifat ta shiga bashi hakuri a kan ya hakura ayiwa ma'aikatan faÉ—a dai, ayi masu afuwa na yau kawai.

Rai a ɓace Omaid ya ce. "Aunty Sharifat kin san me kike faɗa kuwa? Sakacinsu fa ya ja jinin Obaid ya fita, gaskiya ba zan iya yafe blood na ɗan uwana da ya fita ya tafi a banza ba, i can't, dole a hukuntasu, ai wannan basu san aikinsu bane, wai ma manene suka bari a kan tiles ɗin har ya ji maka ciwo haka Obaid? Kuma a ina ne?".

Guyson da yake shiru tun É—azun ne ya ce. "Yah Raj please and please for give them kamar yadda Sharifat ta nema masu alfarma, and Omaid I don't want to hear your voice here again, ka mun shiru".

Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa Omaid ɗin ya wurgawa Guyson ɗin kafin ya ce. "Yah Omar my Obaid fa! Blood ɗin Obaid fa suka zubar mun, am sorry to say i can't for give them wlh". Yana kai ƙarshen maganar ya juya da nufin ya fice daga ɗankin, dan ya lura basu san irin tafarfasar da zuciyarsa take yi mashi a kan zubarwa da ɗan uwansa jini da aka yi ba, da shi suka sanya jininsa ya zuba zai iya yafe masu, amma Obaid gaskiya ba zai iya hakura ba, ransa ya ɓaci sosai, zuciyarsa na ƙuna.

Yana juyawa Obaid ɗin ya riƙo hannunsa yana faɗin. "Don't go anywhere my blood, please stay with me".

"I want to talk to Abbie ne, zan dawo yanzu, you know i can't stay in other place without you".

Da ido suke binsu, Guyson bai sake cewa ko uppan ba, dan yasan a kan Obaid Omaid zai iya haukacewa, shi ma Obaid a kan Omaid ba abin da ba zai iya aikatawa ba, su ɗin kamar chewing gum suke, idan ka taɓa ɗaya ka shiga uku, ɗaya baya hakura ya yafe ɓacin ran ɗaya, sun san kome zasu yi yanzu Omaid ba zai hakura ba, ko da kuwa duka zasu yi mashi bafa zai hakura ba, shi ne yasa kawai suka bishi da ido.

Dr Raj da yake ya yi masu farin sani, dan ya fi kowa daga cikin Æ´an uwan nasu kai masu ziyara a makaranta, kullum kuma ya je complain kala daban daban malaman makaranta suke bashi a kan waÉ—an nan Æ´an albarka, so sanin su in and out yasa ya ce da Omaid É—in. "Ba sai ka É—auki wani mataki ba, just leave the case in my hand, I will handle the case".

Juyawa Guyson ya yi ya fice daga É—akin, da kallo Dr ya bisa, tabbas ya fahimci ransa bai so ba, Obaid kaninsa ne, ba zai zo wani abin ya cutar da shi ba, amma duk da haka bai kamata a hukunta waÉ—an da basu da laifi ba, a haÉ—a masu aiki dukka a hukunta a kan haka ai bai dace ba, wasu ai suna aikinsu da kyau.

Bin bayan Guyson ɗin Sharifat ta yi da sauri, dan ita ma ta lura ransa ya ɗan ɓaci, Dr Raj kuwa ya tsaya da su Obaid yana kara yi masu nasiha. Sai huci Omaid yake yi shi a dole ba zai hakura ya yafe jinin ɗan uwansa da ya zuba ba.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘STEP TWO....✍️📚🔥

After some minutes.

Da misalin karfe 8:10pm. Wani irin jiniyace ta fara tashi tun daga farkon shinfiÉ—aÉ—É—iyar titin da ta keto har cikin gidan Abu Abdussalam, jiniya ce ta daban, ba kamar yadda suka saba jin jiniyar ba, ta yau yadda kuka san filin yaki suka dinfara, kaki ne kala kala har wajen kala huÉ—u, dukkansu sun saki jiniya, mitocin jami'ai ne gaba da bayan, a tsakiya kuma familys car's ne. Gudu suke shararawa na gasken gaske tamkar zasu tashi sama.

Tun daga nesa suke danna horn tamkar zasu tashi unguwar gabaÉ—aya. A É—ari securitys dake tsaron gate É—in suka wangaleta. Yadda suka taho a haukace suna gudu haka suka danna hancin motocin ciki.

Leesharh dake kwance a saman bed ɗinta tana aikin kuka ne ta zabura ta miƙe zaune, tun da Allah ya kawota wannan gida bata taɓa jin jiniya irin haka ba, tamkar zasu tashi garin, sannan bata taɓa jin motocin gidan sun shigo a haukace haka ba. Hakan yasa ta diro ƙasa daga saman gadon nata, da gudu ta nufi wajen windown ɗakin nata domin ta leƙa taga su wanene?.

Dai'dai lokacin da ta leƙa dai'dai lokacin Bilal ya zo wucewa ta tsakar harabar gidan ɗauke da Ramish a saman shoulder ɗinsa ga jini na zuba kamar an buɗewa ruwa hanya, ko motsi Ramish ɗin baya yi, manya manyan jami'an special weapons uku ne suka takewa Bilal ɗin baya suka nufi cikin gida.

Dafe saitin zuciyarta dake barazanar tarwatsewa ta yi da hannu, salati ta fara sakawa tare da tambayar to me ya sami Ramish ɗin kuma? Ya mutu ne?. Babu mai bata amsa, hakan yasa ta yi ƙasaƙe a wajen jiki ba kwari, yadda kuka san wadda aka zarewa laka.

Ta É—auki a kallah 20 mins a wajen tana tsaye, kukan da ta ji yana tinkaro room É—in nata ne ya dawo da ita daga duniyar da ta afka. Da kyar ta iya janyo kafafunta ta koma wajen bed É—inta, ta kasa iya zama, zuciyarta ce ke bugawa da sauri da sauri, tsoronta dai kada ace ya mutu, tunani ta fara yi a kan to meyasame shi?.

Sharifat ce ta afko cikin ɗakin nata tana kuka wiwiwi hawaye bibbiyu kamar ƙaramar yarinya. Tana zuwa ta faɗa jikin Leesharh tare da ƙara sautin kukan nata.

A ruÉ—e Leesharh É—in ta ce. "Sharifat lafiya me yake faruwa?". Cikin kuka ta amsa da. "Harbin Yah Ramish da bindiga aka yi, kuma ni ina ganin kamar ya mutu, wayyo yau na shiga uku na, in ya mutu ya zan yi ni kuma?".

BuÉ—e baki ta yi da nufin ta fara rarrashinta kenan Guyson ya faÉ—o cikin É—akin yana kiran sunan Sharifat É—in, sahunta ya biyo, tun daga emergency room yake ta aikin rarrashinta amma taki yin shiru, Ummie ma ta saka baki, amma taki ta yi shiru, gabaÉ—aya family sun taru a cikin room É—in, ba wanda bai ce ta yi shiru ba, amma taki ta yi shirun, da suka matsa mata da rarrashin ne ma ta fito ta basu waje.

Jin abin da Sharifat É—in ta ce yasa Leesharh sake shiga tsananin tashin hankali, amsa É—aya take son sani shi ne ya mutu ko yana raye? Shi ne abin da kawai take son ji.

Riƙo hannun Sharifat ɗin Guyson ya yi da nufin su tafi. Yah Rizwan ne ya shigo cikin ɗakin, ya biyo bayanta ne shi ma, hannunta ya riƙo suka fice dan su je su rarrasheta, shi Yah Rizwan sarai yasan Sharifat tana son Ramish, dan in baku manta ba a baya na gaya maku tafi shaƙuwa da shi a kan sauran ƴan uwan nata, Rizwan abokinta ne sosai kamar dai Guyson, so saboda kusanci da suke da shi yasa ya fahimci tana son Ramish, amma bai gaya mata ya gane hakan ba, ya dai rabu da ita tana dakon kauna.
Chapter 30 · 0% Book details