← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 211

Sashe 33

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gabansa ya tsugunna yana yi mashi magana, amma bayan wannan ido da yake binsa da kallo bai iya amsawa ba. Ganin hakan yasa Bilal ɗin ya yi tunanin ko dai sun yi mashi wani abin ne? Dan haka sai ya miƙe ya saɓe shi sai saman shoulder ɗinsa. Yana juyawa da shi da nufin ya kaishi cikin motarsa sai suka ji harbi from nowhere, ba kowa aka harba ba kuma face Ramish ɗin, kafin Bilal ya juyo sun ƙara mashi wani harbin, so suke kada wannan dama da suka samu ta ƙubce masu, so suke su kashe shi ta kowacce hali tun da ɗaukarsa su tafi da shi ya gagaresu, harbi biyu suka yi mashi, wannan harbin ya ja hankalin sojojin da suka bi masu motan nan, hakan yasa suka dawo a guje suka bi in da harbin ya fito.

Shi kuwa Bilal da karfin hali kai shi cikin mota ya yi, zuciyarsa na tafasa, yana son bin Æ´an ta'addan ya kamosu dan yana ganin kamar yaran nasa ba zasu iya kamasu ba, yana son binsu ya kamosu amma ran É—an uwansa yafi mashi mahimmanci, hakan yasa ya ja motar kawai da wani mahaukacin gudu ya nufi hanyar komawa gida. A lokacin kuma wani daga cikin sojojin ya yi waya gida a kan wasu jami'an su taho akwai matsala, a hanya Bilal ya ci karo da motocin jami'an gidan nasu wajen motoci goma, umarni ya yi masu a kan su juya ba wasu Æ´an ta'addan azo a gani bane.

Ba musu suka juya suka takewa Bilal É—in baya suka nufi gida. Wannan shi ne abin da ya faru da Ramish É—in.

To bari mu leƙa wani part ɗin kuma mu ga wani hali suke ciki. Amma kafin nan meyasa suke son kafin su kashe Ramish sai sun kamashi sun kai shi in da suke? Da suka gagara kamashi ɗin ne suka fara yunƙurin kasheshi kada damar ta wucesu, sun fa san kama Ramish yana cikin hayyacinsa ba abu bane mai yuwuwa ina ga shiyasa suka ɓullo mashi ta wata hanyar, to fatana dai ni kam Allah yasa RAMISH ɗin yana raye, bari mu leƙa wani part ɗin dai mu gani.

_________________________________🔥💘

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/10/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘STEP TWO....✍️📚🔥

E______________13 and 14

FOREST😇

Mamma ta shiga tashin hankali da damuwa sosai na ganin halin da Kamran ya shiga, yau tsawon kwana bakwai kenan ya ki ya yarda ya ci komai, tun yana rashin lafiya kaÉ—an kaÉ—an har abin tazo ta fi karfin sa, yunwa ba wasa ba, tuni ya fita daga hayyacinsa ga shi da kafiyar bala'in, ya fi mammar tasa iya kafewa a kan abu, komai wuya komai daÉ—i idan É—an tahalikin nan ya yi magana baya canzawa, shi burinsa kawai ya mutu ya huta, Allah mun gode maka da kayomu a musulmai, muka taso cikin ni'ima mai girman da babu wanda yake da shi sai musulmai, Alhamdulillah.

Mamma fa da taga da gaske Kamran zai yi wa kansa illah, dan a halin da ake ciki yanzu yana zube ne ko magana bayayi, gabaÉ—aya ya fita hayyacinsa, ga idanunsa a datse gam yaki buÉ—e su ma bare suyi four eyes da mamman zuciyarsa ta karaya, suna rufe ruf, yanzu fa sai idan mammar ta É—aga shi ko ta kwantar, duk wani karfi na jikinsa ya kare.

Da taga da gaske zai iya mutuwa sai tsoro ya shigeta, ta tsorata sosai ta yadda ta fara nemanwa kanta mafita, tana ganin kamar idan ta kyaleshi ya je nemansu Pretty or mahaifinsa fa to kamar ta sallama shi ne, gani take yi kamar sai dai ta nemi wani É—an ba dai shi ba, kaunarsa yasa bata son ya fita, tana jin tsoron rabuwa da shi kamar hauka.

A kusa da shi ta shigo ta zauna hannunta ɗauke da kayan abinci kamar yadda ta saba kawo mashi, wuka tasa ta yanke igiyar da ta ɗaure shi da shi ɗin. Duk in da ta ɗaure shi wajen igiyar ta shata layi, da yake yana da hasken fata, sai zanen igiyar ta fito ɓaro ɓaro kamar menene, ya yi ba kyan gani, wani wajen kam ma ya ji mashi ciwo har da jini.

Ganin yadda igiyar ta lallata mashi jiki ne yasa mammar ta fara nadamar meyasa ta ɗaure shi? Gaskiya bai cancanci irin wannan hukuncin daga garetaba, duk da su ba musulmai bane, a irin renon da ta yi mashi na rashin imani ma duk ya danne ya yi mata biyayya a matsayinta na mahaifiyarsa, abin da mamaki gaskiya, ita kanta ta jinjina mashi sosai, duk yadda ya kai ga kaunar Pretty kuma yana da damar da a lokacin zai iya kwace kansa ya gudu ya je nemanta ɗin, amma bai yi hakan ba, ya daure ya bi mammar tasa dan baya son zuwa ko'ina ba tare da izininta ba. Tuna hakan yasa ta fara tunanin bata kyauta mashi ba, tsawon shekaru yana bin umarninta bai taɓa saɓawa ba, duk abin da ta ce shi yake yi, yanzu ya nuna abin da yake so meyasa ba zata bi ra'ayinsa ba? Ai a yanzu ya kawo karfi, ko ya buƙaci soyayyar mace shi ma ai bai yi laifi ba.

Ɗaugo shi ta yi ta zaunar, ya kasa iya zama sai langwaɓewa yake yi yana ƙoƙarin sulalewa ya kwanta against, dan bashi da karfi ko na miskala zarratin. Cikin azama ta jinginasa da jikin bangon dutsen, murya a sanyaye ta fara ƙoƙarin rarrashinsa, dan tasan yana jinta, sai dai bata san cewa baya cikin hayyacinsa ba, kunnuwansa dai suna jin komai.

Ta yi magana mai ɗan tsawo ko motsawa daga in da yake bai yi ba bare a sa ran ya ji abin da ta ce. Ganin hakan yasa ta ɗauko tea mai zafi na green tea leaf ta fara ƙoƙarin ɗura mashi, dan tasan yunwa ce ta yi mashi over.

Wajen ɗura mashi sai da suka kusa kokawa, dan kuwa baya cikin hayyacinsa, yana jin abu mai zafi a bakinsa ya fara ƙoƙarin furzarwa ya kwaci kansa, bashi da karfi ko kaɗan, hakan yasa Mammar ta danne shi ta fara ɗura mashi da gasken gaske kamar yaro, dan dole ya fara haɗiyewa ba dan ya so ba, ta toshe mashi hanci ne kungakuwa dole ya haɗiye.

Sai dai ko da ta samu ya sha ba dayawa ba tana cire cup É—in ya fara tikar amai kamar zai amayar da Æ´aÆ´an hanjinsa, bata wani damu da hakan ba, dan tasan fin hakan ma zai aikata, ai ya ji yunwa over.

Basket ɗin magungunanta na gargajiya ta ɗauko, cikin zafi jini ta fara haɗa mashi magani babu wasa, jikinta har wani irin tsuma yake yi. Haka ta rinƙa ɗura mashi haɗe haɗen nata babu kama hannun yaro, yanzu dai burinta ta ga ya warke ya koma kamar da.

In short sai da ta ɗauki kwanaki uku tana ta faman jinyarsa, ta wahala shi ma ya wahala, banda tarin danasani babu wani abin da yake cikin ranta, duk ta shiga damuwa na wuce misali, da kyar da suɗin goshi ta iya samu ta shawo kan matsalar tasa ya dawo daidai. Sai dai kuma ko da ya dawo dai'dai ɗin baya magana, dama can kun san ba yawan magana ne da shi ba, yanzu da ya yi ciwon sai abin ya kara tsananta, abinci ma a baki take bashi, yana karɓa ya ci sai dai baya ce mata ko uppan, abin da yasa yake karɓar abincin ma dan ya ga tashiga damuwa ne sosai, har rama ta yi sosai, yana kaunar mammar tasa sosai, kuma yana yi mata biyayya sosai da sosai, son da yake yi mata ya kai ya iya sadaukar da komai nasa dan ita, hakan yasa ya hakura yake ƙoƙarin cire duk wani tunanin su Pretty a ransa, dan Mamma ita ce duniyarsa, ita ce komai nasa, tun bai san kansa ba take kula da shi fiye da kanta, komai wuyar da zai sha ya gwammaci ya tabbata cikin wannan wuya amma bai saɓa maganarta ko ɗaya ba, ba zai gaji da yi mata biyayya ba, badan ta kula da shi ta rainesa ba yaushe zai girma har ya san da su Pretty a duniya? Da ta yi watsi da rayuwarsa ya makomarsa kenan? So Mamma ita ce gaba da komai kafin sauran abubuwa su biyo baya.

Allah sarki, da ni da ku dukka mun san mantawa da su Pretty a rayuwarsa ba abu bane mai yiwuwa, sun zame mashi wani ɓangare na rayuwarsa, zai azabtar da zuciyarsa ne kawai a banza, amma mantawa da su ba abu bane da zai yiwu mashi.

Ganin ya kara samun sauki sosai ne yasa ita ma Mamma ta samu sukuni har ta É—an fara mai da jikinta. Sai dai rashin maganar nan tasa ya dameta sosai, ba um bare uh uhm, ko ta yi mashi magana sai dai ya É—aga mata gera ko kai, abin yana damunta sosai da sosai.

Kamar kullum zaune yake a saman gadonsa ya haÉ—a kai da gwiwa yana aikin tunani, ba tunanin kowa yake yi ba face na su Pretty and mahaifinsa, yana son sanin wanenen babansa? Wannan itace burinsa a yanzu.

Har Mamma ta shigo cikin ɗakin bai ji shigowarta ba yana can yana tunani, kafin ta shigo kuma sai da ta tsaya almost 10 mins a bakin kofa tana kallonsa, ganin bashi da niyar ɗago kai ya kalleta ne yasa ta ƙariso ciki.

A bakin bed ɗin ta zauna tare da kai hannu ta ɗan shafi wannan tulin uban gashin kan nasa. Yana jinta amma bai ɗago kai ba, dan kwata kwata baya son motsawa komai ƙanƙantarta daga in da yake, a yadda yake zaunen nan ba ƙaramin daɗin zaman ya ji ba.

"Kamran lafiya kake kuwa?" Ta faÉ—a a sanyaye.
Chapter 33 · 0% Book details