Sashe 35
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A takaice ta ce. "Kai dai jeka ka yi shirin tafiya ninzan ɓatar maka da kamannin naka". Tana kai karshen maganar ta miƙe da sauri ta bar ɗakin dan bata son yaga hawayen da take ƙoƙarin dannewa. Allah sarki bata son rabuwa da shi, tsawon shekaru 26 kenan yanzu kullum ba dare ba rana suna a tare, bai taɓa matsawa daga kusa da ita ba, duk in da zai je a faɗin dajin nan dai zai dawo wajenta, ba dan su Pretty bama shi baya zuwa ko'ina, bayyanar su Pretty suka koya mashi fita har ya je wajensu ya yi awa ɗaya zuwa biyu.
Kuka ne sosai mai karfi ya zo mata, É—akinta ta shiga ta fara murzan kuka sosai, rabuwar uwa da É—a babu daÉ—i ko kaÉ—an. Shi kuwa tashi ya yi ya fara shiri, har wani karfi ya ji ya zo mashi.
Duk wani abin da su Pretty suka bashi sai da ya É—auka, ya É—auki wukarsa sannan ya É—auki al'qura'ani mai girma da Sweetie ta bashi. Ya dai gama shirinsa tsab abinsa bai san cewa Mamma tana can tana kuka ba.
Bayan ya kammala duk abin da zai yi ya fito ya nufi in da take. Jin motsin yana nufo wajenta yasa ta yi saurin goge hawayenta tare da fara fito da wasu abubuwa nata dan ta ɓatar mashi da kamanni.
Cike da murna ya shigo cikin É—akin nata, sai zumuÉ—i yake yi zai je ya duba su Pretty daga nan ya É—aukesu su je neman babansa, a lissafinsa ba zai iya tafiya ya barsu a dajin ba, zai je ya É—auki Sweetie ya kawota wajen Mamma É—in tun da ita bata gani, ita kuma Pretty ya tafi da ita neman babansa.......... Tab da kuwa akwai cakwakiya in dai da Pretty zaka tafi neman baban naka.
Zaunar da shi a bakin gadonta ta yi tare da ɗauko abubuwan nata ta fara aikin ɓatar mashi da kamanni. Tas ta yanke mashi dogon gashin kansa saɓanin kullum da take rage mashi tsawon, yau dukka ta yanke, sannan ta aske mashi sajensa ma tas da wani irin ɗan ƙaramin wuƙa na gold mai kama da aska sai kaifin bala'i, tun da yake da ita bai taɓa ganinta da irin waɗan nan abubuwa ba, ko daga ina ta samosu yau kuma? Ya tambayi kansa, gudun kada ya yi mata laifi ta ce ta fasa ya zauna a gida yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai tambayi daga ina ta samo waɗan nan abubuwa ba.
Bayan ta aske mashi sajensa sai ta aske gashin gera ma, ta sanya mashi wani irin powder a wajen da ta aske gashin, wlh sai ya canza kamanni gabaɗaya, kun san idan aka cirewa mutun gashin gera yadda yake canzawa kamar ba shi ba. Haka dai ta zage ta canza mashi kamanni, wlh ba zaka taɓa zaton shi bane.
Ta ɗauko wani dogon towel da ta saƙa ta naɗa mashi rawani da shi, ya fito kamar irin larabawan ƙasar Iraq ɗin nan, ba zaka taɓa cewa shi bane.
Fatan nasara da fatan alkhairi ta yi mashi, sannan ta bashi umarnin tafiya. Duk zumunÉ—in da yake yi na son tafiya sai ya ji jikinsa ta mutu da ta ce ya tafi, nan take ya ji idanunsa sun cika da kwallah, damuwa ce ta bayyana a saman fuskarsa. Juyowa ya yi suka kalli juna, ganin idanun Mammar tasa ms a cike da kwallah yasa na sa hawayen da suka cika mashi idanu suka fara zubowa.
"No Kamran no, kada ka yi kuka, ka tafi kawai, sai dai ina son ka mun alkawarin zaka dawo gareni! Ina zaune ina jiranka".
Matsowa ya yi tare da riƙo hannayenta. "Mamma zan dawo gareki, duk wuya duk daɗi zan kasance da tunaninki a duk in da nake, please Mamma kema kada ki yi kuka kin ji?".
Hug na juna suka yi, hawayen da take ƙoƙarin dannewa ne suka fara zubo mata, tana jin kamar kada ta barshi ya tafi, dan tana ganin kamar za'a gane shi ɗan cikin damisa ne a kashe shi, tana jin kamar zasu rabu rabuwa ta har abada kenan.
Sun jima rungume da juna suna kuka kafin daga karshe ta yi ta maza ta raba jikinsu tare da riƙo hannunsa ta fito da shi waje. A wajen ma tsayawa suka yi tana goge mashi hawaye shi ma yana goge mata nata, da kyar suka iya rabuwa bayan ta bawa Rocky amanarsa.
Da gudu ta juya ta koma cikin gida shi kuma ya nufi kasa har lokacin ya ƙasa dai'na kuka, Rocky ya rufa mashi baya suka tafi a tare. Rocky da Kamran akwai amana, wannan rashin lafiya da Kamran ya yi Rocky ma har ƴar rama ya yi, saboda baya fita ya fatauci nama sosai, koda yaushe yana zaune a bakin kogon nasu yana dakon jiran fitowar Kamran ɗin tun da ba halin shiga ciki.
Kai tsaye wajensu Pretty ya nufa cike da kaguwa na son ganinsu.
TO KAMRAN ALLAH YA TSARE HANYA YA KUMA HAƊAKA DA CIKAN BURINKA NI DAI SHI NE FATANA🥰😇
_____________________________😇â¤ï¸â€ðŸ”¥ðŸ’«
DARK WORLD😇â¤ï¸â€ðŸ”¥
Saboda kuka da wahalar da ta sha yasa ta yi barci mai nauyi wanda bata farka ba sai can wuraren karfi 9 na dare. Tana farkawa kuma abin mamakin da bata taɓa zato ba a rayuwarta shi ne ta farka idanunta suna gani, tamkar a mafarki ta ji kuma take ganin abin.
Tana farkawa kuma da kyakkyawar fuskar Ronnie ta fara cin karo, yana tsaye a gaban gadon nata hannunsa riƙe da wani allura da ya haɗa yake son yi mata, ko alluran menene oho masu, idanunta dai ba aiki suka yi mata suka buɗe mata su ba, su kaɗai suka san me suka yi mata idanun suka buɗe. One thing about Ronnie shi student ne. Har yanzu bai kammala karatu ba, kuma yana zuwa school, sannan yana ɗaya daga jikin ɗaliban likitoci da Dark world suke alfahari da su, yana da kwazo ta fanni karatu sosai, ya kerewa tsaransa. So duk lokacin da yake da class yana zuwa school, suna da babban university da black tiger yasa aka gina masu, ga manya manyan asibitoci da dai sauransu, shi fa black tiger kullum burinsa ƙasarsa ta zamana tana da komai na more rayuwa, ta zama number ɗaya, sai dai akwai ɗan banzan zalinci kuma kamar kafurin farkon zamani.
So Ronnie kwararrene a fannin nan na likitanci, riƙe yake da allura zai yi mata.
A duniya Sweetie bata da burin da ya wuce idanunta su buÉ—e ta yi tozali da Kamran, sai ga shi yau sun buÉ—e ta yi tozali da madarar kyau da ya take na Kamran, sai dai kallon kamar idon sani ta yi wa Ronnie É—in, ta ji kamar ta sansa.
Mamaki da al'ajabi ya hanata motsawa daga in da take kwance, wai yau itace idanunta suka buÉ—e tana gani? Kai abin da mamaki, Pretty and Kamran ne kawai a cikin tunaninta, sai ayyana yadda zata kalli Kamran take yi, Pretty kam already ta san ya kamanninta yake, Kamran take mararin gani. Shekara bakwai tana tare da Pretty idanunta suna gani, so tasa kamanninta saura Kamra
Tuna cewa ga fa in da take yasa idanunta suka ciko da kwallah, zuciyarta na sanar da ita cewa shikenan ba zata sake ganin Pretty and Kamran ba. Kan kace me hawaye sun fara zuba daga idanun nata.
Ronnie bai lura da hawayen nata ba bai ma lura da ta farka ba, hankalinsa naa kan wanna kyakkyawar yarinya mai kula da Sweetien da ta shigo yanzu. Jikinta na sanye da wani guntun wandon jeans baki da t-shirt mai laushi pink color wanda ya tsaya mata a iya kunkuminta, ta ɗaure gashin kanta ta zuba jelar a baya, ta bar wani guntun gashi a gaban goshinta wanda ya ƙara mata kyau sosai, fara ce tas amma bata kai Ronnie ba, a gaskiya ma idan tana gabansa za'a iya ce mata bakar fata, dan shi fa koreans ne, jikinsa kamar madara, tas yake.
Ƙarisowa kusa da shi yarinyar ta yi, ɗan rungumar juna suka yi irin welcome ɗin nan kafin ya sumbaci kumatunta, ita ma sumbatar nasa lallausan kumatun ta yi. A shekaru wannan yarinya ba zata wuci 12 years ba, sai shegen kyau irin na mutanen cikin Dark world ɗin.
"Beb go and bring food for her, ina ga yanzu zata iya farkawa......." Bai kai karshen ba idanunsa suka sauƙa a kanta tana hawaye.
A hanzarce ya ce. "Kash beautiful Queen why are you crying? Baki san kuka a yanzu isn't ur own bane? Kina son kuka ya yi affecting na idanun naki su sake rufewa ki daina kallo ne? Please stop this crying because bana son ki dai'na kallo". Ya kai karshen maganar tare da zama a kusa da ita ya ajiye alluran hannunsa a gefe ya hau goge mata kwallah.
Juyawa Floria ta yi ta nufi room door ba tare da ta yi magana ba. Shi kuma bayan ya goge mata hawaye ya ɗago ta dan ya ƙara rarrashinta da kyau. A kirjinsa ya mannata yana ce mata sorry, sannan ya ɗauko injection ɗin da ya ajiye a gefen, cikin wannan sanyayyar voice ɗin nasa ya fara yin magana tare da matso da bakinsa dab da kunnenta, dan a hankali ya yi magana. "Bari na yi maki injection a jijiyar hannunki ko?"
Ita dai har yanzu gani take yi mafarki fa take yi ba gaskiya ba, gani take yi kamar idan ta farka zata ga idanunta sun rufe, haka yasa ta kafe shi da idanu tana kallonsa, dan ya yi mata mugun kyau, bata son ta yi missing wannan kyau bata gani da kyau ba ta tashi daga mafarki da take zaton shi take yi taga ta koma makauniya.
Sosai take ta kallon kyansa bata ce ko uppanba, shi kuma kallon kalar idanunta da suka burge shi yake ta yi, ya ji kamar ta bashi idanun nata ya ƙara kyau kan kyau.
Shigowar Floria cikin É—akin ne yasa Ronnie kawar da kallonsa daga kanta tare da É—auko alluran ya gyara hannunta da nufin ya yi mata. Tana ta kallon shi ita kuma bata ankara ba bata ji time É—in da ya É—aure hannunta ya nemi jijiya ba sai ji ta yi zafin tsira alluran ya ziyarceta.