Sashe 51
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba musu ta karɓa ta sha sosai, gabaɗaya a rikice take, sai zare idanu take yi kamar wadda taga wani abin da babu irinsa a duniya, ko da yake a wajensu babu irin Jaish a duniya, dan basu taɓa ganin mai kyau irinsa ba, dole su ɗaukesa kamar babu irinsa a duniya........ Ni kam na ce dan ma ba kuga Guyson nawa and Auta Zunaira ba, ai da kun mace saboda kyau.
Sai bayan ta samu nutsuwa ne Bappan ya ce. "Me ya faru Mahnoor?".
A matuƙar tsorace take ta amsa mashi da. "Wannan aljanin da ka kawo ne ya fito daga ɗakinka". Yadda ta yi maganar a ruɗe take.
Ai bata ƙarisa maganar ba ya yi saurin wucewa yana ce masu. "Ku jirani ina zuwa, ai abin da muketa tsumayi kenan tun jiya, farkawarsa kawai muke fata dama".
Kallon Mahreen dake ta sabgar gabanta hankalinta baya a kansu ta yi tare da cewa. "Ke gaji aljaninki ya tashi har ya fito waje". Ta yi maganar tsoro na kara bayyana a saman face dinta. Ai kuwa ita kam Mahreen tsalle ta buga tare da miƙewa tsaye ta ce. "Dan Allah? Wayyo Allah bari na yi sauri na je na gansa". Tana kai karshen maganar ta watsa a guje sai hanyar gida kamar ba yanzu bappa ya ce su jira shi yana zuwa ba.
Kafin Mahnoor ta buÉ—e baki ta dakatar da ita tuni ta wuce kamar wata walkiya, fiw ta wuce kamar iska tsabar iya gudu, daga karshe ma ta riga Bappan nasu isa gidan, a hanya ta wuce shi, kamar bata gansa ba, shi kuwa da ya ganta kafin ya buÉ—e baki ya kirata tuni ta wucewa ganinsa, yadda kuka san iska haka take da gudu.
A dubu sittin ta shiga gidan babu ko sallama. Yana tsaye a in da Mahnoor ta barosa, yana dafe da bango da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya ya dafe kansa yana kallon ƙasa ya sunkuyar da kansa.
Kai tsaye gabansa ta nufa a kuje, da kyar ma ta iya taka birki ta kama kanta bata afka jikinsa ba, tsabar yadda ta shigo gidan a guje, gudu ta yi da iya powerta dukka.
Sarai ya ji motsinta kuma ya ji gudun da ta yi har ya zamana da kyar ta kama birki a gabansa, amma yadda kuka san babu shi a wajen, sam bai motsa ba bare a yi tunanin ya ji shigowar mutum, da ni da ku dai mun san halin kayanmu daman, mun san ya yake, su Mahreen ne baki a sanin halinsa.
"Yauwa ginnaji amin a fini ko? (yauwa alajinmu ka tashi ko)?". Yadda ta yi maganar tana haki zaka fahimci ta saba dallawa a guje, ma'ana ta saba yin gudu, dan bata wani wahala ba, ita kuwa Mahnoor wannan gudun da ta yi sai wani irin haki take yi kamar numfashinta ba zai dai'dai tu ba, amma Mahreen ai shar, wannan da za'a saka gasar gudu a kauye na tabbata sai ta fi kowa, ita zata zo na É—aya, gata Æ´ar siririya, haba my people's karku ga yadda take pella kafafu idan ta arce a gujen.
Sarai ya ji anyi magana, amma bai san da wani yare bane, dan haka bai gane me aka faɗa ba, kuma dai yaki ɗago kai ya kalli wace aljana ce take a gabansa, dan ma Allah ya rufa mashi asiri yau kwalliya kaɗan ta ɗan yi kafin su tafi karatu da suka yi wanka, sai dai ta cika powder nan nata da ta saba a fuska, amma ba'a lapka janbaki sosai ba, dan Mahnoor ta ce mata idan tasa kaɗan ta fi kyau, sannan yau bata ɓata fuskar da bakin kwalli sosai ba.
Ganin bai amsa mata bane yasa ta ɗago da kallonta a kansa, sai a lokacin ta zaro idanun tana kallon tsawonsa da ya fi bappanta, kun san tun jiya a kwance yake, sai yanzu ta gansa da kyau. Ai a ɗari ta ɗaga kanta sama ta kai kallonta saman fuskarsa. Da yake kan nasa tana duƙe ƙasa sai bata wani iya tantance face ɗinsa da kyau sosai ba, amma dai taga kumatunsa da yake jajir saboda mulmula mashi da ta rinƙa yi.
Saboda rashin tsoro irin na yarinyar nan hannu tasa ta ɗan taɓa plat tummynsa, dan a iya nan taawonta ya tsaya, ba zata iya taɓa shi a sama da haka ba. Taɓa shi ta yi tare da cewa. "An kam a wala volwa na? (Kai kam baka magana ne?)".
Daga hannun nata da ta taɓa shi ya fara bi da kallo kafin ya kai kallonsa saman face ɗinta. A lokacin ita ma tana kallon face ɗin nasa da kyau, ai kuwa suka yi four eyes. Ɗan zaro idanu ya yi da ganin face nata da ya yi, ba komai yasa ya zaro idanu ba face kwalliyar dake saman face ɗinta.
Ai kuwa yana zaro idanun nasa da suke ja ta sakesa tare da kurma ihu ta yi baya baya ta faɗi ƙasa, dan kuwa ya bata tsoro, ga idanu manya manya, sannan gasu jajir kamar jini, duk yadda aka yi akwai abin da ya samu idanunsa wlh, dole akwai abin da aka sanya mashi a cikinsu ko kuma ya sanyawa kansa, dan sun yi wani irin ja mai ban tsoro, duk wanda ya kalli cikin idanun nasa sai ya tsorata sosai. Dani da ku dai mun san idanunsa farare ne.
Tana faɗuwa ƙasa numfashinta ya ɗauke diff, shi kuwa yana ganinta ta zube ƙasa bai taimaka mata ba, sai ma hannunsa da ya cire daga saman goshinsa ya dafe cikinsa da shi, dan wani irin murɗa mashi da cikin nasa ya yi da karfi, wani irin zafi ya ji shiyasa ya dafeta. Wani irin kwaɓe fuska ya yi saboda kyama, shi Mahreen kyama sosai ta bashi, a ganinsa ta yi datti over, bai san nan ta sha wankarta ba, kayan nata ne kawai suke koɗe kamar masu datti, amma ba wani datti, dan suna da tsabta sosai.
Shi kuwa mugun kyama ta bashi, barema gidan nasu da ya kallah, dama tun da ya buɗe idanu ya kalli in da yake cikinsa ta fara murɗa mashi, wannan dalilin yasa ya fito waje ko zai samu sassauci. Ai kuwa yana fitowa ya ci karo da su bukka gidan ƙasa nan take kansa ya fara sara mashi, hakan yasa ya dafe kan nasa ga cikinsa na juyawa.
Wani irin amai ne ta kwace mashi. Da kyar ya iya jan kafafunsa ya matsa daga bakin kofar, a tsakar gidan ya dakata ya fara tikar amai mai sautin gaske, kamar zai amayar da Æ´aÆ´an hanjinsa.
A wannan hali bappa ya shigo ya samesa, ga Mahreen a sume kwance a ƙasa. Ganin yana ta amai yana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa dan jikinsa babu kuzari ko kaɗan ne yasa bappa bai bi ta kan Mahreen ba ya yi kansa yana yi mashi sannu da harshen fillanci.
Hannu yasa ya ɗan riƙosa dan kada ya faɗi, sai layi yake yi kamar wanda ya sha wani abin na maye, a hakan ma kuma wai ya yi ta maza ya rike kansa da ɗan sauran karfin da ya rage mashi. Bawan Allah sai Allah ne kaɗai yasan kwanansa nawa rabonsa da abinci........... Tab akwai cakwakiya, anya Jaish zai iya cin abincinsu kuwa? Anya zai iya yarda ya ƙara minti ɗaya a cikin gidan kuwa? Akwai matsala, already kun san shi da muguwar kyankyani dama, ga shegen izza da suna isa, akwai dai matsala babba!!.
A hanzarce bappa ya riƙesa, a lokacin amai ɗin yake tiƙawa da gasken gaske, bai ma san an riƙesa ba, duk in ya tuna kwalliyar kan fuskar yarinyar da ya kallah yanzu wato Mahreen sai cikinsa ta sake murɗa mashi, aman nasa ma banda zallar ruwa dake fita kaɗan kaɗan babu komai, dan babu komai a cikinsa, bai ci abinci ba, sai uban kakari da karfi da yake yi ba wani aman kirki.
Ya ɗan jima a sunkuye a wajen kafin ya fara sassauta mashi, wlh ba karya ya wahala matuƙa, dan wannan kakari da yake yi duk ta ƙara nukurkushe mashi ɗan karfin da ya rage mashi, ba dan bappa da yake rike da shi ba da ya jima da zubewa ƙasa, amma Allah yasa bappa ya riƙesa, ya wahala idanunsa sun ƙara yin jajir kamar wuta, wasu siraran jijiyo ne suka fito mashi a forehead ɗinsa, ga wani uban zufar wahala dake tsastsafo mashi a face ɗinsa, harta zara zaran eyelashes ɗinsa sun jiƙe da gumin da ta wanke mashi face ɗin nasa, red lips ɗinsa sai kerma suke yi alamar yana jin sanyi kuma babu kuzari a tattare da shi, arab hairn nan nasa ya watse caka caka kamar bai taɓa sanin menene gyara ba.
Lokacin da ya ɗan dawo dai'dai aman ya tsaya, a hankali ya ɗago idanunsa da suka yi mashi nauyin ɗagawa, kai kallonsa ya yi ta gefen da bappa yake dan yaga waye ya riƙesa?.
A dai'dai lokacin kuma bappan ya ce. "Allah sarki a yari bone sosai, sannu, joɗu bari mi wandina ma diyam a lota hundukoma be ɓanduma, (Allah sarki ka sha wahala sosai, sannu, ka zauna bari na kawo maka ruwa ka wanke jikinka da bakinka..........."
Ai bai ƙarisa maganar ba ya dakata sakamakon turesa da Jaish ɗin ya yi gefe guda har sai da ya faɗi ƙasa. Tattare dukkan sauran karfi da suka rage mashi ya yi ya ture bappan tare da zubewa ƙasa a saman gwiwowinsa ya cigaba da yin kakarin amansa, sai dai aman taki fitowa, da alama ruwan dake cikin nasa ne ya ƙara.
Ba komai yasa ya ture bappa ba kuma face kyama, a cewarsa bappa na wari, sannan ya ji kyamar kayan jikinsa......... Ni kam nace zan ga wannan cakwakiyar ya zata ƙare, yo idan bappa yana maka wari zanga mai yi maka magani, kai in short ma zan ga wanda zai taimaka maka ka tashi daga wajen da kake yin aman ma kafin aje ga batun magani, gaskiya da babbar matsala!!!.